Showing 15001 words to 18000 words out of 46966 words

Chapter 6 - Mafiya Book Compelet By Mrs Sadauki

zubo masa.
Daga inda nake zaune na baiwa ƙofar umarnin rufewa,da sauri ita matar Illiyan ta juya tana
kallon yadda key ke murɗa kansa handle kuma na motsi.Tana juyowa ta gan ni a zaune kan
table gabanta har ƙafafuwanmu na gugar na juna,cikin ido na dube ta na ce “ ki cire hijabinki”
Idonta ya kawo ruwa amma na san tabbas ba za ta iya musa min ba,haka ta cire shi nan na yi

arba da siffarta mai ɗaukar hankali.Rabon da na yi mu'amala da mace har na manta, wannan
yasa jikina ya ɗau rawa har ban san lokacin da na kai hannuna na zuge zip ɗin rigarta ba.Nan
na yi arba da ainahin surarta,hawayenta da suke ɗiga sam ba su dame ni ba haka na yi mata
sintiri ina shafar dukkan sassan jikinta.Daf da zan cimma burina na ƙarshe na ji sautin muryarta
mai kamar tafasasshen ruwa,cak na tsaya ina sauraren amon muryarta wanda kuka ya gurɓata
shi “ ka sani ni ma mace ce mai daraja kamar uwar da ta haife ka! Yadda baka son wani ya keta
mutumcinta haka ni ma yarona da ke can waje yana kuka bai son a keta nawa” da sauri na yi
baya ina dafe zuciyata ina kallonta ta soma mayar da kayan jikinta.Daidai nan na gama page na
kyauta mai so sai ya biya 500 via 2670215530
ZULFAU YAHAYA
Ecobank sai ya turo da shaidar biya ta WhatsApp +22795045822 .Kawai ki tura in na zo zan
saka ki group,wacce ta san ba biya za ta yi ba ta yi wa girman Allah kar ki yi min magana.


Littafin MAFIYA labari ne ya cakuɗe da true life da kuma wanda na ƙirƙirar,sannan wannan duk
shimfida ce ba mu ma shiga cikin zallar labarin ba.



Talla! Talla! Talla!!!


DULLAHZ CAKES AND MORE


Ina jamaata mutanen kirki ji'bin arziki? Yan kurna, rijiyan lemo,bacirawa,da duk abunda y jibanci
Nan Ina mutanena mutanen Kano kanawan dabo mutanen kirki mutanen da sukasan Kansu,

Ina mata yangayu wadanda basaso gayu y wucesu,biki gareki? Suna? Ko kwarya kwaryan
liyafa qawata? Kinji labarinmu ko yenzu batun ke tafe gareki,

Munayin cake me dankaren dadi cake hadadde a musulmin farashi,akway cupcakes,samosa,
spring rolls,Muna gashin kaji da kayan kwalam d maqulashe kala kala,09111648884

Yayata Muna girkin biki,suna,ko tarbon baki komi kikeso,inma grkine bakijinyi Dan Allah ki kira
dullarz zatamaki shi nantake a gyaremaki cikin warmers me delivery ykaimaki,09111648884

Yar uwata inkinyadda d Allah kibamu yardarki bbu cuta babu cutarwa b ha'inci zaa mki komi
fiyeda yenda ke zakiyi 09111648884

Call:09111648884
[28/11 à 08:15] MRS SADAUKI : *MAFIYA*☠️

LoVe aNd HoRrOr StOrY☠️

*Mallakar:* Chamsiya Laouali Rabo
(MRS SADAUKI✍️)

*Lambar waya:* +22795045822

*FIRST CLASS WRITER ASSOCIATIONS☀️*
Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation.
_____________________


11


Tun da nake babu wata ƴa mace da na taɓa rabawa da kayanta kuma ban kusance ta ba sai
wannan.Har ta kai bakin ƙofa na dakatar da ita “ keee!” ta wani juyo a firgice jikinta na
rawa,idona na kafe ta da su ina son sanin ko tana ɗauke da wani sirri ne na daban amma ban
gansa ba.Na dafe goshina cike da takaici kafin na kwashi kayana na shige Toilet,gaban shower
na je na tsaya na buɗe shi duka ruwan na soma sauka a kaina tsohuwar rayuwata ta baya ta
fara zuwar min kamar wanda aka kunna wa video.


Wannan labari yana ɗaya daga cikin mafi ruɗani da na samu. Yana da gami da madubi. Ba wai
kawai kowane madubi ba, amma ɗaya daga cikin waɗannan abubuwan da ake ganin suna
ɗaukar wani abu fiye da kawai tunaninsu.

A ƴan shekarun da suka gabata, na ci karo da wata kasuwar kayan gargajiya a wani gari da
nake wucewa.Kasancewar ni ɗin direban babbar mota ne,ina son yawo a cikin waɗannan
wuraren koyaushe suna samun abubuwa masu ban sha'awa tare da labari. Ina zagawa wani
tsohon madubi ya kama idona tamkar mayen ƙarfe. Yana da ban sha'awa, tare da firam ɗin
katako da aka sassaƙa, an ƙawata shi da ƙira. Wani katon madubi ne, kusan girmansa kamar
ƙofa, ga fuska kamar ya ɗan dusashe da shekaru.

Dillalin kayan tarihi ya gaya mani cewa wannan madubin ya fito ne daga wani tsohon gidan da
aka yi watsi da shi kuma ya kasance a wurin shekaru da yawa, ba tare da wani ya so ya saya
ba. Ya ce wasu mutane in sun ga wannan madubin suna cewa “yana tattare da damuwa” ba
tare da sun iya bayyana dalilin da ya sa ba.

Tabbas, a matsayina na mai son abubuwan bazata da na ban mamaki sai na yanke shawarar
saya. Na kai shi gida da tunanin zai dace da duniyata.

Tun daga ranar farko da na rataye shi, na ji wani abu mai ban mamaki. A duk lokacin da na
wuce nakan ji kamar tunanina yana kallona ta wata hanya mai ban mamaki. Ba kamar wani
tunani mai sauƙi ba, amma kamar wani sigar ni a cikin madubi yana kallona ta baya, ko da
kuwa bayan na kawar da kaina.
Da farko na ɗauke shi a matsayin gajiya ce da na yi, tunanina kawai hankalina ne ke wasa da
ni. Amma da yawan kwanakin da suka wuce, wannan jin yana ƙara tsanantawa. Abin da ya fara
damuna da gaske shine lokacin da na lura cewa tunanina yana motsawa.

Wata rana da yamma, ina wucewa gaban madubin , sai na ga tunanina ya ɗan juya kaina kafin
in yi haka. Tsawon daƙiƙa ne kawai, amma a fili yake. Har na yi gwaji, ta wurin tsayawa a gaban
madubi ina motsi a hankali. A wani lokaci, tunanina ya lummm a gabana ya kasance da dabara
irin ya ɗan jinkirta abin da na yi .
Na fara firgita sosai, amma na gaya wa kaina tabbas tunanina ne. A daren nan na yi bacci a kan
kujerar falo, kuma madubin yana can hangen nesa na. Da tsakar dare na tashi ba zato ba
tsammani, sai na ji wani yana kallona lokacin da na buɗe idona, sai na ga inuwa a bayana a
cikin madubi, kamar a mafarki amma gaske ne.


Na juyo ba zato ba tsammani sai dai ba komai babu kowa a cikin ɗakin .Zuciyata ta fara
bugawa ba zato ba tsammani na sake duba madubin, kuma wannan lokacin ya fi muni,inuwar
ba ta da kyau, yana can a cikin tunanina can tsakiyar madubi amma ba a cikin ɗakin ba. Ita
wannan inuwar irin siffata ce da ita amma jikinta duk ko ta ina jini ne ke fita,yadda na ƙure ta da
ido ita ma haka take kallona babu motsi. A yadda ake son na fahimta wannan na cikin madubi
ni ne da kaina kamar yadda kowanne mutum in ya tsaya a gaban madubi zai ga kansa,amma ni
nawa ya sha banban da na sauran.In na yi motsi shi na cikin madubin bai motsa wa yana nan a
daskare kamar saƙaƙo,in kuma ni na tsaya ɗam ba tare da na yi wata alamar motsi ba sai na ga
shi ya motsa. A firgice na bar ɗakin a wannan ranar ban dawo ba sai da safe.

Washegari, na yanke shawara mai tsauri. Na rufe madubin da farar ƙatuwar zanen gado. Tun
daga wannan lokacin, ya kasance a can a ɓoye. Amma kuwa duk da na rufe shi har yanzu ina
jin kasancewarsa. Wani lokaci ina tsammanin ina jin ƙararrakin hayaniya suna fitowa daga
wajensa kamar surutu da sautin faɗuwar wani abu kamar tasa ko kuma an cilla dutse a rijiya.
Kamar wanda aka yi wa dole haka kuma na ƙi fitar da madubin,na ci gaba da rayuwa da shi har
wata baƙar rana ta zo wacce ba zan manta ba.Ina kwance ina baccin bayan la'asar aka kira ni a
waya Ammyna ta zame jiki ta faɗi babu hannu babu ƙafa ga kuma zuciyarta ta kumbura.Ko
wanke fuska ban yi ba na ɗauki makullin mota,a ƙa'ida sai jibi zan yi jigilar dabbobi kamar yadda

tsarin yake in na zo asabar sai kuma ranar Laraba zan koma can gida Agadas.Kwana ɗaya da
wuni na yi a hanya kafin na isa,direct kuma asibitin da aka sanar da ni take na nufa,a yadda na
tarar an banzatar da Ammyna sai na ji takaici ya rufe ni don babu wata kulawa ta musamman
tsabar wulaƙanci ma kan tabarma take ba a gado ba. Ba ta iya yin magana ,bakinta ya juye yawu na yi mata dalala,motsin kirki ma ta iyawa sai idonta
da ta kafe ni da su masu cike da rauni da neman agaji a gare ni.

A wancan lokacin da na tambayi nurse dalilin ƙin bai wa mahaifiyata taimako yadda ya kamata
sai ce min ta yi “ sai kun biya kuɗi na gwaje-gwaje,na gado,da kuma alluran da za a dinga yi
mata tausar ƙafarta da ta sandare ” ƴan kuɗaɗen da na samu waɗanda sun kasance na uban
gidana ne da su na yi amfani na bayar aka ba Ammy gado ,sannan da taimakon da ba a rasa
ba.Dandanan goshinta ya fara fitar da zufa sai bacci,ganin haka sai yasa na wuce can gidanmu
domin yin wanka.Mahaifina na tarar wanda shine silar duk halin da Ammy ke ciki,kayan jikinsa
na tarar yana haɗawa da alamu garin zai bari.

Ina kawo daidai nan na kashe shower saboda a duk lokacin da nake tuna rayuwata babu gaɓar
da na tsana irin ta Abbana.Cike da takaici na kimtsa na fito na zauna kan kujera,ina jin tabbas
ya zama dole na mallaki matar Illia direbana.



ILLIA POV


Babu wani tashin hankali da ya taɓa shiga wanda ya wuce wannan,babban takaici ne yau ace
ya miƙar matarsa ta aure ga wani namijin da yayi imanin cewa imani bai wanzu a ƙirjinsa ba
ballantana ya sa ran ba zai keta haddinta ba.
Kamar wani marayan uwa da uba haka ya takure jikin katanga ya rungume Abdul gam a ƙirjinsa
wanda tuni ya gaji da kuka yayi bacci,ido kawai Illiya ya ƙura wa ofis ɗin HAROON tunani iri-iri
na ta zuwar masa .Ya san halin Mariya da tsoro tun a tashin farko za ta sallama kanta ko da
kuwa bai yi amfani da tsafinsa ba.Yana nan jibge kamar kayan wanki ya ga ta buɗo ƙofa ta
fito,da sauri ya nufe ta yana cewa “ me yayi miki?” ba ta basa amsa ba ta karɓe ɗanta ta yi
gaba.Ya take mata baya yana kiranta,duk mutane na kallonsu amma ta ƙi tsayawa haka suka
dinga yin tafiyar ƙasa su biyu har suka isa gidansu duk da kuwa uban nisan da ke da kwai.



“ Mariya mene ne haka? Ina tambayar ki amma kin yi shiru” Illiya ya faɗa bayan sun shiga ɗaki.
Ta dube shi da idonta da suka yi jajur tsabar kuka ta ce “ abin da ka kai ni dominsa shi yayi!
Wato Illiya ban taɓa sanin cewa baka ƙauna ta ba sai yau amma ka sani wallahi na gama
aurenka!” sai kuma ta wuce can uwar ɗaka ta soma haɗa kayanta.

Shi kuwa zaman ƴan bori yayi jin HAROON wai kusance ta,kukan baƙin ciki ya soma yi kamar
ransa zai fita yana da kishi sosai amma yau yana ji yana gani an ɗauki abunsa mafi daraja an
tozarta shi .Wata irin tsanar HAROON ce ya ji ta ɗarsu a ransa,ya ƙudiri aniyar zai yi masa aiki
amma kuma tabbas shine ajalinsa......

My book is only 500 via 2670215530
ZULFAU YAHAYA
Ecobank DM +22795045822




Talla! Talla! Talla!!!


DULLAHZ CAKES AND MORE


Ina jamaata mutanen kirki ji'bin arziki? Yan kurna, rijiyan lemo,bacirawa,da duk abunda y jibanci
Nan Ina mutanena mutanen Kano kanawan dabo mutanen kirki mutanen da sukasan Kansu,

Ina mata yangayu wadanda basaso gayu y wucesu,biki gareki? Suna? Ko kwarya kwaryan
liyafa qawata? Kinji labarinmu ko yenzu batun ke tafe gareki,

Munayin cake me dankaren dadi cake hadadde a musulmin farashi,akway cupcakes,samosa,
spring rolls,Muna gashin kaji da kayan kwalam d maqulashe kala kala,09111648884

Yayata Muna girkin biki,suna,ko tarbon baki komi kikeso,inma grkine bakijinyi Dan Allah ki kira
dullarz zatamaki shi nantake a gyaremaki cikin warmers me delivery ykaimaki,09111648884

Yar uwata inkinyadda d Allah kibamu yardarki bbu cuta babu cutarwa b ha'inci zaa mki komi
fiyeda yenda ke zakiyi 09111648884

Call:09111648884
[30/11 à 07:46] MRS SADAUKI : *MAFIYA*☠️


LoVe aNd HoRrOr StOrY☠️

*Mallakar:* Chamsiya Laouali Rabo
(MRS SADAUKI✍️)

*Lambar waya:* +22795045822

*FIRST CLASS WRITER ASSOCIATIONS☀️*
Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation.
_____________________


12


Cike da takaicin Illiya da matarsa na dawo gida,ina shigowa da sanyi idaniyata na fara cin karo
wato Malama Zainab.Cak na tsaya a bakin ƙofa jin zazzaƙar muryarta na fitar da sautin karatun
Alqur'ani wanda ya zama barazana ga ruhina,ji nake tamkar an watsa mini ruwan zafi.
Tamkar Ammy ta san halin da nake ciki ta dakatar da ita da karatun ,“ Malama gobe in sha Allah
mu ci gaba ga HAROON nan ya dawo,ƙaraso ku gaisa ” Ammy ta faɗa tana murmushi,sai da na
je na ɗauki gorar ruwa mai sanyi na sha sannan na ƙarasa wurin su.

Ammy na fara gaishe wa kafin na zuba wa malamar ido,ta ɗago a hankali ta ce “ ya ƙarfin jikin?”

“Ai na ji sauƙi” na bata amsa ina mai ci gaba da kallonta,da dukkan alamu kuma ta tsargu da
hakan don sai wani takure jikinta take.

“Ka zauna bari na kawo ma wani abu” Ammy ta faɗa tare da nufar kitchen,nesa da Malama na
zauna ina son tantance ta amma sam babu wata ƙofar tauraronta da ke buɗe wacce za ta bani
damar ganin sirrin ruhinta.


Na ja ajiyar zuciya na ce “ ya aka yi yau kuka fara karatu da wuri haka?”

Kamar mai tsoron magana ta ce “ ina da wani aiki mai muhimmancin ne bayan sallar magrib
ɗin”

“Mene ne shi?”

Sai da ta ɗan ƙara sunne kai kafin ta ce “ dama... Dama wanda aka yi mana baiko ne ya d...”
sauran maganar ƙarar fashewar gilas ta maƙale ta.

Ammy ce ta yi ɓarin lemun zoɓo,hankali tashe kuma ta bi ta cikin kwalbar tana mai cewa “ an
miki baiko?”


“Eh tun shekaru uku da suka wuce ni da Sheikh Ali,ba ki dai ji ciwo ba ko Ammy?” ta ƙarashe
da tambayar Ammy wacce ta zuba min ido,ƙila mamakin ganin ban wani razana sosai ba ko na

tayar da hankali.


“Allah sa alkhairi,je ki direba ya mayar da ke” Ammy ta faɗa tare da zubewa kan kujera yayin da
ita kuma Malama Zainab ta fice.A hankali na tashi na tsuguna a gaban Ammy na kamo ƙafarta
da ke zubar da jini.Kwalbar na cire sannan na ɗauko ɗan akwatin da ke da kayan magani na
shafa mata tare da naɗe ƙafar da bandeji.

“ Ka kuwa ji abin da Malama Zainab ta faɗa ?”

“Eh Ammy na ji”

“Shine kuma baka ce komai ba?”

“Ammy a kullum fa ke ce da kanki kike min nasihar cewa duk wanda ya yarda da Allah to komai
nasa zai zo da sauƙi,kin ga kar ki damu Malama ba ta da wani miji da ya wuce HAROON zan je
har gidan nasu na fallasa mata sirrin zuciyata ”


Ammy ta shafi sumar kaina tana wani ɗan murmushi kafin ta ce “ haka take yarona” na miƙe
tare da sakar mata murmushi sai kuma na nufi step,a cikin kwanyata na soma jin ana yi min
magana “ HAROON lokaci yayi da za ka fara amfani da powerka domin sato taurarin mutanen
kirki,ta wannan hanyar ce zaka samu Malama Zainab ”
Kamar wani zararre na tambayi kwanyar tawa “ ta ya kenan zan soma?”

“Je ka fara yin wanka tukunna,sai ka je madubinka zai sanar da kai”

Haka kuwa aka yi,bayan na yi wanka na je na shiga cikin madubina.Direct ajin nan da ake koyar
da karatu na shiga,yau ma Mr Zulu ne ke darasi akan allo yayi zanen baƙar mage mai jajayen
ido yana kuma yin bayani.

“Baƙar mage , waɗanda galibi ana lulluɓe su cikin sirri da camfi, koyaushe halittu ne masu ban
sha'awa, musamman a duniyar mayu da ayyukan sihiri.

Baƙar mage a zahiri suna ɗaukar kuzari mai zurfi, kariya da sihiri. A cikin wasu al'adun arna da
sihiri, ana ganin baƙar fatar mage a matsayin mai kula tsakanin talikai, mai tsaro na ruhaniya.
Ya ƙunshi ma'auni tsakanin haske da inuwa, bayyane da ganuwa.

Wataƙila wannan duality ne ya sa bokaye da matsafa suka zaɓi baƙar mage tamkar abokan
hulɗa masu mahimmanci a cikin aikin sihiri. Suna kawo hikimar dare da ikon kewaya wuraren
ruhi na ɓoye.

A cikin gogewar kaina, baƙaƙen ƙuliyoyi sun kasance sau da yawa jagororina da masu kare ni a
lokutan canji ko haɓakar ruhaniya. Suna tunatar da ni cewa inuwa ba abin tsoro ba ne, amma
illa fahimta. Suna ɗauke da sihiri mai hankali amma mai ƙarfi a cikin su, ƙarfin canzawa wanda
ke ingiza mu mu wuce fiye da kamanni don rungumar ɗaukacin halittarmu.
Baƙar ƙuliya kuma alamun sa'a ne a wasu al'adu, suna kawo albarka da kariya ga waɗanda ke
maraba da su cikin gidajensu. Kasancewarsu na iya zama abin tunatarwa akai-akai game da
sihirin da ke kewaye da mu, yana ƙarfafa mu mu kasance a buɗe kuma mu yi maraba da
mutane wanɗada ba mu sani ba da gaba gaɗi.
Shin kun taɓa haɗuwa da su a cikin ayyukanku ko rayuwar ku ta yau da kullun? Menene
ma'anar waɗannan sahabbai masu ban mamaki a gare ku? ”

Hannu na ɗaga hakan yasa ya ce “ ina jin ka HAROON ”

Na ce

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login