Showing 1 words to 3000 words out of 58434 words

Chapter 1 - A Mafarki Na santa By Faeeh First Lady

25 Jun 2026

448

�A MAFARKI NASANTA �
In my dream I know her
By
Pha'eezah almustapha
Daga alkalamin����Fa'eeh Bungudu

BISIMILLAH RAHAMANI RAHIM
Wanan shine litafina nafarko Dana fara wallafawa Allah Ina rukonka daka bani damar kamalashi
lafiya kamar yanda nafarashi lafiya�

*PERFECT ESSENTIAL WRITER'S ASSOCIATION
�P.E.W.A�
Home of Perfect Writer's together we stand�

ESSENTIAL WRITER'S �🖊�*
Pen 🖊�is mightier than the sword🗡�*

Dedicated to my lovely sis Laila Almustapha Murai�

Yaa Allah ina rokon ka kabani damar rubuta abunda Al umma zasu yi aiki dashi kuma su
Amfana, kabani ikon rubuta shi cikin koshin lafiya na kammala shi lafiya���
Warning!!!Banyarda wani ko wata su juyamin labarina ba ta kowace siga batare batare da an
nemi izini na ba wannan dokace kuma duk wanda yayi ban yafe ba wannan labari kirkira ne
bada gaske bane duk wanda yayi dai dai da labarinsa to yayi hakuri akasine. Daga
cikin abunda littafi na ya kunsa *Tausayi*
*zumunci* *zazzafar soyayya*
*sarauta* *cin amana*
*ta,addanci*

DASUNAN ALLAH MAI RAHMA MAIJINKAI

EPISODE 1�⃣
FREE PAGE1�⃣

Natsatssiyar budurwa ce ke tafiya anatse bata kallon komai face inda take sanya kafafunta, tayi
nisa acikin tafiyarta kenan ta tsinkayi muryar wata budurwa na kwala kiran Halee! Halee! da jin
wannan murya ta budurwar dake kwala kiran Sunan halee ko ba,a fada mata ba tasan khady ce
tsayuwar ta da minti biyu sai ga khady ta iso inda take atsaye. Isowar khady keda wuya ta furta haba Halee kinsan bakya da issashiyar lafiya ya za,ayi kije
Aiken baba ta ta maimakon ki fada mata gaskiyar cewa baki da lafiya nasan zata k'yaleki ni sai
intafi kinga ko yanzu gudo wa nayi bayan bayan tashiga bandaki,nasan da kin sanar mata da ni
sai intafi koh haka ke da dadi ga uwar rana gashi bakya da lafiya,har taga ma mitar ta

kyakkyawar budurwar nan da aka kira da halee bata tanka mata ba.. Daga ni dai yarinyar
miskila ce😄 chan bayan kamar minti biyu haka ta cigaba da tafiyar ta kamar bataji abunda
khady ke fada ba duk da kuwa tana jinta rass kuma tasan tabbas ko ba,a fada ba khady
gudowa tayi tabiyo ta. Da khady taga alamar ba tsayawa zatayi tabata kudin aikar ba na baaba tsaibe,kuma taga
alamar yan miskillancin sun motsa dole haka tabita suka cigaba da tafiya atare har suka iso
kantin da zasu yi siyayyar ta kayan miya
Sallama sukayi atare amsa musu sallamar tsohon dake tsaye akan tebir na kayan miyan yayi
cikin sakin fuska Dan dama baba tsohon yasan su musamman halee ya saba da ita sosai tunda
kusan kullum sai an aike ta yin cefane da sauran aikace aikacen akasuwa.
Washe baki tsohon yayi yana furta a,ah Haleematu sadiya ce kayataccen murmushinta tasaki
jin ya ambaci cikakken sunanta Wanda mutun daya ne ke kiranta da wannan Sunan sai kuma
mutun daya Wanda bata San ko wanene shi agareta ba Amma tabbas aka ambaci cikakken
sunanta tana jin wani iri ajikinta Muryar baba tsohon ce tadawo da hankalinta agaresa yana furta na nawa za,a bada cikin Dan
murmushi ta furta baba tsohon ina wuni lafiya,ita ma halee haka amsa musu yayi duka yana
dariyar halee aransa najin ga tambayar da yayi mata ga abunda ta furta masa shiyasa yarinyar
tashiga ransa Dan akwai tarbiya gata kamila anatse kara mai maitawa yayi" na nawa za,a
bada"cikin Dan yin kasa da kai ta furta acikin zazzakar muryar kamar ana busa sarewa ko
algaitu gata da sanyi Wanda intana magana zakaji har tsikar jikin ka natashi na Dari uku da ta
furta ne yasanya ni dawo wa daga sumar tsayen danayi tun lokacin da ta buda baki ta gaisar da
tsohon.
Toh baba tsohon ya furta aleda ya saka musu baka ya mika musu sallama sukayi masa sukayi
wucewar su, suna tafiya khady na zuba uban surutu alokacin da ita kuma Halee take ta zullumin
komawar ta gida Dan tasan gamuwar su da Babah Asabe bamai kyau bace dan tasan sai ta
mata fadan dadewar ta duk da dama ta saba,Amma yau da yakasance batajin dadin jikinta
tana fama da matsanancin ciwon kai sai take jin shakkun yadda zata iske gidan,tana cikin
wannan tunani sai ga hawaye shar😢 a idanunta gwanin tausayi Khady data lura da yanayin da
take ciki ne duk da ba bakonta ganinta hakan Dan danan hankalinta yatashi Dan tana mugun
son halee kamar jinin jikinta,da tausayinta cikin tausayinta ta furta haba Halee meyafu kuma,
dan Allah kitsaida hawayen nan suna Sosa mun rai kuma kinga kan hanya muke kiyi hakuri
nasan damuwar da kike ciki bata wuce sanin ko ke wacece bah da damuwar baabah ta 'baaba
Asabe' kiyi hakuri in sha Allah komai zai zamo tarihi Halee nah hawayenta ta share mata
wayenda ke tsiyaya a I danunta tana girgiza mata kai alamar ta tsayar dasu da kyar ta tsayar da
hawayen ta ganin damuwa kwance akan fuskar Yar uwarta!tafiya suka cigaba da yi kowa da
abun da yake sakawa aransa,babu Wanda yakara furta uffan har suka iso gidan,
Dan madaidaicin gidane suka tsaya kafin su shiga cikin dar dar musamman Halee gidane dai
dai na talaka mai rufin asiri ginin bulo da filista zauren gidan suka tsaya suna shawarar Wanda
zai fara shiga domin gudun abunda zasu tarar dakyar dai dukansu sukayi shahadar shiga da
sallama abakunan su Sallamar su ta ta katse ganin Baba Asabe na mitar rashin dawowar Halee akan lokaci da
kuma fitar Khady bada saninta ba,
A hankali halee take ta durkusa gurin Yar matashiyar matar da bazata wuce shekara talatin da

uku ba a duniya!Baba Asabe kenan wadda Sunan ta yake Lauratu amma mafi yawan mutane
suna kiranta da Asabe saboda masifarta da ankira Baba Asabe za,a San itace Dan Sunan ta
kaf ya bace.
Cikin sanyin muryarta da yazame mata jiki tace baaba ga kayan miyar kinga na dad'e koh
wallahi Baba tsohon ne mun tarar da layi agurin sh...uwar hararar da baba Asabe ke sakar
mata ce tasan ya ta yin shiru badan ta shiryawa hakan ba,dama kanta adone yake dan bata son
kallon cikin idanun manyanta musamman ma na Baba Asabe ....taci karo da hararar da take
sakar mata,bata ida ganin tsawon hararar ba ta kara done kanta kasa cikin tsoron abun da zai
biyo baya..
Kiran Sunan Allah take yi a zuciyarta Dan tasan yau tata takare sai ta sha rankwashi akai da
gori kala kala da zagin da bata so zuciyarta ce taji tsinke tausayin kanta da kanta yakamata.
Bata ida gama tunaninta ba ta tsinkayi muryar Baba Asabe nama khady fadan binta da takeyi
abaya inta aiketa duk da kullum haka suke muddin Baba asabe ta aiki Halee to tabbas in Khady
tadawo sai ta bita sundawo tare koda kuwa dawowar su daga makaranta ne aka tura Haleen sai
ta yi sand'a ta bita... Baba asabe ce take furta wallahi Hadiza ki shiga taitayinki Dan ubanki na fahimci bakya game
zancen da nake maki ace ke kullin sai kinsaka ni yakar baki ehh~bakinta har kunfa yakeyi
saboda masifar da ke cinta dama Baba Aabe masifaffiya ce ta bugawa ajarida.

Wai nikam nace dama haka masu suna Lauratu suke ne??�
Hankalin khady (Hadiza) yayi dubun tashi bata kanta takeyi ba Dan tasan karshen masifar kan
halee zai kare. Ahankali ta furta innata kiyi hakuri ke dallah rufe mun baki sha shar
banza kawai ana miki gata kina botsarewa,inji cewar Baba Asabe , aikullun haka kike cewa ayi
hakuri tau Dan ubanki ki kara kiga yadda yadda zanyi da suyar namanki agidan nan takai
karshen maganar tana ban kamata harara
Kiwuce ki cire uniform dinki kizo ki Debi ruwan zafi gasu chan nadora miki amadafa.
Toh Khady ta furta cikin tutse bakinta mai makon ta wuce sai ta tsaya taga yadda za,a kwashe
da Halee tana jin tsoron tashin ciwon Yar uwarta Wanda take ganin hard a damuwa kesanya
tashin sa,tana mugun son ta da tausayinta, gashi yanzu haka tana fama da kan daya zame
mata al ada dan duk yatashi tana wahala sosai wasu lokuttan har suma takeyi inyatashi saboda
yadda take samun high temperature.
Bayan Baba Asabe tajuyo kan Halee wadda ke durkushe har yanzu bata daga duk da yadda
rana ke gasata ga sumintin yadau zafi hawaye take zubarwa na tsoron masifar ta Baba Asabe
Dan tasan kanta abun zai dawo ya kare ga ciwon kanta da ke ta kara hawa jikinta sai kara
dumewa yake yi da zafi..hawayene shar suka zubo a I don ta suna sauka abisa kyakkyawar
fuskarta.

Mu hadu a next page domin jinya zata kaya tsakanin Halee da Baba Asabe
Me kuke tunani akan Halee??
Kucigaba da bibiyata domin warware muku duk wani tunanin ku.✌✌
Yawan like dinku da comment shi zai tabbatar mun da kuna bibiyata,in har naga comments da
like da yawa zan kara muku yawan pages.
Nasan zaku ga chanji na sunan Baba tsaibe da yakoma Asabe ga wadanda suka fara

karantawa babu editing

�A MAFARKI NASANTA�
in my dream I know her
By
Pha'eezah Almustapha
Daga alkalamin����fa'eeh Bungudu

*PERFECT ESSENTIAL
WRITER'S ASSOCIATION

�P.E.W.A�

home of perfect writer's together we stand �

ESSENTIAL WRITER'S �🖊�*
Pen🖊�is mightier than the sword 🗡�*


EPISODE1�⃣
FREE PAGE2�⃣&3�⃣

Typing📲📲📲

Gefen hijab dinta tasanya ta share hawayenta muryar Baba Asabe ce tadawo da ita daga
maganar zucin da takeyi
Da masifa take furta munafuka algunguma wallahi bari kiji duk ranar da kika kara bari Hadiza
tabiki in na aike ki wallahi ko na lahira sai yafi ki jin dadi sha sha marar asali kawai tsintacciya
yar gaba da fatiha wadannan kalmomi da Baba Asabe take yawan furta mata suna daga mata
hankali sosai fiye da zaton mai tunani duk ranar da Baba Asabe ta furta su agareta sai tasha
kukan ta ita kadai alokacin kuwa Khady ce kawai ke iya lallashinta.

Har tunani take yi anya kuwa ita badaga sama tafado ba,wasu lokuttan kuma takanyi tunani
kodai ita din yar gaba da fatiha ce kamar yadda Baba Asabe ke yawan furta mata,tunani
barkatai dai ke shiga akanta aduk lokacin da ta tunano da kalmomin masu muni agareta sai dai
kawai takori shaidan da Addu,ar neman tsari daga sharrin zuciya.
Dan tun Tashinta gidan wayennan kalmomin su suka bayyanar mata da ita din wacece agidan
Baba Adee tun alokacin da ta fara mallakar hankalinta ta fahimci cewa ita din ba jinin Baba
Adee bace da Baba Asabe sai dai duk da cewa ta fahimci komai akai bata taba gigin tambayar
dayan su asalinta ba dan gudun maganar da zataji wadda zata iya saka ta rasa rayuwar ta
wadda ayanzu take maleji da ita,Barema koda zata tambayi Baba Asabe baza ta iya sanar
mata da komai ba domin koda Baba Adee ya kawo Halee gidan bai sanar da ita komai akanta

ba,yadai sanar mata ya tsinceta ne akan hanyar shi takomawa gida tsakin gusau da furfuri dake
jihar zamfara wannan kenan.
Cigaba....
Maganar da Baba Asabe ce keyi tadawo da ita daga dogon tunanin da tashiga na munanan
kalmomin da Baba Asabe ta furta agareta Baba Asabe ce ke furta sakarya munafuka ana
magana kina sunne kai kamar takwarai sha sha sha ballagaza kuma wallahi kinji narantse na
kara aikarki kika dade sai kinci ubanki, mtssw taja uban tsaki tawuce warta fuuuu.
Kamar ance tajuya tahango Khady tsaye itama tana tsiya yar da hawaye kamar yadda itama
Halee take zubar da nata hawayen
Yau nina naga ikon Allah inji cewar Baba Asabe wai ke Hadiza Uban me kika hada da yarinyar
nan ne ehhh sha sha wuce kiban guri ko in tattakaki anan mtsww tana sanya hannu ta warci
ledan kayan miyar ta shigewar ta madafa tana mitar ita kadai,Ta dora sanwar rana dan dama
duka aikin gidan Halee ce keyi toh yau ma anyi lattin dora girkin ne kuma tasan Baba Adee
yana nan dawowa bada jimawa ba shiyasanya ta kyaleta bata tilas ta mata yin girkin ba.

Alkalamin����
��fa'eeh bungudu�

�A MAFARKI NASANTA�

Bayan shigewar Baba Asabe a kitchen Khady tayi sauri ta matso inda Halee ke durkushe tayi
zukunnin rakumi cikin uwar ranar da ta bude tana ta faman zubda hawaye ga hannunta dafe da
kanta dan tun lokacinda Baba Asabe ta zage ta da kalmar dan ubanta kanta yakara sarawa
bayan jin wadanchan kalmomin na farkon Baba Asabe take yawan furta mata na marar asali
tsintacciya bayansu babu abunda ke kona mata rai kamar azagi mahaifinta da mahaifiyar
wanda ko da za,a yankata bazata iya cewa ga yadda kamanninsu yake ba ko tana da iyayen
oho?Amma duk aka zagesu tana jin bakin ciki marar misaltuwa wanda bazai fadu ba,tana
sonsu duk da bata taba ganinsu ba ko jin labarinsu.
Dafa kafadanta da Khady tayi ne yadawo da ita daga dogon tunaninta dakuma kara gudun
ruwan hawayenta wanda zuwa yanzu kukanta yafara karfi har da shessheka dago lulu eyes din
ta tayi wayenda suke dauke da zara zaran eyelashes masu tsarin kyau masu dauke da kwarjini
farare tass dasu kwayar idonta har wani walkiya take yi na farin cikin idanun nata,A yanzu kuwa
sunkoma jajaye saboda damuwa da ciwon kan datakefama dashi ga kuma kukan da tafara yi.
Zararan eye lashes nata sunkara curewa guri daya saboda ruwan hawen da suka jika su,Khady
kuwa tunda suka hada idanu da Halee taji guiwoyin ta sun sage dan kuzarin datake dashi taji ya
gushe,tausayi Babbar kawar tata kuma wadda tazame mata yar uwa wadda takejinta kamar
tsoka da jininta. Ahankali ta furta Halee! kanta ta kara dagowa akaro na biyu bayan mayar dashi kasa da tayi
tana tsiyayar hawaye da idanu Khady tama alamar ta tashi suje daki tunda tasan yanzu bata
bukatar wani dogon zance saboda ciwon kanta gashi taji jikinta yakara daukar zafi sannan in
Baba Asabe ta iskosu wata masifar ce sabuwa wadda kuma take tunani ayanzu kwakwalwar
Halee bazata iya dauka ba,Hannunta ta mikamata Halee bata ce komai ba takama hannun

Khady ga gamn ta rike.
Ahankalin suke takawa kowa da tunanin da yake yi azuciyarsa harsuka isa dakin da yake chan
gefe mallakinsu su biyu
Baba Asabe da duk taga komai .....������

�A MAFARKI NASANTA�
daga Alkalamin����

�fa'eeh bungudu�
please like share & comment

� A MAFARKI NASANTA�
in my dream i know her
By
Pha'eezah almustapha
Daga Alkalamin ����
�fa'eeh bungudu�

Dedicated to my lovely sis laila Almustapha murai�

*PERFECT ESSENTIAL

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
google.com, pub-9213700357025247, DIRECT, f08c47fec0942fa0