Showing 15001 words to 18000 words out of 60755 words

Chapter 6 - Amjad Complete Book By Dijensy

Dijensy   

17 Jul 2026

652

  "Babban riga"Cewar Zakia tana dariya.

     " Fools leave now!"

      "Don't you like it?"

       Be amsa su ba ya shige bathroom ya doko 'kofar,a wardrobe sika saka  tukun suka fita
suna dariya.

      Ta 'bangaren Laila kuwa ko breakfast bata samu tayi ba 10am suka fita gidan 'kunshi ita da
Maryam.Jan lalle akai mata shima d'in bata bari yayi ja sosai ba ta wanke ba yadda ba ai da ita
ba amma ta'ki ji,ba'ki kuwa tace bata so Maryam tana ji tana gani aka hanata ba'ki se jan ta
samu itama aka yi mata amma yafi na Laila turuwa.Daga gidan lalle suka juyo gida.
     "Ina 'kunshin yake?" Mami ta tambaya.

      "Gashi" Bako kunya ta mi'ko hannun.

      "Yanzu wannan shi kike kira da 'kunshi,shi kuma ba'kin fa?

     " Mami wallahi wankewa tayi kafin yayi,ba'kin kuma ta hana ayi mana "

    "'Karya take.."

     "Sena doka miki ta'baryarnan akanki idan baki rufen baki ba sakarya,ki nuna wa duniya cewa
ba'kyason auren sesi maganin hakan kinji" Mami ta fad'a cikin 'bacin rai.

    Daga mami se wasu 'kannenta biyu a tsakar gidan sauran ba'kin suna d'aki."Ke Laila meyasa
kike haka ne,so kike ki 'batawa mahaifiyarki rai?"Wata 'kanwar Mami ta fad'a.

     Kai ta girgiza alamar "a'a hawaye suna biyo kumatunta se murza yatsa take ta sunkuyar da
kai.

     " Toh kidena irin haka kinji koh"

     A hankali ta gid'a kai dan bazata iya magana ba,d'aki ta shige ba mutane da yawa  ta juya
bayanta ta dasa sabon kuka dad'i da yunwa da take addabarta rabonta da abinci tun jiya da
rana taci abincin kuma ta'ki.

       9:12pm an gama tsara mata make-up tayi had'uwa iya had'uwa tasha farar gown se walwali
take ga sar'karta mey farin stones ,tasa hill shoe tunda take bata ta'ba sa hill shoe kamar
wannan ba se tsoron mi'kewa take,daga ita se Bahijja 'kawarta suna jiran ango.

        A wajen biki kuwa kowa ya hallara Zakia,Shaheed suna daga mota Maryam da Nusaiba
duk sunyi kwalliya sun fito, Amarya da ango suke jira su iso su taka musu baya.Sun kwashe
kusan 1hr a haka,Mom da Dad kuwa suna ciki dasu Mami.

     
       Mom fatan ta Allah yasa karya bata kunya dan sanda ta  fito daga gida ko kaya be ciro ba
balle yasa.Ganin an sake shafe 30min basu ba alama ta kirashi shiru be d'aga ba.

      Driver dede wajen kwalliyar yayi parking kamar yadda Mom ta bashi address.Maimakon ya
kirata da kansa a'a seya bawa driver wayar yayi mata magana.

      "Hello,madam gamu a waje da...da angon"

      Take bugun zuciyarta ya 'karu."Tir'kashi baze iya magana dani ba"Ta fad'a a ranta.

     "Ya?angon ne?" Bahijja ta tambayeta.
    
       "Eh" Ta amsa a sanyaye.

     Gwiwa ba 'kwari ta mi'ke,kafin su fita ta sauke mata net viel d'in a fuskarta,da'kyar take
takawa saboda rashin sabo da takalmin me tsaho hakan kuma seyayi mata kyau  yanayin
tafiyar.

      Driver ne ya bud'e mata gidan baya 'kawar kuma ta zauna a gaba ,shiru motar bame ko

tari,ta kalli gefe ma ta kasa balle taganshi,'kamshin turare ne kawai yake tashi nata soft 'kamshi
shikam 'karfin nashi tararen ya danne nata.Be d'ago ya kalleta ba dan wayarsa ce a hannunsa
amma yana kallonta ta gefen ido fuskartace de baze iya gani ba,'kawa kuwa besan da zamanta
a motar ba ma.
     Suna isa wajen Zakia suka fito se murmushi take ,ganin  Amjad sanye da babbar riga yasa
su kallon juna da shaheed dan a zatonsu baze saka ba,basu san irin faman da Mom tayi dashi
ba kafin ya yarda zey saka.

     "Handsome Amjad" Ta fad'a.

       Laila kuwa tana gefe separate da inda yake,Maryam da Nusaiba suma suka 'karaso
wajen,se lokacin Zakia ta farga ashe fa ga amarya.Ri'ko hannunta tayi ta matso da ita gefensa
daf,wata uwar harara ya galla mata amma tayi kamar bata gani ba Laila bata san ma yana yi
ba.Shaheed a take ya Shiga yi musu pics kala-kala,seda suka tabbatar sinyi well arranged
tukun Amarya da Ango suka shiga.

     "MashaAllah" Mom ta fad'a ta kasa dena murmushi.

       Mom dakanta ta d'age mayafin fuskar Laila ,nanfa akai ta pics  sede fa ba annuri a tattare
da Amjad gara ma  Laila friends suna d'an sata murmushi,shi gabaki d'aya babbar rigarce yaji ta
isheshi kamar ya 'kwa'be ga hula ma gumi ya tarar  masa a gashinsa.

      Taro anyi angama lafiya kowa ya tafi,driver ne ya kai amarya tare dasu Maryam Amjad kuwa
su Shaheed ya bi Mom suka tafi da Dad.

     Yana isa gida ya yaye rigar tare da wurgar da hular gefe,yana yin shower ya kwanta sanda
Mom ta shigo ta tarar har yayi bacci.

     Laila ko kayan bata gama cirewa ba  ta 'bingira bacci se cikin dare ta farka tukun ta cire.

       The next other day aka d'aura AMJAD da LAILA akan sadaki 100k,tun lokacin da aka ce an
d'aura aure Laila take kuka har ta gaji da zubar ta hawaye se sheshshe'ka take,daga baya ma
satar jiki tayi ta tafi gidan Kawu Yunus tayi kwanciyarta idan aka tambayi Nusaiba setace ta tafi
chanja kaya.Seda Mami ta kirata a waya tukun ta dawo,nan yayyin mami suka yi mata nasu
fad'a maimakon tayi kuka 'kandas dan hawayenta ya gaji da zuba sede kukan zuci.8:30pm aka
kai Amarya kuka ba iya su Maryam ba hatta Mami ma,Laila (Taya za'a ce ita kada tayi,tell me
how?)

*Dijensy❤*
     

   

      🌼🌼 🌼🌼

💦 💦

*AMJAD*


💦 💦

🌼🌼 🌼🌼



*WRITTEN BY DIJENSY★*

*WATTPAD:@dijensy*


🅿 0⃣6⃣


      8:46pm,mutanen dasu ka kai amarya ba wani yawa ne dasu ba,cikin 'kan'kanin lokaci kowa
ya kama hanya se Bahijja da Maryam su d'in ma ba zaman sukai ba 9:30pm nayi suka tashi
zasi tafi,Laila se ro'konsu take kar su tafi dole ta ha'kura tana ji tana gani suka tafi.

       A take ta fara jin tsoro jin tsit,ganin da gaske ta bar gida ta sake saka wani kukan har seda
ta gaji kanta ba abinda yake se ciwo.10:03pm ta gani lokacin da ta kalli agogon dake d'akin,se
yanzu ta kalli ma irin d'akin ta waiwaya can ta waiwaya nan duk irin kyawun d'akin da kayan
dake ciki ba birgeta yayi ba komai duhunsa take gani,ganin lokaci yana sake ja ta tashi.'Kofa
data gani daga can side na d'akin ta nufa ,koda ta murd'a taga  bathroom ne 'kayatacce,seda ta
dawo ta bud'e wardrobe ta dubi wata doguwar riga na bacci har 'kasa ta d'akko.

      Hijab ta soma lalubowa amma bata gani ba,wani mayafi ta samu mey d'an nauyi ta d'akko ta
shiga bathroom, bayan data samu gu ta sa'kale kayan seta tsaya dube-duben bucket na
wanka.Babu shi ba alamarsa haka buta ma balle kuma mod'a.

    "Mtchww!" Tayi tsaki.

   Jacuzzi ta tsirawa ido tana tunanin ta ina zata soma amfani dashi, bathtub d'in ta samu ta
'ko'karta ta had'a ruwan  tana la'kai-la'kai kamar bazata shiga ba,se can ta samu ta shiga ,d'aya
daga cikin shower gel d'in ta d'akko da sponge tayi  using, se bayan 17min tukun ta fito already
ta zira rigarta sauran kayan kuma ta ninke su tasa a wardrobe.

    Kan mirror ta duba wayam ba kayan shafawa,se can data duba drawer tagansu a
jere.Mayukane wanda bata ta'ba shafasu ba,d'aya-bayan d'aya ta bisu tana karantawa yawanci
lighten lotion ne da'kyar ta samu wani mey dama dama tukun ta shafa  ita wai bazatai bleaching
ba😂 komai ta maidashi muhallinsa ta dawo kan gadon ta zauna tare da d'ora hannayenta kan
gwiwoyinta.Se yanzu tunanin wayarta ya fad'o mata ,mi'kewa ta sake yi ta bud'e wardrobe d'in
daga 'kasan kaya ta d'akko ta kamar inda Maryam ta ajje mata.

    "Toh wa zata ma kira?" Ta tambayi kanta.

   Wata zuciyar tace kiyi game,aiko snake ta hau yi lokaci yana taja.

  *Amjad*

       Mom da ta shigo d'akinsa dan tana da tabbacin be tafi ba ,baki ta saki tana kallonsa yana
kwance abinsa bacci yake kamar ba gobe.Ba halinsa bane bacci da wuri amma dan wula'kanci
yau shine tun 9:30pm ya kwanta har 10:36pm.

     "Amjad"

      Seda ta 'karasa tai tapping shoulder d'insa tukun ya d'anyi motsi.

    "Amjad,wake up!"

     "Mom what?"

      "Do I have to tell you?"

        Yana la'kai-la'kai yatashi zaune,yana wani mirza idanuwa.

    "Amjad, do I have to tell you what to do ,it's almost 11pm.."

     "Mom you're sending me away,can't believe it you're sending your own son"

     "No I'm not, how will I send m beloved son away ?"

     "I'm tired I need to rest"

      "Rest!" Ta maimaita ,dariya ma abin ya bata tana kallonsa.

    "Your Dad doesn't know you're here"

     "I gerrit ,don't worry I'm leaving now"Ya fad'a tare da mi'kewa.

     Kallo kawai ta bishi dashi tana girgiza kai,watsa ruwa yayi ya fito ya saka wata black T-shirt
mara nauyi tare da black jeans.Dad yana d'aki besan abinda ake ba har Amjad ya fito,Mom har
bakin mota ta rakoshi su Shaheed daga nesa bakin 'kofa suna waving hand yadda sikeyi
za'asan cewa na tsokana ne shide banza yayi musu Mom a cikin ranta tana jin zafin rabuwa da
d'anta kawai de daurewa take.

      Yana ji tana cewa ya gaisheda Laila amma yayi kamar beji ba ya shiga motar driver ya jasu

     Be bari ma ya shigo dashi har ciki ba daga bakin gate yace ya ajjeshi,a parking space ya
tarar da Marcedes Benz black da Dad ya saya masa ,kallo d'aya yayi mata ya wuce ciki.

       Se yanzu ya sake 'karewa katafaran gidan kallo,direct room d'insa ya wuce wanda  yake
opposite da Laila.

     Yana shiga ya bud'e wardrobe yaga neat kayansa da sauran abubuwansa ,komowa yayi kan
gadon ya d'auki wayarsa ya soma Zombie kill (game),laptop d'in nashi ma ya mance a gida se
yanzun ya tuna.

     Laila kuwa bacci yayi gaba da ita wayar ma a gefe ta yasar.

               ★★★

     6:23am,a gigice ta tashi daga bacci sakamakon mafarki da tayi tana kuka.Agogon d'akin ta
duba taga har subh ya shige ,a kasalance ta mi'ke ta fad'a bathroom tayo alwala ta tada
sallah.Bayan ta idar tayi azkar sannan taja jiki ta jingina jikin gadon tana tunanin sabuwar
rayuwar data tsindima."Koh ni kad'ai na kwana a gidannan?"Ta tambaya a ranta.
      Amjad  a 'bangarensa kuwa bacci yake cikin kwanciyar hankali babu mey tashinsa yau.

     Se 8:16am ya farka daga bacci, se bayan ya idar da sallah ya tuna da zaman wata
Laila,tunani ya shiga yi yaje ya dubata ko kuwa.Daga baya de ya yanke shawarar sauka
downstairs.

     Laila daga d'aki tana jiyo 'karar rufe 'kofarshi,sad'af-sad'af ta tashi kamar wata mara gaskiya
ta la'be jikin 'kofa tana jiyo takunsa har ya sauka.Hakan ya tabbatar mata anan ya
kwana.Kitchen ya shiga dan neman abinda zeci ,seda ya gama dube-dube 'karshe de ya 'bige
da tea da toasted bread dan shi ba gwani bane wanjen wani yin abinci hakan ma ba 'karamin
dagewa yayi ba ya saba sede Mom ta had'a masa.

     Daga kitchen kuma ya fito harabar gidan ya zauna daga kan kujera dake kewaye da flower
plants ,wayarsa ya danna wa Rosie kira karo na farko bata d'aga ba se ana biyu.

     Ita a tunaninta aiki ne ya dawo dashi Nigeria kamar yadda ya fad'a mata dan be gaya mata
asalin gaskiya ba.

     "I missed you" Ta fad'a daga d'aya 'bangaren.

      "I missed you too"Shima ya fad'a.

      Yanda yake fara'a za'a San cewa ya mance da duk wani damuwarsa ,best moment of his
life yaga yana hira da love of his life Rosie.

         
     9:30am ,yunwa ta fara addabarta harta kasa daurewa se shawara take kota fito,sede ita
ganinsa ma bata son yi balle har magana ta had'asu.

     " Toh a ina zan samu abinci ma?"

     "Kitchen mana" Zuciyarta ta amsata.

     Dama mayafinta a yafe yake dan haka fitowa kawai tayi se sand'a take batasan ko ina ba
,'kofa dake opposite da d'akinta ta kalla se gefe ta hangi steps dan haka ta sauka 'kasa nan
d'inma ta gama kalle-kalleta tayi can ta yi can har ta samu kitchen.Sosai ya tsaru ita kanta ya
birgeta mug ta gani empty data duba taga alamar ansha tea dashi."Tea yasha kenan,dame ya
had'a?"

      Ta'be baki tayi ganin ba mey amsa mata ta nufi fridge inda taga kayayyaki birjik se wanda ta
za'ba amma ba'kunta tasa taji bata sha'awar cin kayan ,cikin locker ta hangi cornflakes ta had'a
abinta ba wani 'kosar da ita yayi ba.

       Ta fito daga kitchen tana shirin komawa sama sega Amjad yana shigowa.Tsayawa yayi
yana kallonta itama hakan daga bisani ta soma hawa bene kanta a sunkuye.

     "Hey"

     Chak ta tsaya ba tare da ta waigo ba.

      "What is your name?"Taji ya tambaya.

      "Kutt! Raini" Ta fad'a a ranta.

      'Kin juyowa tayi har seda ya 'karaso inda take tukun ta juyo."I'm asking you,what is your
name?"

     "Laila" Ta amsa ciki-ciki ba tare da ta kalleshi ba.

 
      "Why are you here?"Ya sake wata tambayar.

      "Nima ban sani ba" Yadda tayi maganar da sauri.

      Anzo wajen wannan yaren da baya son ji shi zatayi masa?

     "Talk to me in English"

      Yitai kamar wata kurma tana tsaye batace komai ba.

     "I'am talking to you" Yanda yayi maganar cikeda 'kosawa.

      Anfi 2min batace komai ba kuma bata tafi d'akin ba.

    "She don't understand English? fuck up!"Yayi maganar a hankali.

     Taji sarai amma tayi kamar bata fuskanci mey yake fad'a ba.

    " Aiko inde turanci ne ka dena jinsa inde kana nan,Hausa ce ba fashi"Ta fad'a a ranta.

     Wucewa yayi ba tare da ya sake wata maganar ba tana ji ya doko 'kofa.Itama d'akinta ta
shige ta zauna wayarta dake gefe ta d'auka ta kira Mami.

     "Mami ina kwana"

     "Lafiya lau"

      "Ina su Maryam? Anjima zasu zo?

       " A'a suzo siyi miki meh? bade yanzu ba"Mami ta fad'a .

       "Mami meye a ciki idan sunzo"

      "Bafa zasu zo ba,ki gaida Amjad d'in ba'kina zasi tafi se anjima"

    Bata kuma wani maganar ba mami ta katse wayar.Wata 'kwallar takaici ce ta zubo mata
ganin ba ta ita ake ba basusan halin da take ciki bama.

    Kuka ta shiga yi harda sheshshe'ka cikin 'kan'kanin lokaci tayi bacci.

     Bata yi 20min da kwanciya ba taji 'karar kid'a a gigice ta farka kanta yayi mata wani mugun
nauyi zuciyarta na bugu da sauri-da sauri.

       Amjad da gayya ya 'kure volume d'in so yake kawai ya takura mata.

     "Innalillahi wannan yana kuwa da hankali?" Ta fad'a a fili.

     Baccin da batai ba kenan,tayi game har charge d'inta ya 'kare.Zama tayi-tayi har 'karfe 1pm
tukun ta tashi tayi sallah,'kugin da cikinta yake ne yasa ta kasa sukuni.

      Dole ta fito ta sakko 'kasa kitchen, dube-dube tayi tayi a  locker bata ga komai ba har ta
d'akko bread ta lura da wani corridor koda ta duba taga 'kofa tana bud'ewa taga kayan abinci
taff a ciki.

     Nan da nan ta d'ibo dankali  ta fere a take tayi blending pepper cikin 'kan'kanin lokaci ta
had'a faten dankalinta se 'kamshi yake ta cika 'kasan da 'kamshi.

      Stool taja taci abinta a kitchen ta kora da juice yanzun taji normal ,'yan kwanukan datai
amfani dashi ta d'auraye.Tana fitowa daga kitchen kanta a sunkuye taji tayi tuntu'be da mutum.

          *Don't forget to comment,vote and share*💋

*Dijensy*❤

   

    
    

  

    



    
       

    

      

        
🌼🌼

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
google.com, pub-9213700357025247, DIRECT, f08c47fec0942fa0