Showing 54001 words to 57000 words out of 57967 words

Chapter 19 - Anya Baiwa Ce 1 Complete Hausa Novels

ta har ta nufi wajen wani murgujejen
dutse kai tsaye ta faɗa kai kanta ya bugu da dutsen ta faɗi cen gefe a sume kanta da hancin ta
na zubda jiki. Ɗaya daga cikinsu suka ta sa da sauri ya je ya ɗaukota ya dawo da ita wurin da

aka fara kwantar da ita, rirriƙe ta suka yi suka ci gaba da shafe mata jiki da farin yashi. Azabar
zafin da ya ratsa cikin jikinta ne ya farfaɗo da ita daga dogon suman da tayi, a zabure ta miƙe
wannan karan ko kuka ta kasa yi sai binsu take da wani irin kallo kamar mai taɓin hankali, wani
garin koren ganye suka fara fesa mata nan take ta kuma kwanciya jikinta na wata irin karkarwa
kamar me jin sanyi. Sai a lokacin suka saki Mardid wanda yake kwance a gurin rai a matuƙar
ɓace, da gudu ya tafi gurin ta yana kururuwar kiran sunanta amma ko kallan gurin da yake bata
yi ba saboda batasan ma abin da yake faruwa ba. A haukace ya ɗauketa be tsaya ko ina ba sai
cen sashensa ya kwantar da ita, yana ƙare mata kallo da yadda jikinta ya saluɓe kamar wacce
aka tsoma a cikin tafasashen ruwan zafi. Saboda tsabar firgice ya manta da Muhaibish da ke
cen a hanunsu, hannuwansa ya kalla yaga fatar jikinta ce manne akan tafin hannunsa gurin da
ya ɗauke ta, rushewa ya yi da kuka yana buga ƙasa tare da jin ƙiyayyar ƴan uwansa a
zuciyarsa, sai dai yasan ko yana hauka bazai iya ja da su ba saboda sun fi ƙarfinsa. Ganin
kukan bazai fissheshi ba yasa ya miƙe ya bazama tsinkar ganyayyakin da zai haɗa mata
magani da shi, ya daɗe da fita sannan ya dawo ya fara murza ganyayyakin a cikin ruwa yana
yayyafa mata. Wani irin gurnani take yi tana girgiza kanta, sai dai anci sa'a jikin nata ya daina
karkarwa sai wani irin gumi da yake karyo mata, saboda yawan gumin har ɗiga yake a ƙasa
kamar tsamowarta kenan daga ruwa. Yana nan zaune yana kallon halin da take ciki Ɗan ƙanin
Mahaifinsa ya shigo hannunsa ɗauke da Muhaibish, a fusace Mardid ya karɓeta ya rungume
yana kuma fashewa da matsanancin kuka. Kuka ta fara yi ya rasa yadda zai yi mata ruwa ya
ɗauka ya bata ta sha sannan ya kwantar da ita ta ci gaba da bacci.

Kyauta sai da ta kwana biyar a wannan halin batasan wanda yake kanta ba, a kwana na shida
ne ta farfaɗo lokacin Mardid na tsugunne yana shafa mata maganuguna, suna haɗa ido daɗi ya
kama shi har sai da yaji kamar ya rungumeta, sai dai da ya tuna raunin jikinta yasa ya sakar
mata murmushi yana mata sannu. Bata amsa masa ba ta yunƙura ta tashi zaune tana bin jikinta
da wani irin kallo, sai a lokacin komai ya dawo mata hawaye ta fara yi cikin sanyin murya Mardid
yace, "Sannu ya jikin?" Sam bata ji me yace ba sai dai ta ga yana motsa baki, a hankali ta buɗe
baki ta ce, "Ina Muhaibish?" Motsa baki ta ga ya yi sai kuma ta ga ya nuna mata cen gefe da ta
hango ta tana bacci. Cikin damuwa ta ce masa, "Ni fa bana jin ka bana jin abin da kake faɗa
naga dai kana motsa baki."

Mardid ya zaro ido yace, "Kyauta bangane bakya ji na ba har yanzu bakya jin abin da nake
faɗa?" Ganin ya daina motsa baki yasa Kyauta ta kuma cewa, "Ban san me ya samu
kunnuwana ba amma banajin komai" daga wannan lokacin Kunnuwan Kyauta suka daina ji sai
dai bakinta na magana, haka ta yi ta jinyar jikinta har ta warware. Haka rayuwa ta ci gaba da
gudana cikin azabtarwa da tsangwama, har Muhaibish ta cika goma da haihuwa.

Muhaibish ta taso kyakkyawa da ita gwanin birgewa, sai dai itama haka take rayuwarta
koyaushe a jikin mahaifiyarta, sai a wannan lokacin ta tabbatar da maganar Mardid akan
Muhaibish da yace mata sam ba jinsinta bace, dan ta ga ababuwan da take yi ne ta fahimci
haka. Tun da dangin Mahaifinta suka fahimci ita ce Muhaibish ɗin wannan ƙarnin sai baƙin cikin
duniya ya kama su, saboda a wannan lokacin da sun niyyar yi wa Kyauta, Mardid ko ita mugun
abu tun kafin su aiwatar zai faru da su, a wannan lokacin haka suka dinga asarar rayuka

saboda masu ayyana kashe Muhaibish su suka dinga mutuwa. Wanan yasa rayuwarsu ta ci
gaba da tafiya cikin jindadi babu tsangwama bare fargabar azabtarwa. Wan Mahaifin Mardid
satar jiki ya yi ya tafi cen ƙarshen duniya wurin wani tsohon Bokansu, nan take ya sanar masa
buƙatarsa game da Muhaibish. Bokan numfawa ya yi yace, "Buƙata zata biya amma sai ka
ziyarci kabarin Muhaibish ka ɗebo ƙasar kabarinta kana zuwa kar kayi magana da kowa ka
watsawa ita wannan Muhaibish ɗin, idan ka yi haka duk wani kadarinta zai karye tana ji tana
gani babu abinda zata iya aiwatarwa, wata ƙila tsinuwar Boka ta faɗa kanta. Amma akwai yuwar
bayan wasu shekaru ruhinta ya wanzu a doron ƙasa, bana jin lokacin ma kana raye" Cikin
jindaɗi ya amsa da cewar, "Zan aiwatar matuƙar buƙatata zata biya na ganin dukkansu sun
wulaƙanta, ba damuwa ta bace dan sun dawo ko da har uwarta zasu dawo duniyar." Ya jima a
wurin Boka suna tattaunawa sannan ya tashi ya nufi kabarin Muhaibish dake tsakiyar duniya a
doron ƙasa.


Cikin nasara Kawun Mardid ya samu nasarar ɗebo ƙasar kabarin Muhaibish, kamar yadda
Boka ya sanar masa haka shima ya aiwatar. Yana watsawa Muhaibish ƙasar ta faɗin gurin a
sume sai bayan wani lokaci ta farko, tun daga wannan lokacin Muhaibish ta zama mai matuƙar
hakuri duk wata baiwarta ta gushe, haka suka ci gaba da azabtar da su Kyauta da ayyukan
wahala da tare da al'adatunsu na jinsin Jinnu, musamman Kyauta da bata daga ciki jinsin su.
Shekarar Muhaibish ashirin a duniya Kakanta ya rasu nan suka fara taƙaddamar wanda za'a
ɗora, dan sun san muddin Mardid ya hau karagar mulki watarana ita zata mulkesu, sai dai
babban tashin hakalinsu sun san ko me zasu yi basu isa su ɗora wani akai ba, tun da sun san
duk wanda aka ɗora indai bashi ya cancanta ba a ranar yake mutuwa.

Suna ji suna gani babu yadda suka iya haka suka ɗora Mardid akan karagar mulki tare da cin
alwashin kawar da ita kafin mutuwarsa, haka rayuwa ta ci gaba da tafiya har Muhaibish ta cika
shekara ashirin da biyar ba tare ta yi aure ba, saboda gabaɗayansu babu wanda ya amince da
haɗa iri da ita, kuma tun da Kyauta ta dawo rayuwar cikin jinsin jinnu bata ƙara hauro doron
ƙasa ba, haka daga ɓangaren Muhaibish bata taɓa takowa doron ƙasa ba, tayi gabaɗaya
rayuwarta ne a ƙarƙashin ƙasa. A wannan lokacin ne suka ƙara tsananta musu da iziya
kala-kala har ta sanadin haka suka tsiyayewa Kyauta idanu ita kuma Muhaibish suka yanke
mata hannuwa biyu, Mardid a wannan lokacin ne ya nemi ya yi musu bore amma sai suka nuna
masa sam bazai yuwu ba, yana yunƙurin ɗaukan su Kyauta zuwa doron ƙasa suka kanainaye
shi, su Muhaish da Kyauta suna tsaye haka suka dinga ciccire gaɓoɓin jikin Mardid gida-gida
har yace ga garinku nan, Kyauta da lokacin girma ya fara kamata ban da kuka babu abin da
take yi ita da Muhaibishi, saboda tun da taji ƴan uwansu sun fisgosu da ƙarfin tsiya sun fito da
su jikinta ya bata akwai abinda zasu aikata musu mummuna, kuka take sosai da wannan ƙuncin
rayuwar da suke fuska musamman da ta makance, tun da kafin makancewarta tana ganin abin
da yake faruwa dan har maganar kurame suke da su Mardid, saɓanin yanzu da sai antaɓa
jikinta take sanin yanayin da ake ciki, sai dai har zuwa wannan lokacin bakinta raɗau yake tana
iya magana amma babu damar taji ko ta gani.

Kyauta ce ta fara lalubar hannun Muhaibish, sarƙar da Kaka ya bata ta damƙa mata sannan

ta fara lalubar kunne ta tayi mata raɗa, jikinta ban da karkarwa babu abin da yake yi saboda
firgici da kuma yanayin tsufa. Tana gama yi mata raɗa ta fara hankaɗata tana cewa, "Maza ki
tafi dan karsu illata ki kema nasan tabbas bazasu barmu ba" Yayan Mahaifin Mardid da sauri ya
fisgo Kyauta ganin haka yasa Muhaibish tabi umarnin mahaifiyarta, da gudu ta juya ta nufi
sashensu da sauri ta fara haƙa ƙasar gurin cikin hannuwanta na jinnu masu kama da gatari, sai
da tayi haƙa sosai sannan ta tura sarƙar ta rufe sai kuma ta rushe da matsanancin kuka saboda
tasan yadda suka kashe Mahaifinta itama da Mahaifiyarta bazasu barsu ba, miƙewa tsaye tayi
ta buga ramin ta ƙarfi ta ce, "Ya ke Mahaifiya na san a wanan lokacin bakya numfashi amma na
tabbata sai kin dawo domin ki ɗau sarƙarki tare da fansar abin da waɗancen azzaluman suka yi
mana" tana gama faɗa ta juyo ta fiti daga gurin anan ta yi cikiɓus da ƴan uwan mahifin na ta da
ƙarfin tsiya suka ɗauke ta suka kaita wajen ta gawar iyayenta suke.

Tana zuwa ta sami Mahaifiyarta yashe a gefe kayan cikinta sun fito waye ga maƙogaronta
shima sun fito da shi, a fusace ta juya gun Yayan mahaifinta da wasu jigajigai Biyar da suka fi
tsananta musu ta fara kai musu duka cikin kuka, da ƙarfi suka fisgota suka danneta kallansu
tayi tana huci ta ce, "Tabbas wannan abin da kuka aikata tamkar bashi ne na rantse da
gawarwakin iyaye na sai na cimma buri da muradina akanku" Dariya suka bushe da ita sannan
suka sa hannuwansu suka ɓara bakinta kamar yadda ake ɓare kan tinkiya bayan an yanka ta,
wasu daga ciki kuma suka wara ƙafafuwanta suka raba ta gida biyu."

Ɗan Wanzam ya ɗago da kai ya kalli Sarki Abdallah cikin ladabi yace, "Allah ya taimake ka kaji
ainihin labarinta, kuma maganar da nake maka bana tunanin akwai wani mai magani da zai iya
ja da ita. Cimma buri da muradi ne ya dawo da ita banajin zata ƙyale me yunƙurin yi mata karan
tsaye." Sarki Abdallah ya yi murmushi yace, "Lallai Wanzan ka iya bada tatsuniya me daɗi dan
ko a cikin littafan tatsuniyoyi ban taɓa cin karo da labari me ban ta'ajibi kamar wannan ba"


Lamarin da ban tausayi😥 To fa mun dawo labari zamu ji yadda zata kasance mu kafta🤾🏻‍♀️

_LITTAFIN NAN NA KUƊI NE DA NAIRA 200 ZAKI KARANTA SHI CIKIN KWANCIYAR
HANKALI, ZAKU BIYA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN, FIRST BANK 3090957579 AISHA ADAM,
ZA'A TURO DA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR,0706 206 2624, DAN GIRMAN ALLAH
IDAN KINSAN ZAKI FITARMUN DA LITTAFI NA YAFE CINIKINKI._ [25/11/2021, 18:56] Ameera Adam🌚: 35...


Kamar wanda ya ga sabuwar hallita haka Ɗan Wanzam ya zubawa Sarki Abdallah Idanu
sannan ya russunar da kai ƙasa, yana girgizawa kamar na ƙosasshen ƙadangare. Sauya fuska
ya yi cikin damuwa yana ɗan jin haushin waɗannan kalamai na Sarki Aminullah, saboda yadda
ya ɓata lokaci yana ta kwararo labarin kamar saukar ruwan sama. Amma ace wai duk wannan
zantukan na shi sun tashi a banza, sake ɗago da kai ya yi yace, "Allah ya taimakeka ba zan
tilasta amincewa da batu na ba, amma ina me bada shawara da abi lamarin yarinyar nan a
sannu saboda gujewa hatsarin da baza'a yi saurin shawo kansa ba. Wani abu da na manta ban

sanar da kai ba Ranka shi daɗe wannan masarautar da kake gani a cikinta ne Muhaibish suka
yi rayuwa ita da iyayenta, ba wai ina nufin a doron ƙasa ba. A'a a dai-dai wannan gurin ta cikin
ƙarƙashin ƙasa shuɗaɗɗiyar masarautarsu ta kasance. Allah ya baka yawan rai a wannan karan
Muhaibish maganar mutum biyu kawai zata iya ji su dakatar da ita daga abin da tayi niyya,
bansani ba suma ko sun ƙara dawowa ko kuma ita kaɗai ta dawo? Amma daga Mahaifiyarta
Kyauta sai Mardid su kaɗai zasu iya dakatar da ita daga fitowar da tayi na cimma burinta,
babban kuskuren da akayi kawo ta cikin masarautar nan, kuma bana tunanin akwai ƙaddarar da
zata iya dakatar da ita. Allah ya taimake ka a dubi maganata da idanun basira, nan fada ce ban
isa na faɗi abin da ba haka yake ba" Sarki Abdallah mutum ne me kafiya akan abin da yasa a
gaba, dan haka ko da yaji wannan batu na Wanzam bai sa ko dai-dai da ƙwayar zarra yaji
zuciyarsa ta sauya daga rashin gasgata Wanzan ɗin ba. Ɗan Wanzam ya gyara zaman Jakarsa
sannan yace, "Allah ya baka yawan rai idan an sallame ni zan iya tafiya?" Sarki Abdallah ya
bashi umarnin tafiya nan take kuma Wanzam ya maƙale jakarsa a hammata sannan ya yi
godiya ga Takawa ya fice daga cikin fadar.

Bayan fitowar Wanzam Maleek na rakuɓe jikin bango, haka kawai yaji tausayinta ya kama shi
duk da ya rasa dalilin haka. Kallanta ya yi ya ga tana zubda ƙwalla , kansa ya dafe ya rasa ma
ta ina zai fara yi mata magana, mamaki yake a ransa ta yadda Shukransa duk ta birkice lokaci
ɗaya. Karo na farko kenan da yaji tsoronta ya fara ɗarsuwa a zuciyarsa, jiki a sanyaye ya
ƙarasa gurinta ya miƙa hannu yana san taɓata sai dai yana jin tsoro. Tattaro jarumta ya yi yasa
hannu ya taɓa tana faɗin, "Shukra" Ɗagowa tayi tana kallansa da manyan idanuwanta da suka
rune jawur kamar gauta, lokaci ɗaya yaji ya ƙara shiga taitayinsa. Cikin inda-inda yace, "Me
yake damunki?" Hawayen idanuwanta ne suka ziraro ƙirjinta na bugawa da ƙarfi sannan ta ce,
"Shima yace bazai iya ba. Yanzu haka zaku barni da tabon abin da yake damuna?" Lumshe
idanunsa ya yi ya ware su akan kyakkyawar fuskarta yana kallonta da alamar neman ƙarin
bayani, sunkuyar da kai ƙasa ta yi ta ce, "Babu damuwa zan aiwatar da kowane muradi da
kaina bana neman taimakon kowa bare a nemi dakatar da ni a lokacin da nake tsaka da cimma
burina." Tana gama ta miƙe tsaye ta fara takawa cikin izza da ƙasaita, bin ta ya yi da kallo baki a
sake yana mamakin waɗannan bauɗaɗɗun kalamai na ta, daga kwanakin da tayi a cikin gidan
yaci ace ya fara sabawa da waɗannan bauɗaɗɗun kalmomin nata, sai dai kodayaushe ta yi
doguwar magana sai ya tsinci baƙin kalmomi, kamar wanda aka zarewa laka a jiki haka ya bi
bayanta yana kiran sunanta, Maryo tafiya take kamar za ta tashi sama saboda sauri duk kiran
da yake mata bata waiwayo ta kalleshi ba ballantana yasa ran zata bashi amsa.

Tana shiga sashen su Bayi suka fara zubewa suna gaishe ta amma babu wacce ta kalla daga
cikinsu, tana wucewa suka bi bayanta da kallo sannan suka fara yafitar junansu suna ƴan
gulmammakinsu. Ƙarasowar Maleek ne yasa suka yi ɗif cikin yanayin rashin gaskiya suka fara
yi masa barka da hutawa. Fuska a ɗaure ya kallesu ɗaya bayan ɗaya yace, "Ku fice daga
sashen nan gabaɗaya bana buƙatarku har sai na neme ku..." tun bai ƙarasa maganar ba suka
fara kama gabansu suna yi masa a fito lafiya. Lokacin da ya shiga ɗakin jiki a sanyaye ya fara
kiran sunanta amma shiru yake ji kamar an aiki bawa garinsu, yana shiga uwar ɗakinsu ya
sameta kwance a kan fado tayi ɗai-ɗai tana bacci har da minshari, ga wanda bai ga wucewar
Maryo ba idan ya yi tozali da ita a yadda take baccin nan zai rantse da Allah ta shafe sama da

awa guda tana bacci. Bacci take yi hankali kwance fuskarta tayi fayau sai dai rama da ya lura
tayi, wuyanta ban da ƙashi babu komai ya lura ta yi haske amma gabaɗaya da alama bata cikin
kwanciyar hankali, tausayinta ne ya kamashi ya ga jikinta duk ya wani ɗalli-ɗallin baƙi-baƙi,
mayar da idanuwansa ya yi kan tafin hannuwansa da har wannan lokacin da taruwar jini a
jikinsu, lokaci ɗaya damuwa ta mamaye zuciyarsa saboda sabuwar lalaurar da ke tattare da
matarsa hasalima tunowa ya yi da irin wasannin da suke yi na soyayya shi da ita, amma sai ga
shi yanzu ya taɓa mata hannu ma fargaba yake saboda gudun tsattsafowar jinin da ke fita daga
jikinta, a ɓangaren sa kuma raɗaɗin ne yake damunsa daga baya kuma wurin ya yi taruwar jini.
Gefenta ya koma ya kwanta babu jimawa shima bacci ya yi awon gaba da shi.

Fulani Zaliha aikawa tayi a kira mata Abu saboda tun bayan dawowarsu bata ƙara saka ta a
idanunta ba, da sallama ta shigo ɗakin cen ƙasa kusa da Fulani Zaliha ta zaune tana ƙaƙalo
murmushi ta ce, "Barka da hutawa ranki shi daɗe" Fulani Zaliha kallan tsaf ta yi mata ta ce,
"Zainab lafiya na ga baki fito ba, kin manta kayanki a wurina ko akwai abin da yake damunki?"
Kamar ta soso mata inda yake mata ƙaiƙaiyi hawaye ya fara zubowa daga idanuwanta, dafa ta
Fulani Zaliha ta yi tana kallonta don dama tun shigowarta ta fahimci tana cikim damuwa. Sai da
tayi me isarta sannnan ta ɗago da kai ta ce, "Maryo na gani a bakin kasuwa kafin naje wurinta
ta ɓace mini, na duba wurare amma babu ita babu alamunta." Fulani Zaliha cikin tausayawa ta
ce, "Wace ce Maryo ɗin kuma a ina take?" Abu ta goge ƙwallar idonta ta ce, "Ƴar uwata ce da
Ɗan ƙanwar Takawa ya tafi da ita a zuwan matarsa ce, ya tafi Adamawa da ita amma ɗazun
nan na ganta. Kuma wallahi ba Matarsa bace hasalima Maryo bata taɓa aure ba tare muka taso
a wurin Innarmu." Tana zuwa nan a zancen ta rushe da matsanancin kuka. Fulani Zaliha cikin
rashin fahimta ta ce, "Bangane ba matarsa ba ce kuma ya tafi da ita? Kina nufin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
google.com, pub-9213700357025247, DIRECT, f08c47fec0942fa0