Showing 21001 words to 24000 words out of 46966 words
Chapter 8 - Mafiya Book Compelet By Mrs Sadauki
wani
farin hijabi ta saka tare da fesa turare marar ƙamshi.
Sai da ta yi jarumta sosai sannan ta ƙaƙalo murmushi ta yaɓawa fuskarta mai cike da
damuwa.Da sallama ta fita falon,yana ganin ta ya kafe ta ido ko ƙyaftawa bai yi.Ta zauna ƙasan
capet ta ce “ ina wuni Imam?”
“Alhamdullah malamata fatan kin wuni lafiya?” ya faɗa ba tare da ya janye idon nasa a kanta
ba,cike da tsarguwa ta ce “ Imam babu fa kyau kallon mutum haka”
Yayi murmushi mai sauti ya ce “ haka ne ! Amma kar ki manta saura ƙiris ki zama tawa na yaye
duk wani hijabin kunya a tsakaninmu”
Ba ta ce komai ta miƙe ta je ta kawo masa ruwa da abin da Innarta ta gyara mata domin tarben
baƙon.Tana zuba masa ruwa ya kafe hannunta da ido,nan take jikinta ya soma yin rawa ta ɗaga
kai ta banka masa wata muguwar harara.
Ya ja ajiyar zuciya ya ce “ sai da na ji wani yarrr ” ruwan ta ajiye masa ya ɗauka ya sha,sannan
ta zuba masa abinci har da su cewa ta zo su ci amma ta ƙi.
Bayan ya gama ne ya ce “ Malama Zainab yau muna wace rana?”
Ta basa amsa kai tsaye da “laraba”
Ya ce “to rana irin ta yau kin shiga lalle da yardar Allah,sai a yi ɗaurin aure juma'a,taron biki
kuma asabar”
Shiru ba ta ce komai ba sai ma duniyar tunani da ta lula,ranar farko da suka soma ganin juna da
HAROON ,yadda suka yi baya ta faɗa kan ƙirjinsa,yanayin yadda yake kallonta cikin tako da
kuma salo,yadda yake mata murmushi...
“ Zainab ?” Sheikh Ali ya katse mata tunanin,a ɗan firgice ta ce “ na'am HAROON !”
“Haroon kuma?” ya tambaya da mamaki,sai ta diririce ta soma kame-kame,ita ɗin ba
ma'abociyar yin ƙarya ba ce shi yasa ya gane.
“Kar ki yi min ƙarya Zainab,wane ne HAROON ?”
Ba tare da ta basa amsa ba ta tashi da sauri har da ɗan gudunta ta shige ɗakinta tare da
faɗawa kan bed ta fashe da kuka.......
My book is only 500 via 2670215530
ZULFAU YAHAYA
Ecobank DM +22795045822.
Ki zo ki yi payment domin a yi tafiyar nan da ke, wannan karon salon na daban ne salo ne da
ban taɓa yin irinsa ba.
BONUS! BONUS! BONUS!!!
Ina makaranta kuma ma'abotan son littafan soyayya ko kuma na tsafi? To ku zo MRS SADAUKI
ta yi muku gwanjon Books ɗinta akan farashi mai sauƙi,duk book ɗin 500 za ta bar muku shi ne
a 300 kacal,wanda kuma yake 700 ko sama da haka za ku same shi a 500 kawai .Me kuke jira
kawai ku tuntuɓe ta WhatsApp +22795045822. Domin ku kwashi garaɓasar. [02/12 à 15:50] MRS SADAUKI : *MAFIYA*☠️
LoVe aNd HoRrOr StOrY☠️
*Mallakar:* Chamsiya Laouali Rabo
(MRS SADAUKI✍️)
*Lambar waya:* +22795045822
*FIRST CLASS WRITER ASSOCIATIONS☀️*
Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation.
_____________________
14
Sai da Zainab ta ci kuka ta ƙoshi sannan ta shiga toilet.Tana shiga ƙarƙashin shower tunaninta
ya soma nuna mata ga HAROON nan tsaye tare da ita suna wanka tare da wasanni irin na
ma'aurata.Murmushi ne yayi nasara bayyana a kyakkyawar fuskarta wacce a ɗazu take
shimfiɗe da baƙin ciki.Tamkar wata zautata haka take murmushi na wasar ruwa da niyyar nan
HAROON ne take watsa ma su haɗi da yi masa shagwaɓa.Towel ta ɗaura ta fito ,sai ta tarar da
Inna zaune bakin gado.Ta ƙara sakin ranta kafin ta ce “ Inna?”
“Ungo wannan ki sha,su kuma waɗannan ki dinga zuba a abinci kina ci yaji ne” cewar Innar
tana mai miƙa mata kofi.Karɓa ta yi ta zauna tare da yin Bismillah ta soma shan madarar har ta
shanye,sai da Inna ta ƙarara jadadda mata kar ta saki ta yi wasa da su kafin ta fice.Ita kuwa tsaf
ta shirya cikin riga da wando na bacci ,ta yi sallar isha'i sannan ta zauna ta soma duba takardun
jarabawar da ta yi wa ɗalibanta.Sai dai sam hankalinta ya kasa kwanciya sai aukin tunanin
HAROON ,wayarta ta ɗauka ta kira Ammy bayan sun gaisa sai ta yi shiru.Can dai ta ce “ ina
HAROON ?”
“Yana ɗakinsa,ko na baki shi?”
“A'a turo min dai lambarsa” sai kuma ta yi saurin kashewa tana dafe saitin zuciya haɗi da waro
ido.“ Zainab mi kika yi haka?” ta tambayi kanta,ƙarar shigowar saƙo ta ji da sauri ta duba sai ta
ga lambar ce aka turo mata sai da ta yi ta kallon lambar kafin ta yi saving da “ NAWAN” sai ta
ɗora love daga ƙarshe.
Data ta kunna tana addu'ar Allah sa yana WhatsApp,tsawon lokaci kafin a nuno mata lambarsa
mai ɗauke da hotonsa da Ammy su duka biyun suna murmushi.Da sauri ta ɗauki hoton sai ta
yanke daidai nasa kawai ta tsura masa ido can kuma ta rungume wayar tana mai jan
numfashi.Duba takardun da ba ta yi ba kenan ta je ta haye bed,MP3 ɗinta ta kunna ƙira'ar
Sudais ta soma tashi tana biyar karatun tana kallon hoton HAROON a haka bacci ya ɗauke ta.
Washegari sai da ta tsarkake jikinta kafin ta gabatar da sallah saboda mafarkin da ta yi.Bayan ta
gama ta yi shara da gyaran ɗaki sannan ta ɗumama abincin kari,sai kuma ta je ta yi shirin
makaranta.Cikin ƴar ƙaramar kula ta zuba abincinta kafin ta yi wa Inna sallama,sai da ta zo
bakin titi sannan ta samu abin hawa .Tana isa makaranta ɗalinta suka fara gaishe ta ita kuma ta
wuce cikin aji,sai a lokacin ta ci abincinta cike da tunanin mafarkinta na jiya.Sai da ta yi da
gaske sannan ta hakice tunanin HAROON daga ranta ta gabatar da darasi wanda shine ya
zama na ƙarshe.Tana komawa gida aka shafa mata lalle,don dole ta haƙura tuni kuma aka fara
shirye-shiryen biki kamar yadda abin ya zo mata a bazata haka su ma dangin da abokai amma
duk da haka sai da aka fitar da anko.Har aka kawo lefe aka yi ɗaurin aure ko sau ɗaya Sheikh
Ali bai kira ta ba haka ita ma ta share shi ko saƙo ta kasa tura masa.Yanzu ma da ake ta
hidimar biki babu abin da take sai tunanin da ya daɗe da aurenta,na masoyin da igiyar aure ta
yi mata iyaka da shi .Da zarar ta tuna cewa yau ɗin nan wani zai karɓe budurcinta sai hawaye
su yi ta mata zuba,mutane kuwa tunaninsu kukan rabuwa da Inna ne kasancewar ita ɗaya ce tal
ta rage musu a duniya duk ƴan uwanta sun rasu tun suna jarirai.
Har aka yi kiran sallah magrib Malama Zainab na kuka,da aka ce ta je ta yi wanka domin shirin
kaita ɗakinta ji ta yi kamar ta fasa ihu ta yadda kowa zai fahimci tsananin damuwar da ta luluɓe
sirrin zuciyarta.
Da ta yi wankan sai da ta yi sallar isha'i sannan mai kwalliya ta soma yi mata simple make-up
ba irin tarkacen nan ba.Doguwar rigar less fari sol ta saka sannan ta ɗora alkyaba sama a haka
ma sai da aka ƙara ɗora mata darar amare.Sai da aka yi hotuna da bidiyo da abokan arziki kafin
a ƙara yi mata wata nasihar,daga nan aka ja ta zuwa can waje inda motocin da ango ya turo
suke jira.Banda kuka babu abin da Malama Zainab take yi amma hakan bai hana aka kai ta
ɗakinta ba,har aka gama addu'a kuma ba ta buɗe fuskarta ba.Nan mutane duk suka watse yayi
sauran ƙawarta guda tal Hafsat wacce sai yanzu ta samu damar yi wa Zainab ɗin nasiha “
kukan nan ya isa haka don Allah! Abin da muke ta jiran ranar nan amma ta zo sai kuka kike”
Malama Zainab ta buɗe luluɓin ta ce “ Hafsat tsoro nake ji,wallahi zuciyata kamar za ta fashe
don fargaba don Allah ki taimaka min ki bani shawarar da zan yi amfani da ita wacce za ta hana
Sheikh ya kusance ni”
Shiru ta yi kafin ta ce “ caɓɓɓ! Batu wuya,gurguwa da aure nesa! Amma kin san wannan ba mai
yiyuwa ba ne,wallahi sai ya kusance ki sai in magani bacci za ki basa ya sha” da sauri Malama
Zainab ta ce “ yawwa ko hakan yana yi,don Allah je ki karɓo min ” sai ta zuge zip ɗin jakarta ta
bata kuɗin,sai da Hafsat ta yi ta juya kuɗin kafin ta fita ta je ta siyo mata sai a lokacin hankali
Malama Zainab ya kwanta.Babu jimawa kuwa ango ya shigo tare da rakiyar abokansa,bayan
sun gama tasu nasihar Hafsat ta bi su don su sauke ta gida.
Ido Sheikh ya tsura wa Malama Zainab wacce tun da suka haɗa ido sau ɗaya ta sunne kai.Ya ja
wata ajiyar zuciya kafin ya ce “ amincin Allah ya tabbata ga ma'abociyar ado da kyawu”
Dakyar ta amsa masa da “ wa'aleykum Salam!” sai hawaye shaaa,ya kamo dukkan hannuwanta
ya sauko da ita daga bed ɗin yana mai cewa “ mu je ki yi alwala”
“Ka bari zan yi ni ɗaya” ta furta,sai ya bar ta ɗin ta shiga toilet ta ɗauro alwala bayan ta fito shi
sai ya shiga.Da sauri jikinta na rawa ta ɗauko maganin baccin ta je buɗe ledojin da ya shigo da
su ta zuba maganin cikin lemu sai dai aka yi rashin sa'a tuni Sheikh ya fito daga toilet ya ga
kwalbar sirop ɗin kuma ya fahimci na mene ne.Yayi saurin komawa toilet ɗin ya bata lokacin da
za ta yi rashin gaskiyarta ta gama.
Yana fitowa a karo na biyu ya sakar mata murmushi kamar bai ga komai ba,ya ja su sallah
bayan nan yayi musu addu'o'i ya miƙe ya ɗauko ledojin da sauri ta karɓe ta ce “ bari na zuba
mana” bai ce komai ita ta ɗauko plate da kuma kofinan shan ruwa.
Da ta zuba haka ta daure tana cin kazar shi kuwa tunani ne fal zuciyarsa ‘ mene ne ribar Zainab
in ta bani maganin bacci? Wato ba ta son na kusance ta sai kace ba sadakina na biya na aure
ta ba .Ko dai tsoro ne take ji? A'a ba shi ba ne inda shi ne da tabbas da magiya da kissa irin ta
mata zata ɓulo min’ yayi tambayoyin duk a zuci amma ya kasa samo amsa,ya ƙure ta da ido
lokacin da ta cika masa kofi da lemun ya karɓa a nan take kuma ya tuna da sunan HAROON
wanda y'zuciyarsa ta yanke masa tabbas saurayinta ne.
Kofin ya kai bakinta yana mai cewa “ namijin kirki shine wanda ke fara shayar da matarsa kafin
shi ya sha”
“A'a ka sha ni ma zan sha ai ga nawa nan sai na gama ci na sha” ta faɗa tana zarar ido, Sheikh
ya saki murmushi ya ce “ in dai ba ki sha to ni ma ba zan sha ba sai da na sha ruwan pampo”
Malama Zainab na jin haka ta yi saurin karɓa ta sha ,da tunanin can su yi ta baccin su biyu .Shi
kuwa Sheikh haka ya tsura mata ido har sai da ta shanye tass,ta cika masa kofi ta ce “ saura
kai” ya laƙace mata hanci ya ce “ ai ni bana shan kayan zaƙi saboda suna da illa, dama dai
wayo na yi miki ”
Tamkar wacce cutar sanƙarau ta kama haka ta sandare ta kasa motsi sai idonta da ke tsiyayar
da hawaye tana da na sanin haƙa wa ramen muguntar da a ƙarshe ita ce ta faɗa .Ba a ɗauki
lokaci ba ta ji fitilun idonta na disashewa,sai a lokacin ta miƙe da hanzari ta shiga toilet ta wanke
fuskarta duk don kar bacci ya ɗauke ta sai dai ina tuni ta soma jin jikinta ma na saki.Da sauri ta
fito kamar wata makauniya tana lalube, Sheikh ya je ya kamo ta tare da ɗora ta kan bed yana
mai cewa “ shi yasa aka ce in za ka gina ramen mugunta ka gina shi gajere” sai kuma ya soma
cire mata suturar jikinta.Sai da yayi mata zirr kafin ya cire nasa,jikinsa har rawa yake wurin
ƙoƙarin haura gadon sai dai cak ya tsaya saboda yadda idonsa suka fara nuna masa ba daidai
ba.Malama Zainab yake gani ta rikiɗe masa ta koma lakaɗeɗen maciji sai wani haske take
fitarwa......
My book is only 500 via 2670215530
ZULFAU YAHAYA
Ecobank DM +22795045822
[03/12 à 16:24] MRS SADAUKI : *MAFIYA*☠️
LoVe aNd HoRrOr StOrY☠️
*Mallakar:* Chamsiya Laouali Rabo
(MRS SADAUKI✍️)
*Lambar waya:* +22795045822
*FIRST CLASS WRITER ASSOCIATIONS☀️*
Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation.
_____________________
15
Jikin Sheikh Ali ne ya ɗau wata irin muguwar rawa ganin amaryarsa wacce aka kawo masa yau
ta rikiɗe ta zama lakaɗeɗiyar macijiya sai wani kaɗan bindi take.
Da gudu ya dawo falo ba tare da ya tsaya ɗaukar ko da wando ba ne,ɗakinsa da ya ware tun
can a matsayin baraya ya shiga.Duk uban sanyin da ake zufa ce ke yi masa tsiyaya,tunani ya
soma kamar wani zautace haɗi da suratai.“ Aljana ce aka kawo mini ko kuwa Jinnul ashiq ne da
ita banda labari? Kaicona ni Ali ,ni kam banda rabo a duniya duk yadda nake mararin ganin
wannan daren amma ya zo min ta wata mummunar siffa? Ai kuwa ba zan zauna da ke ba
wallahi dole ki tafi gidanku” sam bai rumtsa ba haka yayi ta zagayen ɗakinsa yana tubka da
warwara.
★HAROON
Tun bayan da Salima ta sha lemun zoɓon nan sai ya zamana a kullum kafin na fita aiki sai ta
shigo gidanmu.Haka za ta yi ta kallona amma ta kasa yin magana,gefe guda kuma Laure mai
aiki na ci gaba da bata maganin da Tony ya ajiye a kitchen.
Yau ma kamar kullum ina zaune ina duba takardun da nasa aka buga min irin wanda in kana
son ganin likita patients ke cira,da sallama Salimar ta shigo.Ammy ba ta falo sai ni kaɗai,ido na
zuba mata sai na ga ta soma kyarma yayin da bakinta ke ta rawa.Na fahimci kalmar so take son
furta mini amma ƙarfin zuciyarta ya hana ta faɗa ,ni kuwa ta wannan hanyar ce kawai zan
cimma ƙudirina a kanta.
Idonta ne ya soma kawo ruwa,da sauri na kawar da kai gefe ina jin wani haushin ta .Sai ta fita a
guje tana kuka,na ja tsuki tare da tashi na fito na shiga ɗakin da na ware domin duba maras
lafiya da kuma masu son a yi musu aiki.
Kamar yadda na tsara sai ranar asabar kawai zan dinga yin aiki,yayin da kuma Iliya direbana
zai dinga karɓar kuɗin ganina sai ya bai wa mutum takardar shaida.
Yau ce ranar farko da zan soma kamar yadda na sanar a sanarwar da nasa aka yi,amma
mutane ne masu mugun yawa suka taru.Ɗaya bayan ɗaya suke shigowa ,in na karɓi
receip/reçu ɗin hannun mutum ni ne zan sanar da shi sunansa da kuma matsalar da ta kawo shi
.Dukkan bayanin kuma Tony ne ke sanar da ni komai,yanzu ma layi ya kawo kan wata budurwa
da ta shigo.Ta miƙa mini takardar hannunta na karɓa ina dubawa “ sunanki Shukuriya,kina son
a yi miki aiki kan Salele don ya saki matarsa ke ya aure ki saboda ba ki son kishiya sannan shi
ma ya faɗa miki bai da tsarin yin mata biyu saboda bai da cikakken lokaci a matsayinsa na soja”
na faɗa ina mai kallon ta,a zahiri fuskarta ce nake kallo amma a baɗini ruhinta ne abin
dubana.Sam ba ta da mutumci ga kuma muguwar zuciya,uwa uba rashin imaninta yayi ƙasa
sosai.Bayan na gama ganin qualitynta sai na saki murmushi,yayin da kuma muryar Tony ke ce
min “ HAROON wannan ɗin ma ka riƙe ta gam da alamu za ta kawo ma ci gaba a tafiyarka ”
“Eh haka ne malam,shine abin da nake so amma nawa zan bada?” ta tambaye ni tana wani
sunne kai.Zama na gyara ina jawo tasar da na zuba ruwan tsafina na soma shafa su,sai na ce “
kina da hoton shi saurayin naki?”
“Sai dai a waya kawai” ta bani amsa,na ce “ nemo ki miƙo min” da sauri kuwa ta miƙo min wayar
don hotonsa ne kan screen.Saitin tasar ruwan na kara hoton tamkar mai yin scanning nan take
zanen hoton ya zauna raɗam kan ruwan,cikin abin da bai kai minti biyar ba na gama kwashe
duk wasu bayanansa.
Na ɗago na dube ta na ɗan wani lokaci kafin na ce ,“me yasa kika yarda da shi har kika basa
kanki? Cewa yayi zai aure ki ko? Yana son ki? To duk ƙarya ce kawai yana wasa da hankalinki
ne,jikinki kawai yake so.Amma zan yi miki aikin da sai ya aure ki,fatan za ki bi duk sharuɗan da
zan gindiya miki?”
“Eh malam in dai zai aure ni koma mene ne zan yi”
“Ina so ki kawo min maniyinsa” na faɗa .
Ta waro ido tare da cewa “ ta yaya malam?”
“Abu mai sauƙi,in za ku yi mu'amala ki saka condom ta mata ko kuma shi ki basa ya saka kin
gane dai ko?”
“To malam zan yi,sai me kuma?”
“Shi kaɗai nake buƙata za ki iya tafiya,in kin samo shi ko yau ne ki dawo” na faɗa ta yi godiya
tare da fita,wasu suka ci gaba da shigowa a cikinsu babu wanda na yi wa aiki sai dai cutarsu da
na yi ina kwashe taurarunsu ina adanawa kaina domin ƙarin power a haka har dare yayi.
Ina shigo wa falo Ammy ta soma yi min sannu tare da addu'ar ci gaba akan aikin alherin da na
soma