Showing 36001 words to 39000 words out of 60755 words

Chapter 13 - Amjad Complete Book By Dijensy

Dijensy   

17 Jul 2026

642

batace ba,can jin shiru yasa ta kasa kunne taji ko ya fita,alwala
ta d'auro ta cire hijab d'in ta had'a da niqab d'in ta ri'ke a hannunta.

      "Am..Amjad" Ta kira a hankali kamar mey rad'a.

     Amjad dake zaune kan gadon dariya ya soma yi yana rife bakinsa.

     "Amjad" Ta sake kira.

     Jin shiru zuciyarta ta raya mata ya fita dan haka ta murd'a handle d'in a hankali,cikin sand'a

ta fara takowa.Data duba ko ina taga ba kowa ta saki hamdala,kamar ance juya ta ganshi tsaye
a bayan 'kofa .

     Da sauri ta kwasa da sauri zata koma bathroom d'in carpet dake wajen ya zamar da ita
"Aghh!" Ta 'kwala ihu tana jira ta jita a 'kasa.

     A hankali ta bud'e ido,taganshi  ri'ke da ita 'kiris ya rage bata kai 'kasa ba ,kallo suke ido cikin
ido ,d'ankwalinta da be gama zama a kanta ba ya zame 'kasa,kitson gaba ya yarfo a goshinta
har yana rufe mata ido d'aya.Hannunsa ya d'ora kan gashin a hankali yana matsar dashi daga
fuskarta.
        "Let me go"Ta fara kici-kici.

        Mi'kewa yayi completely tare da d'ago da ita,hannunta tasa ta ture nasa daga 'kugunta ta
matsa gefe.

      Ring! Ring! Wayarsa tayi 'kara,daya duba yaga daga office ne.Bece komai ba ya fita daga
d'akin,yana fita ta rufo 'kofarta tare da murd'a key d'in.

          ★★★

     Laila tunda ta rufo 'kofarta bata sake budewa ba ,har 4pm tayi gashi yunwa take ji biscuit
dake jakarta ma ta cinye shi.

      Hijab ta zumbula har 'kasa tana ta 'boye hannayenta ciki,sekace mara gaskiya tana
sakkowa daga benen she waige-waige take.Kitchen ta shiga ta bud'e fridge tana dube-dube,fruit
salad ta had'a tasha abinta ,data fito daga kitchen ta bud'e 'kofar waje ta fito.Gani tayi ba
motarsa " Ashe ma ya fita"Ta fad'a.
     Komowa tayi sitting room ta kunna TV,Bollywood ta kai  tayi zamanta kan sofa.Tunawa tayi
da aya mey gishirinta data taho da ita daga gida dan haka ta koma d'aki ta d'akko sannan ta
dawo ta cigaba da kallonta tana yi tana cin abarta.

     Maghrib nayi ta tafi d'aki seda tayi sallah ta sakko kitchen, jollof d'in taliya tayi dede bakinta
tana gama ci ta dawo sitting room ta iske an fara film d'in data ke so.Zamanta tayi harda dad'o
volume.

    9:45pm,ya shigo gida ganin TV a kunne kuma bega alamar mutum a parloun ba ya 'karasa
ze kashe.Se lokacin ya lura da ita tana kwance se bacci take hankali kwance ta d'ora tafin
hannunta a fuskarta ,yawanci haka take baccinta inde zatai bacci seta d'ora tafin hannunta ta
kare fuskarta shiyasa ya zame mata jiki ko bata san tayi bacci ba se tayi haka.
      Ba abinda yake kalla se 'kunshin hannunta daya sake maroon barin ma ga'bo'bin yastsunta

data rufe fuska.Ba sosai ya fiya ganin 'kunshi ba ,dan ko su Mom da Zakia ba yi suke ba inba a
TV ba.

      Idansa ne ya sauka kan 'kafafunta da zanen 'kunshi ya bayyana sosai,'karasawa yayi inda
take ya zauna kan gwiwoyinsa ,zanen 'kunshin ne yaja hankalinsa har da ri'ko hannunta yana 
kalla.

      Kamar a mafarki taji ana motsa mata hannu, kad'an-kad'an tana bud'e idonta har ta bud'e
tar tayi ido hud'u dashi ,a razane ta mi'ke daga kwanciyar ,shi dake zaune seda ya mi'ke tsaye.

     "Is ok"Ya fad'a a sanyaye.

      " Is ok a ina ana shafan hannu"ta fad'a a ranta.

      Tashi tayi daga zaunen ta matsa can gefe,10:05pm taga agogon parlorn ya nuna TVn ma ta
kula har an gama film d'in datake kallan ma.

       D'an 'karamin bowl d'in data zuba ti'kar ayar data ci ta d'auka kan center table d'in ta wuce
kitchen se wuri wuri take.A kitchen d'in ta dad'e ba abinda take tana tsaye se murza yatsunta
take tana kallon hannun.Du da batai 'kunshin ba da ba haka ba.

      "Laila" Taji ya kira sunanta.

    A rud'e ta d'ago ta kalleshi yana daga bakin 'kofa."Are you alright?"

     "Yes" Ta amsa a hankali.

     "Aren't you watching movie?"

      "No I'm not...I will not.." Ta shiga stammering.

      "What are you waiting for?"

       "I'm going to bed"

        "Ok,let's go"

         "Uhn..aa'ai ba ..uh.." Du ta diririce.

      Kamar yayi dariya ganin yadda ta rikice dama yana sane ya fad'i haka,takawa ciki ya soma
yi.Laila ganin yana doso inda take ta fara baya ,gefen locker tayi tabi tana zagayewa the more
yana tahowa the more tana kewaye drawer d'in kitchen d'in.Ganin ya tsaya tayi sauri tabi gefe
ta fice daga kitchen d'in, binta kawai yai da kallo yana dariya.

      Tana shiga d'akinta ta shige bathroom dan gani take kamar d'akin ma she is not safe.Se
yanzu taji gumin daya tsatstsafo  mata a jiki alhali ba zafi.

    "Mey  ya sami kansa a Canadan?" Ta tambayi kanta.

    "Wayyo!"

     
     Washegari

       7:30am ya gama shirinsa cikin blue T-shirt mey long sleeves,se black jeans.Abubuwan da
suka faru jiya ne sukai ta fad'o masa,shikad'ai ya hau murmushi agogon hannunsa yake sawa
amma ya tsaya seda wayarsa yayi ringing ya dawo daga duniyar tunani.

      Laila data farka tun 7:14am amma ta kasa fitowa se le'ken window take tana jira taga ya
fita,aiko cikin le'ken ta hangoshi ta sakankance tana kallonsa yazo bud'e mota kamar ance kalli
ya d'ago kansa.Laila tsabar rikicewa ta kasa barin window d'in kunya ce ta rifeta seda tayi da
tasanin le'kawa,shikuwa be fasa kallonta ba seda ta bar wajen.Murmushi yayi yana zira specs a
idonsa ya shiga motar.

       Tana jin ya fita ta sakko 'kasa ta shiga kitchen domin had'a breakfast.Bayan ta gama
breakfast ne ta koma d'aki tayi wanka ta shirya,jitai shirun ya isheta ta d'auka waya ta shiga
chat.

Amjad:"Mrs Amjad" Yai mata sending ganinta online.

  Laila:"I'm not"

Amjad:"What were you doing at the window ?"

Laila: Nothing

Amjad:You missed your husband.

  Laila:No you're not my husband "

   Amjad: Stop pretending.

    Amjad: Who was your ex bf ? "

      Laila:Someone

     Amjad: Name?

     Laila:You don't have to know "

      Amjad:"Ok,What are you doing now?

     Ganin tambayoyinshi sun'ki 'karewa yasa ta sauka ,aiko ba jimawa sega kira ya
shigo.'Canada'Ta gani jikin screen.Ajje wayar tayi ta'ki picking har ya gaji da kira,daga baya ma
tashi tayi ta sauka parlor ta kunna kallo.

          ★★★

   4:30pm yau ya tashi daga aiki, Laila tana parlour jin shigowarshi yasa tayi saurin mi'kewa ta
koma d'akinta.Tana shigowa yaga ba kowa a parlour sede ga TV a kunne ,hakan yasa ya gane
da tana zaune kallon wata'kila ko taji dawowarsa ne.

     Tana jin sanda ya shiga d'akinsa ,dan haka ta zauna kan gado aikin zama.

      1hr later,Knock! Knock! Taji bugu,tana daga shingid'e tayi saurin mi'kewa zaune zuciyarta na
dukan uku-uku.

    "Laila" Ya kira sunanta.

   'Kin amsawa tayi se wararo idanuwa take wata zuciyar tana ce mata ta bud'e 'kofar bathroom
immediately ta bud'e masa 'kofar seta shige bathroom,haka tayi ta sa'ke-sa'kenta.

     "Laila open this door"

     Hijab d'inta ta d'auka ta zurma ta ma'kale shi a jikinta, a hankali ta bud'e 'kofar ta ra'be daga
baya-baya.Tsayawa yayi daga bakin 'kofar bema shigo ba,wani card dake hannunsa ya mi'ke
mata,a tsorace tasa hannu ta 'kar'ba ba tare da ta d'ago sun had'a ido ba.

    Anniversary  Invitation ne wanda taga yau ne ranar zuwan 8:00pm aka rubuta a jiki,bata gane
nasu waye ba ita de ta karanta.Tana d'ago da kai taga har yana komawa d'aki dan haka ta
shigo ta rufo 'kofarta.

      "Ni naje nayi mey acan? wa na sani a wajen? Tare zamu?" Ta jero wa kanta tambayoyi.    

   Har bayan maghrib bata soma shiryawa ba seda taga ya turo mata text."Are you ready?"

    "No" Tayi reply.

     "What are you waiting for?"

     Bata sake wani reply d'in ba ta tashi ,wardrobe ta bud'e ta soma duba kayan da zata
saka,ganin zata 'bata lokaci ta ciro wani ba'kin abaya me golden duwatsu,nan da nan ta
saka.Powder ,lipstick da kwalli kawai ta sa ta fesa turare mey taushin 'kamshi,red mayafi tayi
rolling dashi.
     Wayarta kawai ta d'auka ta zira takalmi mey matsakaicin tudu golden ta samu waje ta
zauna.7:41 knock! Knock!

    Tsaye ta ganshi yayi shigarsa cikin dark blue suit ciki white shirt da ba'kin jeans ,gashin
kanshi yasha gyara se shining yake,turarensa mey 'kamshin gaske se dukan hancinta ake.

    "Ready?"

    "Uhm" Ta amsa ciki-ciki.

     "Let's go" Yayi nuni da hannu.

      'Kofar d'akin ta rufo tabi bayansa dan ta'ki bari su jera ,a haka har suka sauka 'kasa.A mota
shiru ba mey magana,laila ita tama kau da kai can tana kallon waje.Suna isa gurin mutane an
hallara ,ita de kallo take binsu dashi dan ba wanda ta sani,se gaisawa yake da mutane wanda
yawanci duk abokanan business ne.Wani table suka zauna kafin daga bisani ya tashi amsa
kira,bayan 'kan'kanin lokaci sega iyayen taro sun shigo wajen tare da baby d'insu wanda bata
wuce 3yrs ba sunsha 'kwalliya gwanin sha'awa,ana ta gaggaisawa dasu tana gani Amjad yaje
suka gaisa bata ankara ba taga sun nufo inda take.

     "Wayyo ni Laila" Ta fad'a a fili.

       Matar cikin fara'a ta soma mata magana Laila ma 'karfin hali tayi suka gaisa tayi musu fatan
alkairi,sede taga Nigerians ne kuma hausawa "how come's Amjad ya sansu?" Abinda ta
tambayi kanta kenan dan a iya saninta  dashi baida wani abokai.

   "Laila ko?" Macen ta fad'a.

  "Eh" Ta amsa.

   "Ni kuma Aisha,yau Allah yasa min had'u de"

    "Gaskiya kam" Cewar Laila.

     Sauran ba'ki da suka zo gaisawa da Aishan yasa suka katse hirar da suke,Amjad d'in ma se
hangoshi tayi daga nesa yana gaisawa da mutane.

      Farouq d'an abokin Dad ne yawanci inde suka zo Nigeria suna zuwa gidansu,shekararsu
hud'u kenan da yin aure ,duk a Nigeria shikad'ai ne wanda Amjad zece suna abota ,bayan shi
baida wasu abokai.

      Laila Tana zaune Aisha tazo "Nan hayaniya,taso mije ciki" Ta taso laila dan ta lura kamar
laila bata son hayaniya.

      Cikin gidan nasu ta shiga da laila ta kaita wani parlour."Bari gani zuwa".Ta fad'a tare da
barin parlourn.

    Kitchen ta shiga d'aya daga cikin masu aikinta tasa ta kawowa Laila abinci,kiran waya da akai
mata yasa ta fita zuwa wajen ba'kin .Ita kuwa mey aikin ganin aiki ya mata yawa yasa tasa wata
'yar uwarta da tazo daga 'kauye ta zibawa Laila.

     Kai tsaye ta bud'e wani plate dake kan drawer ganin friedrice tasha chicken akai ga kayan
had'i burjik ,dama ma'kuiyaciyace  yasa kawai tasa spoon ta d'ora plate d'in a tray tare da d'ora
robar ruwa da orange juice ta kaiwa Laila.

     Laila dama tun yamma take jin yunwa,ba 'bata lokaci ta bud'e plate ta soma ci,sede taji
abincin taste d'in ba dad'i cabbage d'in yayi wani iri gashi ba zafi ita a tunaninta ko hucewa
yayi.Haka ta lalla'ba taci, naman ma ba sosai ta iya ci ba,rabi taci ta rife plate d'in.Leman ne ma
tasha da yawa ta kora da ruwa.
       Wayarta ta kunna Tana d'an duddubawa a haka lokaci naja har taci fin 30min.Sede kuma
tun bayan cin abincin ta fara jin suka a cikinta kad'an-kad'an yana murd'awa.
     

      *Let's stop here,yau na fita hakannan na daure nayi  typing coz bana so na barku kuna
jira.Don't forget to comment,vote and share.Love u all💋*

*Dijensy❤*
    

       

  

    

    
      

    

   

   

    

    

           

       

   
   
🌼🌼 🌼🌼


💦 💦


*AMJAD*


💦 💦



🌼🌼 🌼🌼


*WRITTEN BY DIJENSY*

*WATTPAD:@dijensy*

1⃣9⃣-2⃣0⃣


        Wani irin murd'awa cikinta ya hau yi,nan take gumi ya soma keto mata ta rasa abinda ke
mata dad'i wayar ma ajje ta tayi gefe.Tashi tayi a rud'e ta nufi inda taga mey aikin ta shiga,a
kitchen ta tarar da ita tana wanke-wanke.Laila tambayarta tayi toilet tana ta zufa.D'aki ta rakata
wanda yake d'auke da toilet a ciki,da sauri-sauri laila ta fad'a  ciki.

     Minutes later ta dawo parlour gwiwoyinta sun fara sanyi gashi cikin har yanzu be dena
hautsinawa ba,wayarta ta duba taga 3missed na Amjad. Bata ko zauna ba ta fita,a chan 
farfajiyar gidan ta hangeshi yana zaune a table shi kad'ai jama'ar wajen ma sun fara raguwa.A
hankali ta taka zuwa inda yake,sede ta 'karaso ya kula da ita.
    "Where have you been?"

     "Gani na fito ai"Ta fad'a.

      Mi'kewa yayi tsaye ya fara tafiya tana biye a bayansa Farouq da Aisha suka 'karaso inda
suke.

     " Tafiya?"Ta tambayi Laila.

    Laila cikin ya'ke ta amsa da "Eh"

    "Toh bari na kar'bi numbernki".

     Numbernta ta fad'a mata a take tayi flashing itama Laila tayi saving, har waje suka rakosu ita
de Laila kawai basarwa take cikinta ba abinda yake se hautsunawa ta 'kagu su koma gida.

      Tunda ta shiga mota bata ce 'kala ba,gani take kamar ba tu'ki yake ba har wani le'kawa take
tana ganin speed d'in."Mtchww" Tayi tsaki ba tare da ta sani ba.

    "Are you alright?" Ya tambaya.

     Kai ta kad'a alamar "eh" se kad'a 'kafa take tana tapping cinyarta."Innalilahi wainna
ilaihirraji'un"Ta fad'a  a ranta ganin traffic light ya tsayar dasu.

    Da 'kyar ta samu ta iya jurewa har suka koma gida,cikin sauri ta fad'a toilet ko 'kofar d'akin
yau bata rufe ba.Daga dawowarsu zuwa yanzu Laila ta shiga toilet yafi sau uku,gwiwoyinta
gabad'aya sunyi sanyi da'kyar take takawa.Gashi batasan inda zata sami magani ba,lokaci
guda tayi zuru-zuru jinta take kamar kara dan tsabar rashin 'kwarin jiki.
       11:29pm Ring!Ring! wayar ta tayi 'kara lokacin tana toilet har 3 missed call batai picking ba.

   
     Amjad yana d'akinsa dede lokacin yake shirin kwanciya wayarsa tayi 'kara,koda ya duba
yaga Farouq.

      
     Knock! Knock! Ya 'kwan'kwasa 'kofar d'akinta shiru,handle d'in ya murd'a ya shiga beganta
ba.

     "Laila" Ya kira sunanta.

    Tana shirin fitowa taji ya kira sunanta ,zaro ido  tayi ido tana mamakin jinsa a d'akinta a irin
wannan lokacin.

     "Laila ,come on open the door"

       Tsit kake ji ko motsi ta'ki yi gashi tsaiwar ta isheta,kan bathtub ta samu ta zauna ta dafe 
cikinta.

     "Laila,can't you hear me? open the door now stop pretending I know everything"

     "Mey? Waya fad'a masa? Yasan..." Ta dafe kai shikenan tonon silili.

    "Laila don't let  me  open it myself, you know I have a spare key right?"

     "Innalillah" Jiki ba 'kwari ta mi'ke tsaya a daddafe ta 'karasa jikin 'kofar gashi jikinta kayan
bacci ne riga da wando  kusan ¾,inda Allah ya taimaka ma rigar ta hauro kusan
cinya,d'an'kwalin kanta ta ware yadda ze sakko 'kasa , a sanyaye ta bud'e 'kofar kanta a 'kasa.

       "Laila" Ya kira sunanta.

      A hankali ta d'ago da kanta kallo d'aya tayi masa ta maida kanta 'kasa,se jan mayafin take
tana kare 'kirjinta.

    "Uh...you need to see a doctor"

       "I'm fine" Ta fad'a murya 'kasa-'kasa.

       "You're not,you better stop pretending I know you're not ok they explained everything to me,
you ate a spoiled food"

     Shiru tayi bata musa masa ba,ta kasa d'ago da kai dan tsabar kunya a ranta tana da tasanin
cin abincin.

     "We need to go now".

      Tana jin kunya ta wuce zuwa wardrobe ta ciro hijab d'inta ta zira, wata doguwar riga ta
d'auka tana so tasa gashi yana tsaya a d'akin se so take ya fita amma yayi burus sema folding
arms da yayi yana kallonta.'Karfin hali tayi ta ri'ko doguwar rigar a hannu ta wuce bathroom
yana kallonta.

     Tana fitowa ya tafi d'akinsa ya d'auka key ya fito,a sitting room ya taradda ita zaune kan sofa
dan ko tsaiwa ta kasa.

 

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
google.com, pub-9213700357025247, DIRECT, f08c47fec0942fa0