Showing 21001 words to 24000 words out of 60755 words
tace kar mu dad'e"Cewar Nusaiba.
" Ke dalla can seku kwana"
"Tabb bada mu ba" Maryam ta fad'a.
"Meye idan kun kwanan?eyyi?"
Shiru tayi Maryam tana munafikin murmushi tare da kad'a kai "a'a de".
" Bazaki magana ba,nace meye idan kun kwanan?"
Dariya ta shiga yi tana rufe fuska "Mtchww! Sakarya ni tashi muje kitchen d'in" Ta fad'a tana
mi'kewa daga kan sofa dan ta fahimci inda ta nufa.
A hankali suna had'a abinsu har sukai baking, sosai cake d'in yayi dad'i nan ta d'ibarwa Mami
mey yawa ta rage kad'an.Wajajen 5:30pm suka tafi, pictures da suka kawo mata na biki tayi ta
kalla.
Amjad kuwa yana jiyo su daga d'akin yana sane ya'ki sakkowa dama ya shiga da abincin
daya siya a waje d'aki harkokinsa yayi tayi a d'akinsa.
Ita kuwa da dare cake d'inta taci tasha lemo tayi kwanciyarta.
11:35pm, Knock! Knock! Tajiyo bugu tana cikin bacci, tashi tayi duk jikinta yana shaking dan
bugunshi yaso ya razana ta.
"Mtchww! Ze tayar min da hankali ina bacci na" Seda ta yafa mayafi tukun ta bud'e masa.
"Let me have your phone"Abinda ya fad'a kenan banyan ta bud'e.
Seda ta d'an jinkirta kafin ta koma ta bud'e drawer ta d'akko."Gashi"Ta fad'a a ciki-ciki.
"This?" Ya wani kalli wayar tare da nuna ta da yatsa.
A wani wula'kance ya kar'beta bayan ya jujjuyata ya mi'ka mata abarta."This is useless "Ya
fad'a.
" Wacce ka siyamin?"Ta fad'a a ranta.
Kamar yana so ya sake fad'ar wani abun amma de yayi shiru ya fita daga d'akin ta rifo
'kofarta.
"Allah ze sakan tashi na dakai" Ta koma ta kwanta.
***
Washegari tasha mamaki ganin ya siyo mata waya,bata yi tunanin yana da ragowar mutunci
ba,IPhone 7+ silver colour.
Tunda tayi waya ta rage damuwa da rashin mutane a kusa da ita,zatai chat d'inta tayi
kiranta tayi karatun novel wani lokacin tayi kwalliya tayi ta selfie d'inta.
Amjad kuwa kwana hud'u kenan da fara zuwa aiki.Ranar farko daya je company kowa
kallonsa yake a iya shekarunsa a matsayinsa na chief executive officer gashi dressing yake
duk wanda yaga dama har 'yar shirt me gajeren hannu ma yake saka wa ya tsuke abinsa
gashin kannan yasha style.
12:14pm,taji motarsa yai parking tana daga d'aki,labulen window ta d'an bud'e tana ganin
fitowarsa ta ta'be baki ta cigaba da danna wayarta.
Tana jiyo shi ya shiga d'aki,wanka kawai yayi ya sauya kaya cikin farar T-shirt da black jeans
ya shirya shirts, wayarsa da key kawai ya d'auka bayan ya feshe jikinsa da turare ya fito.
Knock! Knock! Taji ya bugo 'kofarta.
"Follow me" Abinda kawai ya fad'a yawuce downstairs.
"Follow you? To where?"
Komawa tayi ta zauna amma kuma ta kasa ci gaba da dannan wayar,seda tayi kusan 8min
a haka tukun ta mi'ke ta yafa mayafinta kan riga da skirt na atamfa dake jikinta ,flat shoe d'inta
ta zira ta ajje wayarta ta sauka 'kasa.
A living room taga bayanan,tana le'kawa waje ta ganshi ya jingina da pillar na
varender.Yana jin motsinta ya waiwayo ,wata uwar harara ya watsa mata sannan ya nufi motar.
"Toh ina kuma za'a? Toh wayata kuma na d'aki"
Wata zuciyar ce tace "kika sani ko gida zey kaiki ,karki koma kuma ya fasa" A hankali ta
'karasa jikin mortar tana d'an ra'be-ra'be kanta a sunkuye.
"Get in" Ya fad'a.
Gidan gaba ta bud'e tana d'ar-d'ar ta shiga,har suka hau titi bame cewa komai tsit"Toh ina
kuma zamu?"Ta fad'a ganinsa tayi ya kauce hanyar da zata sada ta da gida.
Kasa tambaya tayi ta zira ido tana ganin ikon Allah.K'aton gida taga yayi horn an bud'e
masa ya shiga.Har lokacin bata gane inda aka zo ba,seda taga Shaheed yana fitowa daga ciki.
"Are you staying here forever?" Ta jiyo ya fad'a.
Da kanta ta bud'e 'kofa ta fito tana d'an taka wa a hankali so take ya shige gaba."Ina
wuni"Shaheed ya fad'a lokacin da suka 'karasa
"Ina wuni" itama ta fad'a.
Handshake taga sunyi suka jero suna 'kus-'kus wanda ba ji take ba.Suna tafe tana binsu a
hanya har suka 'karasa ciki,ba kowa a parlourn ta samu ta zauna a sofa,tana kallo ya nufi wani
sashen Shaheed kuma ya hau sama.Not more than 3min sega Mom da Zakia sun sakko
fuskarsu d'auke da fara'a suka 'karaso.
"Laila" Ta kira sunanta tana 'karasowa ta zauna daga gefenta tare da tallafo shoulder
d'inta.Laila cikin jin kunya tayi 'kasa da kanta tare da du'kawa ta gaisheta.
"Get up,feel free daughter"
"Ya kike?"
"Lafiya lau" Ta daure ta 'Kalo murmushi.
"Ina yini" Cewar Zakia tana murmushi.
"Ina yini"
"My cutie sister please feel free,this is home"
Itade murmushi kawai take musu Mom tasa mey aikinsu ta kawo mata abin sha.
"Kada ki bari fa aiki yana miki yawa kiyi magana kinji se'a sami mey aiki""
Kai kawai ta kad'a ba tare da tace komai ba,tana hangoshi har ya 'karaso inda sike ko zama
ya'ki yi kawai de ya gaisa da Mom ne Zakia se wani kallon gulma take masa yana harararta ji
yake kamar ya mareta ganin Laila yasa ya 'kyaleta .
"Amjad talk to her to drink something" Mom tayi maganar dan ta gano ya zaman nasu yake.
"She is fasting" Taji ya fad'a.
D'ago idonta tayi har suna kallon juna yayi mata 'kiri gefen fuskarsa d'auke da murmushi.
Mom jinjina kai kawai tayi , inda Allah ya taimaki Amjad Monday ranar ta kasance.Daga
bayan tashi yayi ya fita a mota ba tare da sunsan inda zashi ba,kad'an-kad'an Zakia tana janta
da hira kawai amsata take dan yunwa ta gama kashe mata jiki rabonta da abinci tun 8:30am
saboda yau da wuri tayi breakfast,addu'a take maghrib yayi tasan Mom zata had'a mata kayan
shan ruwa har kusan maghrib Dad ya shigo suka gaisa,suna zaune Amjad ya shigo ko zama
beyi ba yace ta tashi su tafi,Mom ba yadda ba tayi dashi ba ya bari tasha ruwa anan amma ya'ki
dan har tasa an girka mata abinda zata ci,daga 'karshe de yace kawai tasa mata a food warmer
se su tafi dashi.
"Mugu azzalimi" Ta fad'a a ranta.
Daga yadda yaga yanayinta ya gano tana cikin wani hali dan ya'ke kawai take."Let's go"Yayi
mata murmushi.
Har mota suka rakasu suna tsaye suka fita daga gidan.Food warmer d'in tayi ta d'an d'agen
wuya ko zata gansa d baya amma ba alamarsa,hanyar daya kamata suyi taga sun kauce.
"Where are we going to?" Ta tambaya.
"Mall,madam chef" Ya bata amsa yana murmushin mugunta.
Kai ta dafe ta kalli taga har wani duhu-duhu take gani,tana ji tana kallo yayi parking. "Let's
go".
Ac dake busawa taji ta isheta,ji take kamar mey zazza'bi,yana tafe tana binsa a bayan se
wani kalle-kalle yake kafin ya d'auki abu d'aya seya shafe fin 5min.
" Do you like this? " Ya d'akko wata doguwar riga iya gwiwa yana nuna mata.
"My wife is eager to go home ,but her husband is not readyyy"
Ji take kamar ta sha'keshi,haka ya gama d'age-d'agensa harda kara mata a jiki yaga wai yayi
ko beba gabaki d'aya English wears yaita za'ba.8:42pm suka shiga gida ,ko kallonsa bata sake
yi ba har suka shiga.kayan daya siyo leda uku ciki ya mi'ka mata ta'ki kar'ba,kan kujerar ya dire
mata ya koma mota ya d'akko abincin har lokacin da ya dawo tana parlour. Yadda ya rungumo
warmer d'in zaka san cewa ya taki rashin mutunci.
*Need your comment,I'm really busy but I tried hard to update coz I don't want to keep you
guys waiting, I don't know If I can be able to update tomorrow, I'm really really busy.Love ur*í ½í²‹
*Dijensy*❤
í ¼í¼¼í ¼í¼¼ í ¼í¼¼í ¼í¼¼
í ½í²¦ í ½í²¦
*AMJAD*
í ½í²¦ í ½í²¦
í ¼í¼¼í ¼í¼¼ í ¼í¼¼í ¼í¼¼
*WRITTEN BY DIJENSY*
*WATTPAD:@dijensy*
í ¼íµ¿ 0⃣9⃣
Binsa tayi da kallo tana jira taga mey zeyi da abincin,har kusa da ita yazo ya wuce ta gefenta
yana rungume da flask d'in ya haye sama ya barta a tsaye tana had'iyar miyau.
Jitayi kamar ta bishi amma gudun karya wula'kantata ta nufi kitchen, seda ta fara had'a tea
tasha tukun ta d'ora indomie sharp sharp ta gama da zafi-zafinta haka ta samu taci harda
guntun hawayenta na takaici.Se bayan ta gama cin abincin ne ta tuna bata yi sallahan maghrib
da isha'i ba,shima Amjad d'in tunawa tayi beyi ba."Tabb! La'ilaha illallahu maimakon yaje
masallaci ,toh ko dama haka yake wasa da sallah?"Ta tambayi kanta tana mey mamakinsa dan
ita shaf ta mance yunwa ta rufe mata ido batai noticing ba.
"Astaghfirillah" Abinda ta fad'a kenan ta koma d'akinta kayan kuwa ta barsu anan. Seda ta
idar da sallolin da ake binta tukun ta samu nutsuwa,tana yin wanka tayi shirin kwanciyarta koh
phone d'inta bata duba ba dan gajiya.
Washegari da safe kafin ta fito taji fitar Amjad, 8:20am agogon d'akin ya nuna.Inda ta bar
kayan jiya anan tazo ta tarar dasu,ta'be baki tayi tai wucewarta kitchen "Ka kaiwa budurwarka
ba niba"
***
Sati d'aya su Mom suka 'kara a Nigeria suka koma ,kafin su koma seda suka zo gidan
Laila.Amjad ji yake kamar ya bisu ,tun lokacin da suka koma ya dena walwala ko kula Laila bayi
yake ba balle magana ,kaya kuwa bata kwashesu ba se lokacin da Mami zata zo ta d'auke ta
kaisu wani d'akin daban ta rife.
Saturday 8:17am,ta gama shirinta cikin lace black mey red torches,tasa sar'karta mey
stones red color tayi matu'kar kyau ga d'aurinta da ya tsaru fuskarta tayi light makeup se
'kamshin turare take.Tana sauka 'kasa taga parlourn ma ba wani datti yayi ba dama jiya da
yamma ta gyara shi,kitchen ta shiga dan had'a karin kumallo ,yau doya da 'kwai taji tana
sha'awa ,tana d'ora doyan a pot ta nufi drawern dan d'akko bowl ,kasancewar tsahonta baya
kaiwa setayi d'age tana janyo bowl d'in ya su'buce ya fad'o kan babban yatsanta na 'kafa Tass!
Ya fashe pieces a wajen ,take ta saki wata 'kara dan azaba.Fuskarta tuni tayi jazir gumi yana
keto mata,zaman dirshan tayi tana ri'ke da 'kafarta d'anyatsan se jini yake.
"What happ.." Be 'kare tambayar ba yayi shiru da bakinsa ganin yadda 'kafarta ke zubar
jini.
Kuka ta shiga yi sharaf-sharaf hawaye yana zuba.
"Get up" Ya fad'a tare da d'ora hannu kan kafad'arta da niyyar mi'kar da ita.
"Aghhh!" Ta 'kwallo 'kara.
Jin 'karar da tayi yasa ya d'auke hannunsa,tana zaune ita bata tashi ba kuma bata dena
kukan ba."Are you staying like this? "
Banza tayi dashi kamar bata jiba,yana sake d'ora hannunsa a kafad'arta ta kuma tsala ihu fin
da.Ita bama iya zafin yasa ta 'karar ba ta'bata ne bata so yayi.
Tsaki yayi "It left for you" Ya fita daga kitchen d'in.Yana fita ta tashi se d'ingishi take,ganin
jinin yana d'iga a 'kasa ta zauna kan wani couch a living room.Tana hangoshi ya sakko daga
bene hannunsa ya ri'ko first aid.
"Cabb! Zaka ga first aid"
Bata ankare ba taga yaja wani guntun table ya zauna opposite da ita."Let me see"
"Kaga mey? kai likita ne?"
Ko bin ta tata beyi ba ya kama 'kafar se fisgewa take amma ta kasa "Aghh!"Se 'kara take
yayi banza da ita yana goge jinin se kuka take, seda ya gama ya rife ciwon da bandage tukun
ya sake mata 'kafa.
" Allah ya isa"Ta fad'a a fili tana share hawaye.
"You have to be careful"
"Ni matsa min na tashi" Ta fad'a tana 'ko'karin mi'kewa.
Maimakon taga ya tashi seyai zamansa yana kallonta.
Kasa balancing tsaiwarta tayi ta fad'a kan couch d'in.Ganin ya sake matso da kujerar yasa
hantar cikinta ya soma kad'awa,ta sunkui da kai tana jin idonsa a kanta.
"I need to know why,why did you agreed to married me?"
Shiru tayi ta kasa cewa komai tana murza yatsa."I'm asking"Ya sake matsowa har takai
baza ta iya mi'kewa tsaye ba."Please let me go"
"Until you answer my question"
"I never married you because I love you,they..they forced me to"Ta fad'a da 'kyar.
"Wow! I hope what you're saying is true"
"Now what is your plan? Run away?"
"Please!".Ta ro'keshi data bata sake.
Tashi yayi tsaye ya d'auke first aid d'in ya haye sama,tana gani ya tafi tayi sauri ta bar wajen
ta koma kitchen tana d'ingisawa,wajen daya 'baci da jinin ta gyara a daddafe ta 'karasa had'a
breakfast d'in taci kayanta.
Tunda ta koma bata sake fitowa ba se bayan zuhr,tana ganinsa a parlour yana kallo tai 'kasa
da kai bata so ta had'a ido dashi.Shiko be sake yi mata maganar 'kafar ba balle yai mata sannu.
Laila da daddare ta kira Mami tana ta shagwa'ba ita a lalle taji ciwo Nusaiba tazo.Washegari
Mami ta turosu Nusaiba harda Fauzan amma basu kwana ba.
Tun bayan tafiyarsu Laila ta soma jin sauyi game da ita,kad'an-kad'an mararta ta soma ciwo
tun bey takura mata ba har ta kasa jurewa.Ta kwanta se mutsutstsuka 'kafafuwa take tana dafe
ciki,tunani ne ya fara zuwan mata na MP date nata data lissafa taga lokaci yayi." Tir'kashi!"
"Ya zanyi?"Tana ta sa'ke-sa'ke a zuciyarta ko zata samu mafita,8:18pm taga agogo ya nuna
juyi kawai take ta rasa inda zata saka kanta gashi idan a gida ne magani take sha wani sa'in
Mami ta had'a mata black tea ta kur'ba amma yanzu ba d'aya.Hawaye ne kawai yake tsiyaya
daga idanunta tana tausayin kanta na halin rayuwar data shiga.9:03pm a daddafe ta tashi ta
sauka 'kasa ,a kitchen ta had'a tea kad'an ta samu ta daure ta kukkur'ba ga yunwa data ke ji
amma bata jin zata iya cin komai.D'akinta ta koma ta cigaba da aikin juye-juye,gashi tana tsoron
gobe monday tasan da wuri zey fita,idan kuwa ta bari ya fita tana cikin matsala dan bata da ko
sisi balle tace zata fita suyo wani Pad dan duk 'Yan kud'ad'enta ta 'karar wajen saka credit last
siyan ma shine dasu Fauzan suka zo ta aikesu suka suyo mata na 500 d'in.Se can bayan
30min bacci ya kwasheta da ciwon ya lafa.
5:46am ta farka taga har subh tayi,da 'kyar ta iya tashi dan a halin data tsinci kanta mey
faruwa ta faru bata san kuma ya zatai ba yau.Wata zuciyar ce ta bata shawara ta fad'awa
Amjad,tana jin kunya haka tayi knocking 'kofarsa lokacin 6am.
Tafi 6min kafin ya bud'e mata ,daga ganinsa ta gane lokacin ya tashi daga bacci.
"Morning" Yaune lokaci na farko data ta'ba gaisheshi.
Da'kyar yake bud'e idanuwansa "What?"
Wayar hannunta ta mi'ka masa bayan data gama danne-danne a cikin.
Kamar baze kar'ba ba yasa hannunsa ya kar'ba"Read"Ta fad'a tana kallon gefe.
"I want to use pad" Yaga ta rubuta ta note app.
"So?"Ya fad'a ba tare da ya nuna damuwa ba.
Hannunta ta mi'ka alamar ya bata wayarta a lokacin kuwa idanuwanta sun cika da 'kwalla
jira take kawai ta bar wajen.
"Check in what you have thrown away the other day"Abinda ya fad'a kenan ya mi'ka mata
dan yasan bata duba kayan ba dan da ta duba da bazata tambdaya ba.
Tana gama karancewa ta tuna da inda ta ajje kayan,kunyace ta lullu'beta tana da tasani duk
da ba haka ba.A kunyace ta juya zuwa d'akin data yasar da kayan.
Tana dubawa tagani kuwa se lokacin taji relief,da sauri ta komo zuwa d'akinta da pad pack
d'in a hannunta ,mamaki ne da kunya ya sake lullu'beta lokacin da taga yana tsaye har lokacin a
'kofar d'akin kamar jiranta yake.Basar wa tayi ta wuce a hannun hagu ta ri'ke yadda baze gani
ba tai sauri ta shiga.Shi dariya ma ta bashi (Gani na yaushe kuma).Tana shigewa shima ya rufo
'kofarshi,se lokacin yaje ya d'auro alwala dan yin sallah.