Showing 42001 words to 45000 words out of 57967 words

Chapter 15 - Anya Baiwa Ce 1 Complete Hausa Novels

kuma cakumar wuyan Waziri Maleek
ne ya ƙarasa gurinta yana ƙoƙarin kwace shi daga hannunta, kallonsa tayi da runannun
idanuwanta ta ce. "Ka matsa daga nan banasan laifinsa ya shafeka" Galadima na ganin haka
da sauri ya matsa suka ci gaba da kiciniyar ƙwace Waziri amma kamar ƙara turata suke,
Galadima lura ya yi indai ƙarfi zasu sa bazai fisshesu ba, janye hannu Maleek ya yi ya kalleta ya
ce. "Ƴata na haɗaki da girman Allah ki sake shi ki dubi girma da daraja ta" Maryo kamar wacce
aka zarewa laka a jiki haka ta jiyo jiki babu ƙwari ta ce. "Na san dama bazaka taɓa bari ba,
amma me yasa duk irin cutarwar da suka yi mana bazaka bari na aiwatar da muradin ruhina ba"
Galadima da har lokacin bai fahimci inda zancen Maryo yake tafiya ba yace. "Eh naji nidai na ce
ki sake shi." Maryo sakinsa ta yi ta zauna daɓar hawaye na bin idanunta, zamanta babu jimawa
kanta ya ci gaba da sarawa jini ne ya fara ɗiga daga hancinta, hankali a tashe Maleek ya ƙarasa
gurinta yana mata sannu, Galadima da sauran Dogaran gurin kan Waziri suka ƙarasa suna yi
masa firfita da sannu. Sarki Abdallah shiru ya yi yana nazari ganin abun yake kamar al'amara
saboda ko wata guda bai yi da yin makamancin mafarkin abin da ya faru ba, tsoronsa ɗaya
kada mafarkin da yayi munana na bayan kwanakin su biyo baya, numfasawa ya ƙarayi yana
kallan Maryo da take zaune tana share jinin hancinta da ƙyalle. Maleek lallaɓa Maryo ya yi da
ƙyar ya samu ta tashi suka fice daga cikin Fadar tana tafe tana watsawa Waziri mugun kallo, a
hanyar su ta kawawa sashensu ta ƙofar baya ya bi da ita saboda idanun mutane, suna wucewa
ta sashen matan Sarki Maryo ta tirje a gurin.

Maleek ya waigo yace. "Muje mana Shukra" Maryo ta kalli sashen matan Sarki Abdallah ta
nuna da ɗan yatsanta ta ce. "Nan zan shiga" Maleek yace. "Zaki je gaishe da Umma ne?"
Maryo ta girgiza kai ta ce. "A'a wani abun ɓoye nake san tonowa" da mamaki yace. "Abun ɓoye
kuma" bata kalleshi ba ta karkata akalarta zuwa sashen sannan ta ce. "Eh wanda ake cutar da

bayin Allah, alƙawari na ɗaukarwa kaina wannann karan duk wani azzulumi da ke cikin
daularmu dole ya gane kurensa." Har tayi gaba Maleek ya dafe kansa dan gabaɗaya ya rasa
gane kanta, a sanin da ya yiwa Shukra mace ce da bata da hatsaniya bare tashin hankali,
hasalima duk abin da zakayi mata na musgunawa sai dai ta zauna tayi ta kuka amma yau sai
gashi ita ce take bankaɗo da tashe-tashen hankula, yana nan yana tunani bai yi aune ba sai jin
ƙarar buɗe ƙofarta ya yi da sauri ya bita yana ƙoƙarin riƙe hannunta.

Hakimtacciyar matar sanye take da kayan alfarma, dukda kasancewarta mace ce mai cike da
izza, ƙarfin hali, dakiya, jarumta, alfahari da nuna isa uwa uba kissa da kisisina. Amma hakan
bai hana tashin hankalin da take ciki ya bayyana ƙarara akan fuskarta ba, Baiwar nisawa tayi ta
ƙara rissinawa hankali a tashe ta ce. "Wallahi na matuƙar kaɗuwa da yadda aka ce ta yiwa
Waziri nikam anya ba wani asirin ta dawo da shi ba? Ina laɓe fa na hangota ta haƙo abu a wani
rabi muna haɗa ido ta watsomini idanunta wallahi bakiji yadda gabana ya faɗi ba..." Maganarta
ce ta maƙale lokacin da suka ji shigar Maryo ɗakin ta bankaɗa labule, daga gurin da take ta
tsaya tana ƙare musu kallo. Baiwar ce ta miƙe sum sum sum tana cewa. "Na barki lafiya ranki
shi daɗe." Maryo wata uwar tsawa ta daka mata ta ce. "Wallahi idan kika fita ba tare da izinina
ba kin dinga tafiya kenan har abada." A dai-dai lokacin Maleek ya shigo yana cewa. "Shukra wai
me kike yi ne haka? Ki zo mu tafi mana" Fulani ba ƙaramin faɗuwar gaba ta shiga ba amma sai
ta dake ta ce. "Ke Shukra lafiya zaki shigo mini ɗaki babu ko sallama..." tun bata rufe baki ba
Maryo ta ɗaga mata hannu tana dakatar da ita cikin tsawa ta ce. "Baki cancanci sallama ba
tunda bakisan muhimmancinta ba, ki saurara mini ki kuma bani haɗin kan abin da na zo
aiwatarwa, idan kika bani haɗin kai zanyi ingama kuma inyanke hukuncin da naga dama
amma..." Maleek da sauri ya hankaɗa ta gefe yace. "Wai baki da hankali ne Umma Babba kike
gayawa haka?" Fuska babu alamun tsoro Maryo ta kalleshi ta ce. "Akan wannan abar kake
ɗaga mini murya? Ka iya bakinka ina raga maka ne saboda abu ɗaya wallahi kaci albarkacinta
amma ba dan haka ba da tuni labarin wani ake ba kai ba." Juyawa tayi ta kalli Fulani ta ce.
"Maza ki tono mini abin da kika binne yanzun nan?" Fulani rushewa tayi da kuka tana cewa.
"Maleek dama kawo matarka kayi dan ta ci mini mutumci ni zata laƙawa sharri ina zaune ƙalau."

Maryo a hassale ta juyo ta ɗauke Fulani da wani irin gigutaccen mari, ba Baiwarta ba hatta
Maleek sai da ya zaro ido cikin tashin hankali yana ganin haka yasa hannu itama ya ɗauketa da
wani irin gigitaccen mari yana huci yace. "Wannan ya zame miki na farko kuma na ƙarshe,
wannan da kike gani kamar Mahaifiyar da ta haifeni haka nake kallanta, wallahi idan kika kuma
aikata abin da kika yi yanzu zan baki mamaki, karki rainawa mutane hankali mana." Fulani daɗi
taji har cikin ranta sai ma ƙara keɓe baki tayi tana kuka, Maryo murmushi ta fara yi lokaci ɗaya
sukaji tana dariya harda ƙyaƙyatawa.

Kallan Maleek tayi tana nuna shi da yatsa fuska a turɓune ta ce. "Wannan shine marin da
zaka yi mini na farko na ƙarshe dan wallahi sai na hukunta ka." ta juya ta kalli Fulani Babba ta
ce. "Daga yanzu zaki san na shigo cikin gidan nan gado sai ɗan gado gararanba sai ɗan taka
haye, sai kin tabbatar da cewa ni ɗinnan dawowata daularmu bazai taɓa yi miki daɗi ba" tana
gama faɗa ta ƙarasa dai-dai tsakiyar ɗakin Fulani tana tsayawa a gurin ta tsugunna ta fara
bubbuga gurin nan take ƙasar gurin ta fara rozayewa tana fashewa, da ƙarfi ta fara ƙwaƙule

gurin tana zura hannunta tana ɗaukowa sai ga wani ƙaton abu a naɗe a cikin fatar bunsuru,
zazzagesu ta fara yi sai ga kayan Sarki Abdallah harda rawaninsa na faɗowa, daga gefe ɗaya
wata hallita suka gani ita ba mutum ba ita ba dabba ba, Fulani cikinta ne ya kaɗa hankalinta ya
tashi saboda ganin an tono abin da tafi shekara sama ashirin da biyar zuwa talatin da binne shi.
HAPPY WEEKEND🥰

_LITTAFIN NAN NA KUƊI NE DA NAIRA 200 ZAKI KARANTA SHI CIKIN KWANCIYAR
HANKALI, ZAKU BIYA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN, FIRST BANK 3090957579 AISHA ADAM,
ZA'A TURO DA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR,0706 206 2624, DAN GIRMAN ALLAH
IDAN KINSAN ZAKI FITARMUN DA LITTAFI NA YAFE CINIKINKI._ [16/11/2021, 13:32] Ameera Adam🌚: 29...


Tattaro Jarumta Sarki Aminullah ya yi sannan ya kalli Salman yace. "Lafiya Salman me kake yi
anan da daren nan?" Salman da idanunsa suka yi jawur ya furzar da iska mai zafi yana jefawa
Sarki Aminullah mugun kallo a daƙile yace. "Ba komai" yanayinsa ba ƙaramin tsorashi ya yi ba,
haɗiye yawu ya yi cikin ɗari-ɗari sannan yace. "To shikenan ka wuce sai da safe" Salman tsaye
ya yi kamar bai ji me Takawa yace ba, har ya ɗan fara takawa ya juyo yace. "Ranka shi daɗe
me yasa ka bada yarinyar cen suka tafi da ita alhalin ba ka tabbatar da cewar matarsa ce ko ba
matarsa bace?" Sarki Aminullah ba ƙaramin faɗuwar gaba ya shiga ba, tashi ya yi zaune yace.
"Saboda ita kanta yarinyar ta furta da bakinta kuma ga shaida nan mun gani" Salman ya wurga
masa idanunsa da sukayi jawur kamar gauta, Sarki Aminullah kasa ci gaba ya yi da kallan
ƙwayar idon Salman, Salman yaja gajeren tsaki sannan yace. "Wallahi ba matarsa bace dani
tafi dacewa dan haka duk abin da zai faru sai ya faru" yana gama faɗa ya fice daga cikin
turakar.

Abu ba ƙaramin jindaɗi yadda ake tarairayarta a sashen Fulani Zaliha taji ba, tun tana
ɗari-ɗari har ta sake ta fara harkokinta a cikin gidan, bata aikin fari bare na baƙi sai dai taci ta
sha ta kwanta. Sallah da abubuwan da suka zame mata dole su kaɗai take yi, kasancewar
Fulani Zaliha na matuƙar san ƴa mace kuma bata da ita yasa ta ɗauki so da kulawa ta ɗora
akan Abu wacce a yanzu suke kiranta da Zainab. Saif shi yake koya mata karatu addini dukda a
lokacin ba'a wani waye da makarantar boko ba, hakan yasa basu wani damu da ita ba. Tayi
matuƙar mamakin yadda Saif ya iya karatun alƙur'ani tiryen-tiryen tun da kowa yasan irin rashin
lafiyar da Saif ya yi, sosai take gane karatunsa saboda mutum ne me sauƙin kai. Sai da suka
fara wannan mu'amalar da shi ta fahimci yadda yake da saukin kai kamar ba Ɗan sarki ba,
gashi akwai barkwanci da iya magana. Abu ɗaya ta lura da shi daga cikin ɗabi'unsa ba yasan
raini ko kaɗan sai dai shi mutum ne ba me ruƙo ba kuma da kayi abu zai nuna maka
kuskurenka. A gefe ɗaya kuma idan ta kalleshi sai ta ga kamar ba shi ba musamman idan ta
tuna yadda yake yiwa ƴar uwarta sai ta ji babu daɗi, sai ta yi kamar zata yi masa maganarta sai
kuma tsoro da fargaba su ɗarsu a zuciyarta.

Maryo kallan Fulani Babba tayi ta saki wani malalacin murmushi ta ce. "Wannan abun ba ke

kika binne shi ba shekara talatin da suka wuce?" Fulani Babba ta zauna daɓar kamar wacce
aka zarewa laka sai kuma ta fashe da kuka ta ce. "Kai jama'a wai saboda a wulaƙantani a
tozartani shine za'a ƙirƙiro waɗannan abubuwan ina ji ina gani ace daga ɗakina suke, akan
idanun kowa kika aiwatar da siddabarun ki amma dan ni kaɗai kika tsana kice wai nina
binnesu." Baiwar Fulani Babba jikinta ne ya yi sanyi dan tasan sarai Fulani zata iya aikata abin
da ya fi wannan ma, amma kuma ya akayi Shukra tasan da wannan abubuwan to ko ta fara
tsafi ne kamar yadda tayi tsammani. Shi kansa Maleek ba ƙaramin mamaki ya yi ba amma
kuma ya akayi ita ta san da wannan abun, sannan kuma anya ba sharri take san ƙagawa Fulani
Babba ba tun da dama cen ba jituwa suke yi ba. Maryo ce ta yi wata ɗariya sannan ta ce. "Ni da
kika ganni bana ƙwai na sai da zakara ki gama matse-matsen hawayenki wannan kukan yanzu
kika fara, dan wallahi sai na bankaɗa sirrin ki na ɓoye kowa ya gane kalarki da ke da
munafukan cikin masarautar nan, kin ƙaryatani kin ce sharri na yi miki ko?" Fulani Babba tayi
zuru saboda tashin hankali cikinta ban da rugugi babu abin da yake yi. Kasa amsa tambayar da
Maryo tayi mata tai sai binta da take da kallo tana fargabar karta ƙara bankaɗo wani mugun
ƙullin da ta ɓoye shi. Maleek ya tamke fuska yace. "Shukra dan Allah kizo mu wuce banasan
waɗannan abubuwan da kike yi, wannan abun fa kamar kina neman tada hankalin masarauta
ne." Maryo itama tamke fuska tayi tasa farin ƙyalle data wanke shi bai gama bushewa ta goge
jinin da ya ɗigo daga hancinta ta ce. "Ai dama babban burina kenan in tayar da hankalin
Masarauta a fahimci bambamcin ina nan da bana nan, ka bar wahalar da bakinka dan duk faɗin
masarautar nan mutum biyu ne zasu iya dakatar dani daga aikata abin da nayi niyya." tana
gama faɗa ta wuce ta wajen damɓasheshiyar kujerar da Fulani Babba take zaune, ƙirjin Fulani
ne ya shiga bugawa ba ƙaƙƙautawa saboda fargabar abinda zata zaluƙo. Da sauri Maryo ta sa
hannu ta riƙo hannun Fulani ta ɗaga ta daga kan kujerar, ganin haka yasa Maleek takawa
zuwan gurin da niyyar janye ta, tana juyowa ta ce. "Hurmin ga ajiya na baku" Maleek duk yadda
yaso ɗaga ƙafarsa ya ƙarasa gurin kasawa ya yi, Maryo ƙafa ɗaya tasa ta ture kujerar wata
ƙwarangwal ɗin mage suka gani a tsugunne da alama da ranta aka ajiye ta agurin har ta mutu
ta bushe a haka, Fulani Babba shiru tayi gumi na keto mata sai a lokacin Maryo ta kalli Maleek
ta ce."Ku sake shi" Fulani da Baiwarta juyawa suka yi dan su dai basu ga kowa ba, amma sun
tabbata bokan da ya bata sa'a to da makarai take aiki. Maleek ƙarasawa ya yi gurin ya ga
busasshiyar magen nan, Maryo ta kalleshi ta ce. "Ganin buzu a masallaci ya isa tinkiya tayi
karatun ta nutsu, idan wannan kawai bai hankaltar da ku ba akwai wasu ƙullin a gaba amma
wannan da kanta zata kunce su, idan kuma tayi gaddama sai na tara mutanen garin nan
sannan na kunce su da kaina." Ta juya tana kallan Fulani da gumi ya gama wanke mata fuska
ta ce. "Na baki wunin yau ko ki samu Sarki Abdallah ki sanar da shi da iyalansa abin da kika
aikata musu ko kuma na fallasaki da kaina hatta da mutuwar Mai babban Ɗaki" A firgice Fulani
Babba ta ɗago tana kallan Maryo, Maryo tai mata murmushi ta ce. "Kina mamaki ne? Ai ni
ginshiƙin dutse nake kowa yayi karo dani shi zai faɗi. Idan kin aiwatar da abin da na umarce ki
akwai wani a gaba dan kinsan ƙullin naki da yawa." Maryo na gama faɗa ta wuce fuuuuu kamar
zata tashi sama. Tana tafe Maleek na bin ta a baya kamar jela duk inda suka wuce sai dai kaga
ana binsu da kallo, dan ma ba ƙaramin tsoron Maleek suke ji ba hakan yasa suna ganinsa kowa
zai ci gaba da aikin da yake yi, sai sun wuce kaji ƙananan maganganu na tashi.

Suna shiga sashen su Maryo ta shige ɗaki ta datse kofar duk yadda yaso ta buɗe haka ya

ƙaraci tsaiwarsa ya bar gurin har sai da Bayin gurin suka fara fahimtar halin da suke ciki. Yana
nan tsaye saƙo ya iso masa daga fadar Mai martaba, jiki a sanyaye ya wuce fadar dan yasan
ba akan komai za'ayi masa wannan neman na gaggawa ba sai akan matarsa. Yana zuwa ya yi
sallama cikin fadar ya shiga ya zaune daga cen gefen Sarki Abdallah, Maleek yace. "Allah ya
taimakeka ance kana nema na" Sarki Abdallah ya numfasa yace. "Maleek mun aika kiranka ne
ba dan komai ba sai dan muna ganin kamar akwai matsala tattare da iyalinka." Galadima da ke
gefe ya gyaɗa kai, Maleek ya russuna yace. "Haka ne Ranka shi daɗe nima na fahimci haka,
saboda na ga canje-caje daga yanayin mu'amalarmu da ita." Sarki Abdallah ya jinjina kai yace.
"Dan haka ya zama wajibi a nema mata magani saboda gudun abin da kaje yazo, yanzu kana
gani da ba'a kusa me kake tunani zai faru da Waziri" Maleek ya kai kallonsa ga Waziri da har
lokacin da alama bai gama dawowa dai-dai ba. Maleek yace. "Insha Allah za'ayi yadda kace"
Sarki Abdallah ya kuma gyara zama yace. "Abu na gaba da nake so da kai, ka yi bakin
ƙoƙarinka wajen ganin ka hanata fitowa waje har sai ta samu lafiya." Maleek ya gyaɗa kai ya
russuna cikin girmamawa yace. "Insha Allah ranka shi daɗe" daga haka Sarki Abdallah ya
sallami Maleek sannan suka ci gaba da tattaunawa. Galadima ne ya kalli Takawa yace. "Allah
ya taimake ka nifa lamarin yarinyar nan ina ganin kamar harda makarai" Waziri da ke gefe yace.
"Wallahi babu wani makarai nina fi zargin aikota akayi kawai ta halakani" Sarki Abdallah yace.
"Waziri bana tunanin wani zai turo Shukra ta kashe ka, saboda idan ta kashe ka ribar me zata
samu tunda ita ba kowa gareta ba, nafi aminta da maganar Galadima saboda ga dukkan
alamau akwai shafar jinnu a jikinta." Waziri da yake ganin kamar sun take gaskiya ne ya rufe
baki cikin takaici. Sarki Abdallah ya kalli Galadima yace. "Galadima a nemo masu magunguna
saboda a tari matsalar da wuri kar matsalar ta nemi gagarar kundila." Galadima ya amsa
sannan suka ci gaba da tattaunawa


Bayan kwana biyu zaman Maryo da Maleek ba wata matsala sai dai babu mai kula wani a
tsakaninsu daga gaisuwa sai gaisuwa abin da yake haɗa su kenan, Fulani da farko ta so ta
samu Sarki Abdallah da maganar amma da ta yi wani tunani sai ta barshi dan ra'ayin kanta
saboda wani shiri da take ƙullawa. Da safiyar ranar Laraba Maleek ya tafi da Maryo ɗakin baya
da aka tanada saboda masu magani anan zasu dinga dubata, suna zuwa Maryo ta nemi guri ta
zauna tana ƙarewa Mai ganin kallo. Wani ɗan busasshen saurayi ne yana maƙale da jakarsa fa
maganjɓi, zama ya yi ya fara ciro da kayan aikinsa. Daga cikin jakar yaga hayaƙi na fitowa
lokaci ɗaya suka ga wuta ta kama Jakar, tana ƙoƙarin lasar Mai maganin. Maleek baya ya ja
cikin ta'ajibi Maryo kallan Mai maganin ta yi ta ce. "Idan na kuma ganinka ƙafarka a gurin nan ba
jakarka ba hatta kai kanka sai na ƙone ka." tun bata gama faɗa ba Mai maganin ya fice a guje
ko waiwaye baya yi.

Sannu a hankali shaƙuwa ta fara shiga tsakin Abu da Saif dan bashi da abokiyar hira sama da
Abu, itama kuma haka yanzu hatta shan iska idan zai fita sai ya nemi rakiyar Abu suna tafe
suna hira har suje gurin da zasu je. Kamar kullin yauma Abu ce ta shirya cikin kayanta masu
kyau, Fulani Zaliha ce ta bata kuɗin kayan kwalliya su jagira da gazal harda kuɗin kallabi
saboda na Abu sun ɗan yi ƙaranci. Har ta fito tsakar gida Saif ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
google.com, pub-9213700357025247, DIRECT, f08c47fec0942fa0