Showing 18001 words to 21000 words out of 46966 words
Chapter 7 - Mafiya Book Compelet By Mrs Sadauki
“ ta ya za a yi mutum ya mallaki ita baƙar magen? Sannan mutum ɗaya zai iya ɗaukar
ƙuliyoyi biyu a lokaci guda don yin aiki da su ko kuwa sai ƙwaya ɗaya kawai aka yarje masa?”
Mr Zulu ya bani amsa da “ a'a in kana so duk launinkan ƙuliyoyin da muka lissafa zaka iya aiki
da su muddin dai zaka iya ciyar da su.Bari na faɗa muku wani sirrin iya ƙuliyoyinka iya ƙarfin
tasirin alƙalumanka,mai son baƙar mage ina da su da yawa na sayarwa ga su nan na kawo” ya
faɗa tare da buɗe wani tsohon akwatin ƙarfe .Cike yake da jariran baƙaƙen ƙuliyoyi duk idonsu
kuma jajur suke ,nan fa duk kowa ya soma cewa yana so ganin kamar za su ƙare yasa da sauri
ni ma na isa gaban akwatin don zaɓar tawa.Akwai ƙwaya ɗaya wacce ta banbanta da sauran ta
fi su girma haka yanayin fuskarta ma kicin-kicin yake babu fara'a.
“Wannan nake so” na furta tare da kai hannu na ciro ta,Mr Zulu yayi min kallo kafin ya ce “
HAROON ka tabbata ?”
Ba tare da tambayar dalilin da yasa sai ni kaɗai ya yi wa tambayar ba na ce “ eh yalaɓai ita
nake so ” ya saki ɗan murmushi kafin ya ce “ shi yasa Oganku ya ce kai ɗin na musamman ne
taurarinka masu matuƙar ƙarfi ne” ni ma murmushin kawai na sakar masa,magen hannuna ta yi
wani zillo ta ruga da sauri na take mata baya kawai sai na tsinci kanmu a wajen madubi a
tsakiyar ɗakina.
Da ido nake kallon magen wacce ta haye bed ɗina ta yi min ƙuri da ido,da sauri na nufe ta na
ɗauko ta na rungume.Sai yanzu na lura ashe namiji ne muzuru,kansa na soma shafawa na ce “
daga yau sunanka Tony” daga bakin ƙofa aka soma buga wa tare da kiran sunana “ na'am
Ammy gani nan zuwa” na furta tare da tashi na buɗe mata,da faɗa ta soma “ HAROON me yasa
kake son zama da towel,to in ka shirya ka fito ina son ganin ka” har za ta tafi sai kuma ta yi
saurin juyowa tana kallon gadona,sai na kai dubana na ce “ Tony ne fa”
“Yaushe ka fara son ƙuliya ban sani ba?”
“Na sosa ƴar ƙeya kafin na ce zan yi miki bayani daga baya”
Ta fice,ni kuma na rufe ɗakin.A tsanake na shirya na ɗauki Tony muka sauka ƙasa sai wani
kuka yake “minyau!”
Ammy ta ce “ Laure zuba ma magen nan abinci ƙila yunwa take ji,kawai haka nan ka kama ka
rufe ta a ɗaki”
Tony ya wani zille ya bi Laure mai aiki can kitchen,wani tsohon plate ta samu ta zuba masa
abinci tana masifa ƙasa-ƙasa “kawai don mugun hali ka rasa magen da za ka kawo cikin gida
sai baƙa mtsww!” ta ja tsuki,ƙafa ta sa ta bugi Tony ya tsaya yana kallonta “ ni bari kallona
shegiya da wasu ido nata kamar mayya” sai kuma ta fito.
Na dube ta na ce “ kin zuba masa abincin?” yau ne karon farko da na taɓa yi mata magana
saboda ni da ƴan aikin gidanmu gaisuwa ce ke haɗa mu ita ma sai na ga dama na amsa.
“Eh ga ta can tana ci” ta bani amsa.
Na ce “ namiji ne ba mace ba,sunansa Tony ”
“Sai kace dai wani mutum yalaɓai ai duk ƙuliya da sunan mace ake kiranta” Laure ta faɗa cike
da jin haushi tana mai ɗaukar kwanon abincinta ta kama hanyar fita tana gunguni ƙasa-ƙasa
sarai kuma kwanyata ta sanar da ni abin da ta ce.
“Tun da baƙin hali gare mu don muna da kuɗi da kuma jiji da kai ki je an sallame ki daga aikin”
na faɗa cikin ɗaga murya,da wani mugun sauri ta juyo tana kallona kafin ta zo da gudu ta zube
a gabana tana bani haƙuri,tsakiyar idonta kawai na kalla na fahimci Laure irin mutanen nan ne
waɗanda akan kuɗi babu abin da ba za su iya yi ba,sannan tuni hassada da baƙin ciki sun
gama gurɓata ruhinta.Jin daɗina guda da Ammy ta gusa ba ta falon,na saki makirin murmushi
na ce “ zan maido ki aiki zan kuma ƙara miki da wani wanda ya fi wannan albashi na san za ki
iya ”
Ai kuwa ta washe baki tana cewa “ sosai yalaɓai in dai zaka bani kuɗi”
Na ce “ yawwa yarinyar nan Salima ƴar gidan Yakubu soja kin san ta ne?”
Ta ƙara washe baki ta ce “ Salima mai mage ko? Ai har gidansu Hajiya ke aikina”
“Yawwa a kanta nake son baki aiki”
“Koma mene ne zan yi Alhaji in dai zaka bani kuɗi”
“Ok za ki iya tafiya,gobe zan faɗa miki bayanin aikin naki ” ta miƙe ta tafi da ƙarfin gwiwarta,sai
lokacin kuma Tony ya fito daga kitchen yayi tsalle ya ɗare kan cinyata na soma shafa bayansa
ina jin wani irin daɗi na mamaye ni.
Ina nan zaune sai ga Illiya ya shigo fuskarsa kawai na kalla na fahimci damuwarsa,ya zo ya
gaishe ni tare da zama kan capet idonsa suka fara tsiyaya.
“Ai zata dawo ba za ta iya barin ka ba,sai dai ka sani ban janye ƙudirina ba ya zama dole na
ɗanɗani zumarta” na furta ina cije leɓena na ƙasa.
Da sauri Illiya ya ɗago yana cewa “ yalaɓai dama baka kusance ta ba?”
Na kawar da kai gefe ina kallon cikin idon Tony da nake tsintar wasu abubuwa a ciki.
“Yalaɓai wannan muzurun fa?” Illiya ya jefo min tambayar da tasa na maido dubana gare shi na
ce “ faɗa min Illiya ta ya aka yi a kallo ɗaya har ka san muzuru ne? Kana da wankin ido ne ko
yaya?”
Ya ɗan washe baki ya ce “ yalaɓai lokacin baya fa na ɗan taɓa aikin tsibo sai kuma na bari
saboda kusan haukata ni jinnu suka yi”
“Ita ma matar taka da tsafi ka aure ta kenan?”
“A'a wallahi auren soyayya ne ko rubutu ban taɓa bata ba”
“Ya ake samun costumer Illiya ? Ina nufin malaman tsibo ta wace hanya ce za su bi domin ganin
sun samu mutane da yawa?”
“Ta hanyar shiga gidan rediyo da tv,ka yi musu alƙawarin aiki kyauta ne sai buƙata ta biya
sannan mutum sai bayar da abin sadaka”
Na saki murmushi na ce “ to ka shirya min zama da manyan ƴan jaridu da kuma wasu mutanen
da za su bayar da shaidun ƙarya akan na yi musu aiki ya ci sun zo godiya”
Ya saki baki yana kallona kafin ya ce “ yalaɓai kuma bayar da magani zaka koma?”
Na haɗe rai na ce “ tashi ka bani wuri,ka yi abin da na ce su kuma mutanen da zaka samo ka
sanar da su zan biya su ne” da saurinsa kuwa ya tashi,ni kuma na kai baki na sumbaci Tony
don wannan dubarar daga gare shi ta fito.
Bayan sallar la'asar kuwa sai ga mutane sun cika gidanmu,gefe guda ƴan jaridu biyu ne sai
bayan na gama bayanan ƙarya kan cewa ina warkar da dukkan cututtukan duniya sannan
mutane suka soma faɗin abubuwan alkhairin da na yi musu,na biya masu gidan rediyo da tv
domin yi min talla da kuma lambar wayata da za a kira ni.Su kuma masu shaidun ƙarya Illiya na
baiwa kuɗi ya raba musu,kuɗin da ace sun san sune ajalinsu to da tabbas ba za su karɓa ba
amma ƴan magana na cewa kwaɗayi mabuɗin wahala......
NB:Ina ƙara yawan free page ne,niyyar kaina.
My book is only 500 via2670215530
ZULFAU YAHAYA
Ecobank DM +22795045822
Talla! Talla! Talla!!!
DULLAHZ CAKES AND MORE
Ina jamaata mutanen kirki ji'bin arziki? Yan kurna, rijiyan lemo,bacirawa,da duk abunda y jibanci
Nan Ina mutanena mutanen Kano kanawan dabo mutanen kirki mutanen da sukasan Kansu,
Ina mata yangayu wadanda basaso gayu y wucesu,biki gareki? Suna? Ko kwarya kwaryan
liyafa qawata? Kinji labarinmu ko yenzu batun ke tafe gareki,
Munayin cake me dankaren dadi cake hadadde a musulmin farashi,akway cupcakes,samosa,
spring rolls,Muna gashin kaji da kayan kwalam d maqulashe kala kala,09111648884
Yayata Muna girkin biki,suna,ko tarbon baki komi kikeso,inma grkine bakijinyi Dan Allah ki kira
dullarz zatamaki shi nantake a gyaremaki cikin warmers me delivery ykaimaki,09111648884
Yar uwata inkinyadda d Allah kibamu yardarki bbu cuta babu cutarwa b ha'inci zaa mki komi
fiyeda yenda ke zakiyi 09111648884
Call:09111648884
[01/12 à 09:18] MRS SADAUKI : *MAFIYA*☠️
LoVe aNd HoRrOr StOrY☠️
*Mallakar:* Chamsiya Laouali Rabo
(MRS SADAUKI✍️)
*Lambar waya:* +22795045822
*FIRST CLASS WRITER ASSOCIATIONS☀️*
Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation.
_____________________
13
Washegari,afujajan Illiya ya shigo ofis ɗina ko neman izini bai yi ba.
“Yalaɓai ya haka? Dukkan mutanen da suka bada shaidar ƙarya a kan kai malamin tsibo ne sai
ɗauki ɗaiɗaya mutuwa take yi musu”
Da wani mugun kallo na dube shi na ce “ au! So kake na bar su da ransu daga ƙarshe su tona
min asiri? ”
“Yalaɓai kisan kai fa ne jinin wajen mutum goma” ya faɗa hawaye na zubo masa akan kumatu
waɗanda suka sa na ji zuciyata ta yi mugun sanyi don tsabar daɗi,don a yanzu in ga mutum
cikin baƙin ciki shi fi faranta min rai.
Ido na lumshe ina tuna yadda Tony yayi amfani da madubin tsafina ya dinga tsotse jinin duk
mutanen da na bai wa kuɗi,sosai hakan ya ƙara mini ƙarfin power ta yadda a wannan karon har
na yi nasarar toshe bakin Ammy ta yadda duk abin da zan yi ba za ta ga abunsa ba ko kuma ta
yi min magana.
“Yalaɓai ciki fa har da mace mai ciki ” Illiya ya faɗa cikin gwanjin kuka,na buɗe ido jin furucinsa
.Na ce “ ya zancen Salima ka kuwa fara wani shiri a kai?”
Ya saka idonsa cikin nawa yana zancen zucin da nake jinsa raɗau kwanyata na karanto min
shi,‘ dama duk rashin imanina akwai wanda ya fi ni ? Anya akwai zuciya a ƙirjin yalaɓai? Wato
duk wannan iftila'in da ya jefa mutane shi ko a kwalar rigarsa?...’
Tunanin nasa ne na katse ta hanyar cewa “ wani abun jin daɗi ma daga cikin wannan lamari shi
ne kuɗin za su ci gaba da yawo a doron duniya,kuma iya masu son zuciya ne kawai za su je
hannunsu haka kuma zan ci gaba da amfani da tataccen ƙarfin jikin mutane domin inganta
gobena.Illiya ina so ka sa a ranka babu abin da ba zan iya yi ba yanzu,don haka kar ka kai ni
bango yin haka ban kwana ne da rayuwarka.Je ka yi aikin da na saka,ka tabbatar Salima ta
kasance cikin tsaronka sannan duk wani motsi nata ka sanar da ni”
Ba tare da ya ce komai ba ya juya zai tafi,na tsayar da shi “ mene ne sunan matarka?”
Ya juyo da sauri yana kallona tambayar ‘ me za ka yi da sunanta?’ shimfiɗe akan fuskarsa.Na
ƙara haɗe rai ina juya idona zuwa na mage,murya na rawa ya ce “ Mariya ” na sakar masa
murmushi,shi kuma ya fice.
Kan kujera na zauna ina tunanin hanyar da zan ɓullowa mijin da Malama Zainab za ta
aura,wanda alƙaluman tsafina sun tabbatar min da tabbas auren babu fashi .Na ja tsuki ina jin
takaici,kukan Tony na ji ƙarƙashin kujerar da nake zaune.Na duƙa na ɗauko shi na ɗora shi kan
table,jikinsa na fara shafawa tare da soma yi masa magana ina neman shawara “ Tony a daren
jiya na yi bincike akan Malama Zainab kuma an nuna min sai ta auri mijin nan nata,ban so ya
kusance ta ya zan yi?”
“Turen aljani za ka yi wa mijin,tun da ita tana tsare iyakokin Ubangiji sosai babu ta hanyar da
jinnu zai shiga jikinta.Amma kamar yadda ka yi bincike haka ni ma a jiya na yi bincike kan shi
Sheikh ɗin,duk da yayi karatun addini amma fa bai amfani da shi in taƙaice ma dai fuska biyu ce
da shi har da giya yake sha” Tony ya faɗa min da idonsa amma raɗam nake jin sautin murya na
fita daki-daki.Tsabar murna ban san lokacin da na ɗauke shi na rungume tare da miƙe wa tsaye
na soma yin rawa,“ ashe babban sirri ne da mage baƙa har haka? Hohoho! Wato shi yasa Tony
ka kasance na musamman abin da ban saka ka ba yi kake yi domin sauƙaƙe min aiki”
Tony ya ce “ yalaɓai ka manta a daren jiya ka yi min sacrifice? Ai muddin zaka bani jini abin da
zan yi ma sai ka yi mamaki” sam ban damu da cewa illata rayuwar wasu babbar cutarwa ce ba
na ce “ in dai jini ne Tony kar ka damu”.
Ina nan zaune Illiya yayi min waya kan cewa Salima ta tashi daga makaranta,kuma shine ya kai
ta gida da sunan ya rage mata hanya.Duk wayar da nake Tony ya buɗe kunnuwa yana
saurare,bai ce komai ba ya fita da gudu.Na saki murmushi don na tabbata kuwa wani aikin ne
zai yi min,wayata da key na ɗauka tare da ficewa .
Ina draving ina tunanin surar Mariya matar Illiya ,na lashi leɓena na ƙasa ina mai cewa “ ko
fyaɗe ne sai na yi miki muguwa!” a haka na ƙarasa gida.Ina shiga na ga Salima a zaune kan
kujera tana taya Ammy saƙar kayan sanyi,na saki wani murmushin jin daɗi ganin Laure ta fito
daga kitchen hannunta riƙe da kofin zoɓo ta kai wa Salima.
“Ga wannan ki sha Madam yana ƙara gani musamman gare ku masu kallon zare” Laure ta faɗa
amma kafin Salima ta kai ga amsa Ammy ta ce “ Laure miƙo min ganin zoɓon nan har
maƙoshina ya bushe,je ki kawo wani”
Da sauri na ƙarasa ina cewa “ haba dai Ammy ya za ki ce haka? Ita fa wannan baƙuwarmu ce
ita ya kamata a fara karramawa,kuma kin ga ke kina da mura.Laure je ki kawo wa Ammy marar
sanyi,ki dinga kula don Allah ko ta ce ki bata abu mai sanyi kar ki biye ta”
Laure ta miƙa wa Salima kofin,za ta ajiye shi ita ma na tari numfashinta “ Hajiya ƙyanƙyamin mu
kike shine ba za ki sha ba?” da sauri ta girgiza kai ta ce “ a'a wallahi bari na sha to” sai ta kai
kofin bakinta har sai da ta sha rabi sannan ta ajiye sauran.Laure na fitowa na yi mata nuni da
ido kan ta tafi da ragowar wanda Salima ta ajiye,ai kuwa tana miƙawa Ammy nata sai ta ce “
bari na ɗauke sauran kar ya zuba ga capet”
“Laure wane irin abu ne wannan? Ta sha abu ta ajiye shine za ki tafi da shi? In kuma tana son
ƙara sha?” Ammy ta faɗa cikin faɗa ,a doli Laure ta ajiye kofin tana kallona ta koma kitchen.
Hira suke tsakanin Ammy da ita Salimar ni kuma ina gefe ina danna waya,hannun Ammy na
gani ya ɗauki kofin zoɓon ban san lokacin da na ce “ Tonyyyy!” ban ida rufe baki ba ji kake
Ammy na salati haɗi ƴar ƙara tuni Tony ya saka bindinsa ya buge kofin daga hannunta ya faɗi
ƙasa ya zuba a ƙafarta.
Laure ta fito tana tambayar lafiya,na soma shafa bayan Tony da tuni ya zo ya ɗare cinyata kafin
na ce “ zo ki tsabtace wurin nan please ”
Jikinta na rawa ta zo ta goge wurin da ya ɓace ita kuwa Ammy sai faɗa take,a ƙarshe dai na
tashi na bar wurin na koma part ɗina.Ta cikin madubina na ga hanyar da Tony ya bi ya bai wa
Laure maganin da ta zuba a zoɓon Salima,ya ajiye mata shi ne a kitchen da kuma ƴar guntuwar
takardar da yayi bayani daki-daki.
★MALAMA ZAINAB
Matashiyar budurwa ce ƴar kimanin shekara ashirin da bakwai a duniya,ta mallaki hankalin
kanta.Duk wata cikar halitta da ƙima da ake nema wurin cikakkar mace mai ƙima duk ta mallake
su.Mace ce ita wacce ta riƙi bautar Ubangiji matsayin abu na farko a rayuwarta,duk sauran
abubuwa suna biyo wa baya ne.Tausayi,kyauta,jinƙai su ne suka luluɓe duniyarta suka ƙawata
kyakkyawar fuskarta mai cike da hasken ni'imar imani.Tun da take ba ta taɓa soyayya ba,duk
da kuwa maza dayawa sun nuna ra'ayin haka amma ita ba ta ji wanda take so ba.Sheikh Ali ya
kasance cousin nata,tun da ta tasa ya ga tana da addini ya ɗauki son duniya ya ɗora mata tare
kuma da zage dantse wurin nuna mata abin da zai kawo ci gaban karatunta.Wannan yasa ba
tare da wani tunani ba ta amince za ta aure shi har aka yi musu baiko,bayan haka ne ya tafi
Misira wurin karatu.Tun da ya tafi kuma ba wata gamsashiyar waya suke ba kasancewar shi da
ita ɗin duk ba su da wani isasshen lokaci.Kwana biyu da dirar shi a ƙasar Nijar ya nemi a yi
walimar aurensu,wacce kuma tuni aka soma shawarwari tsakanin ahalin biyu kafin shi ma
angon ya nemi su keɓe domin tattaunawa.
Ko da ta fito daga gidansu HAROON direct gida direba ya ajiye ta,zuciyarta cike da fargabar
abin da take gudu take kuma zato kar ace gaskiya ne wato tana son HAROON .
Ɗakinta ta shiga ta yi wanka ta canza kaya,bayan ta yi sallar magrib sai ta shafa mai.Tana nan
zaune tana saƙa da warwara Innarta ta shigo tana cewa “ Zainabu ki fito ga Ali nan ya zo”
Sai da gabanta ya faɗi,amma ta daure ta ce ” to Inna gani nan” sai kuma ta miƙe ta zaɓo