Showing 27001 words to 30000 words out of 60755 words

Chapter 10 - Amjad Complete Book By Dijensy

Dijensy   

17 Jul 2026

661

ita ta gama ba se 8:53am tana gama ajje masa a dinning ta saka hijab d'in ta ta
fice.Yana daga d'aki ya hango fitarta,murmushin gefen fuska kawai yayi ya cigaba da
harkokinsa.

       Lokacin data isa makarantar har an shiga lecture,seda tayi missing wannan lecture d'in.Se
na 'karfe 12pm ta samu 2:30pm ta dawo gida.

      Motar sa da ta gani hakan ya tabbatar mata yana gida,lokacin da ta shiga a living room ta
ajje jakarta ta nufi kitchen ganin plate na d'azu inda ta barsu yasa ta ci birki,'karasawa tayi table
d'in ta bud'e ba abinda aka ci na ciki d'ayan ma haka ,ta rasa ma mey zatayi saboda tsabar
takaici.
  " It's Nasty! It  smells bad"Tajiyo muryarsa.

   Kallo ta bishi dashi almost harara ta shiga kitchen, abinda take so tayi a kitchen d'in ma ta
kasa saboda tsabar ba'kin ciki dan haka ta fasa girka komai ta komo living room ta d'auke
handbag d'inta zuwa d'aki.

     "Allah ya isa" Ta fad'a a fili tana cilli da jakar.

      Ga yunwa tana ji amma haushi baze bari ta iya cin komai ba.Se bayan asr ta sakko ganin
bata ga plates d'in ba yasa ta shiga tunani "Ko yaci?"

     Wainar fulawa ta had'a ta soya kayanta taci a kitchen d'in, wajen daya d'an 'baci a kitchen
d'in ta share lokacin data bud'e dustbin tasha mamaki ganin sandwich a yashe a wula'kance.

     "Wannan ai almabazzaranci ne"

     Haushi de ranar tasha shi,bayan maghrib tayi plunging charge a wayarta ta sakko 'kasa,kan
d'aya daga cikin sofa a living room ta zauna tare da d'aukan remote control ta kunna  TV.

    Chanja channel d'in tayi zuwa Bollywood aiko ta riska ana film d'in da take so "Veer
zaara".Sosai ta bada attention a kai tana jin dad'in kalla dan har taji fishin da take ya tafi.

      1hr later sega Amjad yana sakkowa ,tana jin motsintsa amma tai kamar bata san dashi
ba.Kitchen ya fara shiga ko mey ze d'auka oho ,koda ya fito har ya nufi upstair ya dawo.

     " She's enjoying it"Ya fad'a a ransa.

      "Excuse me!"

       Banza tayi dashi ta cigaba da kallonta,ganin ta'ki kulasa ya 'karaso yayi blocking d'inta
yadda bazata iya ganin komai ba.

     "Are you deaf?"

      Maimakon yaga tayi magana se gani yayi ta mi'ke tsaye tayi tafiyarta d'aki.Har cikin ransa
ba haka yaso ba se yanzu yake daya sanin barinta na tafiya.Laila kuwa a d'aki harda kukanta
dan tsabar takaici ya katse mata kallonta tasan dama abinda yake so kenan kuma burinsa ya
cika,a ranta kuwa ta 'kudura ba'kanta masa itama.
                 ★★★

     Washegari da asubar fari ta tashi da wuri tayi shirinta hatta breakfast datai a flask tasa ta zira
a jaka.7:16am nayi ta fita daga gidan.

    Knock! Knock! Laila! Ya 'kwala mata kira amma shiru ,yana murd'a 'kofar yaga bata ciki.Da
'karfi yayi banging 'kofar ya koma d'aki ,a niyyarsa yau ma ya sake sata dafa masa abinci duk
da ba cin zeyi ba.

     "Nigeria"Sunan da yayi saving number d'inta kenan. Daga yayi dialing seya kashe da 'kyar
ya bari kiran ya shiga.Ya kirata sau biyu batai picking ba,wurgi yayi da wayar gefe sau biyu
kenan yana kiranta bata ta'ba d'aga wa, lokacin bikinsu da yau.

     Laila kuwa tana shiga school tasa wayar a silent,tana zuwa ta samu gu taci abincinta ,a
ranta tana mey jin dad'i dan tasan duk tsiya seya ji haushi.

      Koda aka tashi ba gida ta komo ba gidan Mami ta wuce dama ta dad'e tana planning yin
hakan tunda tayi aure bata ta'ba zuwa ba.

      " Ga yaya!ga yaya!"Fauzan ya tafi da gudu yayi hugging d'inta.

      "Tohh,zuwa ba zato ba tsammani"Mami ta fad'a tana fitowa daga kitchen.

     " Daga makaranta nake"Ta  fad'a tare cire niqab d'in.

      Kowa murnar ganinta yake ,tuni ta mance da rayuwar gidanta.Kitso tasa Maryam tayi mata
bayan sunci abinci,4pm taje gidan Kawu Yunus nan d'inma seda ta shafe kusan awa d'ayan ta
komo gida.

     Amjad 4:23 pm ya dawo gida be sameta ba,Mom ta dad'e tana masa maganar zuwa gidan
Mami se yanzu  yaga dama shine ya dawo su tafi  tare amma be sameta ba,shiru-shiru har
5:15pm bega dawowarta ba dan haka yayi fitowarsa shi kad'ai.

    
       "Laila yanzu dubi hannunki sungul kamar taliya ba ko jan 'kunshi" Mami ta fad'a.

     "Mami makaranta ba lokaci"

     "Toh 'yar boko..." Bata 'karasa ba sega Fauzan ya shigo da uniform d'in islamiyya a
jikinshi."Mami unnhh..yaya Amjat yazo"

     Laila dake shingid'e a wani razane ta mi'ke zaune."Kace mey?"

     "Baki ji ba,mijinki ne yazo dama shi zezo d'aukan ki?"

     "Uhmm..shi..shine" Ta amsa cikin in'ina.

     "Toh ki tashi ki shirya".

    "Mami zaku gaisa ai" Laila ta fad'a.

    "Fauzan kace ya shigo" Cewar Laila.

     Da'kyar ya fuskanci abinda Fauzan yace,lokacin da  Fauzan ya shigo Amjad yana biye
dashi.Yana zaune kan kujera lokacin da Mami ta shigo ya d'an du'ka kad'an shima tuna yadda
Laila tayi sanda taje gidansu ne yasa yayi haka.

      Laila kuwa a d'aki se fiffita take da hannunta tunanin yadda zata fita take."Shikam taya
yasan ina nan?"

    "Laila ki fito toh har ya fita yana jiranki" Tajiyo muryar Mami.

     "Gani" Ta amsa 'kasa-'kasa.

       Jiki ba 'kwari ta shirya tana ta sa'ke-sa'ke a zuciyarta.Har waje Nusaiba suka rakota jiki a
sanyaye ta bud'e gidan gaba ta shiga.A nitse yake tu'kinsa har suka isa  bakin titi,daga gefe
taga yayi parking.

     "Get out" Ya fad'a ba tare da ya kalleta ba.

     "Naje ina ?" Ta fad'a a fili.

      "Dismiss from my eye's!" Ya tsawata.

      Shawara ta shiga yi ta fita ko ta zauna?

*Dijensy❤*


      

      

      

    

      
🌼🌼 🌼🌼


💦 💦


*AMJAD*


💦 💦



🌼🌼 🌼🌼


*WRITTEN BY DIJENSY*

*WATTPAD:@dijensy*

🅿 1⃣2⃣

      Zaman jakarta ta gyara tayi kamar bata jin yaran."I said get out"

     Tayi yun'kurin yin magana ya daka mata tsawa"Now!"

      Cikin sauri ta bud'e 'kofar ta rufe da 'karfi tayi gaba abinta.Shima cikin zafin rai ya figi
motarsa ya bar wajen.Haka tayi ta jiran d'an sahu seda 'kyar ta samu,tana isa gida direct ta
wuce d'aki.

     Knock! Knock taji bugu dede lokacin ta fito daga bathroom, towel ne iya gwiwa a jikinta.Cikin

hanzari ta d'auki hijab ta zira,la'bewa tayi a bayan 'kofar ta bud'e kad'an ba ko ina za'a iya gani
bama a d'akin.

     "What are you hiding?"

      'Sangalalen 'kafarta data ke karewa ya kalla ,se lokacin ya gano dalilinta na 'buyan.

     "What do you think you're doing? I knew this is not the first time.."

     Be 'karasa maganar ba ya saki atishawa ba zato ba tsammani har yana sunkuyawa,hakan
ba 'karamin dariya ya bawa Laila ba amma ta basar."Cha'kwai'kwaiwa yanzu ai kayi shiru"Ta
fad'a a ranta.

     "Don't you ever.." Wata atishawar ce ta sake zuwan masa a jere har uku,Laila harda kawar
da fuska.Harara ya bita dashi ya bar wajen, yana shiga d'akinsa yayi banging 'kofar.

     Bayan sallahr maghrib lokaci guda zazza'bi ya rifeshi harda ciwon kai ga dukkan alamu yana
ji mura ce ta kamashi.Tuni ya fara fita daga hayyacinsa,yana kwance shame-shame hanci se
tsiyaya yake yayi jazir, kwalin tissue ya ajje gefe daga ya share seya cillar duk inda yaga dama.

      Da'kyar ya samu ya mi'ke daga kwance ya d'auko wayarsa ya kira Mom ya wani kwantar da
murya yana mata complain.Ji tayi dama tana kusa dan tasan yanayin dayake shiga idan baida
lafiya rakin tsiya komai se an mashi kamar za'a goya shi.

      "Please try and take your medicine"

       "Get well soon my dear"

        "Mom,my head chest every where is paining"

         "Sorry,wish you quick recovery my love"

      Haka ta dad'e suna waya dashi wai duk dan ya samu relief, da 'kyar ya samu yayi sallahr
isha'i.Laila kuwa bata san halin da ake ciki ba tana d'aki abinta.

     Hancinsa a toshe ko bacci ya kasa yi gashi a lalle baze kashe AC ba shi karya ji zafi,banda
yunwa dake addabarsa a yanzu ba abinda yake bu'kata irin black tea amma mey had'a masa ne
ya rasa.

       Washegari da safe kamar koyaushe ta gama shirinta breakfast ne kawai ya rage.

     Laila! Laila! Tana daga kitchen tajiyo shi yana kiranta.Tea take had'awa seda ta gama tukun
ta hau sama,'kofarsa tayi knocking shiru ba amsa a hankali ta tura kamar bazata shiga ba.

     Yana bathroom tajiyo kakarin amai ,data kalli flow d'in d'akin kuwa tissue ce fal ba adadi duk
ya cillar. Ba iya 'kasa ba hatta kan gadon a birkice yake.

      Ganin ya fito a daddafe ta kawar da kai gefe,tana ji ya 'karaso tare da zama kan gado.

     " Why are you so evil?, do you want me to die here?"

      "Nina d'ora maka?"Ta kalleshi.

     
         "Allah ya 'kara alhaki na ne".

         "Make me tea"

     
           Juyawa tayi ba tare da tayi magana ba, bata  dad'e ba ta had'a masa ta kawo.Tazo ba'kin
'kofa fita ya tsayar da ita.

       "Are you living me like this?"

        "Mey zanyi ma?" Ta fad'a.

         "Speak in English"

          "I'm hungry"Taji ya fad'a.

        "Bring me water"

         Tana turo baki ta tafi kitchen, dankalin data soya ta zibo masa tare da soya masa egg ta
kawo,se bottle of water da cup ta jero a plate.Tana direwa tasa 'kafa zata fita."Laila"Ya kira
sunanta daga kwance.

     "Where are you going?"

      "School" Ta amsa.

       Kai kawai ya girgiza bece komai ba ya d'ora d'aya hannunsa a kai se squeezing yake.

     Tana sauri haka ta fice koh  a jikinta ciwonsa be d'aga mata hankali ba.Yauma bayan sun fito
daga lecture na farko ita da Aliya suna zaune kan bench suna duba wani aiki.

     Ring!Ring!Taji kira ya shigo wayarta,unknown number ta gani seda ya kusan katsewa tayi

picking.

     "Hello"

     "Laila come back home" Taji an fad'a daga d'aya 'bangaren.

      "Who am I talking to?"

      "It's me Amjad"
     
      "Why do I have to come back"

      "I'm dying Laila, I totally can't breath"

       "Then take your medicine"

        "I can't"

        "Naji gani" Ta fad'a tare da katsewa.

        "Mtchww!" Bata san tayi tsaki bama.

         "Tohh,keda wa?" Aliya ta tambaya.

         "Uhnm,tafiya zanyi" Ta fad'a rai a d'an 'bace.

       "Tafiya kuma? Sauran lectures fah?"

       "Ya zanyi? Wata'kila na dawo".

       " Ok,Allah yasa lafiya"

        "Hmm" Abinda ta fad'a kenan ta tashi

         Ita de Aliya kallo ta bita dashi dan har yanzu ta rasa gane kanta.

      10:45am ta koma gida,seda ta shiga d'akinta ta ajje jakar tukun tai knocking d'akinsa."Come
in"Ya fad'a.

     Lokacin data shiga ma yana zaune ita sam bata ga alamar wani tsananin ciwo ba,basarwa
yayi kamar ba shine wanda ya kirata ba."Why are you here? "

     "You called me"

       "I'm fine,you can go coz I don't need you now"

       "Tabd'ijan,wannan yana haukane?" Ta fad'a cinkin ranta.

      "'Kazami kawai" Tayi 'kun'kuni ta fita daga d'akin.

      Abincin data kawo masa ma be bud'e ba se yanzu,loman farko yayi ya ajje fork d'in bayaso
yaci abincinta sam amma dad'in dayaji yayi yasa ya cigaba da ci.Kad'an ya rage badan ba dad'i
ba sedan ya 'koshi,da'kyar ya samu yasha magani tukun ya kwanta.

      12:30pm haka ta tashi ta koma makaranta,lecture d'aya suka 'kara yi ta komo gida duk a
gajiye dan ma seda taci abinci ta taho.Tana watsa ruwa ta kwanta bacci,se kusan maghrib ta
tashi.Tunda ta sakko 'kasa d'aukan ruwa bata sake fitowa ba se wata washegarin.

      Yana 'kudundune cikin blanket yau ma da zazza'bin ya tashi da 'kyar a daddafe yayi
sallah.Tana shiryawa wayarta tayi 'kara koda ta duba taga number da Amjad ya kirata jiya ne.

       "Hello" Ta amsa.

        "Make me ginger tea"

         "Uhum" Ta fad'a ciki bata bari ya sake wata maganar ba ta kashe.

        Seda ta gama abinda zatai tukun ta sauka zuwa kitchen,fara had'a nata breakfast d'in tayi
kafin daga bisani ta had'a masa tea d'in."Come in"Ya fad'a bayan tayi knocking.

     Kan  drawer na gefen gado ta d'ire masa,bako sannu tayi fitowarta.Komawa tayi dinning tayi
breakfast d'inta tukun ta dawo d'aki ta d'auki handbag d'inta tayi tafiyarta.

     Shikad'ai yayi ta fama da ciwonsa,yanzu daya ji wuya ya kashe Ac d'aki kuwa yana nan
yadda yake kaca-kaca.

                 ★★★★

   Yau ta samu lecturen farko ba kamar jiya ba,seda sukai lecture biyu 12:15pm suka tafi
cafeteria.Suna fitowa ne wani saurayi dake ciki ya soma biyo bayansu,yana daga side d'in Laila.

     "Assalamu Alaykum"

     Kamar bazata amsa ba ,ta amsa da "waalaikassalm" amma bata kallon inda yake.

    "Baiwar Allah ko zan iya jin sunan?" Ya tambaya yana murmushi.

    Banza tayi dashi ta cigaba da tafiyarta, Aliya se bugin hannunta take "Ke baki ji ? Ki
sallameshi ya dena bunmu"

     "Please ko zan iya samun number ki?" Ya sake wata tambaya.

       "Bawan Allah kai baka san matar aure bane" Laila ta fad'a rai a 'bace.

       "Ayi min afuwa amma dake matar aure ce nima zan gane hakan,dan Allah ki taimaka ko
numbern ki ne ki bani".

     " Mtchww!"Taja tsuka tayi gaba tabar Aliya anan.

     Kai ta girgiza ta bita a bayan dan ita a tunaninta ta fad'i haka ne saboda ya rabu da ita.Ita
kanta Laila mamaki ta shiga yi na 'bacin ranta bata zaci haka ba.

    "Haba Laila, shine kike yin 'karya da aure akan bakyaso ki kula wani?"

      "'Karya? akan mey zanyi 'karya shi baida tunani ze tare ni..." Laila bata 'kare maganar ba se
ji tayi kuka ya ku'buce mata ,Aliya dake tsaye ta ri'ko kafad'arta ta zaunar kan bench.

     "Abin yakai ga haka?"

      "Aliya baza ki gane ba" Ta fad'a tana 'ko'karin share hawayenta da tissue.

     Shiru sukai na d'an lokaci kafin Aliya ta sake wata maganar."Laila na tambayeki?"

     Kai ta kad'a alamar "Eh".

     "Da gaske ne abinda kike fad'a ,kina da aure?"

      "Ina da aure Aliya.."

      "Kina nufin kice jiya wayar da kikai da mijinki kikai?"

      "Uhmm"

      "Amma  shine kike magana haka? Laila sekace a 'kauye"

      "Please mu bar maganar nan"

      "Keko dan Allah tun yaushe kikai aure?"

      "4month,ki tashi mu tafi ko an shiga lecture" Tayi 'ko'karin kawar da zancen.

     "Idan kince yanzu mu bar maganar ai gobe ma rana ce,idan kikai wasa ma har gidan naki
zanzo"

    "Jibeki ni tashi kin fiya manyancen tsiya"

     "Naji,ke kuma babba dake amm..."

      "Amma mey?"

      "Abar kaza cikin gashinta" Tayi dariya tare da mi'kewa.

      "Oho miki" Suka  jera suna tafiya.

     Lecture da aka shiga yasa basi samu lokacin sake magana ba,ana fitowa kowa ya tafi gida.

    Tana shiga gida taga kiran su Aunty bilki ,nan take fad'a  mata suna hanyar zuwa gidanta ita
da sauran sisters d'in Mami.

      *Short and boring chappy I know,don't forget to comment,share and vote. Love ur❤*

*Dijensy❤*


    

    
🌼🌼 🌼🌼


💦

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
google.com, pub-9213700357025247, DIRECT, f08c47fec0942fa0