Showing 33001 words to 36000 words out of 60755 words
rayuwarsu da suka shafe tare ya shiga yi,ko a mafarki idan aka ce Rosie zata ci
amanarsa baze yarda ba amman yau ya gani da idansa.
Yafi 20 min yana abu d'aya wayarsa da tayi ringing yasa ya dawo daga duniyar tunanin
daya tafi.
"Mom" Ya gani a jikin screen.
Ta kira har sau uku amma ya'ki d'agawa,lokaci guda yaji ciwon kai ya kamashi.Da 'kyar ya
samu ya iya komawa gida, image d'inta ya'ki gushewa daga idansa.
Mom ganinsa ya shigo gida tayi sauri ta 'karasa inda yake."Son, where have you been? are
you ok?"
Kai kawai ya kad'a yana 'ko'karin cire jacket d'inshi.
"Amjad, you're looking sick" Ta fad'a tana dafa kafad'arsa fuskarta d'auke da damuwa.
"Mom ,I just need to rest"Yayi 'ko'karin fad'a.
"Ok ,go to your room I will prepare your a meal immediately you woke up"
Yana shiga d'akinsa ya rufo 'kofar,yana ciro wayarsa daga aljihu sega kiran Rosie.
"Baby boo" Ya bayyana a screen.
Gabaki d'aya wayar yayi switching off ya cilla gefe,ya fad'a kan gadon ya rufe idansa trying to
force him self to sleep.
An hours later,2:30pm ya farka har lokacin kanshi be dena ciwon ba,tashi yayi ya shiga
bathroom ya watsa ruwa yayo alwala ya tada sallah.
Knock! Knock! Mom tayi knocking ,ganin be bud'e ba ta murd'a handle ta shiga,sallah ta tarar
yana yi haka yasa ta koma.Chicken Spaghetti ta dafa mashi tayi arranging,tana gamawa ta
koma sama ta kirashi.
Ga abincin yasa a gaba amma ya kasa ci ,Mom data san Chicken spaghetti ne favorite d'insa
tayi mamaki ganin ko fork d'in be d'aga ba.
"Amjad, don't you wanna eat?"
"I lost my appetite"Yana fad'ar haka ya mi'ke ya bar wajen.
" Am.."Bata 'kare ba taga har ya 'bace mata daga gani.
★★★
Laila
7:12pm suna d'aki ita dasu Maryam se hirarsu suke ta mance da wani Amjad,idan Mami ta
tambayeta suna waya da Amjad setace eh,wani lokacin har alarm take sawa idan yayi ringing
setai pretending kamar kiran waya ne.
Amjad kuwa cikin dare 11:00pm sam ya kasa bacci kawai juye-juye yake akan gado daga ya
rufe ido Rosie yake gani da wannan guy d'in,tashi yayi ya d'auko wani box a 'kar'kashin
gado.Hotuna ne ciki na Rosie harda wanda sukai tare dashi tun suna teens daga gefe kuwa
teddy ne 'karami mey heart a cikinsa wanda Rosie ce ta bashi wani lokaci da yayi birthday.
D'aukansu yayi ya tarkata duka ya fita can backyard ya cinna musu wuta yana kallo har suka
'kone ya watsa tokar a dustbin.Hatta phone d'insa babu wani abu na Rosie daya bari pictures
nata na musamman daya tanada musu folder seda yayi deleting,seda ya tabbata ba abinda ya
ragu nata a wayarsa ya iya samun yin bacci.Amjad sam be iya so ba haka be iya tsana ba,ya
tsani yaudara mutum ne mey zafin kishi ko Zakia idan ya ganta da wani classmate bama
boyfriend ba seya ji haushi.
"I hate you like hell"
"I hate you forever,I never wanna see your face again"
Idansa a rufe yake fad'ar haka ,firgit! Ya farka ,se lokacin ya lura 5:54am yayi,nan ya tashi
yayi sallah.Yana idarwa ya sauka 'kasa "Morning"
"Morning" Mom ta amsa.
Da 'kyar ya samu ya iya yin breakfast d'in, data tambayeshi meyake damunsa ya'ki fad'a.
★★★
Amjad ko kwana uku beyi ba ya koma Nigeria dan ji yake kamar a kan 'kaya yake a
Canada,sede ba wanda yasan Nigeria ya koma 'karya yayi musu yace Ethiopia yaje daga can
ze wuce Nigeria.
Yana komawa Nigeria ya cigaba da zuwa aikinsa dan so yake ya mance da komai har
'karawa kansa lokaci yake kafin ya tashi se wajen 5:30pm,daya koma gida ma baya hutawa
wani aikin ze tsiri yi yaita dube-dube a system, a 'yan kwanakin da akai har ya rame da an
ganshi za'a san yana da damuwa.
Laila kuwa cikin kwanciyar hankali take exam d'inta,ji take kamar ta komo gida kenan dan
ko maganar komawa bata yi.Seda suka kwashe 2weeks da 'yan kwanaki suna exam,yanzu anyi
hutu na 'yan weeks kad'an.Yanzu ta komo hawa online sosai ba kamar sanda suna exam ba
idan ba abu daya shafi karatu ba bata bud'e data.
Yau bayan sun gama cin abincin dare,su Maryam suna parlor suna kallo ita kuwa tana d'aki
se chat d'inta take hankali kwance.
9:45pm,yana d'aki be jima da dawowa ba daga restaurant kullum seya je yaci abinci
acan,yana watsa ruwa ya d'auka waya ya hau whatapp chat ,abinda ya dad'e beyi ba.Contact
ya shiga yana ta duba numbers ,yazo N letter idansa ya sauka kan Nigeria,daya duba kuwa
yaga tana online. Profile d'inta ya shiga viewing inda yaga profile picture d'inta dake d'auke da
photo d'inta tayi rolling da red mayafi kuma fuskarta tasha make-up sede ba duka ta d'ago
fuskar ba ta d'an sunkuya inba wanda yasanta ba baze gane itace ba.
"Hi" Yayi sending da 'kyar dan ya dad'e kafin ya iya turawa.
Tana cikin chat taga "hi" data dubi number d'in taga na Amjad ne ,tafi 10min kafin tayi reply
da .
"Hello" Tayi reply.
"Why are you chatting at this time, aren't you suppose to be reading ?"
"Exam is over ,hutawa zanyi"
"What did you mean by those last words?"
"You don't need to know"
"Ok,can you please change that profile pic with something better? coz you're looking ugly"
"I choosed it myself and I like how I'm looking"
Murmurshi abinda ta fad'a yasa shi."But I don't like it"
"I don't care"
"Ok,where are you now?"
"Home"
"You're Lying, Mom told me everything"
"Your house is not my home, I'm referring to Mami's house"
"Good for you,you're soon coming back"
"No"
"You must"
Laila: "When are you coming back?"
Amjad:" Do you care?"
Laila: "No"
Amjad: "Then why did you ask?"
Laila: "Just wannan know"
Amjad: "I knew you missed me"
"Wallahi a'a"
Amjad:"Lier"
Laila:"I'm not"
Amjad:"You are!"
Daga haka bata sake tura wani abu ba tayi banza dashi ta cigaba da sauran chat
d'inta. Amjad kuwa da tun tini dama da ita yake chat in banda it a ba kowa,ganin shiru ya sake
yi mata magana.
Amjad:"Laila"
Laila:"Mene?"
Amjad:What is your problem?
Amjad: What is the meaning of "mene" ?
Laila :"It means "what"
Amjad: What of "why" Ya sake tambaya dukda kuwa ya san ma'anar kawai jan magana be.
Laila: "Meyasa"
Amjad:I gerrit,what of "Ni nace" You often say the words.
Laila:I'm not a teacher, I'm going to bed"
Amjad:í ½í¸� who care to learn your language? disgusting!
Laila:Eh d'in chat d'in ma baza a sake yi dakai ba"
Amjad:Rubbish!
Sauka tayi daga chat d'in ta zira charger a wayarta tayi shirin kwanciya,tana kwance chat d'in
da sukai yana ta dawo mata wani abun ya bata dariya wani ya bata haushi.Se to 11:30pm tayi
bacci.
Ta 'bangaren Amjad kuwa ganin ta sauka ya koma Instagram,"Lai-mus" sunan da take
amfani dashi a insta.526 followers,jiyai ya damu da yaga followers d'in kad'an-kad'an yana
scrolling jama'a iri-iri maza sunfi ma yawa ,post d'inta ya koma dubawa yaga har 27 sede photo
d'inta a ciki 3 ne sauran duk qoutes pic ne,+200 yaga like da + 62 comment kan wani pic nata
da niqab nema a fuskarta idanuwanta ne kawai suka fito wanda sunsha kwalli rad'au.
Nan take yaji wani Abu ya tokare mashi a ma'kogoro,musamman wani comment dayaga
wani guy yayi."Baby I love your sparkling eyesí ½í´¥í ½í´¥"
Instagram d'in ma fita yayi ya ha'kura da chat d'in,se jin haushi yake ,chat d'in da sukai ya
shiga ya soma dubawa a haka har bacci ya d'aukeshi.
Washegari
Laila bayan tayi breakfast su Maryam dake gida kasancewar yau Saturday basu je
makaranata ba suna parlor suna kallo tare.
"Laila" Mami ta kirata daga d'aki.
"Na'am" Ta amsa tare da mi'kewa.
"Mami gani" Ta fad'a bayan ta shiga d'akin.
"Ke ashe Amjad d'in ya dawo baki fad'a min ba" Cewar Mami.
"Uhmm?" Ta waro ido tana kallon Mami.
"Ehyi,yanzunnan muka gama waya da mamansa take fad'a min jiya ya dawo"
"Uuhm"
"Toh yau zaki koma kenan?"
"A'a Mami ba yau ba" Ta diririce harda kad'a hannu tana maganar.
"Se yaushe kuma?"
"Uhnmm wani satin"
"Kin manta wata shekarar,ke mijin naki ya dawo ma ba ko d'an 'kunshi single kamar
namiji"
"Ni bana so"
"Aiko anjima ki shirya Maryam ta raka ki ,hannu kamar muciya"
Ring!Ring tajiyo 'karar wayarta daga d'aki,haka yasa ta dakata da maganar da suke da
Mami ta tafi d'aukan wayar.
Numbern Amjad ta gani jikin screen aiko ta'ki picking bayan kiran ya 'kare ta saka wayar a
silent.Seda ya kira sau uku ganin batai picking ba dole ya ha'kura.
Wajen 3:30pm Mami tasa Laila zuwa gidan 'kunshi,haka bata so akai mata ja.Ba 'karamin
kyau yayi mata ba yayi maroon a farar 'kafarta ,a hanya zira hannayenta tayi a hijab tana
karewa dan jitake wani iri.
"Toh baga shi ba ,amma da sekace namiji" Mami ta fad'a sanda suka shiga gidan.
Ita de bata ce komai ba ta wuce d'aki,ita kanta se kallon hannun take yana birgeta.Idan ta
tuna da batun komawa gidan Amjad kuwa setaji 'bacin rai.
"Ko bazan 'kara sati ba sena yi kwana hud'u kafin na koma" Ta fad'a a ranta.
Amjad ganin bata d'aga kiran nashi ba seya hau WhatsApp ko ze ganta online amma
shiru ba alama, tashi yayi ya fita daga gidan ,dan yanzu idan yana zaune shi kad'ai tunanin
Rosie ne yake addabarsa.
Har ya dawo gida ya sake dubawa ko ta hau online amma shiru se ha'kura yayi ya kwanta.
Itama ta 'bangarenta tana so ta hau chat amma kuma tana gudun kar yau ma yayi mata
magana ,shiyasa ta ha'kura da chat d'in ta ajje wayar.
★★★
Yau tun 4:30am ya farka bacci amma ya kasa komawa sakamakon mafarkai marasa dad'i
da yayi tayi wanda duk akan Rosie ne.Asuba nayi ya tashi ya fita masjid,koda ya dawo be koma
bacci ba ,wayar tashi ya sake duba last seen d'inta ko zega ta hau jiyan amma still bata hau ba.
Laila kuwa yau se 9:53am ta tashi daga bacci tun bayan sallahr subh,hakan ma seda Mami
ta tashe ta da kanta.
"Yini zaki a haka? sekace kasa"
"Mami goma ma fa batai ba" Ta fad'a tana murza ido.
"Kin ajje waya tun d'azu ana ta kira"
Tana jin haka ta ayyana Amjad ne,bataso ba ta mi'ke ta shiga bathroom tayi wanka bayan
ta shirya tayi breakfast.Data duba wayarta kuwa 6missed call ta gani na kiran Amjad,ganin ta
gaji da ganin numbernshi ba suna ta shiga yi saving, sunan da zata saka mashi tayi ta
tunanowa.Ta san idan tasa Amjad gatsau da matsala dan su Mami zasu iya gani.
'Hus...' Ta fara seta goge."Hauka ma kenan".
'Na dole...'
"A'a"Ta goge.
Finally de tayi saving da " Canada ".
12:34pm suna kitchen da Mami suka ji knock,Fauzan yana d'aki ,Laila ganin ta fi kusa da
'kofar yasa ta tafi bud'ewa.
Tsegege ta tsaya tana kallonsa shima kallon nata yake cikin ido hakan yasa tayi sauri ta
kawar da idonta.
*Don't forget to comment,vote and share.love urí ½í²‹*
*Dijensy❤*
í ¼í¼¼í ¼í¼¼ í ¼í¼¼í ¼í¼¼
í ½í²¦ í ½í²¦
*AMJAD*
í ½í²¦ í ½í²¦
í ¼í¼¼í ¼í¼¼ í ¼í¼¼í ¼í¼¼
*WRITTEN BY DIJENSY*
*WATTPAD:@dijensy*
*Wannan page d'in naku ne masoyan Amjad*
1⃣7⃣-1⃣8⃣
Tana tsaye ita bata ce ya shigo ba kuma bata rife 'kofar ba.
"Can I come in?" Ya tambaya.
"No" Ta girgiza kai.
"OK,then I will wait for you outside"
"Me..? "
"Yes ,you're following me home"
"I will not"
"Stop wasting your time,just hurry up and park your things"
"Laila!" Tajiyo Mami ta kirata.
Sauri tayi ta bar gun ta tafi."Naji shiru,waye?
"Uh..Amjad ne"
"D'aukan ki yazo yi kenan?"
"Mami nifa.."
"Ke mey?,kinga ki shiga ki shirya kayanki"
A kasalance ta shige d'aki,cikin sanyin jiki ta soma shirya kayanta kamar mara laka a
jiki.Hijab d'inta ta d'akko ta zirma ta ri'ke niqab d'in a hannu ta fito d'ayan hannun ta ri'ko
akwatin.
"Kin fito?"
"Uhmm" Ta amsa.
Su Maryam suna daga d'agi suka fito,ganin Fauzan yasa ta fad'in."Mami dan Allah Fauzan
ya bini".
"A'a ba yanzu ba,se anyi hutun makaranta"
Ita tama manta yau Sunday,tana jin haushi ta fita su Maryam suka rakota har bakin
mota,Amjad yana ciki yana jiranta.Da kanshi ya fita ya taimaka mata tasa kayan a baya,kafin ya
koma motar ta rigashi shiga.Niqab dake ri'ke a hannunta ta d'aura a fuska ko idanuwanta ba'a
gani,jin alamar ya shigo motar ta kawar da kanta window.Har suka hau titi ba wanda yayi
magana ,sede lokaci-lokaci yana kallonta.Suna isa gida tayi tafiyarta ko kayan bata bi ta kansu
ba,key dake jakarta ta ciro ta bud'e 'kofar.
Sama ta haye direct d'akinta ta shiga ta rufo 'kofarta.
"An dawo Prison"Ta fad'a a fili.
Knock!knock! Tajiyo bugu,handbag d'in ta ajje sannan taje bud'ewa.Amjad ta gani ri'ke da
akwatinta,jira take taga ya mi'ko mata amma shiru.
"Remove this from your face" Yayi nuni da hannunsa.
"I wanted it this way"
"And I don't like it"
"But you don't wanna see ugly face"
Se yanzu ya tuna ,dariya abin ya bashi dan shi ya mance ya fad'a.Seda ya d'an murmusa
tukun yace"So now you believed you're ugly?"
Komawa tayi cikin d'akin ta barshi a tsaye gun, gefen gado ta samu ta zauna tare da ciro
wayarta cikin jakarta. Akwatin ya ri'ko ya shigo da ita d'akin daga gefen gado ya
ajjeta."Answer my question "
"Did you believed?"
An d'au mintina a haka ita bata amsa ba shi be fita ba yana tsaye a kanta.Laila data gaji da
zaman hakan tashi tayi ta wuce bathroom kafin ya farga ta rufo 'kofar.
"Laila!" Ya kira sunanta.
"I'm not going anywhere until you answer my question?"
"Shiru tayi kamar ba jinsa take ba,niqab d'in kuwa ta yaye shi tana tsaye jikin 'kofar tana
jira ya fita.
" Laila,can't you hear me? talk to me"
Ya gama surutansa ko 'kala