Showing 33001 words to 36000 words out of 57967 words

Chapter 12 - Anya Baiwa Ce 1 Complete Hausa Novels

mata tayi tun daga ƙasa har
sama sannan ta ce. "Bansan shi ba Allah ya taimakeka" Sarki Aminullah ya kalli Maleek da ya
dafe kai da hannu biyu jin kalaman Maryo yace. "Kaji abin da ta ce, dama na gaya maka ba
lallai ita bace saboda wannan Baiwa ce" Maryo kallan Sarki Aminullah tayi cikin rashin jin daɗin
kalamansa ta ce. "Allah ya taimake ka ni ba Baiwa bace..." tun bata rufe baki ba wani Bafade ya
zabga mata doruna yana cewa. "Ƙarya kike ƴar talakawa..." bai rufe baki ba yaji andamƙi
wuyansa nan take ya fara wani irin kakari....


JAMA'A WAI BA ME TAMBAYAR ASALIN TARIHIN SARKI AMINULLAH DA IYALANSA NE🤣

_LITTAFIN NAN NA KUƊI NE DA NAIRA 200 ZAKI KARANTA SHI CIKIN KWANCIYAR
HANKALI, ZAKU BIYA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN, FIRST BANK 3090957579 AISHA ADAM,
ZA'A TURO DA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR,0706 206 2624, DAN GIRMAN ALLAH
IDAN KINSAN ZAKI FITARMUN DA LITTAFI NA YAFE CINIKINKI._ [10/11/2021, 18:26] Ameera Adam🌚: 25...


Fulani Maryama ta murtike fuska ta ce. "Jakadiya ki iya bakinki bar ganin na sake miki fuska
ki nemi ganin makwancina." Jakadiya har wannan lokacin bakin buɗe tana ƙarewa hallitar kai da
fuskar Fulani Maryama, ajiyar zuciya ta sauke ta ce. "Yooo ƙarya nayi wallahi Maryama tun wuri
ki nemar mana mafita idan ba haka ba wallahi sai kin fi Bora ƙanƙanshi agun Takawa, to wai ma
me zaki ce masa idan ya ga kan a haka ko bari zakiyi sai ya kai hannu yaji mulmulallan kai?"
Fulani Maryama shiru tayi tana nazarin maganganun Jakadiya dan a duniya babu abin da tafi
tsana ace Takawa zai juya mata baya, murya a raunace ta ce. "Jakadiya wallahi bansan ya
zanyi ba. Gaskiya Marduska ya cuceni ya taƙauceni" Jakadiya ta keɓr baki ta ce. "Ya cuce ki ko
ya cucemu?" Fulani Maryama ta ce. "Jakadiya ba gwara ke ba. Yanzu saboda Allah duk ranar
da Takawa ya ganni a haka wacce irin kunya zanji? Danma babu wani kataɓus da yake
aikatawa yanzu amma duk da haka ai da kunya." Jakadiya ta ce. "Mu koma gurin Marduska ba
sai asan abin yi ba" Fulani Maryama na shirin magana daga tsakar gida taji ana yi wa Farida
barka da zuwa, da sauri ta janyo Ɗan kwalinta ta ɗaura ta cewa Jakadiya. "Maza ɗaure kanki
naji muryar Farida zata shigo" Jakadiya ɗaure kai tayi ta miƙe ta ce. "To na barki lafiya" A
dai-dai wannan lokacin Farida tayi sallama cikin murna ta ƙarasa ta rungume mahaifiyarta,
barka da zuwa Jakadiya ta yi mata sannan tayi musu sallama ta fice.

Fulani Maryama ta dubi Farida ta ce. "Wai dama da wuri haka zaku sauka na ɗauka sai zuwa
azahar?" Farida ta miƙawa Fulani Maryama Jaririnta da bai fi watannin shida ba sannan ta ce.
"Mama wallahi saukar wuri muka yi ina ta kewarku ina Salman?" Fulani Maryama jin ta ambaci
Salman sai da gabanta ya faɗi tayi ta maza ta ce. "Ina jin yana cen sashensa. Ya Auwal ɗin?"
Farida ta ce. "Lafiya ƙalau ya wuce gaishe da Mai martaba. Mama ya jikin Saif kuwa?" Fulani
Maryama ta ce. "Da yake ƙanin Ubana ne ko? Sai inyi ta bibiyar lafiyarsa" Farida sauya fuska
tayi dan jininta ba ƙaramin haɗuwa ya yi dana Saif ba, duk lokacin da zata zo gida hutu a sace

take zuwa gurinsa su gaisa. Farida ta kuma cewa. "To ya su Ummansu Hidaya da Ummansu
Yusra?" A daƙile Fulani Maryama ta ce. "Lafiya kalau. Zaki dameni da tambaye-tambayen
jaraba ko gama gaisawa bamuyi ba" Farida tayi murmushi sannan ta sakowa musu wata hirar,
suna nan zaune aka dinga shigo da akwatinta da kuma tsarabar da ta kawo musu.
Cikin tashin hankali Sarki Aminullah ya furta. "Subhanallah Yakubu." Da sauri wasu dogarawa
suka ƙarasa gurinsa suna riƙe shi lokacin har ya fara fita daga hayyacinsa. Daga tsakiyar kanta
taji yace. "Ba shi da laifi, a bakin aikinsa yake tun da kike zo a ƙarƙashin masarautarsu dole kibi
umarninsu idan ya mutu ranki zai ɓaci" A hargitse Maryo ta furta. "Furzaan" Abu na ganin haka
danne cinyar Maryo tana mata alamar da ta nutsu tasan a gaban wanda take, Miƙewa Maryo
tayi ta fara kalle-kalle ta ce. "Kana ina ne Furzaan?" bin ta suka yi da kallo kowa na yi mata
kallon ta fara samun taɓuw, ido ta zurawa Dogarin da ke cikin wani hali nan take ya fara jin
komai yana lafa masa a hankali ya fara buɗe idonsa yana kallansu ɗaya bayan ɗaya a wahalce,
Ajiyar zuciya Sarki Aminullah ya sauke ganin Dogarin ya fara dawowa dai-dai. Ɗan more ne ya
taimaka musu aka ɗauke shi aka fice daga fadar. Har lokacin Maryo na tsaye tana waige-waige
ragowar dogarawan tsoron taɓa ta suka ji musamman da suka ga abin da ya faru da Ɗan
uwansu. Inna Habi ce ta kalli Maryo cikin tsawa ta ce. "Maryo nemi guri ɗaya ki zaune ko ranki
ya ɓaci." Ba musu Maryo ta zauna kafin ta kai ga zama hawayen da take maƙalewa ya fara
sharara a fuskarta, Sarki Aminullan ya yi mata kallan tsaf yana nazarinta sannan yace. "Me
yake damunki?" Kamar jira take ta rushe da kuka, sai da tayi me isarta babu wanda ya tanka ta
sannan ta ce. "Allah ya taimake ka Saif ne" Takawa ya gyaɗa mata kai alamar neman ƙarin
bayani ta ci gaba da cewa. "Yanzun nan ya yi mini magana amma kuma ya guje ni" Galadima
cikin tsawa yace. "Ke yarinya ki samu nutsuwa a gaban Mai martaba kike" Maryo ta watsa masa
wani kallo da idanunta da suka rune jawur, tayi ƙwafa ta ɗauke kanta. Sarki Aminullah wani
tunani ya yi sannan ya yi murmushi yace. "Yanzu ki bamu nutsuwarki daga baya sai muyi
maganar Saif ɗin" Maryo goge hawayenta ta farayi ta tattara hankalinta waje ɗaya ta ce. "Ina
jinka Ranka shi daɗe" Sarki Aminullah ya kalli Maleek yace. "Ki dubi girman Allah kiji tsoron
Allah, ki sani zaki muti ki tarar da Ubangiji ki gaya mana gaskiyar abin da kike sani game da
Maleek" Maryo kallon Maleek tayi da Mamaki saboda ita dai ta san tun da take ma bata taɓa
ganinsa ba sai a cikin Fada. Gyara zama tayi ta ce. "Allah ya taimake wallahi bansan shi ba
hasalima ni bantaɓa ganinsa ba sai yau ko Inna" Inna Habi ta gyaɗa kai cikin gamsuwa da
maganar Maryo, Maleek ya yi farat ya ce. "Shukra dan Allah karkiyi mini haka kinsan ko me ya
faru ba laifina bane, ki tuna irin ƙaunar da na nuna miki da bakiki kike cewa duk rintsi duk
wahaka bazaki gujeni ba amma me yasa kika mini..." Sarki Aminullah ya katse Maleek da
cewar. "Maleek ɗan saurara mun" Shiru Maleek ya yi Takawa ya kalli Inna Habi yace. "Menene
gaskiyar labarin yarinyar nan kinga wannan Ɗan ƙanwata ne yanzo yana iƙirarin Ƴarki Matarsa
ce, ki gaya mini gaskiya tsakaninki da Allah" Inna Habi ta share gumin goshinta ta ce. "Allah ya
taimakeka wallahi-wallahi Maryo dai ko auren fari bata taɓa yi na hasalima ko samari basa
kulawa tunkafin mu shigo gidannan" Maleek ya karɓe zancen da. "Gaskiya akwai tuntuɓen
harshe a maganarta, ku duba nan ku gani" ya faɗa yana lalubo salularsa mai kusan ƙirar rakani
kashi wani hoto ya nuna musu da bai fito sosai ba, sai dai ga duk wanda ya san Maryo yana
ganinta zai tabbatar da ita ce a jikin hotonsa duk kuwa da rashin kyawun camerar.Shiru fadar ta
ɗauka kowa da abin da yake saƙawa a zuciyar shi. Baƙin da suka taho daga Masarautar Sarki

Abdallah suma suna gani Maryo suka tabbatarwa da Sarki Aminullah cewar ita ce Shukran da
Maleek yake faɗa.

Itama kuma Inna Habi ta tsaya kai da fata akan cewar Maryo ba Matar Maleek bace, dan ta
ce ko kur'ani zata iya dafata akan haka ita kanta Maryo taci alwashin haka saboda ko a mafarki
bata taɓa sanin ko da mai yanayin Maleek ba bare kuma a zahiri.Tun da aka fara maganar
Salman ban da muzurai da harare-harare babu abin da yake yi, gani Sarki Aminullah ya fi
karkata ga ɓangaren Maleek yasa Salman miƙewa tsaye cikin ƙaraji yace. "Ya isa haka! Kai
Maleek wai me kake faɗa ne? Babu wata alaƙa da ke tsakaninka da ita, Ita ɗin tawa ce nine
kaɗai zan mallaketa dan haka ka iya takunka tun kafin na ɗauki mataki a kanka" Maleek ya kalli
Salman cikin nutsuwa yace. "Yaro man kaza. Matar tawa zaka dinga iƙirari da wacce zaka
aura? Duk masarautarmu babu wanda bai san Shukra matata ce idan ma wani abun ka yi mata
wanda yasa ta mance ni da ikon Allah sai komai ya warware, nina dogara da ikonsa kuma da
sannu zai bayyana gaskiya." Wani kallo Salman ya watsa masa sannan ya saki wani malalacin
murmushi ya fice daga fadar. Inna Habi da duk sauran mutanen gurin mamakin kalaman
Salman suke idan aka cire Sarki Aminullah da Maryo da suka taɓa jin hakan daga bakinsa.
Ganin haka yasa Sarki Aminullah ya umarci su Inna Habi da su koma sashensu bayan wani
lokaci zai kuma nemansu idan buƙatar hakan ya taso, godiya suka yi masa sannan suka bar
cikin fadar. Bayan fitar su idanun Maleek ya ciko da ƙwallah lokaci ɗaya ya fara zubda hawaye
sanna ya kalli Takawa yace. "Allah ya taimakela dan Allah kayi wani abu kar na rasa Shukra
dan Allah" Ba ƙaramin tausayi ya bawa Sarki Aminullah ba dafa kafaɗarsa yace. "Karka damu
Son zan kira Sirikina muyi magana duk abin da ake ciki zaka ji, kai dai ka ci gaba da Addu'a
Allah ya kawo mana mafita." Maleek ya gyaɗa kai sannan ya miƙe ta fice jiki babu ƙwari.


Inna Habi suna tafe magana na cinta har ta kasa daurewa ta cewa Maryo. "Maryo wato
shima wannan Ɗan sarkin sonki yake ko? Saboda ga ki sakarai ki bada kanki kare da doko
kowa naki ne yanzu meye fa'idar haka? Muna neman mafita ga wata matsalar ta ƙara ɓullowa
yanzu mecece mafita?" Maryo tayi shiru kamar bazatayi magana ba zuwan bayan ƴan sakanni
ta ce. "Inna wallahi babu wata alaƙa a tsakaninmu da wancen mahaukacin, shi kuma wancen
mutumin kece sheda ko a mafarki bantaɓa ganinsa ba" Inna Habi ta sauke ajiyar zuciya ta faɗa
wani tunanin. Har sun kusa ƙarasaw ɓangaren bayi ta hango Saif a zaune a kan dadduma da
sauri ta canja hanya ta nufi gurinsa, da sallama ta ƙarasa sannan ta tsugunna har ƙasa ta ce.
"Ina wuni Yaya Saif" Bai ɗago ya kalleta ba yace. "Lafiya" a gefen ta zauna ta ce. "Ɗazu a fadar
Takawa naji kana mini magan. Dan Allah me yasa kake guje mini ko tambayar abin da yake
cikina bakayi, yanzu haka kake san na haihu baka kula da lamuranmu?" har lokacin bai tanka
mata ba Maryo ta fara hawaye tana jin ƙaunarsa na ƙara nuƙurƙusar zuciyarta, ta kamo
hannunsa tana ƙoƙarin kaiwa saitin ƙirjinta ta ce. "Ka tausaya mini kaji yadda zuciyata take
harbawa saboda kai, ni ce wacce a kodayaushe bama rabuwa dare, rana, safiya, zafi, sanyi da
damina..." Da sauri ya fisge hannunsa ya kifeta da mari. Yana ɗago kai yaga wasu bayi har sun
fara taruwa suna kallonsu, ganin ya kallesu yasa suka yi maza suka bar gurin. Maryo kafeshi
tayi da ido sai kuma hawaye ya fara zuba zuciyarta na bugawa akai-akai. Tamke fuska ya yi
tamau ya nuna ta da ɗan yatsa yace. "Wannan ya zama shi ne kashi na ƙarshe da zan gargaɗe

ki da karki ƙara shiga sabga ta idan ba haka ba zan ɗauki mummunan mataki akanki, ke wacce
irin mayya ce ne? Ban da mace Karya wace mace ce take bim namiji yake yakice ta. Uban
waye ya yi miki cikin da zaki haifa? Wallahi idan na kuma jin waɗannan kalmomin naki sai na sa
ankaiki gidan turu" yana gama faɗa miƙe ya wuce har yana hankaɗeta ta faɗi a gefe. Kuka ta
rushe da shi mai tsuma zuciya nan take kanta ya sara ta fara wani irin tari tana tofar da jini, tana
waigawa ta hango Inna Habi a tsaye tana kallonta ga hawaye na zuba daga idanunta. Abu ce ta
ƙaraso gurun ta kama hannunta ta miƙe suka nufi gurin Inna Hani, suna zuwa gurin Inna Habi
saboda baƙin ciki ta ɗauke da mari sannan ta rushe da kuka cikin takaici ta rufeta da duka tana
cewa. "Maryo yanzu a gabana namiji yake dukanki saboda kin bada kanki a banza anya kin
yiwa kanki adalci kuwa Maryo abin da zakiyi mini kenan" nan da nan gurin ya fara taruwa da
mutane. Abu ce ta janye Maryo da har lokacin aman jini take yi, Inna Habi ta wuce su tana
share hawaye sannan suma suka bi bayanta. Kafin wani lokaci tuni maganar marin da Saif ya yi
wa Maryo ya zaga cikin gidan masarautar, dan har da masu yaddawa su Inna Habi da baƙar
magana babu abin da take ce musu saboda tasan duk me ma aka gaya mata Maryo ce ta janyo
musu.

Bayan kwana biyu gabaɗaya Maryo ta ƙara fita daga hayyacinta, ta rame ta lalace ko ruwan
kirki bata iya sha, hatta makaranatar bokon data allon da suke zuwa gabaɗaya ta watsar bata
da aiki sai kuka, idan abin duniya ya isheta sai dai ta wuce cikin daji ta nufi bakin bishiyar
tsamiya ko kuka ta zauna, anan ne take samun nutsuwa wani lokacin har bacci take samu tayi.
Sati Biyu da zaman fadar su Maryo Sarki Aminullah ya tara su a lokacin wannan zaman
harda Sarki Aminullah da da Mahaifiyar Maleek Hajiya Fahima, tun zamansu a fadar Sarki
Abdallah da Hajiya Fahima suke bin Maryo da kallo, waɗansu hotuna Maleek ya ciro ya miƙawa
Sarki Aminullah yace. "Waɗannan sheduna ne na farko" Sarki Aminullah ƙuri ya yi yana kallon
hoton tabbas babu ko tantama wanna Maryo ce, miƙawa wani Dogari ya yi yace a miƙawa Inna
Habi. Karɓa tayi tana kallo gabanta ya faɗi gani mace sak Maryo a kusa da Maleek sauran
hotunan kuma tare da Sarki Abdallah ne da wasu mutane. Ta tsinkayi muryar Sarki Aminullah
yace. "Me zaki ce game da wannan" kafin Inna Habi tayi magana Hajiya Fahima ta ce. "Nima
ina da laifi a cikin wannan maganar saboda da ban musguna mata ba da bazata taɓa gujewa
Maleek ba, ki sani nima nayi haka ne saboda wasu maganganu da aka gaya mini akanki" Sarki
Aminullah ya dakatar da Hajiya Fahima ya kalli Inna Habi. Inna Habi ta ce. "A gafarce ni Allah
ya taimakeka a baya na faɗi haka ne saboda banasan rabuwa da ita amma tabbas Maryo matar
Maleek ce, hakan ne yasa na sauya mata suna zuwa Maryo a madadin Shukra" Ba Maryo ba
hatta Abu a zabure suka kalli Inna Habi da ta sunkuyar da kai tana hawaye. Sarki Aminullah ya
kalli Maryo yace. "Kinji me ta ce haka ne?" Maryo ta kalli Inna Habi nan take hawaye ya
gangaro mata ta kalli Sarki Aminullah ta ce. "Eh haka ne amma ina nemar mata afuwa" Inna
Habi ta ɗago da sauri ta kalli Maryo, Maryo ma ita take kallo tana hawaye. Sarki Aminullah
yace. "Alhamdullah yanzu kin amince zaki bi mijinki" Abu tayi karaf ta ce. "Allah ya taimake ka
yanzu bata da sha'awar zama da shi" Maryo ta sunkiyar da kai ta ce. "Eh ranka ya daɗe"
Maleek ya ɗaga hannunsa yana godiya ga Ubangiji, Hajiya Fahima ta rungumo Maryo ta ce.
"Matso ƴata Allah ya yi miki albarka" Sarki Abdallah yace. "Sirikina godiya muke Allah ya bar
zumunci." Sarki Aminullah yace. "Akaita sashen Fulani Maryama a kintsata cikin shiga ta

alfarma a yau za'a bashi matarsa ya wuce da ita" A firgice Inna Habi ta ɗago ta ce. "Ranka shi
ɗaɗe amma..." Da sauri Maryo ta ce. "Amma barni yanzu ina san ƙeɓancewa da Inna" babu
wanda ya hanata dan haka suka wuce cen sashen su na baya. Suna zuwa Inna Habi ta fisge
hannunta daga cikin na Maryo ta ce. "Barni fada zan koma" Maryo ta ruƙo ta cikin kuka ta ce.
"Me zaki ce?" Inna Habi ta ce. "Zan ce musu ƙarya nake bake bace" Maryo ta ce. "Inna gwara ki
bari na tafi dan ko kin koma bazan fasa tafiya ba, dama tuni nayi niyyar nisa da gidan nan
saboda soyayyarsa kasheni zata yi koda ban bi su ba zaku wayi gari da gawa ta ko kuma na
gudu." Inna Habi ta fashe da kuka ta ce. "Amma me yasa baki ce musu ƙarya nake ba?" Maryo
ta ce. "Ba zan iya ba Inna bazan taɓa kunya ta ki ba" Inna Habi ta ce. "Amma Maryo ya za'ayi ki
zauna da mutum alhalin ba'a ɗaura muku aure da shi ba" Maryo ta ce. "Idam naje dole za'a
ɗaura ku dai kuyi mini fatan alheri" suka rungumeta gabaɗaya suna kuka. Daga bakin ƙofa suka
ji ana magana da Maryo da sauri ta yakice ta nufesu kai tsaye suka wuce sashen Fulani
Maryama.



_LITTAFIN NAN NA KUƊI NE DA NAIRA 200 ZAKI KARANTA SHI CIKIN KWANCIYAR
HANKALI, ZAKU BIYA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN, FIRST BANK 3090957579 AISHA ADAM,
ZA'A TURO DA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR,0706 206 2624, DAN GIRMAN ALLAH
IDAN KINSAN ZAKI FITARMUN DA LITTAFI NA YAFE CINIKINKI._ [11/11/2021, 18:02] Ameera Adam🌚: 26...


Inna Habi na ganin haka ta durƙushe a gurin tana rushewa da wani irin matsanancin kuka,
Abu ma kifa kanta tayi jikin Inna Habi tana rusgar kuka kamar wacce aka yi wa bushara da
mutuwa, Carko-carko mutane suka yi a bakin ƙofar daga cen ƙasa ƙananan maganganu suna
tashi sama-sama, Umma uwar soro ce ta shiga ɗakin da sauri zaninta har yana neman faɗuwa,
tana shiga ta dafa Inna Habi ta ce. "Habi labarin da nake ji ya riskeni

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
google.com, pub-9213700357025247, DIRECT, f08c47fec0942fa0