Showing 45001 words to 48000 words out of 60755 words

Chapter 16 - Amjad Complete Book By Dijensy

Dijensy   

17 Jul 2026

654

kam tayi ta mata fad'a tana kallo Amjad yana kiranta a waya
amma ta'ki d'auka,daga baya taga text nashi.

      Hi,how was the day? Hope you're doing good.

      "Ina ruwanka?" Ta fad'a a fili tayi cilli da wayar.

      "Komai ace aure..aure "

       Tunda ta cillar da wayar bata sake dubata ba tayi baccinta,Amjad kuwa baida tunanin daya
wuce nata ya matsu yaji muryarta yana ta jiran reply amma shiru.Ko washegari ma beyi zuciya
ba da safe seda ya kirawo ganin bata d'aga ba yayi mata message.

       Morning hope you're doing good?

      Laila ba ita taga message d'in ba se to 10am shima 'kin reply tayi ta maida wayar ta ajje.Dan
saboda Mami ta barta taje yinin bikin seta d'auki Fauzan suka je tare da ita aka kai amarya

sannan ta komo gida.

       Messages da missed call ba adadi ta tarar a wayarta banyan ta komo  gida.

     "D'azu kuwa Amjad ya kirani " Taji Mami ta fad'a.

     "D'azu" Ta maimata tana zare ido a ranta tana fad'in Allah yasa Mami bata gani 'karya nayi
ba.

     "Mami se kuka gaisa?" Ta tambaya tana neman 'karin bayani.

      "Ehyi naji yanzu ma ai Hausa ta shiga bakinsa ba kamar da ba"

     "Uhm" Ta fad'a zuciyarta na raya nata Mami batasan komai akai ba.

     "Ashe ma gobe ze dawo" Taji Mami ta fad'a.

      Ita a tunaninta ze iya yin sati d'aya ,nan take murnarta ta koma ciki.

      "Uhm" Ta fad'a a ciki.

        "Toh gobe seki koma da safe aiko"

         Nan ma ta amsa da "Uhm".

      Haka ta kwanta tana jin haushi plan d'inta ya rushe kwana biyun datai d'in ma bata gode
ba.Washegari da safe tayi ta la'kai-la'kai ta gaji da baccin safen ma amma ta'ki tashi seda taga
dama kafin tayi wankan ma tayi ta la'kai-la'kai haka breakfast ma, ba ita ta tafi ba se wajen
1pm,tan d'an sahu taji shigowar text.
      I'm on my way back home

     " Naji"Ta fad'a.

      Tana shiga gida tayi zamanta a d'aki ko kitchen bata kalla ba balle tayi tunanin wani abu shi
girki.Tana yin sallah ta kwanta bacci, bama baccin take ji ba ta dole kawai tayi forcing kanta tayi
baccin.

    3:30pm 'karar doorbell ya tasheta daga bacci,seda ta d'auka mayafi ta yafa dan ta ayyana
shine ya dawo.Fuakarsa d'auke da murmushi  yake kallonta amma ita kuwa...

      Bata tsaya ya shigo  ba ta komo ciki."Laila, you don't like me here?"Ya fad'a bayan ya shigo.

       Shiru tayi bata amsa ba kuma bata cigaba da tafiyar ba haka bata juyo ba.

       "Are you mad at me?"

       "No I'm not" Ta amsa sannan ta hau sama.

      Shide ya rasa gane kanta the more yana showing mata kindness the more tana gudun sa
besan dalili ba.Hakannan ya wuce d'akinsa ya watsa ruwa ,daga shi se singlet ya sakko 'kasa
neman abinda zeci dan yunwa yake ji.

      Babu wani alamar girki daya gani,'karshe se 'bigewa yayi da shan cornflakes,ya fito daga
kitchen d'in ya had'u da Laila.Yanzu ba mayafin daga ita se doguwar riga na material red
colour,'kunshin hannunta ya yi rad'au a fatarta,idanunsa basu sauka a ko ina ba se hannunta.Ba
'karamin dad'i yaji ba ganin tayi 'kunshi,a hankali ya taka zuwa inda take.
    "Beautiful, I like it" Ya fad'a lokacin ya dawo da kallonsa kan Laila.

   Hannayen nata ta 'boye a bayanta tana sunkui da kai.Batayi aune ba taji ya ri'ko hannayenta
biyu kamar yarinya,duka biyun ya d'ago dasu kusa da face d'inshi ta rasa ma abinda zatai illa
tsayawa kallan ikon Allah.

     "Your hands always look good" Kamar 'kiftawar ido taga yayi kissing hannayen ta tsaya uwa
gunki,seda hankalinta ya dawo jikinta tayi saurin 'kwatar hannun ta koma d'aki da sauri ta barshi
a tsaye ya rasa ma mey zeyi sam ya kasa controlling kansa shikansa besan yadda akai haka ta
faru ba.
     Tana shiga d'aki tasa key ta rufe,hannayen nata tayi ta kallo tana tinawa.

      Da'kyar ta iya tashi yin sallahr asr dan tsabar hankalinta ya kasa kwanciya se recalling
take.Yunwa take ji amma ta kasa sakkowa kitchen, har bayan maghrib se shawara take daga
'karshe de ha'kura tayi ta kwanta a haka yunwa na addabarta.

       Washegari 8:12am ya gama shirin office saboda makarar da yayi ko tunanin breakfast ma
beba ,koda ya sakko 'kasa yaga be ganta ba.Haka ya hau bene yayi knocking d'akinta,tana
zaune dama ba zuwa zatai ba yau.

      "Laila" Ya kirata.

   Da farko 'kin amsawa tayi se a karo na biyu ta amsa .

     "Are you not going to school today?"

      "Yes" Ta amsa daga ciki ta'ki tasowa ma daga kan gadon balle ta bud'e 'kofa.

      Jin haka yasa ya kama hanya  ya sauka,yau duk seya ji ba dad'i fitar kasancewar ba
ita.Yana driving kusan rabin hankalinsa baya gurin,ya hau gadar sama yana driving be lura ba
da wuri sega mey d'an sahu ya biyo one way garin kaucewa mey napep d'in   motarsa ta daki
gefen gadar ta fad'a 'kasa,upside down ta sauka ,tayi mugun chanja kamanni,mey d'an sahu ya
daki gini, lokaci guda jama'a aka hau salati a take waje ya d'inke da mutane.

     *Shocked?? Don't forget to comment.*

*Dijensy❤*

     

     

     

     

   

    

    
🌼🌼 🌼🌼


💦 💦


*AMJAD*


💦 💦



🌼🌼 🌼🌼


*WRITTEN BY DIJENSY*

*WATTPAD:@dijensy*

  *Thank you for your warm support sister,Amjad fans kuma ina godiya ,ana tare*


2⃣5⃣-2⃣6⃣


       Mey d'an sahun da aka yi 'ko'karin ciro shi daga d'an sahun aka ga ko numfashi bayayi
,kwance aka ajje shi gefe,daga 'kasan gada kuwa mutane uku ne suka shiga kici kicin bud'e
'kofar motar amma abu ya gagara ,seda ambulance suka 'karaso suka ciro Amjad da 'kyar
sakamakon belt dake ma'kale a jikinsa, jini ya wanke fuskarsa haka aka sanya shi a mota a
sheme.

               ★★★

     2hrs later,tana d'aki tana duba handout wayarta tayi ringing,ganin Canada jikin screen ta'ki
picking.Sau biyu ana kira bata d'aga ba se ana uku."Hello".Cikeda  'kosawa.

      Jin murya daban bana Amjad ba yasa ta gyara zama.Tana jin abinda aka fad'a ta d'ayan
'bangaren ta saki wayar kan gado.

       Ta rasa abinda zatai,wayar ta d'auka ta sake kallan call d'in."Amjad "Ta furta a tsorace.Tafi
10min kafin daga baya ta d'au waya ta kira Mami.

      " Innalilahi wa innailaihirraji'un"Mami ta fad'a.

      "Kina asibitin?" Mami ta tambaya cikin rud'ani.

        "A'a"Ta amsa feeling guilty.

        " Mey kika zauna yi da baza ki tafi ba?"

        "Zan tafi yanzu" Ta fad'a.

         "Toh nima ina tahowa".

Mami kafin ta tafi seda taje gidan Kawu Yunus ta fad'a masa halin da ake ciki,tare suka tafi
asibitin kusan tare suka isa da Laila, Kawu Yunus ne ya kira Dad ya sanar masa.A gabansu aka
shiga dashi theatre room hankalinsu yayi mugun tashi dan yanayin da suka tsince shi.8:15pm
aka fito dashi daga nan aka kaishi d'akin kwanciya,suna kan bench ko d'akin basu samu shiga
se bayan doctor ya fita daga d'akin,Mami da Kawu suka shiga abin tausayi hannunsa yasha
plaster sakamakon karaya se kanshi an zagaye masa da bandage, ga 'karin jini da ake masa.

" Allah ya baka lafiya"

"Ameen" Mami ta amsa cikin nuna jimami.

Kawu Yunus se can dare ya tafi ya bar Mami da Laila data kasa shigowa tana waje kan
bench itama daga baya Mami fitowa tayi ta zauna kan bench d'in.

Mom kuwa basu san mey ake ciki ba se ji sukai Dad yasa su shirin tahowa Nigeria da suka
tambayesa dalili ya'ki fad'a musu.Koda ta kira Amjad d'in ma ta fad'a masa suna zuwa taji wayar
a kashe.

Washegari 9pm suna Nigeria, Mom tunda taga an shigo asibiti jikinta yayi sanyi."Tell me
what's going on?"

"It's Amjad..."

"Mey ya sameshi ? What happened to my son?"

"He had an accident"

Dukansu ba wanda be firgita ba,cikin rashin ha'kuri driver na parking ta fita a motar Dad
yana kiranta amma ta'ki tsayawa,da 'kyar ya samu ta tsaya ganin ba sanin d'akin tai ba.Seda
suka kira Mami ta fad'a musu numbern room d'in.Cikin rud'ani suka 'karasa ,Laila tana zaune
kan bench tagansu tsidik cikin hanzari suka shiga ita de ta bisu da kallo dan har lokacin ta'ki
shiga d'akin.

Har yanzu yana kwance same position ko motsi beyi ba,Mami da Zakia tuni suka fara
tsiyayar hawaye.

"Amjad" Ta 'karasa gefen gadon.

Hannunta ta d'ora kan gashin kansa tana shafawa.

"My child"

Suna tsaye a kansa Mami ta shigo d'akin,bayan sun gaisa suka jajantawa juna Mami se
bawa Mom ha'kuri take amma ta'ki dena sharar hawaye.

"Ina Laila" Mom tayi 'ko'karin tambaya.

"Ta'ki shigowa tana waje" Mami ta amsa.

Mom da kanta ta fita wajenta ta tararda ita ta jingina da alama tayi nisa cikin

tunani."Laila"Ta kira sunanta.

Da sauri ta dawo daga tunanin data tsillima."Mom,Ina yini"Ta gaisheta tana sunkui dakai.

Hannu tasa ta d'ora a kafad'arta."Kiyi ha'kuri kinji,pray for him ze zamu sau'ki"

Kai kawai ta kad'a ba tare da ta d'ago ba,bata ankara ba taji Mom ta jawota jikinta kamar
'yar baby tana shafa bayanta se bata ha'kuri take.Itade Laila tayi lif ita kad'ai tasan abinda take ji
a ranta.

Sun dad'e a asibitin kamar baza su tafi ba Dad ya tashesu suka tafi,aka bar Mom se Laila
Mami ma gida ta koma. Mom bata da buri irin taga ya farka,tafi 1hr tana zaune gefen gadon
tana kallonsa.Laila data shigo d'akin ma daga can baya ta ta tsaya kamar bodyguard ta'ki zama.

Seda dare ya nisa ta zauna kan d'aya daga cikin kujerun d'akin,a hankali gyangyad'i ya fara
d'aukanta daga bisani tayi bacci.Mom data kalleta du setaji tausayinta ya kamata.


★★★

Kullum se su Dad sunzo asibitin ,yawanci su suke kawo musu abinci sometimes Mami ,har
anyi kwana shida amma Amjad be farka ba abin har ya soma damin Mom ko tashi ta shiga
bathroom ba son yi take ba dan gani take kamar idan ta dawo bazata ganshi ba.Laila dan ma
Allah yasa yawancin coaurses d'in duk anyi covering ba zuwa school take ba.
Yau ne ma da Aliya ta kirata take fad'a mata za'ai test shine taje school d'in tana yi ta komo
asibitin.Ganin Dad ,Shaheed Zakia da Kawu duk suna d'akin yasa ta fito ta samu bench tayi
zamanta,sun jima kafin su fito tayi bacci kan bench d'in lokacin 10pm yayi.

★★★

Gidansu Amjad taf yake da mutane,tana shigowa taga su Mami suna zaune kan carpet da
sauran mutanen da ba sanin fuskokinsu tayi ba,Mom ta hanga daga kan step d'in bene gefenta
Zakia se kuka take tana wata magana da baji take ba.Gwiwa a sanyaye ta 'karasa inda suke
bata yi musu magana ba ta haye saman ,'kofa ta gani daga gefen side d'inta a bud'e tana shiga
taga gawa a kan makara cikin likafani ba kowa d'akin a tsorace ta 'karasa tana zuwa taga fuskar
a bud'e ganin Amjad ta saka ihu.

"Amjad!"Ta mi'ke firgit se zufa take ,asibitin yayi shiru se yanzu ta gane mafarki
take,zuciyarta se dukan uku-uku take da sauri ta tashi ta bud'e 'kofar d'akin ta shiga.

Mom ta gani tana bacci a zaune kan kujera,1:28pm agogon d'akin ya nuna.A hankali ta
'karasa gadon tana kallonsa ko 'kifta ido ta'kiyi,gefen gadon ta zauna tana 'kare masa kallo

mafarkin datai yana dawo mata ,zuciyarta ce ta raya mata what if da gaske mutuwa yayi.Tsoro
ne ya hauta lokaci guda, hannunsa ta d'ago ta d'ora a tafin hannunta 'kwallar dake ma'kale a
idanuwanta ta zubo kuka sosai ta shiga yi mara sauti.Mom dede lokacin ta bud'e idanuwanta ta
d'ora su kan Laila dake zaune gefen gadon ri'ke da hannunsa, ganin haka setayi murmurshi ta
maida idanuwanta ta rife a zuciyarta tana mey jin dad'i ta wani 'bangaren tana jin tausayin halin
da Laila ta shiga.Tafi 20min a haka har lolacin bata sake masa hannunsa ba sede yanzu ta
dena kukan,kamar gangan taji motsin yatsansa d'aya a hannunta.Tana kalla taga ba gangan
bane ,a sanyaye ta mayar da hannunsa ta ajje ta mi'ke daga kan gadon zuciyarta kuwa wani irin
farinciki mara misaltuwa ne ya ziyarce ta.Gefe ta samu wani kujerar ta zauna cikin 'kan'kanin
lokaci bacci ya saceta.

Yau ma da safe akai mata waya ake fad'a mata za'ai test dan haka ta shirya ta tafi
school,har se to 12pm akai musu test d'in bayan nan kuma aka shiga lecture,hakannan ta samu
ta zauna se 4pm tukun ta komo asibitin.Tana shiga ta tsaya daga 'kofa ganin mutum ido biyu
tayi yana magana da Mom amma bata san mey yake cewa ba.Ba wanda ya lura da shigowarta
se Zakia ta kira sunanta,se lokacin kallo ya komo kanta Amjad yana daga kwance ya kallota a
wahale idanunsa sun 'kan'kance fuskarsa ta nuna alamar ramewa.

"Laila,I'm glad you're back" Mom ta fad'a tana kallonta sannan ta komar da kallonta kan
Amjad irin alamar ya farka d'innan take nuna mata.Kallo d'aya ta sake yi masa ta kawar da
kanta,duk wani move datake yana kallonta gashi ko magana yaga ta'ki yi ,su Mom kuwa basu
ma lura da hakan ba.Mami da sukai waya da Mom take sanar mata ya farfad'o tare da kawu
suka zo suka duba shi daga nan ta sake tahowa da Laila wasu kayan nata.Se 9:30pm suka bar
asibitin aka bar Mom da Laila,gabaki d'aya ta kasa sake wa fiye da da.

"Amjad you need to eat" Mom ta fad'a dan tun d'azu da rana dayaci chicken spaghetti be
kuma cin wani abu ba.

"No I'm ok"

Fruit salad d'in ta samu ya sha kad'an,ita de Laila kallonsu kawai take duk abinda
suke,jinta take a takure dama ta koma gida da yafi mata take fad'a a zuciyarta.Bayan yasha
magani ya kwanta bacci daga baya Mom itama tayi,Laila 'karshe se tunanin yadda zata 'kare
wannan zaman take.
Washegari 5:40am Mom ta tashi bayan tayi sallah Amjad ya farka ta taimaka masa yayi
taimama yayi sallah,Laila dama bayin sallah zatai ba amma dukda haka takan tashi sede kuma
yau baccinta tayi har se wajen 7:30am ta farka.Tana bud'e ido taga Mom tana gefen d'anta tasa
abinci a gaba tana bashi yana ci da 'kyar,duk kunya taji ta isheta tashar'bi bacci surukarta na
kallo abin kunya tayi tunani a ranta.Kamar ko yaushe cikin rissinawa ta gaisheda Mom ganin ido
yasa shima ta gaishehi harda tambayarsa ya jiki, shikuwa ya'ki amsawa yayi kamar beji ba.

Bayan awanni kad'an sega su Zakia sunzo asibitin,dama haka take so tana ganinsu tayi

fitowarta ta fita can waje ta samu bench ta zauna tana kallon shuke-shuke.

"Mom are you staying here until..." Shaheed be 'kare magana ba Mom tace."No..no I'm not
going to stay here beside I' m going back home today"

"What? Are you leaving me like this?"

"Amjad ,Laila is here and I think is ok like that"

"Yes!" Zakia da ba da ita ake ba ta tsomo baki.

Kallonta kawai yayi ya kawar da kai ba tare da yace komai ba dan yanzu ba lokacin wannan
bane.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
google.com, pub-9213700357025247, DIRECT, f08c47fec0942fa0