Showing 36001 words to 39000 words out of 57967 words
shin da gaske ne wai
Maryo tsohuwar matar Maleek ce Ɗan wajen Fulani Fahima?" Inna Habi bata bi ta kanta ba ta ci
gaba da raira kuka, ganin ta wannan sigar bazai fisshe da uwar soro ba yasa ta fara lallashinta
cikin nuna alamun tausayawa tana cewa. "Kiyo haƙuri Habi ummm ko ba daɗe ko ba jima
kinsan wannan ranar tana tafe bare kuma dama kin saba da ita tun da abaya ma haka ta faru,
oh ashe dai Maryo ba Baiwa ba ce da ƙimarta Habi nikam garin yaya haka ta kasance ne?" Inna
Habi ta ɗago da kai ta ce. "Me yasa baki tambayi waɗanda suka kai miki labarin ba?" Umma
uwar soro ta kyaɓe baki tana wurga mata harara ta ce. "Samun sarararin kuturu gaɗa a cikin
rama, saboda kun taka wani matsayo har kika fara yiwa mutane wulaƙanci, aikin ɓur inji tusa."
Tana gama faɗa ta fice fuuuu daga ɗakin dan haka ta so ba taso ace taji komai daga bakin Inna
Habi yadda zata ji daɗin idar da labarin. Maryo suna tafe banda hawaye babu abin da take yi
har sun kai gabda shiga ɓangaren Fulani Maryama ta ce wa Bayin da suke biye da ita. "Ku
dakata a nan zan je wani uzuri yanzu." Kamar su tanka mata sai dai babu wannan damar, cikin
girmamawa suka ce. "Hutawarki lafiya" Kamar wacce ake janta haka ta dinga bin hanyar daji
tana tafe har sai da ta dangana da bakin murgujejiyar bishiyar kukar da ta saba zama, tun kafin
ta ƙarasa ta farajin sautin shassheƙar kuka waigawa tayi taga babu kowa a gurin daga cen
hanyar rafin ta hango shi tsaye da hawaye ɗauke akan fuskarsa yana miƙa mata hannu alamun
ta taho gareshi, dukda kukan da takeyi hakan bai hanata sakar masa murmushi ba dan haka ta
fara ɗaga ƙafarta da niyyar ƙarasawa gurinsa, daga bayanta taga wasu mutane suna janta da
ƙarfi dan karta ƙarasa gurinsa, fisgewa ta fara ƙoƙarin yi amma babu hali saboda sun fi ta yawa
cikin kuka ta juya ta ce. "Bulbiyat meyasa zaki ci amanar Mahaifina me yasa kika ha'ince mu ku
barni naje gareshi kafin su tafi da ni" Wacce ta kira da Bulbiyat ta bushe da dariya ta ce. "Dama
cen bana tare da Mahaifinki a fuska ne kawai na nuna masa goyon baya amma ni ta hannun
daman Zulik ce ko Mahaifiyarsa bata kaini kusanci da shi ba" Duk yadda taso ƙwacewa daga
gurinsu ta kasa har ta hango shi ya nutse a cikin rafin da karfi ta fisge ta rushe da wani irin
kuka, tana tsaka da rusa kuka daga cen bayanta ta ji ance. "Ke lafiyarki me ya kawo ki nan?"
Tana waigawa ta ga Saif a tsaye ya harɗe hannuwansa, sanya yake cikin kaya na alfarma irin
na ƴaƴam sarakuna ba ƙaramin kyau da kwarjini ya yi mata ba sai dai fuskarsa a murtuke take
babu alamun fara'a ko kaɗan. Goge hawayenta ta fara yi sannan ta fara takawa a hankali tana
murza ɗan yatsan hannunta, sai da ta matsa gabda shi ta miƙa masa hannunta tana zubda
ƙwallah murya na rawa ta ce. "Dan Allah koda bazaka tuna ni wacece a gurinka ba ina san ka
kama hannuna ka sumbace shi ko da sau ɗaya ne a wannan karan ko zan ji daɗi. Wannan
zoben da ka bani ne dan Allah kayi mini kallan rahama ko naji daɗi acikin zuciyata ta yadda zan
ginga tuna irin kallon da kayi mini." shiru ya yi yana kallanta cikin zuciyarsa yana cewa.
"Wannan wacce irin mayyar yarinya ce haka?" Kuka take sosai ta tsugunna a dai-dai
ƙafafuwansa ta haɗa hannuwanta guri ɗaya alamun roƙo ta ce. "Nasan kana jin abin da nake ji
a cikin zuciya inda haka ba bazaka taɓa zuwa gurin nan ba, dan Allah karka juya mini baya
indai zaka amshi soyayyata a shirye nake na bijirewa umarnin Mahaifina da Mahaifin Maleek
saboda ni ba matarsa bace." kukanta ne ya tsananta tana yi ƙirjinta na wani irin suya sannan ta
ci gaba da cewa. "Wallahi ni ba ta shi bace kaine nawa kaine wanda na aminta da shi kaine
wanda mukayi alƙwari tare duk wuya duk rintsi bazamu gujewa juna ba amma me yasa zaka yi
mini haka, nice wacce ka sadaukar da komai naka akaina nice wacce aka azabtar da kai akaina
nice wacce take ɗauke da cikinka Ɗanka ko Ƴarka, dan Allah ceci rayuwa wallahi bazan iya jure
rashinka ba" wannan karanma kukanta ne ya tsananta nan take ta ƙware tare da fara wani irin
tari tana fesar da jini daga bakinta, zaro ido ya yi yana mamakin kalaman da take faɗa ko kaɗan
bai ji tausayinta ko ɗar a zuciya ba har sai da ya ga ta fara aman jini, sai da ta tsagaita sannan
ya ciro wani ƙaton ƙyalle ya miƙa mata. Sororo ta tsaya tana kallansa da mamaki murna ce ta
kamata a tunaninta ya fahimci abubuwan da take gaya masa da sauri ta karɓa ta fara goge
bakinta, sai da ta gama sannan matsa gabda da shi tana wara hannuwa alamar zata
rungumoshi.
Da sauri ya ja baya bata damu ba ta ƙara matsowa ta fara jikinsa tana sauke wata irin ajiyar
zuciya tana runtse idonta ta fara hango rayuwar da suke gudanarwa, da sauri ya yakice ta yana
kifeta da wani irin mari kafin ta dawo hayyacinta ya ƙara ɗauketa da mari, ba marin ne ya ɗaga
mata hankali ba illa rabata da jikinsa da ya yi shine babban abin da ya sa ta cikin damuwa.
Hancinta ne ya fara ɗigar da jini hawaye na zuba daga idonta, da sauri ta riƙe hannunsa tana ja
suka nufi hanyar rafin da take hangowa sai da suka je bakin rafin ta nuna masa tana cewa.
"Kalli nan shin baka ga abin da nake gani ba? Shi ka manta ƙoramar da muke gudanar da
soyayyarmu, ka manta a nan gurin na sanar da kai abin da yake cikin cikina, ka manta irin
albishir ɗin da kayi mini nida abinda zan haifa." hawaye ne ya ci gaba da tsiyaya daga idanunta
ta ce. "Karka manta nan gurin anan ne aka tarwatsa farincikinmu dam Allah karka bari wannan
karan suyi galaba akanmu" Kallan ramin gurin da yake cike da tarin bola ya yi sannan ya kalli
Maryo yace. "Waɗannan abubuwan da kika faɗa a cikin nan abun ya faru?" da sauri ta gyaɗa
kanta. Jinjina kai ya yi ya ja dogon tsaki sannan yace. "To banyi mamaki ba wataƙila aljanune
kikayi rayuwa da su a cikin wanan ƙatuwar bolar amma ba ni ba" yana gama faɗa ya fisgi
hannunta suka koma cen inda suka fara tsayawa da farko sannan ya wurgar da ita da ƙarfi har
kanta ya bugu da jikin bishiya ya fashe ya kalleta a fusace yace. "Wannan ya zama karo na
ƙarshe da zan gargaɗeki wallahi-wallahi kika ƙara yi mini makamancin irin wannan saina
karkaryaki na watsar, banz karya banda mace mara aji kina da aure me zaki yi da wani namijin
Allah ya tsareni daga kaidinki." Yana gama faɗa ya juya ya nufi hanyar cikin gari dan dama
ganyen magarya yaje cira ya haɗu da ita, fasa cirar ganyen ya yi koma gida rai a ɓace. Maryo
kuka ta rushe da shi a gurin kamar ranta zai fita fuskarta tayi jawur ta kumbura kamar wacce ta
kwana ta wuni tana kuka, ƙyallen da ya bata ta rungume tana jin wani irin sanyi a zuciyarta. Sai
da ta yi kuka mai isarta sannan ta miƙe ta nufi cikin gari tana haɗa hanya.
Maryo duk daɗewar da tayi tana zuwa gurin da ta bar bayin da suka zo tafiya da ita a inda ta
barsu a nan ta samesu, gaba ta wuce suna biye da ita a baya har cikin sashen Fulani Maryama.
Lokacin da Maryo ta shiga kallo ɗaya ta yi wa Fulani Maryama ta ɗauke kanta gefe, Jakadiya da
wasu bayi ne suka ɗauki Maryo aka shiga wani ɗaki da ita dan shirya ta. Fulani Maryama da
har lokacin cikin jimamin sabon labarin da ya zo mata take yi ta kalli Fulani Fahima ta ce. "Nifa
har yanzu mamaki nake ace wai Shukra ita take rayuwa a gidan nan batare da wani ya sani ba
sai yanzu" Fulani Fahima ta ce. "Yaya Maryama kenan kinmanta yadda auren Maleek ya
kasance kina ganin yarinya ƙwaƙwaran zaman wata biyar ba muyi da ita ba fa. Kinsan fa ko
lokacin da ya zo mana da ita cikin jikinta ma ya girma, kinga kuwa ta ya za'ai wani ya santa a
nan mu kanmu a waccen masarautar ba kowa ya santa ba" Fulani Maryama tayi zuru kamar me
nazari a gefe guda kuma farinciki ne mamaye a zuciyarta tun da tasan ko ba komai zasu rabu
da alaƙaƙai, babban farincikin ta da Salman bazai samu Maryo a matsayin matar aure ba. Ajiyar
zuciya ta sauke ta ce. "To Allah ya bada zaman lafiya gaskiya yarinyar akwai hankali" cikin
jindaɗin addu'arta Fulani Fahima ta ce. "Ameen bari na zagaya gurin su Yaya Bilkisu na dawo"
Maryo ce aka fito da ita cikin shiga ta alfarma sanye take da alkyabba silva da ratsin ja, ba
ƙaramin kyau tayi ba sai zuba ƙamshi take kamar wacce aka ciro daga cikin kwalbar turare,
gashin kanta aka wanke aka gyara kamar bashi ba. Fulani Maryama ba ƙaramin razana tayi da
ganin irin kyawun da tayi tai ba, suna haɗa ido gabanta ya faɗi. Jakadiya sai sunne kai ƙasa
take lokaci-lokaci taje tamke kanta dan kar ɗankwalinta ya zame ta sha kunya. Kai tsaye fadar
Sarki Aminullah aka wuce da ita sai dai har lokacin fuskarta sata koma dai-dai ba saboda irin
kukan da ta sha, babu yadda basuyi da ita ba akan ta bada ƙyallen hannunta amma fir taƙi babu
yadda suka iya haka suka haƙura suka ƙyaleta da shi. Suna shiga aka zaunar da ita a gaban
Sarki Aminullah da Sarki Abdallah, zamanta babu daɗewa su Inna Habi suka shigo bayan
zaman su Fulani Fahima ta shigi fuskarta ɗauke da murmushi. Sarki Aminullah ne ya fara
magana. "Assalamu alaikum. Dukan yabo da godiya sun tabbata ga Ubangijin talikai, mun
godewa Allah da wannan al'amari ya faru har gashi Maleek da iyayensa zasu koma da matarsa
wato Shukra. Amma ke Habi muna so muji alaƙarki da Shkra tunda Maleek ya shaida mana
cewar akan idonsa aka kashe mahaifiyar Shukra wannan dalilin ne yasa har ya ceci Shukra
daga ƙarshe kuma har Allah ta ƙaddara ta zama matarsa?" Cikin Inna Habi ne ya kaɗa saboda
ko kaɗan bata taɓa zatan zata iya fallasa wannan sirrin a gaban Maryo ba amma babu yadda
ta iya idan tace ita ta haifeta zasu ce ina shedarta ita kuwa bata da wata shaida. Gyara zama
tayi tace. "Allah ya taimakeka a hanya muka haɗu da ita ganin haka yasa na riƙe ta itama ta
zama kamar ƴata saboda gujewa faɗawa cikin ruɗin zamani" Sarki Abdallah yace. "Ina ƴan
biyun da ta tafi da su?" Inna Habi shiru tayi dan batasan me zata ce ba." Maryo tayi karaf ta ce.
"Duka Allah ya yi musu rasuwa" lokaci ɗaya suka nuna jimami sannan aka yi musu nasiha sosai
daga ƙarshe Sarki Aminullah yace an ɗaga likafar su Inna Habi sun tashi daga matsayin Bayin
zuwa ƴaƴan cikin gida. A dai wannan lokacin ne ya zartar da cewar zaman Inna Habi zai koma
Sashen Fulani Maryama yayinda Abu zata koma sashem Fulami Zaliha da zama. Daga ƙarshe
akayi addu'o sannan suka rufe taron Sarki Aminullah da iyalansa suka fita da jiyyar tafiya
Masarautar su.
Maryo jikin Inna Habi ta faɗa tana wani irin kuka mai tsuma zuciya haka itama Abu, da ƙyar
aka cire Maryo daga jikinsu suka wuce da ita bakin mota. A dai-dai nan gurin Salman ya ƙarasa
gurun fuskarsa ɗauke da murmushi ya miƙawa Maleek hannu yace. "Shar kake yau sabon Ango
ina ta ya ka murnar samun Shukra Allah sanya alheri" Maleek ya yi mamakin yadda Salma ya
sake masa fuska saboda yaga rabuwar baram-baram suka yi, shima mayar masa da martanin
murmushi ya yi sannan yace. "Ameen ya rabbi Ɗan uwa, kaima ya kamata kayi gaggawar fito
da mace ko mu kaɗa maka gangar gwauro" Salman ya saci kallan Maryo cikin zuciyarsa yace
mata. "Amaryar Maleek ki shirya takaba, babban albishiri tuni Furzaan antura masa matar da
zai aure dole dai ni ɗin nine mijinki" Maryo ta watsa masa harara ta mayar masa martani da.
"Maleek bazai mutu ba sai dai kai ka muti saboda zuciyarsa me kyau ce, Kaidinka zai koma
kanka domin Furzaan ni kaɗai ce ta shi bazai taɓa auren wata ba, kuma zai yi biyayya ga
Maleek domin ko kaɗan banjin haushin abin da ya yi ba wataƙila yana da gaskiya bansani ba ko
na taɓa rayuwa da shi a baya." Maleek ne ya ce. "Salman kayi shiru hirar ce baka so?" Fulani
Maryama tayi karaf ta ce. "Maleek kaga kaja matarka ku tafi karka biyewa wannan sakaran"
Maryo yana buɗewa ƙofa tana ɗaga kai ta hango Saif dake hango su yana zaune a cikin rumfa
nan take ta fara zubda hawaye, jiki babu ƙwari ta shiga motar su Inna Habi na ɗaga mata hannu
suna kuka, Sarki Abdallah ne ya yiwa Sarki Aminullah sallama sannan motocinsu suka tashi
suka nufi garin Adamawa.
Magariba liƙis suka sauka a Masarautarsu kafin zuwansu anshirya musu tarba da kayan
ciye-ciye kala-kala, Maryo wucewa da ita akayi sashen Fulani Fahima ruwan wanka aka shirya
mata sannan ta shiga tayi wanka ta ɗauro alwala ta fara gabatar da sallolin da ake bin ta, bayan
ta idar aka shirya mata kayan ciye-ciye a gabanta amma gabaɗaya a ciki lemon inibi kawai ta
iya ɗauka ta sha daga haka ta ce musu ta ƙoshi, basu takura mata ba suka ƙyaleta. Kan
shimfiɗa ta alfarma aka kai Maryo gurin baccinta Maryo tun da ta kwanta ta kasa runtsawa
banda hawaye babu abin da take yi har gari ya waye.
Washegari Tun da gari ya waye Fulani Fahima ta fara haɗawa Maryo kayan gyara na mata
kala-kala, saboda ta ce bazat tare ba har sai bayan sati guda da zuwansu. Maryo babu yadda
ta iya haka take turawa tana ci wani taci ya zauna wani kuma ta amayar da shi. A ranar da ta
cika kwana bakwai da gidan da daddare aka shiryata cikin rantsattsatsun kaya masu kyau sai
zuba ƙamshi take, har sashen da aka ware gurin zamansu da Maleek aka kaita tana shiga ta
samu bakin gado ta zauna gabanta na dukan uku-uku. Cikin shauƙin ƙauna da kewar matarsa
ya tako ya ƙarasa gurinta yana zame mata alƙyabbar dake jikinta, sanye take da wata doguwar
rigar mai adon duwatsu an naɗe mata gashin kanta ba ƙaramin kyau tayi masa ba. Kiss ya
manna mata a goshi sannan ya ce. "Shukra nayi kewarki na tsawon shekaru dan Allah nan
gaba karki ƙara hukuntani da irin wannan hukuncin domin ba zan iya ɗauka ba" Maryo shiru tayi
har lokacin gabanya faɗuwa yake, miƙewa ya yi yace. "Tashi ki ɗauro alwala mu gabatar da
Nafila domin wannan ranar jin ta nake kamar sabon ango ya zama wajibi mu godewa Ubangiji."
Kama hannunta ya yi ya nufi banɗaki da ita sai da ya tura mata ƙofar ya ce ta shiga. Tana shiga
ta fara alwala ta ga hannunta ya yi wani irin bau dai-dai gurin da ya riƙe mata hannu nan take ta
ga jini na tsatstsafowa daga gannun, ruwa ta sa ta wanke sannan ta fara gabatar da alwala.
Bayan ta fito sallah suka gabatar ya jima yana addu'a sannan ya fara ciyar da Maryo naman
ƴan shiloli, sau biyu kawai ta karɓa ta ce ta ƙoshi dan har lokacin hannunta raɗaɗi yake mata.
Bayan sun kammala koma Maleek ya riƙe hannunta suka koma saman gado cikin kewarta ya
miƙa hannu ya fara shafa mata fuska cikin so da ƙyauna. Lokaci ɗaya ya ga ta yi wata girgiza
harsai da gadon da suke kai ya motsa. Ɗaya bayan ɗaya ya dinga ganin me siffar Maryo na
tashi daga jikin tana dira a kusurwar bango harsa da guda biyu suka fita daga jikinta, Maryo ce
ta miƙe ta dira ƙasa itama ta koma kusurwar bango ta tsaya, ɗayan kusurwa da ta rage babu
kowa ya ga alamar inuwar namiji a atsaye. Ta farkon ce ta fara cewa. "Muhainish ba matarka
bace" sai ta biyun ta ce. "Kalimsiyat ba matarka bace" sai ta ukunsu ta ce. "Rayzuta ba matarka
bace, sauran duk suna da mazajensu dan haka nima ga mijina nan" ta faɗa tana nuna inuwar
dake jikin ɗayar kusurwar bangon.
KARFA KU SHIGA RUƊU IDAN KUN TUNA BAYANIN BOKA TUN A SHAFI NA UKU DAMA
YACE SHUƊAƊƊUN RUHIKAN ƳAƳAN SARAKUNAN ALJANU NE ZASU TASHI KARSHE
SU YADA ZANGO AKAN TA UKUNSU, DAN NAGA KAMAR WASU SUN RIKITA DA LABARIN
HARDA MASU CEWAR KO WANI LAIFI SUKA AIKATAí ½í¸‚í ½í¸‚ SAM BA HAKA BANE KU DAI
MUJE ZUWA MU HAƊE A COMMENTSí ¾í´¾í ¼í¿»♀️
_LITTAFIN NAN NA KUƊI NE DA NAIRA 200 ZAKI KARANTA SHI CIKIN KWANCIYAR
HANKALI, ZAKU BIYA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN, FIRST BANK 3090957579 AISHA ADAM,
ZA'A TURO DA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR,0706 206 2624, DAN GIRMAN ALLAH
IDAN KINSAN ZAKI FITARMUN DA LITTAFI NA YAFE CINIKINKI._ [13/11/2021, 19:30] Ameera Adamí ¼í¼š: 27...
Maleek ja ya yi da baya cikin tashin hankali, binsu yake da kallo ɗaya bayan ɗaya jikinsa ban
da karkarwa ba abin da yake yi. Inuwar da ke kusurwar bangon ce ta fara takawa a hankali
zuwa gurin Maryo dake kusurwar kudu, dafa shi tayi ta ce. "Ashe kana tare da ni kake ƙoƙarin
juya mini baya?" Maleek zaune yake yana kallon ikon Allah. A hankali ya fara karanta ayoyin
tsari yana tofa musu nan take fara bajewa ta jikin bango suna