Showing 48001 words to 51000 words out of 57967 words
cikinta, faɗuwarta jinta ya yi har cikin jikinsa saindai babu yadda ya iya, hannunsa
ya ɗora akan cikinta yace. "Ina fatan babu abin da ya shafi abin da yake cikinki" gyaɗa masa kai
tayi tana sauke ajiyar zuciya. Ɗaukanta ya yi cak yace, "Rufe idonki" tun bai ƙarasa faɗa ba ta
rufe saboda tasan gida zai mayar da ita.
Tsaye yake da ita a cikin bukkar da babu komi a cikin sai gadon tabarmar kara da buzun
damusa a shimfeɗe, kwantar da ita ya yi ta buɗe idonta, ya kai bakinsa ya sumbaci goshinta
yace ina tare da kai babu abin da zasu iya yi miki da ke da abim da yake cikinki" murmushi ta yi
tana gyaɗa kai motsi suka ji daga baya, nan take Yace. "Ina zuwa." Yana gama faɗa ya zama
gizagizo ya bi ta jikin bango ya koma cikin ragar da ta kasance mazauninsa, Kaka ne ya shigo
ƙugunsa ɗauke da tafka-tafkan ganye waɗanda suka zame masa kamar makari ne na rufe
al'aurarsa.
Tsaye ya yi akanta yana ƙare mata kallo duk sai ya ji yanayinsa babu daɗi, dan gani yake duk
wani abu da zai faru da ita kamar shine silar komai. Tsugunnawa ya yi yana kallon busassun
hawayen idonta, a hankali ya fara yi mata magana cikin tausasawa, "Kyauta! Kiyi haƙuri" juyowa
tayi idanunta na cikowa da ƙwalla bata tanka masa ba, ya russunar da kai ƙasa kamar me
nazari ya ci gaba da cewa, har gobe bazan daina ganin kaina a matsayin mai laifi ba saboda ta
silata ce kika faɗa cikin wannan halin da kika tsinci kanki, ka yafe mini dan na tabbata haƙƙinki
bazai taɓa barina ba matasawar baki yafe mini ba" ɗagowa tayi tana kallonsa murya na rawa ta
tashi zaune ta ce, "Kaka dan Allah ka daina faɗin haka kana sa ina jin babu daɗi a zuciyata. Na
tabbata kayi haka ne ba dan komai ba sai dan ka sama mini gurbin da zan fi samun kwanciyar
hankali, kasan duk duniya bani da kowa bayan kai. Kaine kaci kashi da fitsarina tun da ni da kai
na saba bansan iyayena ba da kai na buɗi ido, na tabbata bazaka taba zaɓa mini abin da zai
cutar da ni ba." Hawaye ya fara saboda ba ƙaramin daɗi yaji ba yadda Allah ya dasa mata
tausayinta a zuciya, katse tunaninsa ta yi da cewar, "Kowanne abu da zai faru da bawa na
tabbata yana daga cikin ƙaddararsa, ni wannan ita ce tawa ƙaddarar, ni kaina ina shiga cikin
ɗimuwa da tashin hankali idan na tuna halin da jinina zai fuskanta idan babu ni" Tana zuwa nan
a zancenta hawaye ya ci gaba da tsiyaya daga idanunta, Kaka shima hawayen yake cikin
tausayawa a zuciyarsa yake jin inama a ce haka bata faru ba, me yasa ko kaɗam bai yi hangen
abin da zai faru a gaba ba. Me yasa bai bari ta kai munzalin da zai yi shawara da ita ba?
Waɗannan tambayoyin yake jerawa cikin zuciyarsa yana jin nadama da dana sani, kamar tasan
abin da yake zuciyarsa ta ce, "Kaka banasan ka dinga jerawa zuciyarka tambayoyin da zasu
saka cikin ɗimuwa da tashin hankali, Ka sani duk duniya bani da kowa sai kai" ta ɗan shiru tana
jin zuciyarta na ƙara raunata sannan ta ci gaba da cewa, "Sai kuma Mirdad, ku kaɗai nake kalla
naji daɗi, idan kuma wani abu ya faru da kai ya kake so nayi?" Goge hawayen idanunsa ya yi
yace, "Na miki alƙawarin haka baza ta taɓa faruwa ba amma kema sai kin cire damuwar dake
zuciyarki, kinsan fa ba ki kaɗai bace ko kina so ki jawa Jaririn da ke cikinki matsala, kina so ki
haifo yarona yana tagumi?" murmushi tayi ta girgiza masa kai sannnan ya miƙe yace, "Amma
ɗazu naga kamar bakya nan ina kika je" Ɗan duburburcewa ta yi ta ce, "Naje gurin Mirdad" ɗan
canja fuska ya yi cikin damuwa yace, "Ki dinga hankali fa ina gudun kar su cutar da ke" Gyaɗa
masa kai ta yi sannan ya fice daga cikin bukkar ya nufi bakin wutar da take ci kamar a maƙera.
Zaune ya yi a bakin wutar ya ƙura mata ido yana kallo yana tunanin rayuwarsa ta baya da
tushen mafarin shigar jikarsa cikin wannan matsala.
ASALIN LABARIN KYAUTA
Damina shine ainihin cikakken sunan Kaka asalinsa Maguzawa ne yana da Mata Dela
dukkanninsu haifaffun garin Kano ne, iyayensu su Fatake ne wanda bincike bai tabbatar da
asalin garin da suka fito ba, Mahaifin Damina dana Dele abokaine dan haka suka haɗa su aure.
Damina ya taso da wata baiwa tun ranar da mahaifiyarsa ta fahimci tana ɗauke da cikinsa, a
ranar da ta fahimci haka a ranar Bayan Mahaifinsa ya fita farauta Allah ya bashi nasara ya
farauto wani ƙasurgumin Zaki wanda ya samu nasarar halakashi tun kafin ya kawo shi gida. Tun
daga wannan ranar sai abubuwaa nasara ya dinga samunsa wanda basu taɓa tsammani ba,
daga wannan lokacin sai suka fahimci Duk tinkiyar da shigo sashen Dela sai to babu jimawa
zata samu ciki, kuma idan ta tashi haihuwa sai dai ta haifi ƴaƴa uku, huɗu har akwai wacce ta
haifi ƴaƴa biyar. Lokaci ɗaya zance ya ƙaraɗe cikin ƙauyen Goron dutse cewar Dela na ɗauke
da cikin Ɗan baiwa, tun daga wannan lokacin aka ɗinga ririta Dela hatta aikin gida bata yi akwai
masu zuwa su yi mata, wannan magana ba iya nan kaɗai ta tsaya ba har sai da je kunnen
Sarkin lokacin wato Sarkin Kano Rabo Juma Dogon gida, ba ƙaramin murna suka yi ba saboda
a ganinsu sun samu Ɗan baiwa dan haka wasu al'amuran nasu zai zo da sauƙi. Akwana a tashi
har Allah ya sauki Dela lafiya ranar da ta haifeshi kuwa aka wuni aka kwana ana tafka ruwan
sama kamar da bakin ƙwarya, dan a wannan lokacin tun da damina ta kama ba'a taɓa tafka
ruwa mai yawa kamar na ranar ba, hakan ne yasa suka saka masa suna Damina, kuma tun da
aka haifeshi yaƙi kama Mama duk yadda aka bashi ƙi ya yi, dan a lokacin har Nonon akuya
dana Saniya aka taso aka bashi amma yaƙi karɓa, sai ruwa suke bashi haka ya ci gaba da
rayuwa.Damina yana girma harkokin baiwarsa na ƙara bunƙasa har ya kai shekara goma sha
takwas, tun daga wannan lokacin yan garin suka mayar da shi wani babban jigo daga
rayuwarsu, dan a lokacin ba dan sun bada ƙarfi wajen bautar Rana ba wasu daga cikinsu da
tuni sun fara bautawa Damina, lokacin da ya kai shekara goma sha takwas dai-dai Aljanu suka
faa buɗe masa ido, har suna taimaka masa wajen bayar da magunguna da warkar da marasa
lafiya. Hakan ne yasa ya fara killace kansa a wata bukka da Mahaifinsa ya tanadar masa,
wacce a cikinta ne ake kai masa ziyara yake bada magunguna, tun tana bayar da magani har
mata suka fara kawo masa tayin buƙatarsu dangane da kishiyoyinsu, sannu a hankali Damina
ya rukiɗe ya koma Boka dan duk abin da kake buƙata kana zuwa gurinsa zai sanar da kai abin
da yake tafe da kai, kuma bazaka bar gurin ba sai da biyan buƙatarka. Ana cikin haka wata
mata tazo da ƴarta nemar mata maganin farin jini tun da Damina ya ƙyalla ido yaji ta kwanta
masa, wani garin magani ya basu akan tayi wanka da shi tun daga ranar yarinyar me suna
Laraba ta kamu da mutuwar sansa, lokacin da iyayenta suka fahimci haka sai suka shiga
ɗimuwa saboda a tunaninsu ta ɗauko Dala ba gamo, amma wani abun mamaki ana tararsa da
maganar sai ya yi na'am da ita. Ba'a ɗauki lokaci me tsayi ba aka sha bikinsu Laraba ta tare a
gidan iyayen Damina, bayan wani lokacin Laraba ta haihu ta haifi Ɗanta kyakkyawa namiji
wanda suka saka masa suna Nomau, haka rayuwa ta ci gaba da tafiya Damina babu wurin da
labarinsa bai karaɗe ba, ba iya garin kano ba har sassan garuruwan da ke makwabtaka da
garin na Kano sun san da zaman Damina. Shekara Nomau goma a duniya iyayen Damina suka
rasu tare da wasu daga cikin mutanen dake kusa da su sakamakon ambaliyar ruwan da ta
same su.
Haka rayuwa ta ci gaba da tafiya har Nomau ya cika shekara Ashirin da biyar cif a lokacin girma
ya fara kama, Damina kuma a wanann lokacin aka yi wa Nomau aure da matarsa Tani, bayan
bikin Nomau da Tani babu jimawa Damina ya nemi alfarma gurun abokinsa Ɗan sarkin fararen
Aljanun ƙarƙashin ƙasa, sai da Aljanin ya gama jin buƙatar Damina sannan yace. "Buƙatarka da
ci gaban baiwarka ga sauran zuri'arka zata cika matsawar ka yarjewa tawa buƙatar, nikuma na
yi maka alƙawarin wannan taimako da muke yi maka kana bada magunguna zamu ci gaba da
buɗewa zuri'arka haska tun daga kan Ɗanka Nomau har zuwa ƙarshen zuri'arka, amma da
sharaɗin zaka bawa Ɗana auren abin da yake cikin sirikarta Tani."
BARKA DA JUMA'Aí ¾í´¹í ¼í¿»♀️
_LITTAFIN NAN NA KUƊI NE DA NAIRA 200 ZAKI KARANTA SHI CIKIN KWANCIYAR
HANKALI, ZAKU BIYA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN, FIRST BANK 3090957579 AISHA ADAM,
ZA'A TURO DA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR,0706 206 2624, DAN GIRMAN ALLAH
IDAN KINSAN ZAKI FITARMUN DA LITTAFI NA YAFE CINIKINKI._
[21/11/2021, 16:24] Ameera Adamí ¼í¼š: 32...
Ban yi dogon tunani da nazarin abin da gaba zata haifar ba na amince da buƙatar Aljani
Mardidas, ba ƙaramin daɗi Aljanin ya ji ba kuma tun daga ranar duk lokacin da zai ziyarce ni
tare yake zuwa da Ɗansa me kimamin shekara goma a duniya wanda na yiwa alƙawarin jika ta,
ni duk a tunanina hakan da na yi ne zai sa baiwar da nake da ita ta karkasu har zuwa kan
zuri'ata ta ƙarshe, Sai dai wayo da dabarata sam basu tasirantu da abin da nayi tsammani ba,
saboda lokacin da cikin Kyauta ya kai wata bakwai a lokacin ne Nomau ya kwanta wata
gajeriyar jinya kuma be daɗe a kwance ba rai ya yi halinsa. A lokacin hankalina ba ƙaramin
tashi ya yi ba saboda duk duniya Nomau kaɗai na mallaka a matsayin ɗana, ga shi sannu a
hankali girma ya fara kamani. Fargaba ta ɗaya kada na tsufa na rasa madafar dafawa wannan
hali da nake ciki yasa na nemi agajin abokina wato Mirdidas, lokacin da yaji bayanina ya
tausaya mini matuƙa saboda duk kusan matsalarmu ɗaya da shi, shima Ɗansa ɗaya a duniya
hakan ce ta sa ya kawo mini wata shawara wanda a lokaci nayi kasaƙe ina sauraronsa cikin
yarensu na jinsin Jinnu, kasancewar idan na juya baki muna magana da shi sai ka rantse nima
na fito daga cikin tsatsonsu ne.
"Shawarar da nake ganin zata kawo maka mafita ba wata ce Damina illa ka tara mutanen garin
nan tun da suna ɗaukar zancen fiye da tsammani, ka ce musu kayi harsashen za'a dinga
samun hasara duk shekara dan haka bayan kowa ya yi noma, duk mutum ɗaya zai sauke maka
buhun gero ɗaya, masara, da dawa ɗaya. Sannan ga waɗanda basa noma sai ka gindayawa
muku su dinga kawo maka kayan sarrafawa, suma daga cikin ka zaɓi wani aiki da zasu dinga
gudanar maka na ka,matarka da sirikarka. Sai dai ka gargaɗesu da cewar wannan kaya da
zasu kawo maka zaka ajiye ne mu mutanenka mu dinga ɗauka saboda rabonmu ne, ga
tabbatar musu da cewar ga duk wanda ya kuskurewa haka to tabbas annobar zata faɗa kansa.
Haka zaka yi dan ka samu rayuwarka ta inganta cikin sauƙi, kuma ni nan zan taimaka maka
akan duk mutumin da ya bijirewa umarninka." Ba ƙaramin jin daɗin jawabinsa na yi ba saboda
ko kaɗan wannan dabarar bata zo mini ba, godiya nayi masa sannan muka yi sallama. Kamar
yadda muka yi da Mirdidas haka na tara jama'ar gari na yi musu bayani dalla-dalla kamar gaske
kuma duk cikinsu babu wanda ya misa mini, dan dama ko kaɗan ban kawo akwai wanda zai
bijiremini ba duba da komai na faɗa musu yana faruwa kuma ina iya basu maganin warkar
abun. Tun daga wannan lokacin abinci dai sai dai na bawa wani, dan abinci na wata shekara
har tarar da na shekara baya yake yi, wannan shawara yasa na ƙara riƙe amini na hannu
bibbiyu kuma amintakarmu ta ci gaba da tafiya lafiya kalau.
Ranar Juma'a aka haifi kyauta kuma a ranar ne aka yiwa Abokina Mardidas naɗin sarauta
dan haka murnar ta haɗe mana, an naɗa sa a matsayin Sarkin fararen alijun ƙarƙashin ƙasa,
wato kujerar mulkin da mahaifinsa ya yi murabus ya bar masa. Wannan dalili yasa ya nemi
alfarmar saka mata suna Kyauta saɓanin Jummai da muka yi niyyar saka mata. Haka yarinya ta
taso gwanin birgewa da ban sha'awa kuma tun da aka haifeta koyaushe Mirdad na tare da ita,
shi yake yi mata wasa da duk wasu abubuwan ɗebe kewa shi yake mata, har ɗaukanta yake
yana kaita cen duniyarsu domin ta saba da yanayinsu tun da alƙawarine cewar matarsa ce
halak malak, Shiyasa ko da Kyauta ta fara wayo bata damuwa idan ya tafi ita dan sai ta shafe
kwana biyu har zuwa uku a gurinsu, sai dai su ajiyewa Uwarta me siffarta a zuwan ita ce,
Shekarar Kyauta bakwai annobar amai da gudawa ta sauka a nahiyarmu hatta ni bata kyale ba,
dan ba ƙaramar wahala na sha ba. Ta wannan sanadin ne akayi asarar rayuka masu yawa ciki
harda Mahaifiyar Kyauta da me ɗakina, wannan mutuwar ba ƙaramin taɓani ta yi ba dan ba
ƙaramin so da ƙyauna nake yi wa Laraba ba, babu yadda muka iya haka muka haƙura.
Kyauta ta taso cikin gata da kulawa gaba da baya duk da kasancewarta marainiya amma tafi
dubbanin masu iyaye gata, shekararta goma sha biyar aka sha bikinta da Mirdad. Sai dai dama
tun kafin bikin take mini ƙorafin ƴan uwansa basa ƙaunarta, dan har akwai masu iƙirarin zasu
kasheta, danma Mahaifin Mirdad wato Mardidas na tsaye tsayin daka yasa suke shakkun aikata
mata wani abun, sai gori, tsangwama da wulaƙanci ba wanda bata sha. Dalilinsu na yin haka
wai dan ta kasance jinsin bil'adam ce, kuma suna ganin irin fifikon da Mardidis yake yi akanta
fiye da ƴaƴansu, saboda ba ƙaramin ƙaunarta yake yi ba sakamakon tsananin san da ɗansa
yake yi mata. Kuma babban damuwarma so suke Mirdad ya auri ɗaya daga cikin ƴaƴansu
saboda jikansu samu damar ɗane karagar mulkin da kowa yake fatan ace jininsa ne akai, da
farko bansan da wannan matsalolin ba har sai da fa fara zama a cikinsu take sanar dani halin
da ake ciki. Abokina Mardidas na samu da maganar cikin jin kunyata ya bani haƙuri tare da
nuna mini kawo ƙarshen matsalar cikin kwanaki ƙalilan, haka na kawo ido na sa amma ƙasan
zuciyata babu daɗi duba da yanayin waɗanda take rayuwa da su amma babu abin da zan iya
dan na lura a duk duniya idan aka cire ni babu wanda Kyauta take ƙauna kamar Mirdad.
Mardidas ne ya tayarwa da ƴan uwansa da suke Uba ɗaya bore saboda dama shi kaɗai
mahaifiyarsa ta haifa, ganin haka ya sa suka shirya masa zagon ƙasa da ƙulle-ƙullen makirci
har ya kwanta wata irin jinya da ni kaina na kasa gano irinta, wannan dalili yasa shima ya yi
murabus ya barwa Ɗansa Mirdad karagar mulkinsa wato mijin Kyauta, kuma anyi haka babu
jimawa Kakan Mirdad mahaifin Mardidas ya mutu. Wannan ya ƙara wutar ƙiyayyarsu a zuciyar
Kyauta dan dole ba dan ta so ba yasa ta haƙura da zaman cikin jinsun su saboda lamarin ya yi
tsanani, sai dai wani abun ɗaure kai da ban mamaki kuma abin farinciki a gurina bayan na
fahimci Kyauta na ɗauke da juna biyu, duk lokacin da wani daga cikinsu yayi niyyar cutar da ita,
ko da bai aiwatar ba wannan abin da ya yi niyyar yi mata shi ba kuma sai abin ya faru da shi,
wannan ne ya ɗan rage mini damuwa saboda na rage fargabar ko zasu cutar da ita, a gefe
ɗaya kuma nake ƙara godewa Abokina Mardidas dan buƙatata ta biya tun da gashi jikata tana
ɗauke da cikin ɗan baiwa kamar ni. Dalilin dawowarta gida gurina kuwa dan ta samu nutsuwa
ne a matsayin da na me juna biyu, saboda ko da babu wani abu da zasu yi mata ya kamata ta
samu hutu daga tarin baƙin cikin da suke ƙunsa mata. Daga ɓangaren abokina Mardidas tun ina
samu na kai ziyara duba shi muna samu muyi magana da shi har ta kai ga ƴan uwansa na yi
mini baraza da rayuwa ta, kuma a wannan lokacin hatta Ɗansa na cikinsa baya iya ganewa
saboda zafin ciwo, wani abin farinciki da ko tunowa nayi da mutuwa ta bana jin fargaba yadda
Mirdad yake tsananin ƙaunar Kyauta da bata kulawa nasan bana numfashi zai riƙe mini ita
amana, tun da dai a duk duniya Kyauta bata da kowa sai ni sai kuma Mirdad, a gefe ɗaya kuma
hankalina na matuƙar tashi idan na tuna kar ƴan uwan mahaifinsa su cutar da Mirdad kamar
yadda suka cutar da Mahaifinsa, idan babu Mirdad babu niwace rayuwa Kyauta zata yi ita da
abin da yake cikinta?"
Amsar da Kaka ya kasa bawa kansa kenan sai ƙwallar dake tsiyaya daga idanunsa, wasu
ƙarare ya ɗiba ya ƙara watsawa cikin wutar sannan ya miƙe a hankali yana takawa har ya koma
cikin wata bukka dake kallon wacce kyauta take ciki.
Bayan kwana biyu da faruwar wannan nazarin na Kaka ya fara wata irin rashin lafiya, a
lokacin Hankalin kyauta ba ƙaramin tashi ya yi ba saboda tun da take bata taɓa ganin Kaka
cikin wannan halin ba, ban da kuka babu abin da take yi. Danma Mardid na bata kulawa da
yana ƙara kwantar mata da hankali akan damuwar da take ciki. Wata rana tana zaune a gefe
Kaka yana fitar