Showing 30001 words to 33000 words out of 57967 words

Chapter 11 - Anya Baiwa Ce 1 Complete Hausa Novels

TURO DA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR,0706 206 2624, DAN
GIRMAN ALLAH IDAN KINSAN ZAKI FITARMUN DA LITTAFI NA YAFE CINIKINKI._ [09/11/2021, 18:13] Ameera Adam🌚: 24...



Marduska ya kalli Fulani Maryama da yadda take ta tada jijiyoyin wuya, wani tsohon ƙoƙon
kan ƙwarangwal ya ɗauko ya kantami wani kore-koren ruwa ya sha sannan yace. "Maryama
meye naki na ta da jijiyoyin wuya bayan duk ƙafafar da kike yi Salman fa ba ɗan masarauta
bane" Fulani Maryama ta kalli Jakadiya da tayi ƙuri tana raba ido kamar shege a rabon gado,
wani yawu ta haÉ—iya me É—aci ta ce. "Marduska duk ba wannan ba. So nake na ji ta ya akayi
yarinyar ta haÉ—a jini da Takawa? Ni ce uwar gidan Sarki Aminullah kuma duk a kan idanuwa aka
haife ƴaƴan sa guda ashirin da bakwai biyu sun rasu, ko a mafarki ban taɓa jin ance wata daga
cikin ƴaƴansa ta ɓace ba, kuma Sarki Aminullah ƙwarƙwararsa ɗaya ƴaƴanta biyu duka mata ta
ina suka haÉ—a dangantaka?" Marduska ya kafeta da ido yana kallo sannan yace. "A inda ba
ƙasa anan ake gardamar kokawa. Duba mini nan" ya janyo wani ɗan ƙoƙo da bai fi tafin
hannuwan kakkauran mutum ba ya nuna mata, daga cikin ruwan ƙoƙon Maryo ce ta bayyanawa
cikin shiga ta alfarma daga cen kan karagar mulkin rangaÉ—aÉ—au fuskar Sarki Aminullah ta

bayyana ɗauke da murmushi, Maryo ce ke motsa baki bayan wani lokaci ta miƙe ta rungume shi
sannan ya sumbaceta a goshi ta fice daga fadar, fitarta babu wuya sai ga mace mai siffar Fulani
Maryama ta ƙaraso ta durƙusa gaban Sarki Aminullah tana gaishe shi cikin girmamawa. Boka
Marduska yasa hannu ya shafe saman ƙoƙon su Jakadiya suka daina kallon, kamar haɗin baki
suka sauke ajiyar zuciya lokaci É—aya.

Jakadiya ta ce. "Marduska ni bansan ta ina zan fara ba saboda al'amuran duk masu
sarƙaƙiya ne? Ka fayyace mana abin da yake ɓoye" Marduska yace. "Bani da hurumin fayyace
muku abubuwan da ba hurumina bane, ina ta ƙoƙarin inbaku haske dai ta yadda zaku fahimci
al'amuran. Amma muddin nayi katsalandan ina iya fuskanta barazana daga waÉ—annan
ɓangarorin guda uku. Karku manta da gaya muku shuɗaɗɗu da rayayyun ruhina ne suke
gwabzawa kuma dukkanninsu zaƙaƙurai ne kowanne ka nemi ka yiwa shisshigi to tabbas zaka
iya zama shuÉ—aÉ—É—e." Lokacin da Marduska ya dire da zancensa ya kallesu a zatonsa zasu
kuma jefa masa tambaya amma sai yaji shiru da alama sun miƙa masa lamuransu. Ya gyara
zama ya ci gaba da cewa. "Zan iya baku satar amsa akan abubuwan da ya kamata ku kiyaye
wataƙila zai taimaka muku wajen binnuwar wasu sirrika na ku. Ku kiyaye zaƙewa cikin
lamarinsu gabaÉ—aya su ukun nan, Rayzuta, Furzaan da Zulik duk kuwa abin da zaku ga sun
aikata a tsakaninsu. Duk irin gumurzun da zasu tafka kar wanda ya shiga tsakaninsu domin a
lokacin idanuwansu a rufe yake, sai a asiri karku kuskura kuce sihiri zai yi tasiri a jikinsu ina me
jaddada muku sai dai ku haɗa da kissa. Abu na ƙarshe da zan gaya muku ba mai daɗi bane
wataƙila ya faru wataƙila ku riski akasin haka, akwai gagarumin tashin hankalin da yake
tunkarar masarautar ku ni dama nasan tunda Kalimsiyat ta wanzu a doron ƙasa dole a zubda
jini. Dan haka lokaci na zuwa da masarautarku take cikin barazanar zubar jini sai wanda Allah
ya tsare. Amma fa ban tabbatar ba bincike ne ya nuna mini ina ƙara ankarar da ku ne saboda ni
nan babu uwar da zan iya yi muku indai ba so nake tsibiri na ya kama da wuta ba." Wata
gwauruwar ajiyar zuciya Fulani Maryama ta sauke Jakadiya ta furta. "Tirƙashi" Fulani Maryama
ta ce. "Marduska yanzu babu wani abin da zaka iya aiwatar mana?" a hassale Marduska yace.
"Babu tun da nima ta kaina nake, bana taɓo tsuliyar dodo ba haka kawai tunda kinji dai ance
kowa ya kwana lafiya shi ya so. Amma akwai mutane huÉ—u a cikin gidanku masu daraja
waɗanda ko kaɗan baza'a taɓa cutar da su ba. Sai kuma wasu tsirarin bayin Allah da naga suna
da riƙo da addini suma dai bance akwai wani abu mummuma da zai faru da su ba. Sannan
meye tuƙwicin ziyarar mu tunda Rayzuta ta hana mu ɗaukan rayuwakan masarautarku" Jiki
babu ƙwari Fulani Maryama ta ce. "Duk abin da ka faɗa" Marduska yace. "Yanzu ki ciro mini
gashin sassan jikinku zanyi wani aiki da shi daga haka kun biya ni sai kuma wani jiƙon"
Jakadiya ta hau raba idanu tana wuri-wuri Fulani Maryama ta ce. "Da me zamu yankar maka?"
Marduska ya yi wani nazari yace. "Karku damu zan tura Murduss zai É—ebar mini da kansa" cikin
halin ko'inkula suka yiwa Marduska sallama suka koma Masarautar Kano jiki a sanyaye saboda
rashin nasara.

Sarki Aminullah kallanta yake yana jin yadda zuciyarsa ke yi masa wani iri musamman da ya
ga yadda duk ta bi ta rame kamar wacce ta yi jinya, lokaci É—aya kuma yaji yana jin kewar
matarsa saboda ko babu komai yasan ita É—in ta dabance a cikin mata. Ganin irin kallon da yake
mata yasa ta ƙara tsuke fuska tana ƙara gyara zaman alkyabbarta tare da sunkuyar da kai

ƙasa. Sarki Aminullah ya kalleta yace. "Zaliha yaushe Saif ya samu lafiya ban sani ba?" Wani
ƙululun baƙin ciki ne ya turniƙe zuciyarta, ta ɗago tana kallonsa kamar bazata yi magana ba a
daƙile ta ce. "Rannan" sai da ya ja shiru na ƴan sakanni sannan yace. "Me yasa baki sanar da
ni ba?" Wannan karan bata É—ago ta kalleshi ba ta ce. "Saboda na ga kamar bai shafe ka ba"
wani irin kallo ya wurga mata a É—an fusace yace. "Saboda ba nine mahaifinsa ba ko" Ita É—in ma
a fusace ta kalleshi ta sauke a jiyar zuciya sannan ta ce. "Idan ma kaine wani abu kake masa
da zai tabbatar da cewar kai mahaifinsa ne" Sarki Aminullah ya tamke fuska cikin tsawa ya ci
gaba da magana. "Karki manta a gaban wanda kike magana idan ba haka ba ranki zai yi
mummunan ɓaci, banasan rashin kunya Saif dai Ɗana ne ko kina so ko bakya so dan haka na
fiki iko da shi ace ĆŠan cikina yana fama da wannan lalurar har ya warke baki sanar da ni ba,
wallahi da ace ƙaramin yaro ne babu abin da zai hana na ƙarɓe shi na bawa sauran matana
riƙonsa. Sakarcin banza sakarcin wofi ko dan kinga nasa a kira ki ne har zaki nemi ki yi mini
wulaƙanci?" Tun da ya fara zazzaga Faɗa idanunwanta suka fara zubda ƙwallah, tuna irin baƙar
hawalar da ta sha akan Saif tayi da irin wulaƙancin da yake musu ita da shi har sauran matansa
suka ara suka yafa, tun yana tsumma har ya yi wayo take wahala, tunowa tayi akwai ranar da
Saif ya je fada gurinsa amma yasa aka dawo da shi gurinta wai zai yi baƙi kar su ganshi yaji
kunya. Tana jin ya dire zancensa a zafafe ita ma ta É—ora da nata faÉ—an dan kamar wacce ta
manta a gaban Sarki take, Sarkinma Sarkin Kano Sarkin da duk inda yaje aka ambaci
masarautar da ya fito sai an bashi girma kuma an jinjina masa.

"Ni kaina da nasan maganar da zata kawo ni kenan da ban tako na zo turakarka ba, Wai me
ka É—auke ni ne ko dan kana matsayin Sarki? Kana tunanin a duniya bayan Ubangiji akwai
wanda ya isa ya karɓe Saif daga hannuna? Wallahi idan zanyi yawo tsirara babu wani wanda ya
isa ya rabani da ĆŠana. Wato saboda yanzu ya warke ya koma cikakken mutum kamar kowa,
babu nakasa a jikinsa shiyasa har zaka nuna shi wani mai muhimmanci ne a gurinka. Saif ĆŠana
ne nina ci wahalarsa ban ƙyamaci abuna ba, safe, rana, dare, sanyi zafi da damuwa ban taɓa
jin kunyar wani ya ganni da shi ba saboda ni uwa ce a kowane yanayi ĆŠana yake bazan guje
shi ba, Dan Allah idan zakayi iko kayi da ĆŠan lelenka wanda kasan ciwonsa baka jin kunyar
nuna shi a idon duniya ba Saif da ya zame maka Alaƙaƙai ba. Na roƙe ka da girman Allah ka
ƙyale mini Ɗana tun da na samu Allah ya bashi lafiya, karka jawo shi a jiki a nemi a salwantar
mini da shi tunda ni shi kaɗai na mallaka."Tana kaiwa nan ta miƙe fuska ba walwala ta gyara
alkyabbarta sannan ta juya ta ce. "Ranka ya daÉ—e na barka lafiya" ta yi ficewarta ba tare da ta ji
daga bakinsa ba.

Sarki Aminullah ko kaɗan bai ji haushin maganganunta na ƙarshe ba domin ga duk wanda
yake cikin gidan yasa Salman shine É—an gaban goshinsa, sai dai wannan karan tsakaninsa da
Allah yaji yana marmarin jan ĆŠansa a jikinsa ba wai dan ya samu lafiya ba. A gefe É—aya tunanin
su Maryo ne ya faÉ—o masa maganganun da suka dinga furtawa ne suka shiga kai komo a
ƙwaƙwalwarsa, a hankali ya furta.
"Wacece ita yarinyar nan? Meye ma asalinta ya akayi tazo gidan nan a matsayin baiwa."
Shiru ya yi yana nazarin yadda yadda take furta kalamanta da yadda ta tako cikin fadarsa ba
tare da tsoro ko shakka ba, a ɓangare ɗaya ya lura da rashin kwarjinin da ya yi mata uwa uba
ga kalaman da take furtawa Salman kai tsaye. Salman da kowa a cikin gidan yake tsoron yi

masa laifi ko da a cikin kuskure ne amma ace har Baiwa ta tsaya tana gasa mata maganganu
haka. A fili ya furta. "Saif! To meye alaƙarta da Saif? Shi da ba wata isasshiyar lafiya ba"
Lumshe idanunsa ya yi kamar wanda aka tsirawa allura a zabure haka ya buÉ—e su yana cewa.
"Ita ce yarinyar da aka kama a turaka ta da wuƙa yanzu kuma ta dawo kan Ƴaƴana, ANYA
BAIWA CE? Anya ba wani ne ya turo ta domin tayi masa aiki a kaina da iyalaina ba kuwa?
Tabbas dole ayi mini binciken sirri domin na gano inda ta dosa." Yana rufe baki Wayarsa ta fara
ringing yana dubawa ya ga sunan Sarki Abdallah Abdulmanaf, daidaita nutsuwarsa ya yi
sannan ya É—auka da sallama.
Bayan sun gaisa Mahaifin Maleek yace. "Sirikina ĆŠanka ya zo mini da wata magana" da yake
sukanyi wasa a tsakaninsu kowannensu yana kiran kowa da Sirikina. Sarki Aminullah yace.
"Sirikina wacce magana kenan" Babu ɓata lokaci Mahaifin Maleek ya zayyane masa duk abin
da Maleek ya kira ya sanar da shi ya ɗora da cewa. "Ka san yaran zamani da ƙwallafa rai akan
abin da suke so, yaron nan babu yadda bamu yi da shi akan ya yi haƙuri ya fauwalawa Allah
lamuransa akan mutuwar matarsa amma ina abun ya faskara, yanzu dai na taso mutum biyu
daga nan akan su zo su zama sheda akan ita ce ko ba ita É—in bace." Sarki Aminullah ya fahimci
wacce Maleek yake nufi jikinsa ba ƙaramin sanyi ya yi ba, mamaki haɗe da jimami ya kamashi.
Sai da ya tattaro jarumta yace. "Shikenan Siriki Allah yasa muji alheri" daga cen ɓangaren ya
amsa da Ameen sannan suka yi sallama. Sarki Aminullah ya jima a zaune yana nazari sannan
ya tashi ya É—auro alwala ya fara gabatar da sallar Nafila.

Inna Habi ba ƙaramin tashin hankali ta shiga ba, da sauri ta nufi kan Maryo tasa aka ɗebo
mata ruwa ta fara yayyafa mata, sun jima a tsaye a kanta sannan ta sauke ajiyar zuciya.
Carko-carko mutanen gurin suka yi ana kallon abin da yake faruwa, ganin haka yasa Abu ta ce.
"Dan Allah ku bamu guri ko ta sha iska" ba dan sun so ba suka marmatsa daga gurin ƙananan
maganganu na tashi daga tsakar gidan. Inna Habi ce ta zurfafa cikin tunani ganin Maryo ta fara
wahallalen bacci cikin zuciyarta take cewa. "Ya Allah ka kawo mini ɗauke a cikin baƙon yanayin
da muke ciki, nikam dawowar mu cikin gidan nan sam bai amfanar da ni komai ba. Haƙiƙa
akwai ɓoyayyen lamari saboda Maryo sam bata da waɗannan ɗabi'un, amma me yasa zata
sauya haka me yasa zata yarda da hurewar kunnen É—a namiji har ya kai ga cutar da rayuwarta.
Allah kana gani nayi bakin ƙoƙarina akan tarbiyyar yaran nan, ya Allah ka kawo mana salama a
cikin halin da muke ciki." hawaye ne ke gangarowa daga Idanun Inna Habi, Abu na ganin haka
ta matsa kusa da ita ta ce. "Inna dan Allah ki daina kuka. Addu'a ita ce mafita." Inna Habi kamar
jira take ta ci gaba da zubda ƙwalla cikin kuka ta ce. "Abu kina ganin halin da Maryo take ciki,
yaushe rabon da ciwon ta na zuciya ya tashi? A ƙalla amfi shekara kusan biyar bai tashi ba, ki
ga yadda yarinya ta lalace duk ta fita hayyacinta akan ĆŠa namiji, Abu ki dubi fa Maryo ko abinci
bata ci yarinya ta zama kamar taɓaɓɓiya sai dai tayi ta magana ita kaɗai tana kuka, da rana
kuka da daddare kuka koyaushe kuka alhalin wanda take yi dominsa ma baisan tana yi ba.
Yanzu ya kike so muyi idan abun ɓoye ya fito fili? Ina zan sa kaina da kunya Abu? Kinsan dai
yadda gidan nan yake" Abu itama hawaye take ta ce. "In sha Allah, Allah zai kawo mana mafita
amma har yanzu gani nake kamar mafarki ne Inna ace wai Maryo na da ciki." A daidai lokacin
Maryo ta buÉ—e idonta tana yamutsa fuska saboda yadda cikinta yake hautsina mata da tsananin
yunwa, a hankali ta ce. "Abu zan sha ruwa" da sauri Abu ta miƙa mata wani saurin ruwa kamar
mayuwanciya haka take É—aÉ—É—akar ruwa har sai da ta shaye duka, tana gama sha da sauri ta

fice daga ɗakin tana yunƙurin amai. Daga Inna Habi har Abu bin Maryo suka yi da kallo da take
ta kwara amai kamar zata amayo hanjin cikinta. Abu ta miƙe ta kai mata ruwa a buta sai da ta
kuskure baki sannan ta taso suka shiga É—aki, a wahalce ta zauna tana mayar da ajiyar zuciya.

Inna habi kallan Maryo ta yi ta ce. "Me kike sha'awar ci" A kunyace Maryo ta saci kallan Inna
Habi a hankali ta ce. "Kunun tsamiya kawai nake so" Inna Habi bata bata amsa ba ta miƙe ta
fice daga É—akin kai tsaye ta wace madafa domin nemowa Maryo kunu dan basa rasa kunun
tsamiya da kunun kanwa a madafar.
Washegari tun asuba Jakadiya ta kasa zaune ta kasa tsaye sai kaiwa da kawowa take,
Umma uwar soro ce ta leƙa ɗakin Jakadiya ta ce. "Jakadiya lafiya ke kaɗai sai ɓuruntu kike ko
bakya jindaɗi ne?" Jakadiya ta kwaɓe fuska kamar zatayi kuka ta ce. "Cikina ne yake ɗan
hautsina mini" Umma Uwar soro ta ce. "To sannu ko wani abun kika ci, kizo randar magani ki
É—iba kisha ko ya É—aure miki ciki" Jakadiya daga É—akinta ta amsa. "To bari sai zuwa wayewar
gari" Jakadiya cen ƙuryar ɗaki ta shige ta tura kanta tana tura bakinta cikin zanin rufarta ta
fashe da wani irin kuka, sai da tayi me isarta sannan ta kai hannunta ta ƙara shafa ƙwaryar
molon da ta wayi gari da shi a kanta, kuka ta ƙara rushewa da shi ta zura hannunta cikin
hammatarta nan ma taji siÉ—ib kamar wacce aka sa wa aska aka aske. Duk wanda ya ga
Jakadiya zai fahimci irin tashin hankalin da take ciki duk tayi zuru-zuru, tana ganin gari ya waye
ko ta kan kayan kari bata bi ba kai tsaye ta wuce sashen Fulani Maryama. Bayin Fulani
Maryama sunyi mamakin ganin Jakadiya dan haka sai da suka shiga suka sanar da ita sannan
aka yiwa Jakadiya iso.
Jakadiya na shiga ta tsugunna gaban Fulani Maryama ta rushe da wani irin kuka, wanda
dama jiran wannan sukunin take dan ta samu tayi kukanta san ranta, sai da tayi me isarta ta ce.
"Maryama yau na wayi da tashin hankali abin da bokan ya yi mini ya shammace ni, dubi kaina
yadda na wayi gari da shi da ƙwaryar molo" sai kuma ta fara tattare hannun riga tace. "Dan
Allah leƙa hammata ta ki gani" kukan kura Fulani Maryama tayi cikin kuka ta ce. "Jakadiya kanki
ko kaina yanzu me zan cewa Takawa? Dubi fa yadda kika san silba haka kaina ya koma É—azu
da na kalli mudubi har É—auke kaina nayi, a haka Takawa zai dinga kallo na?" Jakadiya ta saki
hanci da baki tana kallon rankwalelen kan Fulani Maryama ta ce. "Maryama dama haka kike da
rafkeken kai kamar na jinjirin Jaki, wallahi idan Takawa ya ganki a haka idan bai nemi tsari da
ke ba shegiya nake."

Sarki Aminullah zaune a cikin fada cikin ƙasaitacciyar shigarsa ta alfarma irin ta ƙasaitattun
sarakuna, Maleek ne a gefensa na dama sai Salman dake gefensa na hagu, wani bafade ne ya
shigo ya russuna yace. "Allah ya taimakeka suna tafe ita da Mahaifiyarta da Ć´ar uwarta." Jinjina
kai Sarki Aminullah ya yi sannan Bafaden ya fita, daga cen gefe baƙin Sarki Abdallah ne sai
Waziri da Galadima daga cen bakin ƙofa Ɗan more ne sai dogarawan ƙofa.
Inna Habi ce a gaba Maryo da Abu suna rufa mata baya har suka ƙarasa cikin fadar, cikin
girmamawa suka russuna suka gaida Mai martaba. Maleek da tun shigowarsa ya kafe Maryo da
kallo ba ƙiftawa, Inna Habi kana kallan ta zaka fahimci tana cikin tashin hankali ta russuna ta ce.
"Allah ya taimakeka ance kuna buƙatarmu a fada" Sarki Aminullah ya gyaɗa kai a hankali ya
fara motsa baki yace. "Hakane! Munaso mu ji sunayenku" Inna Habi ce ta fara gabatar da kanta

sai Abu daga ƙarshe Maryo ta gabatar da kanta tana watsawa Salman harara." Sarki Aminullah
yace. "Maryo kinsan wannan" Maryo kallan Maleek da aka nuna

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
google.com, pub-9213700357025247, DIRECT, f08c47fec0942fa0