Showing 45001 words to 48000 words out of 57967 words
dakatar da ita suka tafi tare
suna tafe suna hira, duk inda suka wuce a cikin gidan sai anyi gulmarsu saboda wasu har sun
fara yi musu wata fassara, wasu suce soyayya suke wasu kuma suce shaƙuwa ce kawai kowa
dai da abin da yake faɗa. Kai tsaye kasuwar rimi suka wuce Abu take ta siyayya har ta
kammalla, wasu kayan Saifa ne yake riƙe mata wasu kuma ita take riƙewa. Kamar almara ta
hango Maryo gaban wani me sayar da kayan ƙore da jigidar mata, sakin baki tayi da murnarta
tana nunawa Saif ta ce. "Maryo! Yaushe kuka zo?" Saif yace. "Wace Maryo kuma" gurin da take
nuna masa ya kalla hango ya yi tsaye itama su take kallo, nan take ya tsuke fuska Abu ta matsa
zata ƙarasa gurin da sauri ya riƙe hannunta yana cewa. "Wallahi idan kika matsa daga nan sai
ranki ya ɓaci" juyowa tayi ta kalleshi idanta cike da hawaye ta ce. "Maryo ce fa ƴar uwata" fisge
hannu tayi da niyyar zuwa gurinta amma ga mamakinta sama ko ƙasa haka ta nemi Maryo ta
rasa.
_LITTAFIN ANY BAIWA CE NA KUƊI NE DA NAIRA 200 ZAKI KARANTA SHI CIKIN
KWANCIYAR HANKALI, ZAKU BIYA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN, FIRST BANK 3090957579
AISHA ADAM, ZA'A TURO DA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR,0706 206 2624, DAN
GIRMAN ALLAH IDAN KINSAN ZAKI FITARMUN DA LITTAFI NA YAFE CINIKINKI._ [17/11/2021, 11:17] Ameera Adamí ¼í¼š: 30...
Kurɗawa ta dinga yi cikin mutane tana laluben Maryo haɗe da ambatar sunanta, tana gaba
Saif yana biye da ita yana kiranta. Idanunta ne suka ciko da ƙwallah ganin har zuwa wannan
lokacin babu Maryo babu alaminta, gefe tana tana zubda hawaye ta ce. "Maryo ina kika shiga
ne me yasa kika tafi ne?" Saif ya ƙaraso gurinta fuska a ɗaure yace. "Baza fa ki ganta ba." Abu
ta goge ƙwallar idonta ta ce. "Saboda me?" Saif ya ɗaga kafaɗarsa alamun shima bai sani ba
sannan yace. "Da tana so ki ganta da baza ta tafi ta barki ba kinga kuwa tana sani ta ɓoye miki,
dama ke kika damu da ita ban da haka da ta damu dake bazata..." da sauri ta katse shi da
cewar, "A'a wallahi akwai dalilinta na san ɓoye mini. Maryo ba yadda ka fassara ta take ba, na fi
kowa sanin wacece ita amma..." Shima katse ta ya yi yana tsareta da dara-daran idanuwansa
yana faɗin. "Wuce mu tafi ina ga ta fara yi miki gizo ne dan da ita ce a yadda kika faɗa kinga
bazata tafi ba" Ganin zata ɓata musu lokaci yasa ya riƙo hannunta suka wuce tana tafe tana
waiwaye, har sai da ya ga sun bar wajen kasuwar sannan ya sakar mata hannu. Har lokacin
Abu hawaye take dan zuciyata taƙi aminta da cewar wai gizo Maryo take yi mata, suna
ƙarasawa gida a gaggauce ta ƙarasa gurin Fulani Zaliha ta ajiye kayan da suka siyo kai tsaye
ta wuce sashen Fulani Maryama.
Sallama ɗauke a bakinta ta shiga sashe sai da ta fara shiga wurin Fulani Maryama ta
gaisheta, sama-sama Fulani Maryama ta amsa fuska a tsuke ta ce. "Lafiya me kika zo yi a
nan?" A ɗan duburburce Abu ta ce. "Dama nazo na gaishe da Inna ta ne." Fulani Maryama ta
taɓe baki ta ce. "Ba fa koyaushe na fiye san a dinga yi mini zarya a sashe ba, dan haka ki
kiyaye idan ba haka ba zan sa a dakatar da zuwanki." Abu ta russuna ta ce. "Za'a kiyaye Allah
ya taimake ki." Fulani Maryama kamar ba za ta amasa ba sai kuma ta ce. "Ki gaggauta zuwa
kiyi abin da ya kawo ki dan ina da abin da zansa ta tayi mini" Abu ta russuna ta miƙe ta godiya.
Abu na shiga ɗakin Inna Habi ko kyakkyawar gaisuwa basu yi ba, cikin raɗa tace. "Inna wallahi
na yau a bakin kasuwa naga Maryo wai kafin na ƙarasa na neme ta na rasa" zaro idanu waje
Inna Habi tayi cikin zumuɗi ta ce. "Me yasa baki mata magana ba?" Abu hawaye ta fara yi tana
bawa Inna Habi labarin yadda sukayi, jiki a sanayaye Inna Habi ta ce. "Abu kuma kina ganin
maganar Saif bata hanya kuwa? Gani nake Maryo zata zo amma taƙi ƙarasowa gidan nan?
Idan Maryo bata Adamawa ai da tuni munji labari daga gurin Takawa. Ina ganin yawan
tunaninta ne yasa kika fara ganin tana miki gizo." Motsi suka ji daga bakin ƙofar Fulani
Maryama da sauri Abu ta ce. "Inna sai anjima ni zan wuce dama cewa nai bayi nazo na gaishe
ki" Baiwar Fulani Maryama ce ta ce. "Inna Habi Fulani ta ce kije ki matsa mata ƙafa." Inna Habi
jiki na rawa ta ce. "To muje" Abu cikin tausayi ta kalli Mahaifiyarta tana jin tausayinta dan tabbas
tasan bata jin daɗin zaman gurin Fulani Maryama, ta so ace ita take zaune a ɓangarenta
Mahaifiyarta na sashen Fulani Zaliha amma babu yadda ta iya, jiki babu ƙwari kamar kazar da
ƙwai ya fashewa a ciki. Zuciyarta babu daɗi ta koma sashen Fulani Zaliha, tana shiga ta wuce
kan katifarta ta kwanta tana tunanin halin da ƴar uwarta take ciki.
Akan idanunta suka wuce suka tafi lokacin da take leƙensu tana daga wani ɗan lungu a ɓoye,
lokacin da ta fito daga gurin da take ɓoye a dai-dai lokacin Saif ya juyo suna haɗa ido ya watsa
mata harara hannunsa riƙe da na Abu, da sauri ta koma lungun ta ta jingina ta bango ƙirjinta na
bugawa nan take taji wani abu na sukarta a zuciya, hawaye ne suka zubo mata saboda
gabaɗaya rayuwar tayi mata zafi. Tana nan tsaye taji an dafa ta ta baya da sauri ta juya dan
ganin wanda ya dafa ta, wata tsohuwa ta gani suna haɗa ido taji gabanta ya faɗi tsigar jikinta ta
shi, ɗauke idanunta ta yi saboda bazata iya ci gaba da kallonta ba, tsohuwar ta katse mata
tunani da cewar. "Ki ƙara haƙuri. A rayuwa dukkan tsanani yana tare da samu, da sannu ƙuncin
rayuwa zai yaye miki ki dai karki cutar da kowa ki zauna da kowa lafiya, karki shiga haƙƙin wani
ki riƙe Allah da manzansa indai kika riƙe wannan zaki ci ribar rayuwa." gyaɗa mata kai tayi ta
sunkuyar da kai tana goge hawaye tana ɗago da kai ta nemi tsohuwar ta rasa, ba ƙaramin tsoro
ta ji ba da sauri ta bar gurin jikinta har rawa yake saboda tashin hankali.
Wannan karan tsoro ne ƙarara ya bayyana akan fuskar Maleek yana san ya yi mata magana
yana tsoron kar shima wani abun ya same shi, daga waje wani Dogari ne ya leƙo yace. "Allah
ya taumaki Yarima labari ya ishewa Takawa akan tafiyar mai maganin, yanzu haka akwai wani
Sarkin wanzamai yana bakin ƙofa idan ka bada umarni a shigo da shi yanzu, Mai martaba yace
shima zai jarraba tashi basirar." Maleek yawu ya haɗiya mai ɗaci dan shi kansa ƙarfin halin
zama ya yi a ɗakin da take, ajiyar zuciya ya sauke yace, "Ba damuwa a ce ya shigo" yana gama
faɗa suka haɗa idanu da Maryo lokaci ɗaya ta sakar masa murmushi wanda ya sa cikinsa
murɗawa ba tare da yasan dalili ba, dan ya yi imani da Allah wannan murmushi da take yi ba
lallai ya zame musu alkairi ba. Yana nan tsaye Mai maganin ya shigo hannunsa rataye da jakar
wanzancinsa, Dattijo ne dan da alama zai yi shekara hamsin zuwa hamsin da biyar. Cikin
girmamawa ya russuna ya gaida Maleek sannan ya kai dubansa ga Maryo da ke zaune a gefe
ta harɗe ƙafafuwanta, suna haɗa ido ta miƙe ƙafafuwanta sannan ta ce masa. "Idan zaka iya
zan baka wani aiki, nima ba hurumi na bane da na aiwatar da shi tun tuni." Wanzamin kallanta
ya yi yana ƙarewa yanayinta kallo ya ɗan tsorata da yadda ya kalli yanayinta, cikin ƙarfin hali
yace. "Wane aiki ne? Idan bai gagara ba na aiwatar da shi" Maryo a hankali ta tako ta ƙarasa
gabansa, Maleek dake ƙoƙarin zama yana kallonsu cikin mamaki, dan ya yi tsammanin shima
wutar zata saka masa. Idanunta ne suka ciko da ƙwalla ta sa hannunta ta shafo hawayen
idonta, hawayen ta dangwala a ƙasan tabarmin kaba. Nuna masa tayi ta ce, "Wannan abun
nake son kaje ka tonr mini shi a fadar Daulatul Ujuran zan baka kyautar abubuwan da baka
taɓa tsammani ba, zan baka sirrikan daga cikin irin ayyukanku, dan Allah wannan kaɗai zaka
iya yi mini ka ceci rayuwata da ta Mijina." Maleek ido ya zuba musu dan shi dai babu abin da ya
iya gani a gurin yana tabarmar gurin take haka yake kallanta, yana tsaka da tunani yaji
Wanzamin yace, "Allah ya taimakeki wannan fa ba ƙaramin aiki bane, kuma maganar gaskiya
nikam ina jin tsoro saboda kin ce kema ya gagareki, ina gudun halin da rayuwata da na iyalaina
zamu shiga." Maryo ta share hawayenta ta ce, "Ba wai ya gagareni bane saboda ba zan iya ba,
a'a kasan yadda ahalin Bidayatul jinn muke da kowanne irin rami. Da ace idan na shiga zan iya
cimma burina babu yadda za'ayi na nemi agajin wata halitta, don Allah ka taimaka ka ceci
muradin da aka jima ana ƙoƙarin cimma burinsa." Wanzamin sharce gumin kansa ya yi yace,
"Gaskiya wannan aikin yafi ƙarfina haka zalika ni banma san ke zan yiwa magani ba, da babu
abin da zai sa na zo gidan nan." Maryo ta miƙe ta koma gurin zamanta na farko ta ce, "Na baka
lokaci kayi nazari dan na fahimci duk gidan nam babu wanda ya fahimci halin da nake ciki"
Maleek idanu ya zura musu dan gabaɗaya kansa ya kulle, Wanzamin ya gyara zaman jakarsa
sannan yace, "Ya kamata ki sanar da su dan su fita daga hurumin da ba nasu ba, wannan yaƙin
naki ne ki daina tunanin wani zai iya taimaka miki idan ba haka ba bazaki taɓa nasara ba, ki bar
tunanin zan iya yin wani abu akai domin kin fi kowa sani waye Zulik da mugun halinsa,
matsawar yana raye bazai taɓa barin wani yaga wallensa ba. Ke kaɗai ce bazai iya cutarwa ba
dan haka ke kike da yaƙin kuma kike da nasarar a hannunki." Maryo cikin gamsuwa da
jawabinsa ta ce. "Alƙawari na ɗauka san raɗin kaina bazan waiwaye su ba, ba zan koma
gurinsu ba har sai lokacin da suka fahimci cewar ni ba tasu bace, sai sun tabbatar da cewar
kama da wane bata wane. Ina so su fahimci bambamcin dake tsakanin fari da fari-fari idan yaso
dan kansu sai su yanke hukuncin da ya dace da kansu, amma ko da soyayyarsa zata kashe ni
tabbas bazan taɓa kunyata baiwar Allah da ta taimaka mini a lokacin da bani da kowa ba, ta yi
mini sutura a lokacin da nake tsirara ta maye mini gurbin uwa da uba a lokacin da nake
marainiya gaba da baya." Wazamin ba ƙaramin tausayinta ya ji ba a hankali ya miƙe ya ɗauki
jakarsa yace, "Zan yi ƙoƙarin na wayar da kansu akan su san halin da ake ciki har game da
masu maganin da suke nema ido rufe, ina miki fatan nasara akan abin da kika sa a gaba." yana
gaba faɗa ya zagaye ramin da ta nuna masa har ya kai bakin ƙofa ya juya ya ce mata, "Ki
ƙoƙarin ɓatar da tasawirar ramin nan domin kinsan mugu bai da kama, bana fatana a ƙara miki
wani ƙullin akan wani dan kinsan cikin gidannan ma maƙiyanki sunfi masoyanki yawa." ficewa
ya yi daga ɗakin yana sauri kamar zai tashi sama. Maleek da ya jiƙu da mamaki ya kalli Maryo
da ta ƙarasa bakin gurin da sa ɗigon hawayen tana shafe gurin da hannunta, bayan ta gama
shafewa ta kai hannunta kan gashinta ta shafa akan gashinta ta ƙarasa yi tana girgiza kanta.
Wanzamin na fita bai zame ko ina ba sai fadar Sarki Abdallah, yana shiga ya nemi guri ya
russuna cikin girmamawa ya ƙara gaida Sarki sannan ya ɗan jim dan yanasan sanar da shi abin
da zai ɗaure musu kai, sai dai bai san ta siffar da zasu karɓi maganar ta shi ba. Sarki Abdallah
ne ya kalli yanayinsa ya kalli wasu Dogarawa ya umarce su da su basu guri, fadar ta rage daga
Ciroma, Galadima sai Ɗan more. Sarki Abdallah yace. "Ɗan Wanzam ya ake ciki ina fatan jin
nasara daga bakinka" Wanzamin ya gyara zama yace. Allah ya taimakeka ka gafarceni amma
labarin ba me daɗi bane, kuma ina fatan wannan jawabin nawa zai warware wasu wasin da
kuke ciki dangane da abin da na sani zan sanar da ku. Maganar gaskiya wannan yarinyat duk
wani Mai magani da zaku kira sai dai yaci kuɗinku dan babu wata nasara da zai samu a kanta,
shekaru goma da suka wuce akwai wani abokina wanda ya kasance yana daga cikin jinsin
aljanu, ya bani labarinta dan haka zan sanar da ku idan kuna da buƙata." Sarki Abdallah
mamaki ne ya kama shi ya kallai Wanzami ya gyaɗa kai, Wanzamin ya ci gaba da cewa. "Wasu
dubannin shekaru da suka wuce..."
Yanzu sai kuna hakuri wallahi sbd rashin wuta bana samun caji akai akai idan kun lura yawan
typing ya ja baya ku karɓeshi yanda ya samu plsí ½í¸¥í ½í±�í ¼í¿»
_LITTAFIN NAN NA KUƊI NE DA NAIRA 200 ZAKI KARANTA SHI CIKIN KWANCIYAR
HANKALI, ZAKU BIYA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN, FIRST BANK 3090957579 AISHA ADAM,
ZA'A TURO DA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR,0706 206 2624, DAN GIRMAN ALLAH
IDAN KINSAN ZAKI FITARMUN DA LITTAFI NA YAFE CINIKINKI._
[19/11/2021, 19:26] Ameera Adamí ¼í¼š: 31...
SHEKARU DUBU ƊAYA
DA ƊARI BIYAR BAYA
Ƙorama ce mai cike da yalwar tsuntsaye da kala-kalar korayen ganyayyaki mabambamta,
ban da kukan tsuntsaye babu abin da yake tashi a gurin sai tsirarin kukan hallitun dake cikin
ƙarƙashin ruwa. Waɗannan kukan hallitu kaɗai sun isa zaburar ko tsoratar da duk wata hallitar
bil'adama da tai gangancin halartar gurin, saboda tsari da yanayin gurin bai daidaitu da zubi da
mazaunin hallitar da ta kasance Bil'adam ba. Ilahirin hankalinta ya tafi ga tunanin abin da yake
faruwa dangane da makomar rayuwarta, a hankali take ɗaukan waɗansu irin duwatsu masu
kama da ruwan zaiba tana jefawa a cikin ruwan, dukda a lokacin hawaye ne ke malala a saman
fuskarta. A hankali ya tako ya ƙaraso gurinta cikin shauƙin so da ƙauna ya rungumota jikinsa ya
fara yi mata magana cikin harshe yaren su na Jinnu.
"Har bis kilman dilfaskinbat miladu war kibtinga rautiku filsin yaytarku lilbaitu wurgas yaftis
gurman?"
(Barka da hutawa Sarauniyar duniya shin akwai wani abu da bai yi miki daɗi ba dangane da
zaman ki a gurin nan?"
(AI MUN ƊAN TAƁA YARENSU KOí ½í¸‚)
Hawayen idanuwanta ne suka ci gaba da malala kafin tayi wani yunƙuri yasa hannunda yana
goge mata fuskarta yana cewa, "Zubar hawayenki dai-dai yake da zubar dalma a dandamalin
zuciyata" a gaggauce ta ɗago tana kallonta dan ita kanta sheda ce dangane da abinda ya faɗa
sai dai wannan jiginanniyar ƙaddarar ba lallai ta bar cikar burinsu ba, murya a sanyaye ta fara
magana cikin irin yarensu na aljanu duk da kasancewarta cikin jinsin Bil'adam. "Ka mayar da ni
gida kar su neme ni su rasa" hancin ta ya ja yace, "Idan sun tambayeki ai sai ki ce musu kina
gurin mijinki" sunkuyar da kai ƙasa tayi ta ce, "Kasan Kaka ya hanani daɗewa a gurin nan sabo
da yana tsoron abin da kaje yazo, kafi kowa sanin yadda ƴan uwanka suka ɗauke ni basa sona
basa ƙunata, ina tsoronma wata rana karsu fara farautar rayuwata, amma na kasa haƙurƙurtar
da zuciyata akan soyayyarka me yasa? Meyasa bazasu duba irin soyayyar da mukewa juna
ba?" A wannan karan kukanta ne ya tsananta saboda yadda kalaman suke fitowa daga ƙasan
zuciyarta, rungumota ya yi yana lallashinta yana jin kukan nata har cikin zuciyarsa. Sai da ya
lura kukan nata ya fara tsagaitawa ya kalleta yace, "Dukkan tsanani yana tare da sauƙi. Ki daina
kuka saboda hakan shi zai ƙara raunatar da tawa zuciyar, kin fi kowa sanin yadda nake
ƙaunarki kuma bana tunanin ƙiyayyar da suke nuna miki zata iya tasiri a zamantakewar mu,
kedai mu ci gaba da haƙuri wata rana sai labari." Da sauri ta fisge hannunta ta ce, "Har sai
yaushe labarin zai zo ne sai yaushe zasu daina cin kashi a kaina yadda suka ga dama, dan
Allah kayi wani abu mana me zai hana mu tafi wani gurin domin muyi rayuwarmu" sunkuyar da
kai ya yi sannan ya ɗago da kai yana yi mata wani irin murmushi sannan yace, "Kinfi kowa
sanin ni kaɗai Mahaifina ya mallaka kuma a yanzu yana cikin halin rashin lafiya, shin idan na
tafi na barshi nayi masa adalci kenan?" Nine maganin masarauta Mahaifina yana da tarin ƴan
uba kina ganin zasu kula da shi? A kan idonsa ma meye basa yi mana balle ace na tafi na
barsu su biyu shi da Mahaifiyata." Cikin gamsuwa da kalamansa ta ce, "Tabbas hakane amma
wannan shirun da kake yi a kodayaushe bazai fusshemu da komai ba." Murmushi ya yi mata
yace, "Karki damu wata rana sai labari." gyaɗa masa kai tayi sannan ya sumbaci kumatunta,
miƙewa ya yi yana riƙe da hannunta suka fara tafiya, suna gabda fita daga ƙoramara daga
bayanta taji an fyaɗe ta tafi ta kifa ta faɗa kan cikinta, ƙara ta ƙwalla tana dafe baya cikin azaba,
da sauri ya ƙarasa riƙeta Allah ya taimaka ma bata ji ciwo sosai ba, a hankali ta ɗago ta kalleshi
suna haɗa ido ya wurga mata kallan tsana yana cewa. "Wannan cikin har abada bazaki haifeshi
da sannu sai mun salwantar da ku gabaɗaya." Hawaye take yi a hankali ya ɗagata yana kaɗe
mata kayan