Showing 57001 words to 57967 words out of 57967 words
Maleek ɗan
wajen Fulani Fahima da suka koma Adamawa?" Abu da sauri ta gyaɗa kai ta ci gaba da cewa,
"Ni tsoro ma nake ji wallahi karta faɗa wani wurin, dan nasan kafiyar Maryo bazata taɓa
dawowa gidan nan dan ra'ayin kanta ba, na tsaya zan nemo ta Yaya Saif ya janyo ni muka
dawo wataƙila da na gano ta" Fulani Zaliha ta sauke ajiyar zuciya ta ce, "To Takawa yasan ba
matarsa bace kuma ya barsu suka tafi da ita, wanne irin lamari ne wannan kamar ba a ƙasar
musulmai ba" Cikin Abu ne ya kaɗa sai a lokacin ta lura da irin sakin bakin da tayi, tsoro ne ya
kamata musamman da taji Fulani Zaliha ta fara faɗa tana cewa zata samu Takawa da maganar,
a tsure Abu ta kalli Fulani Zaliha ta ce, "Allah ya taimake ki dan Allah karki cewa Takawa a
bakina kika ji, ina jin tsoron hukuncin da zai yi mini. Amma wallahi ko Inna ta zaki kira ki
tambaya zata gaya miki Maryo ba matarsa bace, ko aure ma ba'a taɓa yi mata ba" Jikin Fulani
Zaliha sanyi ya yi haɗe da tausayinta, cikin zuciyarta take faɗin, "Wai Mai martaba me yake so
ya zama ne, bayan rashin adalcin da yake nunawa har kuma da shiga haƙƙin aure da
musulunci. Anya ya cancanci ci gaba da mulkar dubbanin al'umma da.." Abu ce ta katse mata
tunani da cewa, "Dan Allah Ranki shi daɗe ki..." Ƙaƙalo murmushi Fulani Zaliha ta yi ta katse ta
da cewa, "Karki damu Zainab babu abin da zai faru bazan sanar masa ba, kawai ina mamakin
yadda lamarin ya kasance. Kiyi ta yi mata addu'a in sha Allah babu abin da zai faru da ita sai
alheri." Abu ta amsa da, "Ameen" Fulani Zaliha sallame ta sannan ta faɗa duniyar tunani da cin
alwashin dole ta tunkari Sarki Aminullah da wannan maganar.
Yamutse fuska take kamar wacce tayi ta ci kashi, duk wanda ya kalli fuskar Jakadiya zai
tabbatar tana cikin matsananciyar damuwa. Tana gabda shiga sashen Fulani Maryama suka yi
karo da wata baiwa, da sauri ta dafe goshi tana zabga ruwan masifa, "Kai waɗannan yara dai tir
da halinku jarababbu kuna tafe da kawuna a sama kamar raƙuma." Dije da take mulmula goshi
ta ce, "Allah ya baki haƙuri Jakadiya ban san kin taho ba" A zafafe Jakadiya ta ce, "Ina zaki
sane kina fama da ido yana karuwar akuya, wacce uwar kika ƙunso kike sauri kamar sabon
kwarto" Ƙunshe dariyarta Dije tayi dan sun lura kwana biyu Jakadiya acikin masifa take, tana
shirin bata amsa Jakadiya ta ce, "Ba magana nake yi miki ba Dije? Idan Uwarki Laraba ce zaki
yi banza da ita" Dije ta tsuke fuska ta ce, "Ke dai wayon zagi ne kawai ban da haka me na yi
miki da zaki zageni, yanzu ka rama cibi ya zama ƙari, ƙari ya zama ƙababa. Haka kawai
tsohuwa sai jaraba" tana gama faɗa ta bi ta gefen Jakadiya fuuuu ta wuce. Baki a sake
Jakadiya ta bi ta da kallo tana tafa hannu ta ce, "Biri ya yi kama da mutum. Wallahi ba banza ba
wannan yarinyar sai mun binkiceta dan naji har wari-warin maza take, ban da haka har ni zata
gayawa haka bari na shiga na fito dole mu zauna da Laraba mu lalube ta tass." tana gama faɗa
ta shige ciki. Zaune ta samu Fulani Maryama da alama itama tana cikin damuwa, bayan sun
gaisa Jakadiya ta saluɓe ɗankwalin kanta ta ce, "Maryama anya Marduska ba aljabu yake
turowa suna kankarar naman kaina ba, dubi ki ga wani ɓamɓori kullin ta Allah idan na cire
ɗankwalina sai na karkaɗe wannan farin garin, ina gudin a wayi gari aga kaina ya marmashe
tass" Jakadiya ta faɗa cikin damuwa. Fulani Maryama bata tanka mata ba itama ta fisge
ɗankwalin kanta sai ga wani irin farin gari na marmashewa. Jakadiya dafe ƙirji tayi ta ce,
"Maryama! Yoo ai nawa shafar mai ne a haka kike zuwa shimfiɗar takawa gari na zuba? Wai ma
kuwa ya kuka ƙare da takawa nasan dai har yanzu ba'a ce bai shafo hallitar kanki ya ji yadda
kanki ya koma ba"
Juye-juye yake ga gumi yana tsattsafo masa ta ko'ina, firgigit ya farga daga mummunan
Mafarkin da yake yi bakinsa ɗauke da Addu'a. Kallanta ya yi har yanzu bacci take miƙewa ya yi
jiki ba kuzari ya faɗa banɗaki ya ɗauro alawa zai wuce masallaci, har yaje bakin ƙofa ya dawo
ya fara bubbuga fulonta yana tashinta, ganin bata tashi ba har zai iya rasa jam'i yasa ya fice da
niyyar idan ya dawo ya tashe ta. Fitarsa harabar gidan ya hangi taron jama'a zagaye a wurin
kamar zai wuce sai ya hangi Ƙaninsa Sulaiman, yafito shi ya yi da hannun alamun yazo nan
take ya ƙaraso wurinsa. Maleek ya tambayashi, "Me yake faruwa ne naga mutane da yawa.?"
Mamakin fuskar Sulaiman ne ya ƙaru, ya juya yana nuna masa wurin sannan yace, "Yaya Me
babban ɗaki aka gani zaune a wurin" Wani kallo Maleek ya wurga masa yace, "Baka da hankali,
shirmen naku har kan Mai babban ɗaki shekarar baiwar Allahr nawa ta rasuwa ina jin tun baka
da wayo ta rasu ka ce mana ita ka gani a zaune, ya akayi ka santa?" Sulaiman yace, "Wallahi
da gaske haka naji su Baba Ciroma suna faɗa..." Maleek bai gama jin maganar Sulaiman ba ya
hango Mahaifinsa da wata tawaga sun nufi hanyar da mutane ke tsaitsaye.
Ina muku fatan alherií ¾íµ° Mu haɗe a commentsí ¾í´¾í ¼í¿»♀️
LITTAFIN NAN NA KUƊI NE DA NAIRA 200 ZAKI KI ACOUNT ƊIN, FIRST BANK 3090957579
AISHA ADAM, ZA'A TURO DA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR,0706 206 2624, DAN
GIRMAN ALLAH IDAN KINSAN ZAKI FITARMUN DA LITTAFI NA YAFE CINIKINKI._