Showing 27001 words to 30000 words out of 57967 words

Chapter 10 - Anya Baiwa Ce 1 Complete Hausa Novels

zaka yi mini haka? Me
yasa zaka guje ni a lokacin da na fi kowa buƙatarka?" Hannunta ta ɗago tana kallan zoben dake

jikin ɗan yatsanta ta ce. "Ashe zaka iya manta alƙawarin da muka ƙulla da kai me yasa haka
idan wasa kake mini ka farka dan Allah" tana rufe baki kamar wacce aka ce ta juya daga cen
tsallaken bishiyar ta hango wasu mace da namiji suna wasanninsu sai dai sun jiya mata baya
yadda bata iya ganin fuskoki su, sautin muryoyinsu ta fara ji tare da wata irin sarewa mai tashi a
tsakiyar ka, a hankali ta miƙe zata ƙarasa gurinsu sai dai tana miƙewa ta hange su suma sun
tashi sunyi gaba suna suna ci gaba da wasanninsu. Maryo batayi ƙasa a gwiwa ba ta cigaba da
binsu suna gaba tana binsu a baya har sai da suka yi tafiya mai tsawo, sannan ta hango
hangesu sun nufi wani kogi itama batayi ƙasa a gwiwa ba ta nufi hanyar kogin. Kamar daga
sama taji kiran da wasu Fadawa suke mata hannuwansu ɗauke da wasu manyan itatuwa
wanda da alama bishiya suka saro a gurun. Ƙiƙam ta tsaya tana kallonsu ɗaya daga ciki yace.
"Ke Maryo kanki ɗaya kuwa me ya kawo ki cikin wannan dajin da rana tsaka" Maryo dai har
lokacin bata tanka musu ba. Ɗaya daga ciki ne ya ƙarasa gurin ya fisgota da ƙarfin tsiya ganin
taba gabda da nufa bakin wani rami da babu komai a gurin sai tarin bolar da ake zubawa a
gurin.

Murya a raunace ta ce. "Ganin nayi suna tafiya shiyasa na bi bayansu wallahi kamar nasansu
ji nake kamar nice tare da Furzaan kuma sai suka faɗa cikin kogin cen" Ɗayan Bawan ne ya yi
mata kallon baki da hankali yace. "Ramin bolar ne ya miki kama da kogi kina cikin hankalinki
kuwa?" Ɗayan da ya ƙarewa Maryo kallo yace. "Kai Bulama riƙo hannunta mu ƙarasa ciki
kawai" ba musu suka wuce Maryo na biye da su har lokacin bata daina waige ba har suka
ƙarasa cikin jama'a. Sai da suka shiga cikin mutane ya saki hannunta sannan suka wuce gidan
bayi suka tura Maryo sannan suka wuce kai itacen da suka ɗauko.Maryo ɗakinsu ta shiga
kamar koyausne zaune ta ga Inna Habi ta zuba tagumi ga hawaye na bin fuskarta ɗaya bayan
ɗaya, Inna Habi gabaɗaya ta rame ko abincin kirki bata ci. Abu na ganin Maryo ta janyota da
sauri ta ce. "Abu ina kika shiga muna ta nemanki tun ɗazu" Kamar an buɗe famfo haka Maryo ta
faɗa jikin Abu ta fashe da wani irin kuka, Inna Habi da sauri ta ɗago ta kalleta sannan ta kauda
kanta gefe ɗaya tana rumtse idonta. Wasu bayi da ke cen gefe ne suka juyo suna kallon Maryo,
dukda basusan abin da yake damun Maryo ba amma da jin irin kukan da take yi ka san daga
cikin zuciyarta kukan yake fitowa. Abu bubbuga bayanta ta fara yi cikin tausayin ƴar uwarta ta ta
ce. "Me yake faruwa Maryo?" Maryo hawayen ne ya kuma zubo mata da sauri ta kama hannun
Abu ta kai saitin ƙirjinta. Abu zaro ido tayi jin yadda zuciyar Maryo ke bugawa da ƙarfi cikin
sauri. Kafin Abu tayi magana ta ce."Duk bugun numfashi yana sauka da dakom soyayyarsa Abu
mutuwa zanyi ba zan iya rayuwa babu shi ba, shi ya koya mini zallar soyayyarsa yanzu kuma
ya juya mini baya. Ina ji a jikina kamar ba shi bane kamar ba zuciyarsa bace idan har zuciyarsa
ce a jikinsa babu yadda za'ayi baiji abin da nake ji a zuciyata ba, Abu ki taimaka min bansan
sanda na fara sonsa ba ban san yaushe na dulmiya cikin tekun ƙaunarsa ba, abu ɗaya na sani
wallahi ina sansa ina ƙaunarsa amma ya juya mini baya Abu kin ga" Maryo ta janyo hannun Abu
ta ɗora akan ɗan yatsan da zoben hannunta yake kai ta ci gaba da cewa."Har nuna miki na yi a
ranar da muka haɗu da ke da hannunsa ya bani, tun kafin wannan ranar kowa yasanni da shi
amma me yasa lokaci ɗaya yi mini haka. Abin da ban taɓa tsammani bane amma yau ya mareni
a gaban mahaifina Abu ki duba irun hallacin da mahaifina ya yi masa, bansan laifin da nayi
masa amma duk laifin da nayi ban cancanci irin wannan hukuncin..." bata ƙarasa magana ba
Abu ta sa hannu ta toshe mata baki saboda yadda mutane suka fara taruwa a bakin ƙofar suna

leƙensu, rumgume ta Abu tayi a saitin kunnenta ta ce mata. "Kiyi shiru Maryo mutane suna
kallonmu kinasan a dinga yi da mu a cikin gidan nan kenan?" Sororo Maryo ta yi tana kallon
Abu cikin sanyin murya ta ce. "Shikenan Abu na bar maganarsa kenan?" Abu da gyaɗa mata
kai.
Abu ta fara girgiza kai ta ce. "Bakiji yadda zuciyata take yi mini ba Abu, ba zan iya ba..." bata
ƙarasa magana ba wani irin tari ya sarƙe ta nan take ta fara wani irin kakari sai ga wani irin
aman jini na fita daga bakinta nan take numfashinta ya fara ɗaukewa ta yanke jiki ta faɗi a
gurin.
Lokacin da aka kaishi masauki kwanciya ya yi akan katifa ringingine idanunsa sun ciko da
ƙwallah yana tuna soyayyarsa da Shukra.

Zaune take a wani ɗan madaidaicin ɗaki ta ga ya shigo hannunsa ɗauke da wata babbar
leda, turo baki gaba tayi ta ce. "Ya Maleek wallahi tun ɗazu nake jiranka har na fara jin tsoro"
hancinta ya lakace yana kwaikwaiyar muryarta yace. "Tsoron me bayan kinsan ba daɗewa zan
yi ba" Juya masa baya tayi alamun tayi fushi tana ajiye ɗinkin hular da take yi, ta bayanta ya
rumgumota ta faɗo jikinsa yace. "Tuba nake amma kinsan dai nima ba da san raina na daɗe ba"
Kafin ta yi magana ya fara buɗe ledar da ya shigo da ita sannan ya ɗauko Ƴar tsala ya sa mata
a bakin yace. "Na cika alƙawari dai tunda ga ƴar tsalanki" ci ta fara yi harda lumshe ido tana
haɗiyewa kamar wacce ta haɗiyi maɗaci ta fara kakarin amai, da sauri ya janyo mata rigarsa
dake rataye yasa a gabanta nan ta hau amai har sai da ta amayar da duk abin da ta ci" cikin
tausayawa ya fara mata sannu ta langaɓar da kai ta ce. "Ya Maleek anya ba mutuwa zan yi
ba?" ta faɗa hawaye na zuba daga idonta. Ya sa hannu ya goge mata yace. "Shukura ki daina
faɗin haka, laulayi ne kawai. Kina tunanin idan kika mutu zan iya rayuwa ne" Murmushi tayi ta
ce. "Ba sai ka kula da abin da zan haifa ba"

Tashi ya yi zaune yana goge hawayen da ke zuba a idonsa, a hankali ya furta. "Shukra me
yasa me yasa zaki yi mini haka" kamar wanda aka mintsina haka ya zabura ya miƙe zaune ya
ciro wayarsa lambar Mahaifinsa ya kira har sai da ta tsinke ba'a ɗauka ba, kira ya ƙarayi sannan
ya ji murya mahaifin nasa a tsakiyar kansa sakamakon dogon tunanin da ya shiga.
"Maleek ya akayi?" Maleek ya shafa kai yace. "Ranka ya daɗe barka da hutawa" Mahaifin
nasa ya amsa sannan yace. "Allah ya taimakeka naga Shukra a gidan Kawu" da mamaki
Mahaifin nasa yace. "Wace shukuran?" Maleek yace. "Shukra dai tawa" ajiyar zuciya Mahaifinsa
ya yi sannan yace. "Maleek Allah har yanzu baza ka sawa zuciyarka salama ba, ka taɓa ganin
wanda ya mutu ya dawo" Maleek kamar zai yi kuka yace. "Wallahi da gaske nake yi na ganta da
idona" Muryarsa ce ta fara rawa ya ci gaba da cewa. "Amma ko kaɗan bata nuna ma ta sanni
ba Mai martaba" Mahaifin nasa yace. "Maleek ba tun yau ba fa na ce maka ka dage da addu'a
domin na lura mutuwar yarinyar nan yana san taɓa maka ƙwaƙwalwa, Shukra yau shekararsu
nawa da mutuwa ina jin ta kusa biyu idan ba mantawa nayi ba, saboda irin haka nace maka
dama ka fitar da wata matar ka yi aure amma fir kaƙi" Maleek ya taƙarƙare ya fara zabga
rantsuwa.

"Na rantse da girman Allah ita na gani Ranka shi daɗe, kasan bazan maka wasa ba a cikin
fadar Kawu fa na ganta ta fita tana hawaye da alama ma kamar shari'a yake musu, ni dama na
daɗe da ji a jikina Shukra tana nan da ranta bata mutu ba tunda har gobe ba'a tsinci gawarsu
ba." Mahaifinsa yace. "Dama ya za'ayi aga gawarsu bayan wuta ta cinye su ƙurmus, wallahi
Maleek ina tsoron kar yarinyar nan ta fara yi maka fatalwa" Maleek yace. "A fadar Kawu fa na
ganta ka yarda dani wallahi ka turo wani daga nan yazo ya ganta idan ƙarya nake." Ganin ya
dage yasa Mahaifinsa yace. "To shikenan zan yi nazari akai" suna yin sallama ya kira
Mahaifiyarsa ya sanar da ita halin da ake ciki itama ba ƙaramin kaɗuwa tayi da jin zancensa ba,
bayan ta gama sauraronsa ta ce. "Maleek ka tabbatar da abin da ka faɗa gaskiya ne kuwa kar
na kira Yaya naji akasin haka" cike da ƙarfin gwiwa yace. "Wallahi da gaske nake Umma" har
lokacin mamaki take ta ce. "To amma wannan lamari akwai ɗaure kai to Ina Hassan da
Hussanin ko baka gansu ba? Kuma ita me tace maka?" Maleek yace. "Bangansu ba Umma,
kuma ba wata doguwar magana mukayi da ita ba, bige ni tayi gar ta miƙo mini kayan tana bani
haƙuri" Umma tayi jim ta ce. "Anya Maleek wannan lamarin naka akwai ƙamshin gaskiya, ace
Shukra ta ganka amma ta kasa nuna farincikinta a fili? Amma babu damuwa zan kira Yaya zan
ji daga bakinsa." Maleek ya sauke a jiyar zuciya yace. "To Umma" daga haka suka yi sallama da
ita, tashi ya yi ya dinga kaiwa da kawowa lokaci-lokaci yana naushin iska. Gabaɗaya kansa ya
kulle banda faɗuwar gaba babu abin da yake ji.


Saif na shiga sashen Mahaifiyarsa ya kusa karo da Baiwa Bintu dukda alokacin ba ƙwarin
jikinta taji ba haka ta rissuna cikin girmamawa ta ce. "Tuna nake ranka ya daɗe" Gyaɗa mata
kai ya yi yana binta da kallon tausayi har ya shiga ɗakin yana jin matsanancin tausayinta, zama
ya yi ya gaishe da Mahaifiyarsa sannan yace. "Ammi wannan ba baiwar nan bace ni bansan
sunanta ba" Fulani Zaliha ta ce. "Bintu ba ita ce wallahi baka jinyar da yarinyar nan ta sha ba
kamar bazatayi rai ba, bayan na asibitin da akayi na hausa ma fa haka ake ta fama kasan jikar
uwar bayi ce baka ga tashi faɗin da ta dinga yi ba, ciwo kamar mayu kamar kuma iska gashi
nan dai" Saif yace. "Amma me ya kawo ta nan ba Baiwar Umman Salman bace.?" Fulani Zaliha
ta gutsiri tufa ta ci gaba da cewa. "Eh a baya baiwarta ce amma gaskiya har yanzu bata koma
mata ba tunda jikin nata har yanzu da saura, yanzu ma langa ta kawo mun wacce Uwar bayi ta
tafi da tuwo rannan" Shiru Saif ya yi yana ƙara jin tausayin Bintu a ransa lokaci ɗaya yaji ta
kwanta masa a zuciya a hankali ya furta. "Allah ya bata lafiya" Fulani Zaliha ta amsa da Ameen
sannan ta ce. "Dama tun ɗazu na ji ka shiru ance min anga fitarka Saif banasan ka dinga nisa
da gida fa" Saif yace. "Ammi dama naje gaida me martaba ne" ɗan tsuke fuska ta yi sannan ta
ce. "Hakan ya yi kyau amma ka dinga lura" Saif yace. "In sha Allah! Ammi naga wani baƙo yazo
amma naga yana yanayin kama da ni naji Mai martaba yana kiransa da Maleek" Murmushi
Fulani Zaliha ta yi ta ce. "Ɗan uwanka ne ai" sai kuma yanayin fuskarta ta sauya cikin damuwa
ta ci gaba da cewa.

"Dan dai baka sansu ba, amma ɗan wajen Addanku ne Adda Zainabu me tsokanarka idan
tazo" Murmushi ya yi yace. "Kai amma me yasa bansan shi ba" Fulani Zaliha ta ce. "Ai kasan
shi sojan ruwa ne basu cika zama ba idan yazo kuma a ya daɗe ya kwana ɗaya" Saif ya jinjina

kai yace. "Ai ta daɗe ma bata zo ba" ta ce. "Ai kuwa dai" daga haka suka ci gaba da hira Saif
yana san sanar da ita yadda sukayi da Maryo a fadar Sarki Aminullah amma yana kokwanto,
daga ƙasan zuciyarsa kuma yana jin kamar bai kyauta ba amma lokaci ɗaya sai yaji haushinta
ya kamashi dan a duniya yanzu babu wacce yake jin haushi kamarta.
Tsaye suke a bakin tsibirin Fulani Maryama ta kalli Jakadiya ta ce. "Jakadiya wannan karan
bafa zuwa na bane ni kaɗai, zuwan mu ne domin nemarwa kanmu mafita" Jakadiya sai raba
idanu take ta ce. "Eh haka ne amma wallahi nikam lamarin yarinyar nan ya fara bani tsoro"
Fulani Maryama ta yi mata wani kallo tana shirin magana akayi musu iso zuwa cikin kogon
dutsen Boka Marduska. Kamar ko yaushe yanzu haka ma yana zaune a gaban wuta daga shi
sai wata rigar fata me baza da wandon fata. Kallo ɗaya ya yi musu ya ɗauke kai ya ci gaba da
sha'anin gabansu kamar ma bai gansu ba, kallan juna sukayi tsakanin Fulani Maryama da
Jakadiya saboda tun da suke zuwa Marduska bai taɓa yu musu irin haka ba. Fulani Maryama
ce tayi ƙarfin halin fara magana.

"Barka da aiki sarkin bokayen duniya Marduska me dogom zamani" Marduska ya kalleta bai
tanka mata ba ya ci gaba da watsa wasu ƙasusuwa a cikin wutar sannan ya ɗago yace.
"Maryama meke tafe da ke?" a nan ta fahimci Marduska fushi yake da ita saboda kana zuwa
gurinsa kafin ma ka buɗe baki zai sanar da kai abin da yake tafe da kai. Ta russunar da kai ta
ce. "Muna neman yafiya da alama munyi gagarumin laifi" Marduska yace. "Nasan akan Ɗanki
Salman kika zo da Rayzuta" Jakadiya tare da Fulani Maryama kamar ƙadangaru suka gyaɗa kai
lokaci ɗaya. Bushewa ya yi da wata mahaukaciyar dariya sannan ya kallesu yace. "Wuya ko da
magani ba daɗi. Maryama dubi yadda kuka yi zumu-zumu kamar an jiƙa kasa a ruwa. To
maganar gaskiya Maryama gidan ku na cikin wani irin yanayi ni da kike gani na wannan ƙurar
tafi ƙarfi na dan bazan iya dakatar da ita ba. Shuɗaɗɗun ruhika haɗe da rayayyun ruhika ne
suka gogawa a tsakani kinga kuwa ni meye nawa a ciki, maganar da Saif ya gaya miki tabbas
haka ne domin Ɗanki sam baida imani irin zuciyar ubansa gareshi, wallahi kika nemi ki bashi
matsala yana iya aikaki ƙiyama sannan matsawar kika bari aka ɗaura masa aure da Rayzuta to
na tabbata mai ƙwatar kansa a gidan nan sai mai yawancin kwana. Ke in taƙaice miki labari
wallahi gidan zasu tada gabaɗaya dan ko Sarki Aminullah banajin zai tsira da numfashi, domin
tsoguwar gaba ce kuma kema kina da hannu a cikin wannan shuɗaɗɗiyar gabar." Fulani
Maryama ta zaro idanu tana dafe ƙirji ta ce. "Marduska me ye nawa a ciki?" Murmushi ya yi bai
tanka mata ba yace. "Kafin zuwan wannan ranar nima bansan da haka ba har sai da Zulik ya
bayyana, duba nan" ya ƙarasa faɗa yana nuna mata wata ƙwarya kusan lokaci ɗaya suka leƙa
ita da Jakadiya, Fulani Maryama ce zaune a gaban wata sarauniya tana motsa baki da alama
magana take yi mata, kafin ta gama fahimta suka ga ya ɗauke. A razane Fulani Maryama ta ce.
"Marduska yaushe haka ta faru? A iya sanina bantaɓa zama baiwar wata ka duba fa ka gani
kowa yasan ni ƴar Sarki ce gaba da baya kuma Sarki nake aure" Marduska yace. "Wannan
amsar tambayar taki tana gurin Zulik wato Salma ki bishi a sannu shi zai warware miki komai ko
shi ko Rayzuta, amma karkiyi fatan Rayzuta ta waiwayoki domin sam bazai yi miki kyau ba." ya
nuna Jakadiya yace. "Ke kuma ina jiye miki ranar da Saif ɗan wajen Zaliha zai juyo gareki
tabbas a lokacin me ƙwatarki sai Allah, dan sai ya ƙasƙantar da ke a cikin gidan sannan kuma
ya yi miki kisan wulaƙanci domin Furzaan cike yake da baƙin cikinki" Jakadiya ta ce, "Waye

kuma Furzaan ni ƴasu" Marduska yace. "Ɗan wajen Zaliha ne sannan ita kanta Rayzuta bata
kyaleki ba ko dan abin da kika yiwa Sarki Aminullah domin Mahaifinta ne" A zabure Fulani
Maryama ta miƙe tsaye ta ce. "Me kake faɗa? Yarinyar ce ƴar gidan Takawa?"

Daga cen Masaraurar Adamawa wata mata na gani Aƙalla zata yi shekara Arba'in da biyar,
safa da marwa take ta yi a cikin ɗakinta cikin tashin hankali. Wayarta ta ɗauka ta doka kira babu
jimawa aka ɗauka ko amsa sallamar ba'ayi ba ta ce. "Ka san wanne mummunan labari na samu
yanzu? Wai Maleek ya je Masarautar Kano gidan Wan Mahaifiyarsa ya kira Mai martaba wai ya
ga Shukra a cen" daga cen ɓangaren yace. "Fulani me kike faɗa ne wai? Yarinyar da muka
bankawa wuta ita ce ta aka gani a masarautar Kano?" Matar da ya kira da Fulani ta ce. "Wallahi
da gaske nake fa yanzu haka Sarki ya tashi Mutum biyu daga nan sun tafi cen yanzu ina muka
kama idan yarinyar nan ta bayyana? Kasan asirinmu ya gama tonuwa dai.Ni kam har bansan ya
zanyi ba wallahi" Mutumin yace. "Lallai tsugunne bata ƙare mana ba, Amma kuwa dole musan
abin yi matsawar Shukra ta dawo gidan nan hatta zaman duniyar ma sai ya gagaremu."


INA MUKU FATAN ALHERI🥰

BA WANI PAGE DAN WALLAHI WUTARMU TA LALACE TUN KWANAKI KUYI HAKURI DA
ERRORS

KU HAƊE A COMMENTS🤾🏻‍♀️🤣

_LITTAFIN ANYA BAIWA CE? NA KUƊI NE DA NAIRA 200 ZAKI KARANTA SHI CIKIN
KWANCIYAR HANKALI, ZAKU BIYA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN, FIRST BANK 3090957579
AISHA ADAM, ZA'A

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
google.com, pub-9213700357025247, DIRECT, f08c47fec0942fa0