Showing 1 words to 3000 words out of 57967 words

Chapter 1 - Anya Baiwa Ce 1 Complete Hausa Novels

[21/10/2021, 19:43] Ameera Adam🌚: 11..


Maganar Boka Marduska na sauka a kunnen Fulani Maryama ji tayi kamar saukar aradu
muryarsa har wani amsa kuwwa take mata a kunne, nan take jikinta ya É—auki tsuma bakinta har
tuntuɓem harsge yake a hargitse ta ce. "Marduska ka taimaka mun ka tallafi rayuwata ka sanar
dani ta yaya zan gane wace ce ita?" Boka Marduska wani kallo ya wurga mata yana ci gaba da
hura wutar da ke cikin ƙoƙan ƙan ƙwarangwal yace. "Maryama me yasa taurin kai gare ki ne?
Wannan maganar ba baƙuwar magana bace a gurinki ni kaina bazan iya ja da wannan yarinyar
ba, hasali duk wani bincikena na gagara nemo ainihin kamannin yarinyar, abinda nake ta
shakku a raina wai ma mutum ce ko itama ta fito cikin sigar aljanu? WaÉ—ancen da suka shuÉ—e
ɗaya ta fito cikin fararen aljanu ɗaya kuma ta fito daga baƙaƙaen aljanu. Abin da ban sani ba
shin wannan ita daga wanne ɓangare take, taimako ɗaya zanyi miki Maryama idan har bincike
ya bani dama..." Fulani Maryama har kusan faÉ—awa kanshi tayi jiki na rawa katse shi.
"Marduska ka taimaka mun ko kamanninta ne ka gaya mini ta yadda zan fahimci wace ce daga
ciki" Marduska ya tsuke fuska yace. "Maryama me yasa kin fiya rawar kai kamar wacce taci
sadakar miji ne? Kinsan Allah da kin faÉ—a kan wannan wutar da kin gwammaci haÉ—uwarki da
Rayzuta dukda kuwa karonku da ita ba alheri bane, kinsan wannan wutar ko yaya ta taɓa jikinki
sannu a hankali nama jikinki zai fara zagwanyewa ga É—oyin da zaki dinga yi kamar mushe"
Fulani Maryama ta russuna ta ce. "Tuba nake sarkin bokayen duniya."

Marduska ya cigaba da bincikensa a cikin wuta yana jefa waÉ—ansu littafan tsafinsa, daga cikin
wuta take wani fili ya bayyana, wata matashiyar budurwa ce a tsaye ta juya baya hannunta na
saƙale da wani matashin saurayi." Yarfe gumin fuskarsa yayi sannan yace. "Maryama zo ki
gani" Da sauri Fulani Maryama ta fara leƙawa fuska ɗauke da damuwa ta ce. "Marduska ban
gane komai ba na hangi mace da namiji a tsaye, ka taimaka ka wayar mun da kai ka dubi
girman tsafi ka siffanta mini ita" Marduska yace.

"Yarinyar Æ´ar doguwa ce amma ba tsayi cen sosai ba tana da É—an kauri kaÉ—an, kuma ba fara
bace ba kuma baƙa wuluk bace. A taƙaice ruwan tarwaɗa ce sai dai a fuska kyakkyawa ce tana
É—auke da manyan idanu da dogon hanci yanayinta kamar na buzaye sai dai har yanzu ainihin
siffarta yaƙi bayyana ta yadda zamu gane wace ce ita ya kamanninta yake, ni ina jin tsoron
bincike akanta sabida rannan dana tura aljanu su É—auko mun ruhin baiwarki Bintu ta kashe mun
aljanun da suke mun wannan aikin, ina gudun karta fara waiwayo ni saboda tana É—auke da
ƙarfin iko akan mutane da aljanu." Fulani Maryama gabaɗaya ta haɗa gumi sai zare ido take
kamar shege a rabon gado, hankali a tashe ta ce. "Marduska gabaÉ—aya kaina ya kulle ga
wannan yarinyar ga warkewar Saif yanzu wane magani zaka bani wanda zai kuma nakasashi
kuma idan na gano wace ce ita wane irin mataki zan iya É—auka a kanta? Zan iya nasaka ta ko
kuma na illa ta ta." Marduska wani kallo ya wurga mata sai kuma ya bushe da wata irin dariya
har yana ƙyaƙyatawa.

Sai da ya yi me isarsa sannan ya kalli Fulani Maryama da ta haÉ—e fuska kamar zata yi kuka,
yanayinta ba ƙaramin ɗariya ya bashi ba nan take ya kuma bushewa da dariya ya ce. "Lallai

Maryama yanzu na ƙara tabbatar da baki da hankali, yarinya da nace miki ta hallaka aljanu ita
ce zaki iya karawa da ita? Shin idan hankalinki ya tashi tunaninki gushewa yake yi ne? Bazan
ce miki komai ba ga fili ga me doki dan haka jiki magayi, wai bahaushe yace kowar tuba dan
wuya ba daÉ—i. Idan kina ganin zaki iya da ita sai kin gwada, amma ki sani wannan abinda zakiyi
kamar tarar aradu da ka ne. Shawara É—aya zan baki ita ce, bayan kin gano ta kiyi yadda zakiyi
Sarki Aminullah ya koreta daga cikin masarauta ta hanyar ƙulla mata sharri ko wani abun,
wannan ita ce damar da zakiyi nasara akanta. A ɓangaren yaron kuma maganar gaskiya sai dai
kiyi haƙuri dan babu wani abu zan iya aiwatarwa akanshi saboda ina gudun fushinta ya sauka
akaina, ina me tabbatar miki wanann kogon da nake ciki tana iya rushe mu dasu gabaÉ—aya da
ni da komai mu hallaka."

Fulani Maryama gabaÉ—a zuciyarta ta gama dagulewa rasa abin yi tayi nan take ta rushe da
wani irin matsanancin kuka.

Sai fa tayi me isarta sannan ta fyace majina ta ce. "Mardusk me yasa al'amura suke ƙoƙarin
juya mun baya ne, naji shawararka kuma zanyi amfani da ita kuma ina san ka ƙara mun ƙarfin
iko agurin Takawa, ta yadda duk abinda na bashi umarni zai zartar ba tare da ya musa mini ba."
Boka Marduska É—an jim yayi sannan yace. "Wannan kam za'a iya aiwatarwa sai dai me zaki
fansar mun saboda banasan na ƙara tura aljanu na nayi asararsu."Fulani Maryama ta ce. "Faɗi
duk abinda kake so ya kai wannan babban boka mai cikakken iko" Boka Marduska yace. "Ga
wani farin ƙyalle cen a cikin tsohon kabarin ce ki ɗauko shi ki dangwalar min jinin da kike yi na
ɓarin cikin da kika yi." Fulani Maryama kanta tsaye ta wuce wajen da Boka Marduska ya nuna
mata ta aiwatar da ya umarceta sannan ta dawo gurinsa, tana dawowa Boka Marduska yace.
"Tashi karki zaune mini wuce ki tafi wannan buƙatar dai ta biya sai dai wata kuma." Yana gama
faɗa ya ɓace daga gurin, Fulani Maryama miƙewa tayi ta fice daga cikin kogon dutsen.


Lokacin da Fulani Zaliha ta ƙarasa gurin Saif da yake ta kwara amai riƙe shi tayi cikin tashin
hankali tana kururuwar neman ceto, da sauri wasu bayi suka ƙaraso gurin suka taimaka mata
suka rirriƙe shi da alama baya cikin hayyacinsa, jikinsa banda karkarwa babu abinda yake yi ga
wani irin zafi da jikinsa ya É—auka. Hatta da gumin da ke tsattsafowa ta jikinsa da wani irin zafi
yake fitowa, Bayin da suka riƙe shi gazawa suka fara ƙoƙarin yi saboda zafin da yake azabtar
da hannunwansu. Fulani Zaliha da gudu da nufi fadar Sarki Aminullah ta sanar dashi halin da
Saif yake ciki, Salman na gefensa yana jin haka ya fara cika yana batsewa haÉ—e da wurga mata
wani mugun kallo, cikin kallan tsana yace. "Wai kina nufin kwantaccen ne ya tashi?" Sarki
Aminullah ya kalleshi yace. "Nima abin da nake mamaki kenan Saif yaron da ko rarrafe bayayi
sai jan ciki wannan lamarin da mamaki" Fulani Maryama ranta ba ƙaramin ɓaci yayi ba ta ce.
"Kai hawainiyarka ta kiyayi ramata a hir É—inka banasan rashin kunya wallahi duk ranar da
bakinka ya ƙara kuskuren laƙabawa ɗana mummunan suna irin wannan ranka zai yi mugun
ɓaci" Salman dariya ya bushe da ita sannan yace. "Ƙarya nayi ba kwantaccen bane ko kina
bakin ciki ne baya taka ƙasa har yanzu?" Fulani Zaliha a hassale ta kife Salam da mari ta ce.
"Da alama tarbiyya tayi ƙaranci a gurinka..." a zafafe Sarki Aminullah ya katse ta. "Ke Zaliha
baki da hankali ne? A gaba na kike niyyar nasaka É—ana saboda naki É—an nakasasshe ne? Daga

yau karki ƙara idan ba haka ba zan ɗauki mata ki akanki kuma matakin bazai miki daɗi ba."

Idanun Fulani Maryama ne suka ciko da ƙwala ta ce. "Ranka ya daɗe ni kake cewa
mahaukaciya akan wannan yaron shikenan ni ka wulaƙanta akanshi ko? Wallahi na gaji yau
tsawon shekaru amma da ashirin ana abu ɗaya nida ɗana bamu da ƴanci sai wulaƙanci da cin
zarafi, kullin ka tashi baka taɓa alaƙanta Saif da Ɗanka sai dai kace Ɗanki to babu komai tunda
baka ƙaunarmu zamu fita daga rayuwarka, gani kake idan bama tare da kai bazamu iya rayuwa
ba ko? Babu komai idan adalci kake mana zaka gani idanma ba adalci kake yi ba zaka ga..."
bata ƙarasa maganar ba Sarki Aminullah ya zabga mata wani gigitaccen mari harsai da ta
durƙushe a gurin, wani irin matsanancin kuka ta rushe da shi jiki ba ƙwari ta tashi ta fice daga
gurin.

Lokacin da ta koma Saif na kwance a gurin yana ta malala wani irin amai, sauran Bayin duk
sunyi carko-carko a gurin Fulani Zaliha banda hawaye babu abinda take yi. Da sauri ta kira
wasu Dogarai ta sa suka É—auki Saif suka wuce da shi cen sashenta, wucewarsa da shi yayi
dai-dai da dawowar Maryo saboda yadda taga yana aman ba ƙaramin tausayi ya bata ba,
hanyar sashen Fulani Zaliha zata bi dan ganin halin da yake ciki, da sauri Abu da janyo ta tace.
"Ke Maryo me kike shirin yi haka? Dan kinga yau da safe mun shiga sashen Fulani Zaliha shine
yanzu zaki koma?" Bakisan yanzu da bambamci tsakanin É—azu da yanzu ba? Ke fa yanzu
Baiwar Fulani Maryama ce kinsan idan labari ya ishe mata ranki zai yi mummunan ɓaci? Wai
ma wace ce ke a gidan nan da zaki dinga tura kanki cikin Mutane masu daraja, karki manta mu
fa Bayi ne ƙasƙantattu marasa galihu ɗazu ina ce saƙo muka kai gurin Fulanin" Maryo da
idanunta suka ciko da ƙwalla ta ce. "Abu ni kaina bansan me yake damuna ba sai nayi kamar
na koma sashen mu sai kuma gangar jikina ta hanani aiwatar da haka, sai in dinga jina kamar
yana da haki akaina idan ban taimakeshi ba kamar ban kyauta ba. Wani tsagi na zuciya ta na
yawan raya shakku akan ni kuwa ANYA BAIWA CE? Sai in dinga wani irin tunani daban" Abu ta
ce. "Wane irin taimako zaki yi masa baki ji labarin da aka bamu ba akace masu magunguna da
yawa sun mutu akanshi, ki rufa mana asiri Maryo mu zauna lafiya a gidannan banda ma
yaudarar kai har kin dinga tunanin ke ba baiwa bace idan ke ba baiwa bace mece ce?"

Maryo ta ce. "Tambayar da har gobe bani da amsar ta hasalima bansan da me zan taimaka
masa ba amma wallahi Abu tun É—azu da nayi arba da wannan É—an Sarkin naji zuciyata ta harba
akansa lokaci ɗaya naji na kamu da ƙaunarsa." Abu ƙwalalo idanu tayi da sauri ta fisgi hannun
Maryo ta ce. "Maza zo mu wuce tun ba'a yanke mana mummuna hukunci ba."
Maryo ba dan ta so ba ta bi Abu suka wuce cen saahen su na Bayi kai tsaye suka wuce
madafa domin sarrafa abincin da zasu ci. Bayan magari ba suna zaune a tsakar gida saboda
zafi suna shan iska, daga cen nesa ta fara ganin giftawar mutane kamar wacce a ka tsikara
haka ta tashi, suna ganin tasowarta suka juya suka fice daga gurin ita kuma ta rufa musu baya.
Basu tsaya a ko'ina ba sai tsakankanin manyan bishiyoyin kukar nan guda biyu. Tana zuwa
gurun ta hangi mace mai kama da ita sak tana rungume da wani namiji jikinsa duk jini da alama
baya numfashi, matsawa ta fara yi a hankali tana ƙare mata kallo sai dai da alama kuka take
rerawa cikin wata irin murya. Maryo matsawa tayi zata taɓa ta sai ji tayi ance. "Kije ki ceci

rayuwarsa yana cikin wani hali wannan ne kawai taimakon da zaki iya yi masa."


_LITTAFIN ANYA BAIWA CE? NA KUÆŠI NE DA NAIRA 200 ZAKI KARANTA SHI CIKIN
KWANCIYAR HANKALI, ZAKU BIYA TA WANNAN ACCOUNT ÆŠIN, FIRST BANK 3090957579
AISHA ADAM, ZA'A TURO DA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR,0706 206 2624, DAN
GIRMAN ALLAH IDAN KINSAN ZAKI FITARMUN DA LITTAFI NA YAFE CINIKINKI._ [23/10/2021, 19:44] Ameera Adam🌚: 12...

ÆŠaga kanta tayi tana waigen me maganar amma babu shi babu alamarsa dawo da kallonta
tayi wajen me kama da ita, tsugunnawa tayi tana ƙare musu kallo, a hankali ta sa hannu zata
taɓa ta saboda yadda taga tana gursheƙen kuka, ba ƙaramin tausayi ta bata ba. Tana kai hannu
taji ta ce."Dan Allah ki ceci rayuwarsa iya abinda zan iya sanar da ke kenan bana fatan sake
rasa shi" tana nan durƙushe ta hango wani ya tunkaro gurinta kafin ta ankara taji ya fara fisgarta
da ƙarfin tsiya, Maryo so take ta ƙwace amma ta gagara saboda mutumin ya fita ƙarfi nesa ba
kusa ba, yana cikin janta ta fara kururuwar neman taimako tana ihu haɗe da roƙo kamar wacce
ta tuna abu haka ta fara karanto addu'in da duk suka zo bakinta, nan take taji ya saketa kuma
ya ɓacewa ganinta.

Waigawa tayi ta hango har zuwa lokacin wannan mace da namijin suna zaune da hawaye
ɗauke a fuskarta, daga cen nesa taji ana ƙwala mata kira ba ƙaƙƙautawa jiki a sanyaye ta juya
da niyyar ta ƙarasa gurin da take hango wannan mace da namijin da sauri taji Inna Habi ta ja
hannunta tana cewa.
"Ke Maryo kanki É—aya kuwa me yake damunki zaki taho dokar daji a daren nan lafiyarki
kuwa?" Maryo idanunta ne suka ciko da ƙwalla ta ce. "Inna wallahi sai roƙona suke akan na
taimaka musu ni bansan taimakon da zanyi musu ba, amma wallahi da alama suna buƙatar
taimako na Inna" Inna Habi zaro idanu tayi tana kallan gurin da Maryo take kallo tana mata
magana, amma ita bata ga komai ba. Inna Habi hannun Maryo ta ja ta ce. "Maryo anya kuwa
makarai basu fara buÉ—e miki ido ba? yanzu cikin dokar dajin nan kizo kice wai wasu na yi miki
magana, maza wuce mu tafi karki jaza mana masifa" Maryo juyawa tayi ta ga waccen me kama
da ita tana hawaye ta miƙe tsaye ta riƙo namijin yana ɗingishi suka ɓace daga gurin. Maryo
hannu ta fusge ta ce. "Shikenan Inno wallahi sun tafi kuma yana cikin wani hali nidai Inna
gaskiya..." Da saurin Inna Habi ta fisgi hannunta suka fara tafiya har sai da suka baro gurin,
suna shiga sashensu Abu ta ce. "Maryo ina kika je tun É—azu Fulani Maryama ta aiko kiranki?"
É—igon jinin hancinta da ya fito ta goge kanta na ci gaba da sarawa, idanunta take suka rune
jawur hannuwa biyu ta sa ta dafe kanta ta ce. "Abu kije a madadina wallahi bana jin daÉ—in jikina"
Abu zaro ido tayi ta ce. "Fulani Maryama fa ita take kiranki gaskiya bazan iya zuwa ba, ki lallaɓa
ko a hankali ne kije kuma kisan ƙaryar da zakiyi mata dan ta aiko kiranki yafi a irga." Inna Habi
ta ce. "Gaskiya Maryo akwai abinda yake damunki anya bazamu fara nema miki maganin
makarai ba, wannan jikin naki ba lau ba yanzu ki wuce kije kiran da Fulani Maryama take miki
banasan abinda zaki yi wanda za'a hukunta ki da horo me tsanani." Maryo tafiya ta fara yi tana
haɗa hanya hannunta ɗaya dafe har ta ƙarasa sashen Fulani Maryama. Tana gabda shiga

rumfar Fulani Maryama ta yanke jiki ta faÉ—i wanda yayi dai-dai da shigowar Jakadiya.

Jakadiya na ganin haka ta rafka salati tana tafa hannuwa ta ce. "Yau me nake gani ni Kubura
ke Æ´ar nan ya na ganki a sheme kamar gawar goÉ—iya jama'a ku kawo É—auki" Fulani Maryama ce
ta leƙo ta ce. "Jakadiya ihun me kike yi?" Jakadiya ta zaro ido ta ce. "Wannan mai kama da ƴar
bararojin ce na samu ta faÉ—i a gurin" a yatsine Fulani Maryama ta kalleta ta ce. "Jakadiya maza
ki fitar mun da ita idan kin kaita cen sashen su ki dawo ina san ganinki"

Jakadiya ta kalli Maryo da take wani irin karkarwa ta ce. "To Allah gamu gareka Bawan sarki
ya rasa doki, yanzu ki rasa inda zaki yi farfaÉ—iyar ta ki a babban sashe na Fulani Maryama,
kekam ki haɗani da jaraba ɗaukar kamar ki ai sai na shirya. Ga dai yarinya a haka da ƙuruciya
kamar na nauyi amma wallahi wannan sai ta kusa ɓalle mun baya, gwara na kira waɗancen ƴan
iskan dogarawan su zo su tayani kwasar..." Fulani Maryama gajiya tayi da surutan Jakadiya ta
ce.

"Jakadiya bansan surutu a kwashe mini ita daga gurin nan?"

Jakadiya juyawa tayi fara ƙwalawa Dogaran bakin ƙofa tana magana. "Kai Badaru kana ina
kuzo" kafin su ƙaraso Maryo ta ɗan jin saukin yanayin da take ciki miƙewa tayi jiki ba ƙwari jiri
na ɗaukanta, Jakadiya juyowa tayi ta taɓe baki ta ce. "Feleƙe ratayar jaka a duwawu dama
farfaÉ—iyar ba ta gaske bace, to muje karki jazawa uwar É—akina masifa ki mushe mata mu shiga
uku." Jakadiya tasa Maryo tayi a gaba tana tafe tana zazzaga mata surutai suna gabda wuce
tsoron tsakiya Maryo ta fara haÉ—a hanya, ji tayi ta yi karo da abu wanda yayi dai-dai da tafiyarta
luuuuuuu. Kafin ta kai ƙasa ya taro ta dukda idanunsa a rufe suke jin alamun mutum yasa yayi
saurin taro ta. Jakadiya ta kuma rafka salati tana cewa. "Shikenan wannan yarinyar zata ja mun
taɓa gawa ina zaman zamana" Fulani Zaliha hannunta da yake sarƙe dana Saif ta ce.
"Subhanallah Jakadiya lafiya?" Jakadiya ta ce.

"Allah ya taimake ki wallahi yarinyar nan ce tana zuwa zata shiga sashen Fulani Maryama
kawai ta zube ƙasa" Jakadiya ta ɗaga kai cen ta fara hange-hange sannan tayi ƙasa da murya
ta ce. "Kinsan dai ba kowa yake da wadataccen Imani ba banda haka ya yarinya tana cikin
wannan halin ace wai a fita da ita kamar wata kayan wanki" Fulani Zaliha ta ce. "Jakadiya ba
wannan na tambayeki ba yanzu ina zaki kaita" Jakadiya ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
google.com, pub-9213700357025247, DIRECT, f08c47fec0942fa0