Showing 42001 words to 45000 words out of 60755 words
tayi da sauri
tana kici-kicin bud'e 'kofar bathroom ,kamar rufewa take sake yi 'kofa ta'ki bud'uwa,haka ta gaji
ta 'kyale 'kofar amma ta'ki waigawa ta kalli inda yake.
"Mey zeyi a d'akinnan inba neman masifa ba?"Ta fad'a a ranta.
" What are you waiting for?"
Ta'kowa yayi ya 'karaso har inda take ya mi'ka mata Biro"You left it in my car?"
Ko waigowar arzi'ki ta kasa illa mi'ka hannunta da tayi ta kar'ba sede kuma bawai ya cika
biro d'in bane duka, yana ri'ke da farko tana ri'ke da 'kasan biron. Tunda ga sama har 'kasa
yake ta binta da kallo tana jin idonsa a kanta ta rasa inda zata saka kanta ji take kamar ta nutse
a zuciyarta se zagin towel d'in take dan iya cinya yake ,biron ta sake masa ganin ya'ki cikawa
shima sakinsa yayi ya fad'i 'kasa.
"Pick it up"Taji ya fad'a cikin tattausan harshe.
" Innalilahi"Ta fad'a a ranta.
"I ca.." Bata 'kare ba ta tsaya da maganar dan kar ayi irin ta jiya batasan ya za'a 'kare ba.
A sanyaye ta waiwayo tana dafe da towel d'in ta dur'kusa ta d'auka jelar gashinta dake ta
kwanta gadan bayanta.Tana d'aukan biron bata ko tsaya a ko ina ba se wajen wardrobe cikin
sauri ta ciro hijab ta zira,yana kallonta ta gama zire-zirenta be sake cewa komai ba ya fita daga
d'akin.
"Yanzu akan biro shine za'a biyoni har d'aki mtcww!"
Tun bayan komawarsa d'akin ba abinda ke yawo a kansa irin image d'in Laila a yanayin
daya ganta d'azu,da yayi 'ko'karin kauda tunaninta seya kasa ,laptop d'insa ya d'akko ya soma
dann-danne amma sam hankalinsa ba anan yake ba faga baya ya d'auki waya ya soma game
a thinking of Laila,pillow ya d'ora kansa ya kwanta ko zeyi bacci.Ko Rosie da take sak English
wears matsastsu dasu mini skirt be ta'ba jin abu a kanta ba kamar irin Laila."She is pretty"Yaji
zuciyarsa ta fad'a.
Laila kuwa bayan ta gama shirinta cikin atamfa riga da skirt ta d'aura d'ankwalinta,lokacin
ruwan ma ya tsaya yamma tayi li'kis maghrib ya kusa.Windown d'akin ta bud'e tana kallon
yadda flower plants sukai kore shar ga furannnin sunyi fresh sosai view d'in ya birgeta jitake
kamar ta sakko sede kuma tana gudun had'uwarsu.Seda taji anyi kiran sallah ta zuge windown
d'in tayo alwala itama.Bayan ta idar da sallah kuwa a jakarta ta d'akko meatpie data siya a
school gida biyu ta soma ci dan yunwa ta isheta,taci abu kuma ba ruwa.
Shawara tayi-tayi daga 'karshe de ta sakko 'kasa,cikin sand'a ta shiga kitchen da sauri ta
d'akko bottle d'in ruwan ta fito zata hau sama taji 'karar tsawa ,harda dur'kusawa kamar wacce
za'a kama."Terrified"
Bata kalli inda take tsammanin daga nan yake ba tayi sauri ta hau sama,tana shiga d'akinta
ta rufo ,ba ita ta sake fitowa ba se washegari.
Yau d'inma da sauri ta yi shirinta sede tana sakkowa 'kasa ta ganshi a dinning yana shan tea
se biscuit a da'n plate.Da kamar ta koma kuma ta daure ta wuce kitchen."Morning "Taji ya fad'a.
Ko amsawa kasa yi tayi na d'aya tasan ita bata ta'ba gaisheshi ba na biyu bata sani ba ko
d'aya daga cikin abunsa ne na tsokana.A kitchen d'in ma ta rasa mey zata dafa,dankali ta soya
tayi 'yar chicken sauce.Sauri tayi taci gudun kar ayi ta d'ayan ranar yasa koh wanke plates d'in
bata tsaya yi ba.
Tana fitowa ya bar wajen,direct ta koma d'aki ta d'akko jakarta,cikin 'kan'kanin lokaci ta fito
daga gidan.Yana komawa d'aki ya d'akko key d'in motarsa,ganin bata kitchen yasan har ta
fice.Ba 'bata lokaci ya fita,a hanya ya tarar da ita tana tafiya,horn yayi tayi mata amma ta'ki
juyowa,sede ya fito yayi mata magana tukun ta shiga.
" Ko yaushe aka gyara motar?"Ta tambayi kanta.
"Oho" Ta fad'a.
Shiru bame cewa komai har suka isa makarantar,tana fita ta rufo 'kofar ta kama hanya ta
wuce,be ja motarsa ba har seda tayi nisa yana kallonta kan daga bisani ya tafi.
Tunda ya shiga office ko aikin kiriki ya kasa banda tunanin Laila ,tun farkon aurensu zuwa
wannan lokacin yayita tunawa.Shi kad'ai yana murmushi,ana knock a 'kofar office d'insa amma
hankalinsa baya gun.
"Sir,sir!" Yajiyo ana kiransa.
Se lokacin ya farga ya dawo daga duniyar tunanin daya tafi.
2:30pm nayi ya tashi daga aiki be tsaya ko ina ba se school d'insu Laila. Da farko yayi niyyar
kiranta daga baya kuma ya fasa dan yasan zata iya 'kin fitowa.Haka ya zauna a mota zaman
jira kad'an-kad'an yana ganin students na fitowa amma be hangota ba ya kwashe kusan 1hr
20min kafin ya hangota tana tahowa bakin titi.Motarsa ya 'kara yin gaba da ita dede inda take a
tsaye ya sauke glass d'in motar.Ta kalleshi sarai amma seta matsa gefe,tana jin wasu cikin
'yan mata a gurin suna gulmarsa.
"Yana shigowa school d'innan,ko d'azu naga motarsa".
"Wannan za'a ga kyawawan 'ya'ya"
" Kamar balarabe ne naga" D'ayar tace"A'a bature ne.
"Ke india ne bakiga irin gashinsa ba ai turawa farin gashi garesu"
Ita dariya ma suka so bata dan yadda taga hankalinsu yana kanshi se kallon motar suke
kamar saje su shiga.
Basu suka rud'e ba seda suka ga ya fito,basu kad'ai ba hatta wasu mata dake gefe seda
suka kalleshi.Tana ganin tahowarsa ta gefen ido ta'ki juyo wa."Laila come on get into the
car"Taji ya fad'a cikin tattausan harshe.
Gefen fuskarta ta waigo tayi masa wani kallon banza,ita bata so taga yana shishshige
mata"Nina ce kazo d'aukana"Ta fad'a 'kasa-'kasa dan beji mey tace ba.
Badan kar ta yarfa shi cikin mutane ba da bazata bishi ba,a hankali ta taka wajen motar.Kallo
suka bita dashi suna mamaki."Wace wannan d'in?"
"Matarsa..."
"A'ina d'in"
"Matar aure ce ai" Wata daga cikinsu ta fad'a.
Da ido suka bi motar da kallo har suka bar gun suna mamaki.
"How was the lectures?"
Banza tayi dashi bata amsa ba kamar bata ji ba tama kawar dakai tana kallon window.
"Are you hungry?" Ya sake mata wata tambayar.
"A'a" Ta bashi amsa a ciki ciki.
Ganin ba son magana take ba shima yai shiru a tunaninsa ko stress ne.Suna komawa
gida ya sake fita cikin 'yan mintina se gashi ya dawo da leda a hannunsa.
"Knock! Knock! Taji an bugo 'kofar d'akinta ko wankan ma bata shiga ba,hijab d'inta ta zira
tukun ta bud'e.Ledar ya mi'ka mata fuskarsa a sake ita kuwa ko d'an sakin fuskar ta'ki yi,hannu
tasa ta kar'ba batace komai ba ta koma ciki ta ajje kan drawer, da ya tsaya kamar zeyi wata
maganar se kuma yayi shiru ya tafi d'akinsa.
" Better "Ta fad'a.
Se bayan ta fito daga bathroom ta duba ledar,burger ne da baguettes se sauce da tana
bud'ewa ta ta'be baki "'Karni ma take Allah kad'ai yasan wacce ta dafa,Allah yasa ba miyar
'kwad'o bace dan shima baze rasa ci ba ko kuma ma tsutsa"
Koda ta gama shirinta bata kalli abincin ba dan a 'koshe take ,haka ta 'karachi zamanta har
se bayan isha'i ta janyo ledar ,burger d'in kawai taci ta ajje saura baguettes d'in kuma ta sauka
'kasa a kitchen ta ajje, miyar kuma ta ajje a fridge.Cock da bottle of water ta d'auka ta komo
,tana hawa bene shikuma yana sakkowa daga d'aki sukai karo har kayan hannunta suna
fad'uwa,kusan shine sila tunda shine da sauri-sauri yake sakkowa.
*Don't forget to vote, comment and share.love urí ½í²‹*
*Dijensy❤*
í ¼í¼¼í ¼í¼¼ í ¼í¼¼í ¼í¼¼
í ½í²¦ í ½í²¦
*AMJAD*
í ½í²¦ í ½í²¦
í ¼í¼¼í ¼í¼¼ í ¼í¼¼í ¼í¼¼
*WRITTEN BY DIJENSY*
*WATTPAD:@dijensy*
2⃣3⃣-2⃣4⃣
Nan take ta dur'kusa tana dafe 'kafarta,ha'kuri ya shiga bata "I'm sorry ,I'm so sorry Laila".
" Ba wani sorry kana sani"Ta fad'a tana ri'ke da 'kafar.
Cock d'in ta kalla daya gangara 'kasa dan shi take tunanin ya fad'o mata a 'kafar.Mi'kewa tayi
tsaye ta fara tafiya amma ta 'kasa take 'kafar se d'ingisawa take."Let me help you"Ya taho da
shirin ri'ke hannunta ya d'ora a kafad'a aiko tayi saurin matsawa garin haka ta take
'kafar."Aghh!"Ta tsala 'kara.
Bata ankare ba taji an raba ta da 'kasa anyi mata d'aukan amarya, tuni ta shiga wutsul
-wutsul tana d'uma masa duka a kafad'a."Mami!"Ta hau kiran sunan Mami.
Har seda ya kaita d'akinta sannan ya direta kan gadon."Stubborn ".Ya fad'a.
"Nan da nan idanuwanta sun cika da 'kwalla seda taga ya sauketa a d'akinta ta d'an nutsu."
You can leave now"
"You're sending me away,what did you think I'm doing? Sometimes you're crazy"
Fita yayi daga d'akin bayan 'yan minti kad'an ya dawo da man zafi a hannunsa.Jira take
taga abinda yake 'ko'karin yi,tana gani ya zauna gefen gadon tare da ri'ke 'kafar ta matsar da
'kafar."Na iya shafawa"
Duk da be fahimci abinda ta fad'a ba ganin ta matsar da 'kafarta ya mi'ka mata man "Rub it".
Kar'ba tayi cikin sanyin jiki ta bud'e man ta soma shafawa a 'kafar a hankali sekace mey
tallan mai.Ta sakankance taga ya wafce man ya soma shafa mata yana matsa 'kafar,hannunsa
tasa tana 'ko'karin janye nasa hannu amma ta kasa sema ri'ke hannayenta biyu da yayi waje
guda ta kasa ku'bucewa ,haka tayi ta raki har seda ya gama.
" Toh sake min hannun tunda ka gama"
"Mey kika fad'a?" Taji yayi magana.
"Tunda ka iya yaran ai zaka sani"
"I can speak hausa for the whole entire day"Yadda yayi pronouncing d'in hausar kamar like
" Hosa"
"Ok,start"
"Ok,yanzu" Ya fad'a yana murmushi.
Itama murmushin tayi tana kallon arm d'insa data buga d'azu har wajen yayi ja kasancewar
singlet ce a jikinsa.Shikuwa murmushin datai ne yasa ya kasa dena kallonta dan ba 'karamin
kyau tayi ba.Saurin kawar da ido tayi ganin ita yake kallo,wayarta dake gefe ta d'auka ta hau
dubawa dukda ba abinda take da ita.
"Na fita?"Taji ya tambaya.
"Eh"Ta amsa kanta a sunkuye.
" Ok,I'm going but you have to answer my questions "
"Questions".
"Yes".
Kai kawai ta girgiza tana tunanin irin tambayar da zeyi mata."Do you have feelings on me
? don't lie"
Sam batayi tunanin wannan tambayar zeyi mata ba duk da bata rasa amsar fad'a masa ba
sede kuma tana mamakin dalilinsa na tambayar.Ya tsireta da ido kawai jiran amsarta yake.
"No" Ta amsa ba tare da ta bari sun had'a ido ba.
"No" Ya maimaita abinda ta fad'a.
"Ok,let's assume I love you? Will you love me back?"
"No"
"Why?"
"Because I don't love you"
"Your heart is for only one person?"
"I want to sleep" Ta fad'a tana janyo blanket d'in.
"Are yo sleeping like this?"Ganin ba sleeping dress bane a jikinta.
" Uhm"Ta rufe kanta.
Tashi yayi yazo fita ya kashe wutar d'akin sannan yaja 'kofar,tana jin fitarsa ta bud'e kanta,
tambayoyin da yayi mata ta shiga yi ,seda ta jima kafin bacci ya d'auketa.
12:13am ya farka daga bacci ,da tunanin Laila a ransa ya farka.Drawer side lamp ya kunna
ya tashi zaune agogon d'akin ya kalla yaga 12am,mi'kewa yayi tsaye ya bud'e 'kofarsa ya fita
zuwa d'akinta,yana murd'a handle d'in yaga a bud'e 'kofar ma take.Tana ta baccinta yau ma
tafin hannunta na kan fuskarta kamar rannan hakan yasa shi yin murmushi yanzu ya fahimci
d'abi'arta ce haka.A hankali ya d'akko stool d'in mirrorn d'akin ya ajje opposite da ita ya zauna
se 'kare mata kallo yake,tuna ko pic d'inta bashida yasa ya koma d'akinsa ya d'akko wayarsa ya
komo ,hannun data kare fuskarta dashi ya matsar yadda fuskarta zata fito,pictures kala-kala
yayi ta d'auka har kusan 12:40am tukun ya koma d'akinsa.
★★★
Kwanaki suna sake yin nisa ,Laila lecture d'insu yayi nisa kullum Amjad ne yake kaita
school baya ta'ba bari ta tafi da kanta,hatta dawowa gida wasu lokutan shi yake d'akkota hatta
saba ma yanzu ta dena gudun.Haka ta 'bangaren abinci ma inde tayi girki zeci inba wai yaga
besan irin abincin ba.A kullum Laila sake shiga ransa take duk wani abu da tayi birgeshi take
haka idan yana office yata kallon photos nata kenan ,tunanin ta ba 'karamin d'auke masa
hankula yake ba daga al'amuransa na yau da kullum ana meeting seya tsinci kanshi yana
tunaninta wanin sa'in harse P.A d'insa ya masa magana.
Yau ma bayan ya tashi daga aiki ya biya mall 'yan siyayya,wani henna ya gani wanda ya
tuna masa da 'kunshin da Laila tayi kwanakin baya,jiyai yanaso yaga ta sake yi dan haka ya
siya mata.
Yana zuwa school d'insu tana fitowa,suna tafiya yana mata tambayoyi da suka shafi school
d'inta rabi maganar da yaran hausa yake dan yanzu ya fara iya hausa sosai sede wajen
pronouncing ne ake samun kura-kurai , kad'an -kad'an take bashi amsa dan ita har yanzu ta'ki
sakin jiki dashi.Seda suka isa gida tazo fita ya kira sunanta."Laila"
Tana juyowa taga ya mi'ko mata package na henna d'in.Seda ta 'karewa lallen kallo sannan
ta dawo da kallonta kansa daga bisani kuma ta kar'ba ba ko godiya tayi ficewarta.
Tana shiga d'aki ta bud'e drawer ta ajje ciki ta rufe ta wuce bathroom tana fitowa bayan ta
shirya tayi sallahr asr.
Knock!Knock! Taji bugun 'kofarta.Dama hijab d'in ta na jikinta ta tashi ta bud'e,yana tsaye
bakin 'kofar fuskarsa d'auke da murmushi.
"I just wanna inform you that I will take a trip tomorrow morning"
Kai kawai ta kad'a a ranta dad'i kamar ta ziba ruwa a 'kasa tasha.
"Alhamdulillah " Ta fad'a a ranta.
Dama gobe Saturday bikin Bahijja 'kawarta,tasan idan yana nan ba yadda za'ai ta kwana a
gida yanzu kuwa setai amfani da wannan damar.
Yayi tunanin zega ta damu amma yaga sa'banin hakan ,du seyaji jikinsa yayi sanyi,gwiwa ba
'kwari ya koma d'akinsa.
Laila da farinciki ta kwana a ranta da sassafe ta soma had'a kayanta,dan tsabar farinciki
kota kan breakfast bata biba,se wajen 9:30am ta sakko 'kasa a kan dinning ta hangi wata
takarda dake ninke.Har zata shige ta ta dawo, tana bud'ewa taga short note.
I'm sorry for leaving without saying goodbye, I don't wanna wake you up.
Amjad
Duk da ba wani damuwa tayi ba amma seda taji wani iri dan tayi tunanin yana d'aki,ninke ta
tayi ta ajje kan table d'in sannan ta shiga kitchen had'a breakfast.
Cikin azar'ba'bi tayi sauri tayi breakfast tana kammalawa ta koma d'aki ta shirya,kit d'in
data sa kayanta ta d'auka ta fito daga gidan ,a hanya ta kira Maryam ta fad'a mata tana
tahowa.Laila tana isa gida ta tafi gidan 'kunshi aka tsantsara mata ta dawo gida.
"Gan d'oki" Mami ta fad'a.
"Nice fa babbar 'kawa Mami"
"Da haka nan aka ce kiyi 'kunshi da tuni kina nan kina zun'buro baki amma dayake kin sa
kanki har rawar jiki kike"
"Kwana nawa zeyi?"
"Sati d'aya" Tayi 'karya.
"Abin nema ya samu"
Kallon Mami kawai tayi a ranta ta san 'karya take.Wajajen 4:30pm ta tsantsara kwalliyarta
ta rangad'a d'auri ta yafa gyale d'an 'karami ta fito.
"Inde a haka zakije kuwa sede bazaki fita ba,haka kike fita mijin naki ya barki?"
"Mami biki ne fa?"
"Koh meye zaki wani d'ora mayafi a wuya ke bakisan babbancinki da 'yan mata ba?"
Bata fita ba seda ta koma ta sauya mayafin ,ita kad'ai ko 'yan rakiya ma bata d'auka ba.
7:30pm ta komo gida Mami