Showing 12001 words to 15000 words out of 46966 words

Chapter 5 - Mafiya Book Compelet By Mrs Sadauki

na soma
yin tsafin da zai kai ni inda mai kama da ni yake,aka yi katari kuwa yana cikin mota direba na
tuƙa shi.
Bayyana ta cikin motar yayi daidai da lokacin da direbana ke ƙara saita madubin gaba na
mota,yayi ƙara tare da sakin sitiyarin motar sai a lokacin ɗayan ya ɓace saura ni.Na tashi da
sauri na tsayar da motar tare da zama gefensa,direba ya dafe zuciya yana kallona kafin da
sauri ya maido dubansa gare ni sai na fahimci tabbas ya ganmu mu biyun duka.

Na saki murmushi na ce “ shi yasa bin didigi da ganin ƙwaf bai da kyau,duk yawan sa idon bai yi
maka ba sai da ka nemo yadda za ka yi ka tantance shin mu biyu ne ko a'a .To ka tuƙa motar
nan izuwa wani wurin cin abinci na ga alamun har da yunwa kake ji daga nan sai na aika ka
barzahu”
“Yalaɓai don Allah ka yi haƙuri!” ya furta tare da ƙoƙarin fita sai dai tuni na ƙargame dukkan
ƙofofin yayin da kuma na saka motar ta soma tuƙa kanta da kanta .......



My is only 500 via2670215530
ZULFAU YAHAYA
Ecobank DM +22795045822 saura page ɗaya na gama free page in sha Allah.



Talla! Talla! Talla!!!


DULLAHZ CAKES AND MORE


Ina jamaata mutanen kirki ji'bin arziki? Yan kurna, rijiyan lemo,bacirawa,da duk abunda y jibanci
Nan Ina mutanena mutanen Kano kanawan dabo mutanen kirki mutanen da sukasan Kansu,

Ina mata yangayu wadanda basaso gayu y wucesu,biki gareki? Suna? Ko kwarya kwaryan
liyafa qawata? Kinji labarinmu ko yenzu batun ke tafe gareki,

Munayin cake me dankaren dadi cake hadadde a musulmin farashi,akway cupcakes,samosa,
spring rolls,Muna gashin kaji da kayan kwalam d maqulashe kala kala,09111648884

Yayata Muna girkin biki,suna,ko tarbon baki komi kikeso,inma grkine bakijinyi Dan Allah ki kira
dullarz zatamaki shi nantake a gyaremaki cikin warmers me delivery ykaimaki,09111648884

Yar uwata inkinyadda d Allah kibamu yardarki bbu cuta babu cutarwa b ha'inci zaa mki komi
fiyeda yenda ke zakiyi 09111648884

Call:09111648884
[27/11 à 09:31] MRS SADAUKI : *MAFIYA*☠️


LoVe aNd HoRrOr StOrY☠️

*Mallakar:* Chamsiya Laouali Rabo
(MRS SADAUKI✍️)

*Lambar waya:* +22795045822

*FIRST CLASS WRITER ASSOCIATIONS☀️*
Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation.
_____________________

Last free page

10

Ni kaina ban san taƙamaimai ina ne motar za ta je ba,gudu take tamkar aljani ne ke tuƙa
ta.Cikin abin da bai wuce minti biyu ba har mun fita daga cikin garin Yamai mun shiga ƙasurgin
daji sai a lokacin kuma motar ta tsaya cak tare da buɗe kanta.Na fito zuciyata na sake azalzala
banda wani buri baya da na kashe direbana wanda har izuwa yanzu bakinsa bai gushe da bani
haƙuri ba.Finciko shi na yi da sauri ya zube kan gwiwansa tare da kama ƙafafuna ya ce “yalaɓai
ka yi mini rai ,na yi maka alƙwari zan kasance bafaɗenka mai yi maka hidima.Zan zama tamkar
Kare da mai ikonsa,ka yarda da ni zan yi maka duk abin da kake so amma kar ka kashe ni ina
da buruka masu tarin yawa da nake son cikawa kafin na bar duniyar nan!”



Cikin ƙaraji na ce “ Illiya ka tabbata duk abin da nake so za ka yi shi?”

“Eh yalaɓai koma mene ne zan yi” ya amsa mini cikin haƙiƙanin gaskiyarsa.

“Za ka zama mataimakina kamar yadda ka ce akwai ayyuka masu tarin yawa da za ka yi min,in
ka kuskure kuwa ka sani daidai yake da fitar numfashinka ”

“Na gode sosai yalaɓai” ya furta tare da tashi har yanzu jikinsa bai bar rawa ba,haka muka
shiga mota na lumshe idona ina jin wani matsayi ya hau kaina saboda na fara samo wa
ƙungiyarmu member sannan duk wani wanda ya shigo ta sanadiyar ka to a ƙarƙashin kulawarka
yake kamar yadda doka ta tsara.

Ko da nake buɗe ido sai na tsinci kanmu a tsakiyar babban titin Yamai,na ɗan saki murmushi na
ce “ Illiya na tambaye ka mana”

“Eh yalaɓai ina ji tambaye ni” ya faɗa murya na rawa.

“Matanka nawa?”

“Matata guda yalaɓai da kuma yaronmu ɗaya” ya bani amsa a tsorace.

“Zuwa gobe ka kawo min ita a babban ofishina ina son ganinta” na faɗa cike da gadara.

“Yalaɓai ai ba ta yi makaranta ba”

“Yaushe na ce ma zan ɗauke ta aiki ?” na yi masa tambayar a tsawace.

Ya ce “ka yi haƙuri yalaɓai”

Na juyar da kai ina kallon titi har muka isa gida,ina fita sai da na tsaya ina ƙarewa Illiya kallo
gajere ne shi baƙi yana da ƴar ƙiba amma ba sosai ba,idonsa irin na munafukan mutanen nan
ne masu son sanin sirrin wani.

“Yalaɓai na faɗa ma zan yi duk abin da ka ce,ka yarda da ni ” ya faɗa cikin tsoro,na shafi sajena
kafin na ce “in ma ba ka yi ba ai ka san meke jiran ka! Sannan duk faɗin duniyar nan ba za ka
taɓa ɓoye min zan lalubo ka” ina gama faɗa na wuce ciki.


Yau Ammy ba ta falo ban kuma nemi na san inda take ba kawai na shige ɗakina,wanka na
soma yi kafin na fito ɗaure da towel.Kai tsaye kusan madubina na je na tsaya,ina son sanin
abubuwa da dama game da MAFIYA wacce a yanzu garɗinta nake ji.Kamar wanda zai shiga
ɗaki haka na yi na ratsa ta cikin madubin na shiga ciki,yau ɗin ma kamar waccan lokacin
yanayin duniyar hazo-hazo ce sai dai hakan bai hana ni ganin abin cikinta ba.Wani aji na gani
inda aka rubuta “TSAFI DA MATSAFI” babu wani tunani ai kuwa na je na tsaya sai na ga wata
malama a tsaye tana koyawa wasu karatu,ba tare da neman izini ba na je na zauna ina kallon
darasin . Tana gamawa kuma sai ga wani shi ma malamin ya bayyana kamar daga sama,kamar
wani rediyo kuma ya soma yin magana.


“Sannu Matsafana da kuma Mayuna!A yau za mu gano abokiyar sufi da muka fi so wato: cat da
turanci,wacce a Hausa za mu kirata da mage ko kuma ƙuliya.Wannan halitta ko da yaushe tana
da alaƙa da sihiri da mayu.Za ku ga a gidajen Mayu,matsafa ko malaman tsibo suna ƙawata shi
da mage ko kuma ƙuliyoyi wanda normal mutum zai ɗauka iya soyayya ce kawai amma yanzu
zan muku gwanjon sirrikan.Bari mu fara da labarin da zai burge ku!” sai ya tsaya da magana
tare da soma yin rubuta a ƙaton allon da ke cikin ajin.


# Cat da Bokaye: Tsohuwar ajiya a cikin kundin Labari na ƙarni biyu.

Shine abin da ya rubuta kafin ya soma yi mana bayani dalla-dalla.

“Tsawon ƙarnoni, ƙuliyoyi sun kasance abokan bokaye. Masarawa sun bauta musu a matsayin
alloli. Indonesiya sun yi imanin cewa ƙuliyoyi na iya gani fiye da mayafi. A takaice, abokanmu na
sirri sun fi dabbobi kawai.

Abu na gaba shine :

# Ikon Sufanci na Mage

A naku hange me yasa mayu suke son kyanwa sosai? ” Mr Zulu na kawowa nan sai ya tsaya
yana tambayar mu,wato ya bamu damar tsoma baki a ciki kamar yadda malaman makaranta ke
yi.


“ HAROON ko za ka faɗa mana dalili?” ya jefo min tambayar,duk sai hankalin kowa ya dawo
kaina.


Na ce “Domin suna da ƙarfin ikon sihiri”

Yayi alama da babban yatsansa irin na jinjina kafin ya ce “ba shakka! HAROON yayi gaskiya a
cikin halittun da duniyar Ruhaniya ta aminta da su mage nada kaso casa'in na ƙarfin tsafi yayin
da sauran halittun kuma nada ƙarancin rinjayen.Daga cikin quality ɗin mage akwai:
* Hankali, Cats suna jin kuzari da ruhohi mara kyau. Mafi dacewa don kiyaye gidanku.Ma'ana a
duk lokacin da wani mummunan abu zai faru cikin gida mage tana sani kuma za ta iya kare
mamallakinta daga wata cutar wa ita abin ya same ta.

* Kariya :suna tunkuɗe mugayen ruhohi da munanan kuzari.Daga lokacin da mugu ya shigo
gida zai ji ya kasa zama a ciki saboda wanzuwar ƙuliyar.
* Warkarwa : Tsaftace su yana da tasirin warkewa, cikakke don rage damuwa.In mutum na cikin
wata damuwa ta dalilin yadda yake mu'amulantar magensa zai iya samun sauƙi daga abin da
ya shige masa.
Sannan ku sani bayan wannan ɗin akwai wani ɓoyayyen sirri a tattare da kowacce mage.Abu
na gaba da nake son ku sani shine TASIRIN LAUNI,kowacce mage da kuke gani da nata tasirin
sannan ba haka kawai ake mallarkarsu ba sai an cika sharuɗa.Amma kafin nan bari na sanar
da ku tasirin kowacce daga cikinsu.
Kowane launin yana da ma'anarsa ta sihiri da tsafi.

_Baƙar fata: Yana nuna kariya da sihiri. Saɓanin camfi suna kawo sa'a.
_Fara: Yana wakiltar tsarki da waraka.
_Grey: Yana jawo hikima da hankali.
_Ja: Yana jan hankalin sa'a da kuzari.

_Tiger: Yana wakiltar sassauci da daidaitawa, cikakke don lokutan canji.

Zan tsaya a nan sai wani lokaci ” Mr Zulu ya faɗa tare da yin ɓaton dabo.Ina zaune dai cikin
mamakin wannan lamari sai ga kuma wani tsoho shi ma ya shigo ajin tare da rakiyar dog.Na
gyara zama don jin wane darasi ya zo mana da shi kawai na tsinkayo murya Ammy na faman
kiran sunana,a dole na tashi na fito abun mamaki har yanzu jikina na ɗigar da ruwa kamar
yanzu ne na fito daga toilet.

Ƙofar na buɗe ina ƙirƙiro murmushi na ce “ Barka da maraice Ammy!”
Ta dube ni da kyau kafin ta ce “ HAROON wai meke damunka ne? Ka dawo daga aiki amma ba
za ka zo ka gaishe ni ba? ”

“Yi haƙuri Ammy na gaji ne sosai,kaina kamar zai tsage haka nake ji shi yasa na soma yin
wanka.Amma kina zuciyata ” na yi ƙaryar ciwon kai saboda shi ne abin da ke sa hankalin Ammy
gusashe wa a duk lokacin da ta kama ni da wani laifi ni kuma ina gudun ta yi min faɗa .

“Tun yaushe ka fara jin ciwon kan?” ta faɗa hankali tashe,na ce “ bai wuce minti goma” ba ta ce
komai ba da sauri ta fita sai kuma ta dawo da ruwan ƙanƙara da towel,kamar ƙaramin yaro haka
ta zaunar da ni ta soma yi min tausar kai har sai da na ce mata ya daina na bar ji.Wata irin
wawuyar ajiyar zuciya ta sauke wacce har sai da na ɗora ayar zargi da tambaya na ce “ Ammy
me yasa hankalinki ke tashi in nace kaina na yi min ciwo?”

Ɗan daburcewa ta yi kafin ta ce “ ka saka kaya ka sauko ƙasa na yi maka girki mai daɗi” tana
gama faɗa ta fice,na bi ta da kallo ina cewa “ tabbas akwai wani ɓoyayyen sirri da Ammy take
ɓoye min” haka na miƙe na kimtsa sannan na sauka zuwa ƙasa.


Ammy ta zuba min abinci amma na kasa ci,ta zauna kusa da ni tare da soma bani a baki tana
mai cewa “ zama da yunwa bai da kyau yana haifar da cutar olser,ka yi niyya ka yi aure
HAROON ko hankalina zai kwanta na san matarka za ta kula da kai” ban ce mata komai ba sai
murmushi. Da sauri na juya bayana jin kukan mage yau a gidanmu ,magen fara ce sol ko tabo ɗaya ba
tada kuma dumul-dumul da ita kana gani ka san ba ta da yunwa.

“Ammy ina kika samu mage?” na yi tambayar ina kallon magen sam na kasa ɗauke idona a
kanta .

“Ka jira yanzu mai ita ta shigo ” cewar Ammy tana dariya,babu jimawa kuwa sai ga wata
kyakkyawar budurwa fara tas da ita har da wani ƙaton baƙi a goshinta na sallah .Sallama ɗauke
da bakinta sannan kuma ta gaishe da Ammy,kafin ta soma kiran sunan magen “ Mira! Mira! Zo
mana” kamar uwa da ƴa haka magen ta je da gudu wurinta,ita kuma ta duƙa ta ɗauke ta kafin ta
zo ta miƙawa Ammy key ta ce “ ga shi in Mama ta zo ki bata ni zan koma makaranta” Ammy ta
karɓa ita kuma ta fita,da sauri na yi jarumtar tattara nutsuwata na share zancen magen na ci

abinci.

Kiran sallar magrib aka soma,“ HAROON je ka yi alwala ka wuce masjid ni zan shiga daga ciki”
cewar Ammy,a dole na amsa mata da “ toh” sai kuma na fita can harabar gidan.


Da hannu na yi wa Illiya alama da ya zo,da sauri ya ajiye butar da yake alwala ya zo jikinsa na
rawa .“ Ga ni yalaɓai”

“Yarinyar nan da ta fita yanzu Mai mage wace ce ? Ka san ta ne?” na tambaye shi .
Ya ce “ Eh yalaɓai Salima ce ƴar gidan Yakubu soja tana karatu a babbar jami'a ne”

“Ina son ta ne,ka san yadda za ka yi ta yarda da hakan” na faɗa kai tsaye.

“Amma yalaɓai Malama Zainab fa?”
Har sai da ƙarar rawar zuciyata ta motsa jin an ambaci sunanta,na saki wani murmushi na farin
ciki kafin na ce “ ita wannan ta musamman ce” sai kuma na bar shi nan na koma ciki.



ILLIYA POV

Bin bayan HAROON kawai yayi da kallo yana mamakin wane irin rikitacen mutum ne shi,a haka
ya koma yayi alwala ya je masallaci.Har aka yi sallar isha'i yana ta tunanin hanyoyin da zai bi
ɗin ya sanar da Salima,da kuma ya tuna zancen Yalaɓai na ya kai masa matarsa gobe sai
hankalinsa ya ƙara tashi.Haka dai ya samu ya fito daga masjid ɗin ya je bakin hanya ya samu
taxi ta kai shi can gidansa,yau ko motar bai tafi da ita gida ba kamar yadda ya saba.

Yana shiga kuwa ɗansa Abdul ya rugo yana tara masa hannu,sam ya manta bai shigo da komai
ba kamar yadda ya saba musu ba.”Yi haƙuri Abdul na manta ban sayo ba ka bari har zuwa
gobe” yana gama faɗa yaron ya fashe da kuka,hakan ya jawo hankalin matarsa Mariya ta fito
tana kallon mijinta ta fahimci ba ƙalau ba,gaisuwar da ta yi masa ma dakyar ya amsa.
Ruwan wanka ta kai masa,haka ya je yayi ya fito ya zo ya shige can uwar ɗaka ya rabka uban
tagumi.
“Baban Abdul” ta faɗa cikin Hausarta da ba ta dafu ba.
Ya zabura ya ɗago ya dube ta,sai kuma ya haɗe rai ya ce “ lafiya kike wani kirana haka?”

“Kai dai zan tambaya lafiya duk ka bi ka sauya haka?”
“Mariya haka ya dace a tarbi miji in yana cikin damuwa? Ko abinci fa ba ki bani ba” ya faɗa
wannan karon ya sassauta murya.Ta ja ajiyar zuciya kafin ta ce “ ka yi haƙuri bari na kawo ma”
sai ta fita ta je ta kawo masa.Ya ce “ ina Abdul?”
“Ya gaji da kuka har yayi bacci ” ta basa amsa tare da zuba masa abinci a plate ya karɓa ya

soma ci yana ƙare mata kallo,bafulatana ce ita kyakkyawa ba ta da ƙiba hakan yasa ƙirjinta har
yanzu a cike suke kuma tsaye daram .

“Lafiya kake ta ƙare min kallo kamar yau ka fara gani na?”
“Kin san ke ɗin ce kullum kyau kike ƙarawa” ya faɗa tare da kashe mata ido ɗaya yana
murmushi,ita ma dai ta ɗan saki ranta ta soma yi masa surutunta da wannan ta ɗan sassauta
zuciyar Illiya har suka yi bacci,amma tsakar dare ya tashi a firgice saboda mummunan mafarkin
da yayi.Sam kasa komawa yayi sai yayi zaune yana ta saƙa da warwara har garin Allah ya
waye,suna tsaka da cin abinci kiran HAROON ya shigo wayarsa,gabansa ya faɗi rasss haka
yayi ta kallon kiran har ya yanke wani ya sake shigowa amma shi ma ya ƙi ɗauka sai ana uku
ne yayi ƙarfin halin tashi ya fita can tsakar gida sannan ya ɗaga idonsa na kawo ruwa ya ce “
yalaɓai ina zuwa yanzu nan zan kawo ta” yana gama faɗa kuma aka kashe kiran daga can
ɓangaren.Illiya ya goge ƙwalla kafin ya dawo ɗaki,Mariya ta kafe shi da ido sai dai bai bata
damar yin magana ba ya ce “ Ogana ne bai da lafiya yanzu nan aka kira ni,tashi ki saka
hijabinki mu wuce”
Ganin yadda mijin nata ya shiga tashin hankali yasa ta bi umaninsa kawai,Abdul ta kimtsa ta
goya shi sannan suka fito bakin titi ya tsayar musu da taxi ya faɗa masa sunan babban
kamfanin da za su je.



HAROON

Da abu uku na kwana daren jiya,na farko soyayya da ƙaunar Malama Zainab,na biyu kuma son
mallakar magen Salima,na uku kuwa shine son ganin matar Illiya . Wannan yasa gari na
wayewa na yi wanka na shirya,shayin Ammy kawai na sha kafin na fito sai kuma na tarar Illiya
bai zo ba na yi tunanin don kar ya cika umarnina ne ya ƙi zuwa wannan yasa na soma jera
masa kira domin yi masa gargaɗi sai kuma ga shi ya bani tabbacin zai kai ta.
Ɗaki na koma na ɗauko key na mota,da kaina na yi draving na isa can kamfanina.Ko sauraren
gaisuwar mutane ban tsaya ba na shige ciki,babu jimawa kuwa sai ga Illiya ya shigo shi da
matarsa wacce idonta ƙurrr a kaina masu cike da mamaki da tambayoyi.

Kujeru na nuna musu ,ta kwance goyonta kafin ta zauna shi kuwa Illiya ya ma kasa zama da
alamu jira yake ya ji dalilin zuwan nasu.
Rigar rashin mutumci na sake yaɓawa kaina kafin na ce “ Illiya karɓi yaron nan ku fita waje ina
son yin magana da ita” jikinsa na rawa ya ɗauki yaron da tun da muka haɗa ido da shi ya soma
kuka,Illiya ya je bakin ƙofa ya waiwayo yana kallona na banka masa harara da sauri ya fice ina
mai ganin ƙwalla na

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login