Showing 51001 words to 54000 words out of 57967 words

Chapter 18 - Anya Baiwa Ce 1 Complete Hausa Novels

da numfashi da kyar gefe ɗaya Mardid ne yake kallansu cikin tausayawa, miƙa
hannu ya yayi da sauri Kyauta ta miƙa hannuta cikin tafin nasa hannun. Miƙawa Mirdad ɗayan
hannu ya yi shima ya miƙa masa nashi hannun, haɗa hannun Kyauta da na Mirdad ya yi yana
runtse idonsa ya fara magana cikin ƙarfin hali, "Mirdad ga amanar Kyauta nan nikam tawa ta zo
ƙarshe, ka kula min da ita amana da ita da abin da zaku haifa nan gaba, nasan da yadda ƴan
uwanka suka ɗauki Kyauta sai dai nasan haɗuwarka da ita akwai wani ɓoyayyen al'amari,
amma a kowanne hali kuke ka taimaka ka riƙe amanar dana baka, sannan ka isar yi mini da
saƙo ga mahaifinka koda baya magana amma zai ji wannan wasiyyar da zan baka." wata sarƙa
Kaka ya ciro daga wuyansa ya damƙawa Mirdad ya ci gaba da cewa.

"Wannan sarƙar Mahaifinka ne ya taɓa bani ita sama da shekara tamanin, shi kasan har yau
ya kasa sanar dani inda ya samo wannan sarƙar. Idan kaje karka bari wani yaji wasiyya ta ku
kaɗaice daga kai sai Kyauta sai Mahaifinka, ka ɗora masa a ƙirjinsa kace ya yafe mini idan har
wani abu ya taɓa haɗa mu mara daɗi, sannan wannan sarƙa ka mallakawa Kyauta ita halak
malak ita ce kaɗai abin da zata dinga gani tana tunawa da ni. Ina ji a jikina Kyauta zata fuskanci
jarrawabawa kala-kala, sai dai har numfashi ya fita daga jikina a ƙasan zuciyata zan yi ta yi miki
fatan ɗaukaka akanki da abin da yake cikinki, duk abin da zaki gani kiyi haƙuri domin rayuwa
bata zuwar maka yadda kake son ta kasance maka..." maganar Kaka ce ta katse nan take ya
fara kakari da tari kafin su miƙa masa ruwa yace ga garinki nan. Kyauta wani irin kuka ta fashe
da shi mai tsuma zuciya nan take mara da bayanta ya amsa ta shiga murƙususu da alama
naƙuda ce ta taso mata gadan-gadan. Kafin Mirdad ya yi wani yunƙuri sai jin kukan Jaririya ya
yi ta faɗo, rasa yadda zai yi ya yi nan take wata dabara ta faɗo masa, shafe ganin gawar Kaka
ya yi ga mutane yana gurgiza sai ga shi ya rikiɗa cikin siffar Kaka, da sauri ya fice ya nufi
maƙotan bukkarsu ya sanar da wata tsohuwa halin da ake ciki, da murnarta ta ƙaraso tana yiwa
Kaka barka duk a tunaninta Kaka ne, ta fara gyara Kyauta da ke tsugunne wanda har lokacin
ban da kuka babu abin da take yi, musamman idan ta ɗaga ido ta kalli Mirdad dake cikin siffar
Kaka wanda tasan ya yi haka ne dan ya kauda shakku a zuciyoyin mutanen da suke ma'amula
da su Kaka.

Lokacin da aka kwantar da Kyakkyawar Jaririyarta a gefen makwancin Kaka, duk abin da
yake faruwa tsohuwar bata lura da gawar Kaka dake gefe ba saboda Mirdad ya kauda ganinta,
Mirginawa Jariryar tayi tana mutsu-mutsu hannunta ya hau kan Sarkar da Kaka ya bawa Mirdad
ya ajiyeta lokacin da zai kira tsohuwar, Kyauta dake gefe tabi Jaririyar da kallo, Mardid ne ya

ƙarasa ya ɗauki yarinyar yana jin ƙaunarta a zuciya sai dai gefe ɗaya yana tausayin Kyauta,
ɗaga ta sama ya yi bayan tsohuwar ta fice yace, "Barka da zuwa Muhaibish, tabbas harsashen
Kaka da alama bazai tashi a banza ba" Kallan Kyauta ya yi da tai zuru tana kallansa ya ci gaba
da cewa, "Kyauta kiyi haƙuri! Na saka mata suna Muahaibish ne saboda na lura mafi rinjayen
hallitarta daga ɓangarena ne na jinsin Jinnu, akan idon kowanne bil'adam ne zai ganta a
matsayin mutum amma sam ba haka bane."

Mahaibish ta diro💃🏻 Su waye zasu biyo ni muje suna😜

_LITTAFIN ANYA BAIWA CE? NA KUƊI NE DA NAIRA 200 ZAKI KARANTA SHI CIKIN
KWANCIYAR HANKALI, ZAKU BIYA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN, FIRST BANK 3090957579
AISHA ADAM, ZA'A TURO DA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR,0706 206 2624, DAN
GIRMAN ALLAH IDAN KINSAN ZAKI FITARMUN DA LITTAFI NA YAFE CINIKINKI._ [22/11/2021, 15:13] Ameera Adam🌚: 33...


A firgice Kyauta ta ɗago da kai tana kallon Mardid hawaye na ci gaba da tsiyaya kamar
wacce ta shiga gasar kwaranyar hawaye, wani abu ne ya tsarga mata a tsakar kanta da wani
dunƙulallen abu mai ɗaci da tsaya mata a zuciyarta, wannan ne karo na farko da Kyauta tana ji
rashin jindaɗin zamantakewarta da Mardid, yanzu ace ƴarta ta cikinta wai ta tashi cikin jinsin
aljanu. Mardid ganin yanayin Kyauta ya canja yasa ya tsugunna kusa da ita yana tallafo
fuskarta da tayi ja saboda kukan da tasha yace, "Kyauta! Ko bakiji daɗin kasancewarta haka
ba?" Ɗagowa ta yi ta kalleshi idanuwanta na ci gaba da hawaye ta girgiza kanta, tana cusa
kanta cikin jikinsa tare da fashewa da matsanancin kuka. Runtse idanunsa ya yi yana jin
kukanta har cikin zuciyarsa, hannu yasa ya fara bubbuga bayanta kamar yarinyar goye, har sai
da ta tsagaita da kukan da take yi sannan ya saketa ya ci gaba da cewa, "Na yi miki alƙawari
zan kula da ku na tabbatar bazaki yi maraicin Kaka ba" Gyaɗa masa kai tayi sannan ya sa
hannu yana goge mata hawayen idonta yace, "Yanzu ki tashi ki fita ki sanar musu da mutuwar
Kaka idan yaso bayan an binne shi sai mu koma cen Masarautarmu da zama" wannan karan
tashin hankalinta ya bayyana ƙarara a saman fuskarta har sai da ta ɗan firfito da manyan
idanuwanta, ya fahimci halin da take ciki ba ƙaramin tausayi ta bashi ba dan haka ya tattaro
jarumta yace, "Karki damu na tabbata babu wani abu da zai faru daku ki kasance jaruma me
jarumta karki bari raunin zuciyarki ya yi tasiri a gangar jikinki." Gyaɗa masa kai tayi tana ƙoƙarin
ɗauke damuwar fuskarta wanda tsanani damuwar tata ya ƙaryata haka. Kallanta ya sake yi a
karo na babu adadi yace, "Je ki kirawo su lokaci na ƙurewa" ya ƙarasa faɗa yana ɗaukar Sarƙar
da Kaka ya bashi. Jiki a sanyaye ta miƙe ta fita tana zubar da ƙwalla, ta fara sanar wa tsirarun
mutanen da suke kewaye a wurin. Tsohuwar da ta gyara Kyauta lokaci ɗaya ta ƙaryata dan gani
take wannan kamar wasan yara ne, amma suna tozali da gawar Kaka ba ƙaramin sanyi jikinsu
ya yi ba, kuka suke sosai dan Kaka na da matuƙar muhimmanci a cikin rayuwarsu, musumman
ga Dattawan da ke rayuwa a wurin, matasan yanki ne basu ɗaukake shi kamar yadda iyaye da
kakanninsu suke kallansa ba, duba da lokacin da girma ya kamashi ya tarkata kayan aikinsa
wuri ɗaya ya daina duk wasu taimako da yake yi musu na bada magunguna, idan ba gani ya yi
mutum na cikin wani irin tsanani ba.

Bayan an binne Kaka Mardid ya ɗauki Kyauta suka koma cen Masarautarsu ta fararen aljanu
dake ƙarƙashin ƙasa, lokacin da suka shiga hannunsa rungume da Muhaibish Kyauta na miye
da shi a baya gabanta sai faɗuwa yake. Yana shiga fadar ya gansu a tsaitsaye wasu na zaune
sai dai ga dukkan alamu fuskarsu babu walwala wanda yake nuni da cewar suna cikin
gagarumin ɓacin rai, dama ya tabbata sai sun ji labari tun kafin isorwarsu saboda yadda suke
bibiyar rayuwarsu, Mardid jinin jikinsa yasha dan tabbas yanayinsu baya rasa nasaba da shi,
Mardid ne ya gaishesu cikin girmamawa ganin yadda ya yi yasa Kyauta itama ta gaishe da su.
Babu wanda ya tanka mata hasalima gabaɗaya a wurin uku ne suke zaune cikin siffar bil'adam,
gabaɗaya sauran jama'ar wurin a rikiɗe suke cikin siffarsu da Jinnu. Wannan sam bai dame ta
ba saboda ta yi sabo da ganin wannan hallitun nasu tun tana ƙarama amma wannan yanayin
nasu ba ƙaramin razanar da ita ya yi, har sai da tsoronta ya bayyana a fili ƙarara. Mardid ne ya
fara takawa wajen Yayan Mahaifinsa dake kwance cikin siffar dorinar ruwar da kan Jaki sai
wasu tsili-tsili ƙafauwansa masu kama da ƙafafun zakaran hausa, yana zuwa ya miƙa masa
Muhaibish cikin ladabi yace, "Kyauta ta haihu ga yarinyar na saka mata Suna Muhaibish, amma
a gafarceni na yanke hukunci ba da saninku ba" A firgice ya ɗago yana kallonsa, wagegen
bakinsa ya buɗe me matuƙar muni ya furta, "Muhaibish?" Gyaɗa masa kai Mardid ya yi a ƙufule
Junduru ya miƙe yace, "Dole a canza sunan yarinyar nan bazai taɓa yuwuwa a kira ta da suna
kamar wannan mai matuƙar muhimmanci ba" Kyauta da ke gefe da ba ta san ma'anar sunan ba
amma ko da ba ta san me sunan yake nufi ba, ta fahinci sunan me muhimmanci da matuƙar
amfani ne a gurinsu, dan ta tabbata da banzan suna ne baza su taɓa ƙorafi akai ba tun da ta
san ba ƙaunarta suke ba, kuma ta san bazasu ƙaunaci abin da ya fito daga jikinta ba.

Mardid ya kalli kawun nasa da tsananin mamaki yace, "Saboda me za'a canza sunan?" A
hasaale Junduru yace, "Saboda sunan me tsarki ne dan haka bazamu yadda ka banzatar da
sunan ga wata bil'adam cen mara galuhu ba, kuma kai kanka ka sani ba kowanne yaro ne yake
cin wannan sunan rayuwarsa ta ɗore ba, ka sani kuskuren tsinuwa na bibiyar me sunan nan me
yasa zaka janyo mana jafa'i cikin ahalinmu, ka san tarihin Muhaibish tun daga farko har ƙarshe.
Ka karanta yadda Boka Bugudur ya kuskurewar bakinsa har ya tsine mata, kanasan tsinuwar
bakinsa ta sauka akan ƴar ka ne? Ko kuma so kake tsinuwar ta waiwayo har cikin ahalinmu?
Sam ba zai taɓa yuwu ba! Dole ma a canza mata suna" Mardid wannan hakan bai ɗaga masa
hankali ba ya gyara tsayuwa yace, "Ina ji a jikina wannan Jaririyar bata daga cikin waɗanda
Tsinuwar Boka Bugudur zata hau kanta, ina ji a jikina daban take da sauran ƴaƴa. Jarirai da
dama sun rasa rayuwar su da dama wasu ma daga ranar da aka ambace su da Sunan
Muhaibish kwana ɗaya basa ƙarawa suke mutuwa, amma wannan bazai karya mini gwiwa ba
domin na tabbata akwai wani al'amari ɓoyayye dangane da rayuwarta, amma ka gafarceni
Kawu idan maganata ta sosa maka rai" Ai kuwa kamar jira suke haka suka yo masa caaa kowa
da abin da yake gaya masa, ban da zagin Kyauta babu abin da suke yi da aibanta ta. Ɗaukan
ƴarsa ya yi ba tare da yace musu uffan ba ya riƙo hannu Kyauta da take kuka suka wuce cen
sashensa. Suna shiga Kyauta ta saki kukan da take riƙewa tun daga cikin fadar ta su, kallanta
ya yi yana jin wani irin babu daɗi aransa, janyo hannunta ya yi ya zaunar da ita yace, "Kiyi
haƙuri! Dama nasan haka sai ta faru saboda ba ƙaunarmu suke ba" Kyauta ta kalleshi da
jajayen idanuwanta ta ce, "Ka san da haka me yasa zaka saka mata sunan da zai zame mana

matsala gabaɗaya, kana ji fa yace mutuwa yara suke itama so kake mu rasata, daga haihuwa
ko zafin haihuwarta bai gama sakina ba? Wai ma wacece wannan Muhaibish ɗin da ambatar
sunanta na ga duk ya firgita su, wacce irin tsinuwa ce Bokan ya yi mata, baka gudun tsinuwarsa
ta shafi zuri'armu gabaɗaya? Gaskiya ka sauya mata suna saboda banasan na zama silar
rabuwar kawunanku, gani zasu yi nice nake saka komai tun da dama ba ƙaunata suke ba."
Yana gama sauraronta ya sakar mata wani lallausan murmushi kamar babu wani abu da yake
damunsa sannan yace, "Ki kwanta ki huta kina buƙatar hutu saboda jikinki babu ƙwari" wani irin
haushi ne ya kamata nan take hawaye ya ci gaba da shatata, kallansa ta yi ta ce, "Babu wata
nutsuwa da zan iya samu matsawar baka sanar da ni ainihin waɗannan tambayoyin da nayi
maka ba" Ganin da gaske take yasa yace, "Muhaibish wata shuɗaɗɗiyar shugabarmu ce, zamu
iya kiranta ta uwarmu gabaɗaya a Jinsin Aljanu. Wani abun ta aikata wanda mu mun ɗauke shi
a matsayin gagarumin abun kunya, ku kuma a jinsinku wannan abin da tayi ba komai bane.
Hasali ƙiyayyar da ƴan uwana suke miki akwai wani ɓurɓushin dalili da suke kallo yasa suka
ɗora miki wannan karan tsanar, wanda ya faru ne sanadin ƙaddarar Muhaibish. Macece da
wannan tsayuwar tawa bazata wadatar da ni na baki ainihin labarin halayenta na gari ba, sai dai
wani kuskure da ta aikata tsakaninta da jinsin bil'adam yasa Babban Bokanmu na wancen
ƙaranin ya fusata har ya tsine mata, wannan tsinuwar ce take bibiyar duk wanda ya saka wa
ƴarsa suna Muhaibish. Na san zakiyi mamaki yadda jarirai suke mutuwa amma ba'a daddara
wasu suke ƙara saka sunanta, labarin me tsayin ne akwai ɓoyayyun al'amura dangane da ita.
Sannan bayani ya gabace mu cewar za'a haifi Yarinyar da zata ci sunan Mahaibish matsawar ta
haure kwana da wuni bayan raɗin sunan batare da ta mutu ba, wannan yarinyar ita zata
kasance Muhaibish ta wannan ƙarnin, bazan ce miki komai akan baiwar da yarinyar zata taso
da ita ba, matsawar ya kasance Muhaibish ɗinmu ce. Ina ji a jikina ita ɗin ce ma saboda
mafarkan da na dinga yi a cikin bacci na, ki kwanta ki huta kina buƙatar hutu" Kyauta kamar
wacce aka zarewa laka a jiki haka ta zaunn daɓas tana tunanin wannan rayuwa da zasu
fuskanta. Tana shirin kwanciya ta ji dirowar tafkeken wani tsuntsu a tsakiyar bukkarsu me ɗauke
da kawuna biyu, a razane Kyuta ta ja da baya Mardid ya haɗe fuska dan ganin yadda suke
neman tsoratar da matarsa. Kafin ya yi wani yunƙuri Tsuntsun ya fara magana cikin harshen
jinsin su, "Ka gaggauta fito da matarka domin gabatar mata da wankan al'ada na masu jego ita
da ƴarta" ƙirjinsa ne ya buga har sai da yaji ƙafafuwansa suna neman kasa ɗaukansa, "Ta ya
zasu ce agudanar mata da wankan al'ada bayan sun san ba jinsun su bace? Anya ba da biyu
suka yi hakan ba tun da sun san ba za ta iya ɗauka ba?" Yana cikin tunani ya kuma riskar
maganar tsuntsun yana ci gaba da cewa, "Idan kuka ɓata lokaci kasan hukuncinta" yana gama
faɗa ya bi ta jikin bukkar ya fice.

Ɗagowa tayi ta kalleshi dan bata fahimci wane irin wankan al'ada ne suke zancensa ba,
tausayinta ne ya kamashi yana jin anya zai iya ci gaba da zama a cikin masarautarsu kuwa,
tuno halin da Mahaifinsa yake ciki da wasiyyar da Kaka ya bashi ya yi, nan take hankalinsa ya
ƙara tashi. Katse masa tunani tayi da cewar, "Mu je kiran da suke mana banasan ka ƙara laifi a
wurinsu." Motsa bakinsa ya yi a sanyaye yace, "Kyauta ba za ki iya ba, sam ba za ki iya jurewa
ba saboda ba al'adarku bace." Murmushin ƙarfin hali ta ƙaƙalo ta ce, "Ka daina tunanin akwai
wani abu na daga al'adarku da zai gagareni tun da ni na amince zan iya zama da kai" Ta ƙarasa
faɗa tana riƙe hannunsa suka nufi hanyar waje har lokacin hannunsa na rungume da

Muhaibish. Suna fita cen farfajiyar masarautar cike gurin yake maza da mata manya da yara,
wani fili aka zagaye wanda wata ƴar ƙoramace a tsakiyarsa. Ruwan jawur yake da wasu
ɗaiɗaikun korayen furanni, gefe waɗansu irin duwatsun ne masu ruwan zaiba sai wani farin
yashi da yake ta walƙiya yana ɗaukan ido.
Kyauta da take jinta cikin ƙwarin gwiwa suna zuwa wurin taji gabanta na faɗuwa, karɓar
Muhaibish Luliya tayi ta ɗaga sama sannan ta damƙi yashin ta birsine ta da shi gabaɗaya, kuka
take tsalawa kamar ranta zai fita. Duk yadda Kyauta taso dakewa ji tayi ta kasa, cikin kuka ta
kalli Mardid da ya sunkuyar da kai ƙasa ta ce, "Ka karɓo min ƴata wallahi kasheta za su yi"
girgiza mata kai ya yi yace, "Babu abin da zai yi mata wannan kukan da take yi yana da nasaba
da ɗigon jinsin jikinki, sai dai tsorona bansan yadda naki wankan zai kasance ba" Shiru tayi
zuciyarta na bugawa tsakanin uwa da ɗa sai Allah, Kyauta ji take inama wankan yashin da suke
wa Muhaibish ta karɓeshi ya dawo kanta. An ɗauki lokaci me tsawo ana yiwa Muhaibish
wankan al'ada da kala-kalan kayan al'adarsu sannan aka kira Kyauta, tana zuwa da ƙarfin tsiya
suka dannata cikin wannan ruwan ƙoramar, wata irin azababbiyar ƙara ta ƙwallah saboda
azabar da ruwan yake yi mata a jiki. Jikinta ne ya fara sauya launi zuwa baƙi-baƙi nan take
fatarta ta fara darewa. Mirdad na ganin haka ya bazama da gudu da niyyar ciro Kyauta da sauri
ƴan uwansa suka shatalo shi suka danne shi suna cewa, "Yadda ake wa matanmu babu abu
ɗaya da za'a raga mata."


😥Akwai tausayi wlh

_LITTAFIN NAN NA KUƊI NE DA NAIRA 200 ZAKI KARANTA SHI CIKIN KWANCIYAR
HANKALI, ZAKU BIYA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN, FIRST BANK 3090957579 AISHA ADAM,
ZA'A TURO DA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR,0706 206 2624, DAN GIRMAN ALLAH
IDAN KINSAN ZAKI FITARMUN DA LITTAFI NA YAFE CINIKINKI._ [23/11/2021, 18:54] Ameera Adam🌚: 34...



Mardid da ƙarfi ya shiga fisgewa yana ambatar sunan Kyauta amma bahaushe yace, "Sarkin
yawa yafi sarkin ƙarfi." Mardid yana ji yana gani haka Kyauta ta ci gaba da kwarara ihu wanda
da alama tana yin sa ne ba tare da tana cikin hayyacin ta ba, Bayan an fito da ita daga cikin
wannan ƴar ƙoramar jikinta gabaɗaya ya yi wani fatsi-fatsin baƙi ga fatar jikinta duk ta daddare,
ko numfashi da ƙyar take sauke shi sabida wahala idanunta arufe suke jikinta duk ya saki kamar
wacce babu sauran numfashi a jikinta. Kwantar da ita suka yi sannan suka ɗauko farin yashin
nan suka fara fursuna mata a jikinta, a zabure ta miƙe ta zuba a guje cikin fitar hayyaci tana ta
zabga gudu tare da kwarara ihu me ban tausayi. Gabaɗaya kallon gurin da tayi suka yi suna
ƙyakyacewa da wata irin dariyar mugunta, Mardid na ganin haka ya zabura cikin ƙaraji yana
kwalla ƙara tare da ambatar sunan Kyauta, suna hango

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
google.com, pub-9213700357025247, DIRECT, f08c47fec0942fa0