Showing 9001 words to 12000 words out of 46966 words

Chapter 4 - Mafiya Book Compelet By Mrs Sadauki


Yar uwata inkinyadda d Allah kibamu yardarki bbu cuta babu cutarwa b ha'inci zaa mki komi
fiyeda yenda ke zakiyi 09111648884

Call:09111648884
[23/11 à 07:44] MRS SADAUKI : *MAFIYA*☠️


LoVe aNd HoRrOr StOrY☠️

*Mallakar:* Chamsiya Laouali Rabo
(MRS SADAUKI✍️)

*Lambar waya:* +22795045822

*FIRST CLASS WRITER ASSOCIATIONS☀️*
Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation.
_____________________


08

Tun da uwar da ta haife ni ban taɓa ganin inda mutum ɗan Adam yayi aman kuɗi ba sai
yanzu,tamkar wasu ruwa haka takardun kuɗin ke fito wa daga bakin kowanne members har sai
da suka kusan cika ƙaton capet ɗin.Ni kuwa banda kyarma babu abin da jikina ke yi,a nan take
a inda nake tsaye kuma na ƙaryata fassarar da na yi wa sunan MAFIYA daga “cikar muradi ”
zuwa “tsafi da shan jini”.



Ashe ban kai maƙura wurin mamakina ba sai da na ga kuɗin na ware kansu suna yin
dunƙule-dunƙule na 100k ,kamar ƙyaftawar ido suka jeri rasss a hakan kuma kowace takardar
kuɗi ta san wanda ya amayar da ita .


“ HAROON wannan ɗin duk kuɗinka ne!” Oga ya faɗa yana murmushi haɗi da bubuga gefen
kafaɗata.
Na ce “ duk me zan yi da uban kuɗin nan?”

Sai duk suka hau yi min dariya,can suka tsagaita Oga ya ce “ ka manta akwai aiki jajur a
gabanka? Ko da kanka za ka dinga bin maƙabartu kana ciro likafanin?”

“Wane irin likafani kuma?” na tambaya cikin tsoro.

Oga ya haɗe rai ya ce “ wanda zai taimaka ma ka yi tsawon rai nan gaba,ko ka manta ne?”

Murya na rawa na ce “ ban manta ba amma Oga ai sai nan da shekara biyar ko?”

“Bayan wannan akwai wasu sharuɗan! Kowanne ƙarshen wata za ka samo mana jinin period na
budurwa,kar ka tambaye ni ta yaya .Ka fara tunanin hanyar da za ka bi ka kawo na wannan
watan don yau muna ashirin da uku ga wata”


Wasu irin yawu na haɗiye masu mugun ɗaci,ido kawai na tsura musu da alamu ko a jikinsu sai
harakar gabansu suke suna saka min uban tulin kuɗin a jakakuna.




“Amma Oga ina zan ajiye kuɗin nan? ”
“Bisa kaina”
“Ka yi haƙuri in na je da su gida Ammy za ta zarge ni ”


Ran Oga ya ƙara ɓace wa ya ce “ HAROON ka fita idona,kana yawan matsa min da zancen
Ammynka in ba ka yi sa'a ba kai ne za ka yi silar mutuwarta ”


Gabana ya bada rasss jin wata lukutar masifa,amma na kawar da tsoron gefe na ce “ wannan
shine babban kuskuren da za ka yi kuwa a duniya shine taɓa Ammyna,duk duniyar nan banda
tamkar ta.Kar ka manta silar ta ne a yau nake cikin wannan ƙazamar rayuwar,Ammyna ita ce
komai nawa in babu ita ban ma ga tsiyar da zan yi a duniya ba” duk wurin tsit yayi suna kallona
shaye da mamaki,na sani sarai yadda duk ake tsoron Oga ni ma ina tsoronsa amma ba zan juri
a taɓa Ammyna ba ko kaɗan ai gwara ya yanki fatar jikina ya fi yi min sauƙi.



Ban taɓa ganin Oga cikin fushi irin haka ba sai yanzu,tako ɗaya yayi ya isa inda nake idonsa
sun kaɗa sun yi ja sosai.

“Ōgāfōr̃!” furucinsa kusan tsinke igiyar da ke saita mini numfashi yayi,na riƙe hannunsa tare da
roƙonsa “ please Oga kar ka hukunta ni ta hanyar kai ni ɓoyayyar duniya” sai dai da alamu
roƙon nawa a banza ne wai an tsikari kakkausa.Tuni ƙasa ta soma darewa ginin cikin ƙasa ya
bayyana,idona na zubar da hawaye na tashi cikin iska kafin na yi nitso cikin dogon ramen a

haka ƙasa ta rufe da ni ruf sai gani tsaye a gaban baƙar ƙofar nan a karo na biyu.


Yau ɗin ma Dōr̃anī ne suka buɗe min ƙofar tare da yi mini iso a ciki,sai dai fa wata jahar suka
kai ni ba nan fara isa ba.


“Wannan karon kuma wane laifin ka yi mai yawa har Oga ya ce a kai ka sashen bauta ?” ya
tambaye ni.

Ƙin basa amsa na yi sai ma tunanin yadda zan yi na fita na soma,“ fatan dai ba wani sirrin
ƙungiyar ka fitar ba?”

“Ban fa iya surutun nan yau ka bar ni da abin da ya sha min kai” na faɗa cikin masifa,daidai nan
muka iso wata duniyar mai cike da abubuwan ban mamaki mutum da jikin maciji,ko kifi,ko
doki,mage mai ƙafa ta fi ɗari,ko kuma mage da kan mutum.Maciji mai magana,kare da shan
sigari.

“Ina ne kuma nan? Me zan yi a nan?” na tambaya a firgice,banza suka yi da ni sai tafiya suke
ina take musu baya har muka isa gun wasu tsofi.

“Ina ka samo mana ɗan saurayi kuma?” ɗayar tsohuwar ta faɗa tana wani kashe mini ido,yayin
da wasu biyun suka taso suka soma shafa ta da sauri na soma ture su ina son guduwa.


Dōr̃anī ya ce “ ladabtar da shi za ku yi,shi ɗin yana da muhimmanci ga uwa MAFIYA don haka
kar ku taɓa lafiyarsa”

Yana gama faɗar haka duk suka ɓata rai waɗanda ma suka yi min ƙawanya sun gusa daga
jikina,su ma Dōr̃ānī tafiyarsu suka yi.

Wacce ta fi su tsufa duka ita ce ta miƙe tsaye ta ce “ ɗan samari biyo bayana ”
Dole dangin naƙi haka na take mata baya zuwa wani sashe mai cike da yana don ta cikinta ma
muke bi muna wucewa,mun ɗan yi tafiya sosai kafin ta ja ta tsaya.


“Ruhinka nada ƙarfi sosai ta yadda har yanzu Octoba ya kasa karɓe shi duka duk da kuwa ka
sayar da shi,uhum! Amma me yasa kake fusata shi haka? Ka san mene ne za a yi maka a nan
ɗin?” tsohuwar ta tambaye ni.

“Mene ne zan yi a nan ɗin?” na tambaye ta tare da share duk sauran zancen da ta yi.

“Matso kusa ka gani” ta faɗa ,na ɗaga ƙafata na isa gare ta abun mamaki sai na hango
duniyarmu ta Bil'adama.Wasu abubuwa ta dinga furta wa nan gidaje da ababen hawa suka
dinga wuce wa kamar mai yin tariya har ta isa ga asibitin da aka shimfiɗe ni.


Wani irina na gani zaune kan gado Ammy na ɓare ayaba tana basa yana sha,gefe guda kuma
direbana ne ya ƙura masa ido yana kallo.


“Ko ka san me yasa waccan mutumin yake kallon mai kama da kai?” tsohuwar ta tambaye ni.

“Eh saboda ba haka nake zama ba,sannan in zan ci abu da hannun dama nake riƙe shi ba hagu
ba.Ban cika son mutum ya ƙure ni da ido yana kallo ba” ina gama faɗa sai na ga mai kama da
ni ɗin ya mayar da ayabar a hannun dama yana cewa “ Ammy har yanzu hannun ga nawa ciwo
yake,kai kuma lafiya ka tsare ni kana kallo? Fita ka ban wuri”
Direbana ya miƙe da sauri da ya kai bakin ƙofa sai da ya sake waiwaya wa,nan ɗin ma sai da ta
tambaye ni “ me yasa ya waiwaya?”

“Saboda yi wa mutum tsawa da hantara ba tabi'ata ba ce” na bata amsa kai tsaye.

“To da zarar ka koma duniyarku ya zama dole ka kashe direban can”

Sai da na dafe ƙirji na ce “ saboda me?”
“Amsar na wurinsa” tana gama faɗa ta wani kamo hannuna muka yi suka tare da sauka can
doron duniya mun iso bakin kwalta na ja na tsaya,ta wani ja hannuna tana mai cewa “ kai gara
iya ruhinka ne kawai a nan gangar jikinka na can sama”

Haka motoci ke ratsawa ta cikinmu ba tare da mun kauce musu ba,wani gidan cin abinci muka
je.Da murna take cewa “ tsawon lokaci kenan da ban shigo duniya ba ,ina son abincin nan ya
kamata in nemi gangar jiki na shiga ta yadda zan ji daɗin abinci”
“Ta ya kenan?” ba ta bani amsa ba ta je jikin wata budurwa wacce ke tsaye jikin mota ita da
saurayinta,a gaban idona tsohuwar ta shige jikin yarinyar.Ta ja hannun saurayin suka zauna ta
yi odar kaji da lemun kwalba,“ yau sai na baka mamaki zan cinye dukkan kaji biyun nan”
budurwa ta furta wanda a baɗini esprit ɗin tsohuwar nan ne.Aka kawo kaji biyu ta cinye su
tasss ta sha lemun kwalba,tana gamawa ta fice daga jikin nata ta zo daidai inda nake tsaye
tana dariya “ na tsani soyayya,yau na yi silar raba su” sai kuma ta ja ni muka tashi cikin iska
muka koma can inda muka fito,gangar jikina na gani a tsaye tana zaman jirana sai dai ban san
ya zan yi na koma ciki ba........

My book is only 500 via 2670215530
ZULFAU YAHAYA
Ecobank,DM +22795045822 .Saura page biyu na gama free page kafin nan zan yi discount ga
mai so ya biya 400 sai ya tura min shaidar biya ta WhatsApp.



Talla! Talla! Talla!!!


DULLAHZ CAKES AND MORE


Ina jamaata mutanen kirki ji'bin arziki? Yan kurna, rijiyan lemo,bacirawa,da duk abunda y jibanci
Nan Ina mutanena mutanen Kano kanawan dabo mutanen kirki mutanen da sukasan Kansu,

Ina mata yangayu wadanda basaso gayu y wucesu,biki gareki? Suna? Ko kwarya kwaryan
liyafa qawata? Kinji labarinmu ko yenzu batun ke tafe gareki,

Munayin cake me dankaren dadi cake hadadde a musulmin farashi,akway cupcakes,samosa,
spring rolls,Muna gashin kaji da kayan kwalam d maqulashe kala kala,09111648884

Yayata Muna girkin biki,suna,ko tarbon baki komi kikeso,inma grkine bakijinyi Dan Allah ki kira
dullarz zatamaki shi nantake a gyaremaki cikin warmers me delivery ykaimaki,09111648884

Yar uwata inkinyadda d Allah kibamu yardarki bbu cuta babu cutarwa b ha'inci zaa mki komi
fiyeda yenda ke zakiyi 09111648884

Call:09111648884
[25/11 à 13:14] MRS SADAUKI : *MAFIYA*☠️


LoVe aNd HoRrOr StOrY☠️

*Mallakar:* Chamsiya Laouali Rabo
(MRS SADAUKI✍️)

*Lambar waya:* +22795045822

*FIRST CLASS WRITER ASSOCIATIONS☀️*
Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation.
_____________________

09

Wannan tsohuwar ce ta nuna min yadda matsafa ke yi wurin fitar da ruhinsu daga cikin gangar
jiki da kuma yadda ake yi a koma.
Cike da jin daɗi na isa inda gangar jikina take a tsaye kamar saƙaƙo,yadda ta koyar da ni ɗin da
shi na yi amfani na koma ciki.Daga nan sabbin abubuwa ta soma koya min,irin yadda zaka juya
tunanin mutum,kashe mutum ba tare da kaca masa wuƙa ko bindiga ba,yadda za ka cutar da
wani normal mutum ba tare da shi kansa ya san an cuce shi ba.
Daga wannan kuma sai ta soma yi min wani bayani da ya tafi da ruhina.

“ HAROON ita duniyar MAFIYA da kake ganinta kowanne members yana samun power ne daga
aikin da yake yi,wato iya yawan sacrifice iya adadin yadda ƙarfin ikonka zai ƙaru.Samun power
ƙwaya ɗaya ya fi a baka miliyan ɗari,saboda su kuɗin za su ƙare ita kuwa power zaka iya
sarrafa ta sosai ta yadda za ka samu dubban abubuwa marar ƙirguwa.Ka ga ko ita wannan
wacce kake so ko? To tabbas kana iya yin galaba a kanta muddin dai ka samu power
dayawa.Bari na nuna maka wani sirri na musamman da ba kowa ya san da shi ba” sai kuma ta
miƙe ta ɗauko wani tandun kwalli ta miƙo min.Na karɓa ina dubanta,ta ce “ shafa shi da idonka
sai ka sanar da ni me ka gani”

Ban musa ba sai kawai na bi umarninta na shafa kwallin ga dukkan idanuwana,sanyi ne ya
ratsa su kamar na ƙanƙara wannan ya sa na ɗan lumshe su.Ina buɗe su kuma na yi tozali da
tsohuwar matar nan ta zama tamkar lagwami duk jikinta tattakaken ƙwarangwal ne babu
kyawun gani.

Ta ce “ wannan kwallin yana taimakawa wurin gane taƙamaimai asalin mutum da kuma niyyarsa
a kanka,sannan zai ƙara ma ƙwarjina ta yadda babu wanda ya isa ya kalle ka cikin ido ciki
kuwa har da Ammynka”sai ta yi shiru na wani lokaci kafin ta ɗora da “abubuwan da suka fi kawo
maki a Mafiya sune mata da ƙananan yara,sai kuma mahaukata.Kowanna daga cikinsu da tasa
rawar da yake takawa,in kana son a kowace irin jarabawa ko sabga taka ka yi nasara to da
buƙatar ka yi sacrifice na ƙaramin yaro da bai balaga ba...” da sauri na katse ta da tambayar “
amma saboda me?”

“Saboda ƙwaƙwalwa yaro a wanke take babu komai cikinta na tunanin wata matsala,sannan
zuciyarsa ma haka fara ce fesss babu baƙin cikin kowa .Bakinsa kuwa gaskiya ce tsagwaron
ta,irin haka ne zaka samu wasu mutanen da daɗin baki in sun yi magana sai ka ji tasu ta fi ta
kowa”

“Su kuma mata me yasa ake son sadaukar da su?” na tambaya.

Ta yi wani murmushi kafin ta ce “ akwai wanda ya fi mace wuyar sha'ani a duniya? Ita fa kamar
sawun keke take baka gane gabanta ballantana bayanta ,wannan ya saka Mafiya ke da buƙatar
mata.A sassan jikin mace akwai waɗanda in aka yi tsafi da su aikin ya fi kyau ,daga ciki akwai
al'aurarta da kuma mamanta,abu na ƙarshe kuma shine ana yi mata wankan ƙaddamawar sai
namiji yayi amfani da ita irin haka ne ke janyo farin jini da dukiya mai tarin yawa”



Na jinjina kai na ce “ su kuma mahaukata fa wane dalili ne?”

Kai tsaye ta bani amsa da “ a gaskiya sabbin members na MAFIYA waɗanda suke son yin kuɗi
sun fi amfani da mahaukata,dalili kuwa shine shi hauka launin cuta ce da ke zuwa daga
ƙwaƙwalwa wasu ta jinnu ce wasu kuma haka aka haife su da ita,to ita kanta wannan launin
cutar tana da matuƙar muhimmanci a mafiya tana sa member ya ji gamsuwa fiye da in da
mutum mai hankali ne ka kusanta”


Shiru na yi ina nazari,abin da na ƙara fahimta game da Mafiya wani rikitacen al'amari ne marar
kyau.Duk abu na ƙwarai a wurin su ba mai kyau na ne sai gurɓatace,“ to amma yin mu'amala da
mace yayin jinin al'ada fa me yake ƙarawa?” na jefo mata tambayar.


“Yin haka tamkar rufe ƙofofin taurarin ita macen ne,sannan duk wasu lamurranta za su iya
kwaɓe mata yayin da shi kuma namijin rayuwarsa ta ɓoyayyar duniyar za ta yalwanta ”

Kasaƙe na yi ina zancen zuci ‘ kenan so ake duk na disashe taurarin Malama Zainab?’

“Bari ka ji HAROON ,babu abin da sheɗanu suka fi ƙauna irin warin jini musamman na al'ada
yana da matuƙar muhimmanci a duniyarmu”

“Wane irin sheɗanu kuma?” na tambaya kamar wani gara.
Sai da ta sheƙe da dariya kafin ta jefo min tambayar ta saka zuciyata tsananta bugi,“ kai a
tunaninka kai mutum ne? Bani amsa kai mutum ne?” shiru na yi na kasa cewa komai.

Ta ci gaba da cewa “ ka sani tun ranar da ka kwashe kayanka a gaban Manzo ka fita daga
sawun mutane,kai sheɗani ne HAROON !” ta faɗa cikin wani sauti wanda ya saka yanar da ke
yaɓe ta ko ina ta soma kaɗawa kamar ana iska.




“ Tashi ka bani wuri” ta faɗa cikin fushi,da sauri na ce “ na fita na je ina? Ki yi haƙuri amma ni

ban ga abin ɓacin rai ba” ina gama rufe baki ta ja hannuna ta matso ni kusa a nan take
madubina da ke can gida ya bayyana a nan.


“Wannan ita ce siffar mutum? ?” ta tambaye ni tana nuna ƙwarangwal ɗin da ke cikin madubi
,na girgiza kai na ce “ a'a ba mutum ba ne fatalwa ce”

Madubin ne ya ɓace ita kuwa sai ce min ta yi “ ai HAROON gwara fatalwa da kai,saboda kai
sheɗani ne na musamman.Wai ma mene ne dalilin Oga na zaɓar ka alhalin ga dukkan alamu
baka san muƙamin da ke jiran ka ba?”


“Muƙami?” na maimaita.

Dōr̃ānī ne ya shigo yana mai cewa “ lokacin komawar ka yayi” haka na bi bayansa muka fita.

Sai da ya kai ni wani sashe aka yi min wanka da wasu korayen ruwa sannan na ci na sha kafin
yayi min rakiya zuwa bakin ƙofa.Yau ɗin ma kamar kullum haka ƙasa ta dare na fito sai dai fa
wani uban canji na ji,jin kaina nake yana hayaƙi yayin da kuma zuciyata nake jin tamkar an yi
min musanyar ta,sauran tausayin da ya rage min ya kau a yadda nake ji ko wuyan jinjiri zan iya
murɗe wa ya mutu.Ban gama mamakin kaina ba sai da na ga sauran members sun miƙe suna
gaishe ni cike da girmamawa,yayin da shi kuma Oga yayi kicin-kicin da fuska haɗi da nuna min
wata kujera da aka ƙawata ta da ado.A yau sai na yi wa Oga dubin uba mahaifi wanda kuma
ban san dalilin yin haka ba,zuwa na yi na zauna nan ɗin ma wani sabon canji na ji amma dai na
yi shiru ina ta nazarin komai daki-daki.


“Daga rana irin ta yau na wakilta HAROON matsayin mataimakina wato shugabanku,in ba ni ga
wuri shi zai ɗaukar matsayina sannan duk wani hukuncin ƙungiya da za a zarta ko ya shige
muku duhu shine zai bada umarnin ƙarshe” Oga na gama faɗa suka shiga taɓa min kafin ya
sallame su wurin ya zamana sai mu biyu kawai.

“Wannan ɗin duk na mene ne Oga?” na samu dakyar na tambaya.
Ya bani amsa da “ tun da aka kafa ƙungiyar nan kai ne na farko da ke iya maida min martani,
wannan yasa na baka wannan muƙamin kana iya tafiya” ban sake ce masa komai ba

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login