Showing 30001 words to 33000 words out of 60755 words

Chapter 11 - Amjad Complete Book By Dijensy

Dijensy   

17 Jul 2026

662

💦


*AMJAD*


💦 💦



🌼🌼 🌼🌼

*WRITTEN BY DIJENSY*

*WATTPAD:@dijensy*

1⃣3⃣ - 1⃣4⃣


Lokaci guda cikinta ya d'uru ruwa,ba shiri ta fito daga d'akinta ta sakko laundry room anan ta 
d'akko broom stick tare da mop.Tunanin yanda zatai masa bayani ta shiga yi kafin tayi knocking
tafi 4min,jin shiru yasa ta murd'a handle d'in 'kofar ta shiga.Gani tayi baya ciki kuma ba alamar
yana bathroom ,hakan ba 'karamin dad'i yayi mata ba.Cikin sauri ta fara  gyaran d'akin tana yi
tana masif-masife."K'azami kawai ,dubi  kan katifa mtchww!"ba dan Allah ba haka ta gyara
d'akin tass bathroom d'in ma haka ta gyaresa.Tana goge kan mirror ne taga wani d'an 'karamin
doki da aka sassa'ka da katako,d'auka tayi  tana ta kallansa ta juya can ta juya nan garin haka
ya su'buce ya fad'i,aiko tana dubawa taga kansa ya gutsire,salallami ta hau yi tana tarkatoshi.

    D'akinta ta koma ta d'akko wani super glue ta shiga mannawa a wuyan, daya jonu seya
'bintire har ta 'karar da glue d'in gashi duk ta 'bata dokin yayi fari-fari a brown colour d'in

        Amjad kuwa jin zaman d'akin ya isheshi yasa ya fice waje garden yayi zamansa,seda ya
shafe 'yan mintina ya komo.

    "What is she doing?" Ya fad'a a ransa ganinta bakin mirror ta juya baya.

      "What are you doing in my room?"

       Nan da nan ta soma mutsu-mustsu ,da sauri ta 'boye dokin a bayanta,gashi yau ba gyale a
jikinta doguwar rigar atamfa ce da d'ankwali.

    "You're hiding something" Ya 'karaso inda take a fusace ya mi'ka mata hannu ta fito da
abunda take 'boyewa.
  
     "Let me see"

      "Ni babu abinda na d'auka" Ta turo baki.

      Ganin zata 'bata masa lokaci ya mi'ka hannu bayanta ze kar'be abinda take 'boyewa,da
sauri ta juya  bayanta gam ta ri'ke dokin kamar nata.Kici-kici suka shigayi yana murd'e mata
hannu tana ihu amma ta'ki saki,jin nauyinsa gabaki d'aya a bayanta yasa tayi saurin saki da
'karfi ya wafce body d'in dokin. Ba shiri taja jiki ta matsa gefe du se taji wani irin dama bata ri'ke
ba.

     Ganin tsurar doki ba kai yasa Amjad ya waigo ya dubeta."You broke it "

     Shiru tayi bata ce komai ba kan dokin na hannunta na hagu ta dam'ke.

    "Give me the other part" Ya mi'ka mata hannu.

     Tana so ta bashi kuma tana tsoro kar yayi mata wani abun dan ta kula ta irin expression d'in
fuskarsa d'auke da guntun murmushi mey manufofin.

     A sanyaye ta bud'e ta mi'ka  masa daga nesa -nesa,ganin hannunta be kai ba ta d'an matsa
aiko abinda take tunanin shiya faru.Hannunta ya janyo har kan dokin ya fad'i 'kas ita kuma ta
fad'o jikinsa.

       "Can't you apologize?"

          "Ka cika ni,kai kayi min godiya?"

           Ta kasa ku'bucewa sam se raba idanuwa take."Shut up!"

       "Toh ka cikani"

        "Keep your mouth shut"

         Ya sake matso da fuskarsa har numfashinsu na had'uwa.Tsoro ne ya fara kamata dan
haka tayi shiru mutsunma ta dena idanunta a rufe.

        Door bell rang qlin! Jin haka yasa ya cika mata hannu har tana shirin fad'uwa da'kyar ta iya
balancing kanta,a kunyace tayi sauri ta fita daga d'akin.

      "Aunty" Ta furta lokacin data bud'e 'kofar.

        "Sannunku da zuwa" Ta fad'a tana bud'e musu 'kofar widely.

        Waje suka samu suka zauna su hud'un ,bayan data gaishesu ta kawo musu drinks."D'ayan
d'an kunnen fad'uwa yayi?"Wata daga Cikin 'kannan Mami ta tambayeta.

    Se lokacin ta shafa kunnenta taji ba d'an kunne d'aya,zuciyarta ce ta bata a d'akin Amjad ta
yar.

     Amjad bayan fitarta ya lura da d'an kunnen ma'kale a jikin shirt d'inshi,kallo d'aya yayi mishi
ya bud'e drawer ya cillar a ciki coz yana expecting zata zo kar'ba.

     Hira suka shiga yi irin ta 'yan uwa har wajen maghrib tukun suka tafi.Suna tafiya ta koma

d'aki ta d'akko mayafi ta yafa ,d'akkunen kuwa ta cire ta sauya wani dan bata jin zata iya
komawa ta d'akko kayanta.

              ★★★

     Tun abinda ya faru Laila bata sake yarda ta shiga d'akinsa ba ,Amjad ya samu sau'ki har ya
koma aikinsa.Aliya a makaranta daga tayi mata maganar aurenta seta share zancen gashi
lecture tayi nisa  yanzu har sun fara test,tana dad'ewa ma bata sakko 'kasa ba rabon data had'u
dashi tun da safe yanzu har 10:23pm gashi an shigo watan azumi gajiya take sata kwanciya da
wuri.

      Amjad ma yanzu da wuri yake barin wajen aiki kuma yaci abincin ta ya'ki ko tayi dayawa
sede ta bawa mey gadi da yazo kwanannan,wani lokacin fita yake restaurant ko ya siyo ya taho
dashi kullum a wahale.

     Aliya haka tayi ta 'ko'karin turo mata video girke-girke iri-iri idan taga dama tayi wani kuma ta
share musamman idan taga mey wuya ne.

     Yau ba school,tunda ta tashi take jin alamar ciwon mara kad'an-kad'an aikuwa wajen
11:30am azuminta ya karye,dan haka ta shiga kitchen dan had'a abinda zata ci indomie kawai
ta dafa bayan taci tasha magani ta komo d'aki tayi kwanciyarta.

      Amjad shaf ya mance be tafi da key ba,2:30pm ya dawo a gajiye.Qlin!Qlin ya danna door
bell shiru, har ya soma gajiya da tsaiwa.Laila kuwa baccinta take ta shara bata san yana yi
ba.Gwada kiranta yayi a waya amma switchoff tana charge.

     Ransa ba 'karamin 'baci yayi ba gashi ko mey gadi baida key d'insu na ciki,cikin mota ya
koma ya kunna Ac.Se wajen  3:45pm ya koma ya sake ringing,dede lokacin ta sakko 'kasa ita a
tunaninta ma ko ba'ki tayi.Yana tsaye fuskarsa ba annuri kamar ya sha'keta haka yaji, gefe ta
matsa ya shigo tukun ta rufe 'kofar.
      "I spent more than 1hr waiting for you to open this fucking door"

       "Ni na hanaka fita da key"

        "You..." Ya nuna ta da yatsa.

        Matsawa tayi daga pointing d'inta da yayi ta waiga gefe."You're disrespecting me"

      "Nasan   matsalarka ,yunwa" Ta fad'a a ranta.

      Ring! Ring! Wayarsa tayi 'kara, Dad ya gani  jikin screen.Be sake wata maganar ba ya bar
gun.Gwalo ta bishi dashi ba tare da yasan tana yi ba.

   Da lokacin shan ruwa doya da 'kwai kawai tayi ta d'ibawa mey gadi saura data ci ta ajje,Amjad
yau ko fita ya siyo abincin beba koda aka sha ruwa iya fruits yasha da. dabino.Seda ya dawo
daga masjid ya lura da flask d'in da ta ajje doya da 'kwan,d'aya ya d'auka yasa a baki yana
feeling taste d'in.
     "Not bad" Ya fad'a kafin ya sake d'aukan wata ya lun'kume a wasa awasa har ya kusan
cinyewa.

    
Washegari da safe bayan ta gama shirinta tayi toasting bread da d'an yawa saboda zata je
school dashi.Tana cikin yin breakfast Amjad ya shigo,jitai kunya ta kama ta lomar dake bakinta
ta had'iye da 'kyar ,saboda gudun karya ganta yasa bata ci a dinning ba amma duk da haka
seda ya ganta.
     "Are you suppose to eat? You don't even feel guilty of what you're doing"Ya 'karaso yana
janye plate d'in gefe ,kuma ya gane amma jan magana yasa shi yin haka.

    " Meya shafe ka?"

     "Repeat what you said, I can understand little of it"

     Jin ya fad'i haka tayi shiru bata kuma wata maganar ba.

   "Yarinya I'm soon living you here alone"

    D'agowa tayi ta kalleshi jin ya anbaci yarinya"Toh a ina ya fara koyan wannan?"

      "Surprised koh?"Murmushi kawai yayi ya fita daga kitchen d'in, abincinta ta cigaba da ci
tana tunanin yadda ya fara iya Hausa.

     Tunda aka fara azumi sau d'aya ta sake zuwa gida yanzu har za'a 'kar'kare.Tana d'aki bayan
ansha ruwa yazo yace mata ta shirya su fita,seda suka tsaya a mall tasan inda zasu.Siyayyar
kayan sallah suka yi,daga nan suka komo gida ,su Maryam da suka zo ta basu suka kai mata
d'inki,ranar sallah ji take kamar ba sallah ba ita kad'ai sede idan kunna chat tayi,jitai tayi missing
tuwon Mami na sallah ,kira tayi a ways race su kawo mata ko abincinta 'kinci tayi tana jira
anjima su Nusaiba su kawo mata tuwo.

    Basu suka zo ba se 4pm,ganin 'kunshinsu datai taji ya birgeta jitai dama itama taje anyi mata
,Aliya seda tayi ta fad'a mata amma ta'ki.

    Biyu ga sallah ta shirya zata gida,Amjad ne ya d'auketa badan yaga dama ba saboda Mom
tace yaje.Suna tafiya a hanya ta ciro mirror d'in powdernta tana kallan fuskarta." You better stop

it ,you're not even beautiful "Taji ya fad'a.

    Har cikin ranta taji haushi" Banyi dan kace nayi kyau ba"Tayi maganar a fili.

     "I can understand all you're saying better watch your tongue"

     Baki ta zun'buro ta mayar da mirror d'in, sam bata lura dashi ba yana ta satar kallonta,kayan
jikinta ya amsheta sosai.Lace tasa maroon da torches golden se sar'karta ma golden data
kwanta a wuyanta,fuskarta ma tayi makeup dede ,lipstick maroon tasa da eye liner kwalli ya fito
tar a idonta.Mayafinta ma golden ne tayi d'aurin....(guess).
   Zaman kurame sukayi har suka isa gidan Mami,ta bud'e  'kofar zata fita ya tsayar da ita."Don't
expect me to take you back home ".

     " Better "Ta fita.

     Se bayan ta shiga ya shiga gidan ,yana gaisawa da Mami ya fita daya had'u da Fauzan  a
'kofar gida ya bashi 10k 'yan 500 sabbi.

    " Ashe de da sauran mutunci"Laila ta fad'a sanda Fauzan ya shigo yana nunawa su Mami.

     "D'azu nayi waya da Maman shi take fad'a min Amjad d'in zeje can Canada d'in" Mami ta
fad'a.

    "Uhm..eh" Ta fad'a a ranta kuwa tunani ta shiga yi,da gaske yake ashe.

     "Mami yaya gida zata dawo ko?Nusaiba ta tambaya.

     "Eh toh.."

     "Ehmana nan zan komo" Laila tayi saurin fad'a.

      Dad'i taji sosai dama exam zasu fara ba dad'ewa ,a ranta tana fad'in"Na huta yaje can ya
'karata da ba'kin halinsa".

       Laila bayan ta 'kare wuninta a gida wajen 5 :30pm ta tashi tafiya dan tasan ba zuwa ze
d'aukanta ba.Lokacin da ta koma gida ta tarar yana gida,d'akinta tayi wucewarta.

     Haka ta 'kare sallah ba inda ta sake zuwa,bayan 1week suka koma school,yanzu
shirye-shiryen exam suke ba dad'ewa suke ba 12pm wani sa'in ta komo gida,ita jira take taji
yayi mata maganar tafiyarsa amma shiru beyi ba.

       8:05am ta sakko 'kasa,'karamar trolley dake girke a living room ta tsaya kallo bata gama

sa'ke-sa'ke ba sega Amjad yana sakkowa daga steps. Yau ana ganinsa za'a san yana cikin
farinciki,specs dake idansa ya zare.

     "Home alone" Taji ya fad'a.

      "Ni nace maka anan zan zauna?"

      "You can speak the way you like to but you can't change it ,I'm leaving now".Yaja trolley ze
fita Laila tace." I'm not staying here alone "

      "That is none of my business, the decision is yours" Yayi mata waving bye cikin rainin
hankali.

     Tana gani driver ya amshi trolleyn yasa a bayan mota ,Amjad ya shige baya abinsa driver ya
jasu suka fice. Bata 'kara ko minti d'aya ba tayi sauri-sauri ta haye sama.Nan take ta soma
had'a nata kayan duk wani school things ta d'auka tazo duba phone d'inta kan drawer ta lura da
kud'ad'e kan drawer d'in 50k ta gani.Handbag d'inta kuwa ta d'auka ta zira a ciki tasa wayarta
key d'in gidan ta d'auka ta sakko bayan data kulle d'akinta,sauran doors na 'kasa ma ta rife
tukun exit door taja akwatinta ,mey gadi ne ya samar mata Napep ta tafi.

    Tun a hanya ta kira Mami take fad'a mata tana hanya.Tana shiga gida ta ajje akwatinta a d'aki
,se murna take."Se yaushe ze dawo?"Mami ta tambaya.

     "Uhnmm.uh..3weeks" Ta kintata ta fad'a.

      "Allah ya kaimu"

      "Ameen" Ta amsa.

       "Mami wainar gero nake son ci" Laila ta fad'a.

        "Toh ta rashin ta idon zaki min" Cewar Mami.

      Ita kwata-kwata Laila bata zaci za'a d'auki hakan da wani manufa ba da bata fad'a ba,kawai
de ta dad'e bata ci bane shiyasa taji sha'awa.

    "Kai mami nifa.."

     "A'a kina sani kawai de  tareraya irin ta yaran zamani"

     Tashi tayi ta koma d'aki ta d'auko handout d'inta ta soma duba kayanta tunda su Maryam
basa nan gidan shiru,wainar ma fasa siyowa tayi.

              ★★★

   Amjad kuwa koda ya isa be damu da kiranta ba ,shi sam hankalinsa ba anan yake ba baida
buri irin ya had'u da Rosie.

     Mom ,Zakia da Shaheed  ne suka taro shi a airport,Dad yayi tafiya,Mom ce first d'in ganinsa
cikin sauri ta 'karasa tayi hugging d'insa tightly."My baby ,missed you so much"

     "Missed you too"

      Jitai kamar karta cika shi,su Zakia ma sukai hug lastly Shaheed, brother's hug

      Tunda suka taho a mota zuwa gida Mom hirar Nigeria take masa tana tambayarsa amma
yana amsa mata kad'an -kad'an wani abun ma 'karya yake mata idan yaga ta isheshi.

     "Laila told me she's staying there with her Mom" Yaji Mom ta fad'a.

     "Uhmm" Ya kawar da maganar amma a ransa yayi 'kwafa dan shi bece mata ta tafi ba.
    
       Dinner na musamman aka shirya masa, se ji dashi Mom take zakia har tana tsokanarsa
momy's bae amma wannan karan be taya ta ba.Sam ranar be samu chance ba balle yaje wajen
Rosie, se washegari da safe 10am bayan sunyi breakfast yace zeje wajen Sam abokinsa duk
da kuwa Mom jikinta ya bata wajen Rosie zeje.Be tashi zuwa ba seda ya siya mata flowers da
bracelet mey tsadan gaske,har wani rawar jiki yake.

       "Angel I'm on my way to your house"Ya tura mata text.

     Few minutes later ya isa gidan,3missed call yayi mata bata d'aga ba,yasan wani lokacin tana
yin haka idan tana so tayi surprising d'inshi sometimes seya shiga gidan.'Karasawa yayi
hannunsa ri'ke da flowers d'in se bracelet d'in a aljihunsa ,knock! knock! Yai knocking ba'a bud'e
ba.Handle d'in ya murd'a ya Shiga.  
      " Hello"

      "Hello"Ya 'karasa living room." Hel...."

      'Karashen lo d'inne ya ma'kale a ma'kogoro dan tsananin tashin hankali ,jiyai kunnensa ya
dena jin sound tsaiwar ma da'kyar yake.Irin yanayin da ya tsinceta yasa ya kasa  magana,a
zuciyarsa yana 'kokonto anya Rosie d'insa ce.Tana zaune a cinyar wani guy da besan waye ba
suna kissing passionately ,tana sanye da wani fitinannun sleeping dress wanda dashi da babu
duk d'aya.Guy d'inne ya fara lura da Amjad dake tsaye kamar gunki,ganin guy d'in ya dakata
yasa ta d'ago tana kallon direction da yake kalla."Amjad "Ta fad'a a hankali cikeda mamaki....

*Duba da yanayin lokaci azumi na tahowa ,shiyasa na maidashi page 2 in 1,and na 'kara
tsahon page d'in,hope hakan yayi muku.Don't forget to vote.*

        
 
*Dijensy❤*

   

   

    

   

  

 
  
    

    

    

   

    

   

     

   

     

     
🌼🌼 🌼🌼


💦 💦

*AMJAD*


💦 💦



🌼🌼 🌼🌼


*WRITTEN BY DIJENSY*

*WATTPAD:@dijensy*



*Sorry for the late update*


1⃣5⃣ - 1⃣6⃣


       A inde yake tsaye ya yasar da flowers d'in ba tare da ya san yayi hakan ba ,kamar 'kiftawar
ido ya fita daga gidan. Da fitarsa da shiga mota be wuci 'yan sakanni ba,tu'ki yake amma besan
inda zashi ba,seda ya tabbata yayi nisa da area d'in ya samu yayi parking can bayan
gari."No!"Ya daki steering d'in motar ya zira yatsansa cikin sumarshi se mutstsukawa yake
kamar ze cire gashin kansa."It can't be,No! Rose why? why?"be ankara ba yaji idanuwansa na
tsiyayar hawaye,feeling his heart broken into pieces.
Tunanin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
google.com, pub-9213700357025247, DIRECT, f08c47fec0942fa0