Showing 1 words to 3000 words out of 62089 words

Chapter 1 - Aure Da Karatu Book Complete Rumaisa Sidi

Rumaisa   

18 Jul 2026

510

*AURE DA KARATU*




*RUMAISA SIDI*





Page 1 (dandano)








Kamar yanda na riga na al'adanta na gyara gidana tareda kicaniyar hadawa 'yan makaranta
abin kari sauri-sauri nake komai saboda banson suyi latti har takai ga an dokesu a makaranta






Duk abinda nasan zai saka yarana farinciki har su aje hankalinsu suyi karatu inayi kama daga
kan cimarsu,suturunsu( uniform) har izuwa abubuwan da zasu taimaka musu suyi karatu duk
term nake canja musu uniform saboda makarantar kudi sukeyi suna ganin yanda akewa sauran
yara to nima ina bakin kokarina gurin yin abinda zan iya saboda kullum ina nuna musu ba zaka
taba cimma wani ba kaima wani bazai cimma ba







A kan wannan na dorasu suma akanshi suka ginu duk abinda suke so ina kokari in musu da
dan abinda nake rufa ma kanmu asiri

A halin yanzu ba abinda nakeso sama da yarana su kadai ke sakani farinciki su kadai suka
ragemin idan har kaga dariyata to ina tsakiyar yarana suna min labarin makaranta da kuma
burikansu da kullum suke kara yawa a kaina




Yarana uku Safwan shine babba shekararsa 12 sai Aysha dake binshi ita kuma shekararta 9 sai
auta Amra 'yar rigimata kenan itama shekararta 6 kuma farincikinmu gaba daya








Karfa kuga na cikaku da zancen yarana ku kosa dani ko kuyi tunanin ina b'ata muku lokaci ko
d'aya labarin bazai tafi yanda nakeso ba sai yarana sun shigo a farkon labarina









Zakuce a ranku to duk wayannan yaran ina mahaifinsu?????

Mahaifinsu Lawal muhammad yananan kuma muna tare da shi har yanzu
saidai.......................Jin girkina na neman konewa ya ankaraddani bayan dogon zangon tunanin
da naje da sauri na hada wa kowa nashi saboda nima makaranta zanshiga saboda inada
lecture karfe 10










Kukan Amra da naji yasa nayi saurin fita ganin fitowa ta yasa tayi gurina tana kara doka kafarta
kasa irinna rigimammun yara










Mommy kinga Esha ta dakkomin socks ko? hannunta na rike ina karasawa cikin falon







Ina Eshar? meyasa zaki dauka mata socks?

Wallahi mommy bandauka mata socks ba kawai na duba na dau nawa shine wai tunda na taba
mata abu saita rama a tawa








Murmushi nayi araina nace "Rigimammiya"










Daurewa fuskata nayi sannan na nuna Aysha "Karki kara tabawa shalelena kaya bakisan
batason ana sama ta datti a kaya ba karki kara"








Kama kunne Ayshar tayi tana kunshe dariya "Am so sorry mommy bazan kara ba"









"To kowa ya zauna kuyi breakfast tun school bus bata iso ba" shayin na hada safwan ya
zubawa kanshi ya zubawa Aysha ni kuma aka barni da 'yar lelena (dama aikinta sai ni)

Tsittt naji gidan yayi bayan wucewarsu zama nayi nima nayi break sannan na hada kofunan da
mukayi amfani da su na wanke sannan na wuce dakina don in shirya kar inyi latti











Kallo guda nayiwa gadon da yake kwance na kawadda kaina inada tabbacin ko sallar asuba
baiyi ba don yanda na fita na barshi haka na dawo yanzu ma na sameshi











Har nayi wanka na shirya yananan kwance saida na kammala komai sannan naje gefen gadon
daurewa nayi na taushe abinda nakeji idan tuna abinda yamin jiya bubbuga filon na shiga yi

"Abban safwan" na shiga kiranshi a hankali kar yace na mishi ihu amma shiru Filon naci gaba
da bugawa juyawa yayi yana yamutsa fuskar da har yau na kasa tantance abinda na gani
gareshi da har na dage sai shi










A kufule na buge filon wannan karon sai gashi zaune tsakiyar gadon yana aikomin sakon harara
" Waike wace irin matace kashemin dodon kunne za kiyi? tun safe keda yaranki kun ishi mutane
da surutun tsiya yanzu kuma ke kinzo min ihu a kai"












Hadiye bacin raina nayi sanin ba abinda zai amfana min "Dama zan wuce makaranta ne kuma
gidan ba kowa ba'a san mai shigowa ba"

"Yanzu dama saboda banzar makarantarki za ki hanamin bacci nasha gayamiki ba abinda ya
shafeni da wata makaranta taki idan kin cika in kinje karki dawo kuma wallahi idan har kika
wulakanta min aure ke da Allah"












Sauri-sauri na bar dakin ina mayadda kwallar da ke neman zubomin tare da tunatarda kaina
alkawarin da na daukarwa kaina na bazan kara zubarda hawayena akan Lawal ba











Tunda na shiga makaranta na watsar da tunanin damuwata na fuskanci abunda nazo yi lecture
daya ce dama 12 na fito daga makaranta inata sauri in isa gida in hadawa yarana abinci kafin
su iso

Cikin sa'a kuwa muna fitowa na samu napep na shige ina yiwa abokan karatuna sallama ina jin
lokacinda Nafisa ke cemin "Sai gobe uwar son 'ya'ya" haka suke cemin wani lokaci suna ganin
kamar na cika son yara ina musu uzuri wani lokaci saboda basu san abinda yasa nakejin kamar
nafi kowace uwa son 'ya'ya










Kamar yanda na tsammananta yana zaune akan bencin mai shagon da ke haya kofar gidanmu
suna gardamar siyasa "ai wannan fagen ka kware" na fada a raina kudin mai napep din na
bashi ina kokarin juyawa yaro ya iso wurina yana bani mukullin gidan "gashi inji abbansu
safwan" karba nayi tareda wucewa na bude gidan na shige











Hmmmmmm salon na dabanne🥰💃






Ga sabon littafin mu mai taken AURE DA KARATU comment dinku shi zai bayyana karbuwar
littafin ko akasin hakan

AURE DA KARATU

NA


RUMAISA SIDI





Page 2







Gyale na na kwabe tare da wucewa daki na watsa ruwa sannan na dauko doguwar rigata mara
nauyi na dora hula akai na fito







Kaitsaye kitchen na wuce na shiga hadamana abinci jallof din shinkafa na dafa da dan sauran
kifin da muka ci jiya sauri-sauri nake komai kar su dawo bankare ba







Karfe 1 dayan mintuna naji tsayuwar bus dinsu bayan na kammala hada komai Amra ce a gaba
tana kwallamin kira "Mommy Mommy" tashi nayi tsaye kamar yanda muka saba kullum
rungumeni su kayi su duka ukun kowa na fadin "Ni ne first, ni ce first" hadesu nayi duka ukun
nima na rungumesu ina jin wata kaunarsu ta musamman tana ratsani tareda tausayinsu

Dakinsu suka wuce suka cire uniform tareda aje kayansu Aysha ta canjawa Amra ni kuma na
zubo mana abinci kafin su iso yasha iska suma basu ja lokaci ba suka fito





Tsakiya na aza tiren abincin muka zagayeshi saida muka zauna na tuna da ruwa safwan na
duba "Yaya dakkomana ruwa a fridge" tashi yayi ya dakkoma kowa sannan ya zauna muka fara
cin abinci






Amra ce tasaka rigimar ita zata fara bani abinci wannan ka'ida ce idan muna cin abinci to kowa
zai bani a baki nima in basu wannan karon ma kowa saida ya bani nima na basu bayan mun
kare safwan ya gyara wurin Aysha kuma ta kai kayan kitchen







Jin an fara sallah safwan ya fita masallaci ni kuma na hadasu muka je muka yi sallah
kasancewar yau alhamis ba islamiyya muka dawo falo saboda zafi gashi ba wuta system dina
suka dakko suna game ni kuma na dau wayata ina duba costomers dina na whatsapp wayanda
ke bukatar kaya ina tura musu suna zabawa

Na shafa'a ga mutanen arzikina har na ware ina chat da kawayena a wani group dinmu na
makaranta har safwan ya dawo shima ya jone dasu Aysha suna game sam banji shigowarshi ba
ganinshi kawai nayi a kaina "Wannan wane irin iskanci ne ana miki magana kamar bakyaji to
yama za'ayi kiji kina hira da samarinki duk abinda kika fita kikayo bai isheki ba sai kincimin
mutuncin aure a cikin gidana to wallahi baki isaba "







Kallon bangaren da yarana suke nayi suna nan zaune Safwan da Aysha sun sauke idonsu kasa
amma sunbar game dinsu Amra ko kyam ta zubomana na mujiya "Safwan kuje dakinku kuyi
game din" kamar mai jira suka mike






Saida naga wucewarsu sannan na maida hankalina gareshi "Haba abban safwan sau nawa zan
gayama bai kamata kake fadar kowace irin magana a gaban yarannan ba ina gujema hakan ya
janyo ma raini"




Kamar wanda ke jin haushina ya zaburomin "Raini na nawa kuma? bayan kingama nuna musu
banida muhimmanci a garesu kina kallo nuna suke kaitsaye sun fi kaunarki a kaina kingama
hore musu kunne wallahi nayi nadamar aurenki"




wani bakinciki ne ya tunzuromin nima na mike tsaye ina kallonshi cikin ido ina kara jin tsanarshi
fiye da yanda nakeji "Kaine da kanka ka kada girmanka a wurin yaranka lawal kuma wallahi
nafika nadama da danasanin aurenka bansan bakinciki ba saida na aure ka bansan wata cuta
hawan jini ba sai a gidanka kaine..........." shiru nayi jin kowane irin lokaci kuka na iya kwacemin
wayata na dauka na wuce daki shima a sanyaye ya juya yabar gidan

Da darema tare da Aysha na shiga kitchen na dafa mana abinci daidai cikinmu don alkawari na
dauka bazan kara ciyadda shi ba zan nuna mishi wannan karon nima 'yar kodimo ce bazan kara
daukar iskancinshi ba








Bayan mun kammala cin abinci kowa ya dakko littafanshi sukayi home work ina duba musu da
inda basu ganeba ganin dare yayi nace suje su kwanta Amra tasa rigimar ita tare dani zata
kwanta nace zuje su kyaleta "Ku tabbatar kunyi addu'a yaya"









Banjima ba nima na fara jin baccin tashi nayi nadauki Amra da ta dade dayin bacci dakinsu na
kaita kayan wutar dakin na kashe tareda tofesu da addu'a







Shirin baccin nayi nima zan kwanciya naji yana kokarin rufe gidan na gyara kwanciyata kamar
nayi bacci ya dan jima da shigowa gidan sannan ya shigo daki kamar mai tunani yayi tsaye
tsakar dakin yana kallona sai can ya karaso yana buga filon da nake kwance kamar mai baccin
kwarai na shiga kifta ido tare da tashi zaune "Yadai" na fada tareda dage gira ina kallonshi
kame-kame ya shiga yi "Am nace MY ZEE baku rage abinci bane wallahi yunwa nakeji kuma
naje gida na taradda Salma ta haihu tana asibiti to abincin duk ankai can"(salma kanwarshi ce

da tayi aure shekarar da ta gabata)


Abin mamaki sai banji tausayinshi kamar lokacin bayaba da wancan lokacine da dasauri zan
tashi koda abincin da zan cine to ni zan hanama cikina in bashi amma wannan karon kai tsaye
na dubeshi "Wallahi babu shi duk mun cinye" daga haka na juya na gyara kwanciyata ina fatan
bacci ya daukeni







Sai asuba na farka baya dakin da alama ba ciki ya kwana ba fita nayi na wuce dakin yarana na
tadasu saida naga sun tashi sunyo alwala sannan na fito hangoshi nayi kan doguwar kujerar da
ke falon karasawa nayi wurinshi na shiga tadashi kamar yanda ya saba kullum idan na tadashi
wannan karon ma harara ya bankomin "Lafiya kuma" murmushin tura haushi na mishi sannan
nace "Lokacin sallah ne yayi abban safwan nace bari in tadaka karka rasa jam'i"








Wani kallo yake bina dashi kamar ya shakeni"To ina ruwanki da sallah ta kabarinmu daya dake
wai ni menamiki har haka zainab da kika bi kika addabi rayuwata ne ko so kike shima kwanan
gidan in barmiki keda yaranki iye" ganin yanda yake daga murya kar ya janyo mana hankalin
makwabta yasa na juya nashige daki kar in rasa jam'i wurin neman magana







Har suka wuce makaranta yau ma yana daki ni kuma ina falo ina duba abokan business dina
ina yin order kayan da mutane ke bukata nishadin da nakeji ne ya jani izuwa status din jama'a
ina kallo wasu hotunansu suke posting wasu kuma sana'unsu can nakai ga status din Hannatu

cousin sister dina wakokin soyayyane kala-kala tayi status tareda emojies na soyayya murmushi
nayi "Su soyayya manya" na fada a raina ina tuna irin soyayyar da muka buga nida lawal kamar
ba gobe idan naga masoya suna zuba soyayya saidai kawai nayi dariya tareda fatan suga mai
kyau don nikam ba abinda ta tsinanamin sai tarin bakinciki






Na tuna lokacin da lawal yake duke gabana yana kuka yana fadin "Ki taimakamin my zee kar na
rasaki wallahi idan na rasaki to zan iya rasa raina na miki alkawarin rayuwa mai inganci nasan
gidanku gani suke bazan iya rike ki ba saboda ina talaka wallahi zee indai kika aureni ko dako
ne zanyi in ciyadda ke da abinda kika saba ci a gidanku"






A wannan lokacin nima zubewa nayi a gabanshi ina kuka "Ka kwantarda hankalinka Nisful ba
abinda zai rabamu ni kai nakeso da kai zan zauna banajin kona second daya zqn iya kula
namijin da ba kaiba na tabbata inhar na dage kai nakeso abba zai auramin kai dawowarshi
kawai nake jira"





Hawaye naji suna zubomin "Allah sarki abba Allah ya gafarta ma gashi ka auramun abinda nace
inaso na guji zabinka ni kuma ga abinda nake gani Allah na tuba ka yafemin"

Hmmmmmm muje zuwa dai🤔

AURE DA KARATU
NA
RUMAISA SIDI


Page 3

Kuka nayi marar misali saboda tuno abinda nake kokarin mantawa taurin kai duk shi ya kaini ga
fadawa halinda nake ciki a yanzu bana zargin kowa da lalata rayuwata sai ni da kaina mahaifina
mahaifiyata yayyena da duk wani masoyina ba wanda bai shawarce ni akan abinda suke
hangomin ba amma na take saboda wata banzar soyayya tawa banci riba ba sam ba wani
amfani da hakan yamun

"Wannan wace irin mummunar dabi'ace me kuma aka miki yanzu da zaki zo kina min kuka a
cikin gida ko sharrin naki ne ya tashi? to wallahi wannan karon a shirye nake da duk wani dan
uwanki da zai nunamin yatsa ba wanda ya isa ya wulakanta ni "

Da kallo na bishi har ya shige kitchen hawayena na goge banjin zan iya kula shi a wannan
lokacin na gaji da biyemishi duk safiya muna raba hali gyara kwanciya ta nayi kan doguwar
kujera tare da saka earpiece ina sauraren karatun qur'ani ina fatan samun nutsuwa da rahama
a cikin zuciyata saboda abinda nakeji kowane lokaci rashin lafiyata zata iya tashi
Dawowa yayi falon yana maganar da sam banaji saboda abinda ke cikin kunnena a hankali na
sance kunne daya ina watsa mishi idanuwana da yake kira da oily eyes a lokacin da muke kan
soyayyarmu yasha gayamin wani sanyi yakeji a ranshi idan ina kallonshi da su

"Ina breakfast dina fita nakeso nayi" Cikin isa yake maganar kamar wanda yasiyo komai ya aje
ya zo ya taradda babu

"Hmmmm" na sauke ajiyar zuciya tareda kara kallonshi " Mun cinye" na fada kaitsaye tareda
kokarin mayadda earpiece dina maganarshi ta dakataddani " bangane kun cinye ba kyaleki fa
nayi ko jiya daga abincin rana har na dare ba wanda naci a gidannan yanzu ma don tsabar
mugunta daga ke sai 'ya'yanki zaki cinye"
"Anzo gurin" na fada a raina " Banyi tunanin kana bukatar abinci a gidanka ba saboda duk
maigidan da ke bukatar hakan fita yakeyi ya nemo ya kawo a dafa aci amma kai banga hakan a
tare da kaiba kuma wannan abin da kake kiran ba'a baka ba wanda kace kafi karfin wulakanci a

wurinsu ne suka aje kaga ko bazaka ci ba"

"Ai ba yau kika fara yimin gori ba Zainab ba yau kika fara nuna 'yan uwanki ke daukar nauyinki
ba kuma ba wanda nace yayiwa 'ya'yana wata lalura abarsu su rayu kamar yanda nake rayuwa
nima rashin sirrinki yasa kika gama zubarmin da mutunci a gurinsu shi aka nunamin tun farkon
neman aurenki naki fahimta ana nunamin illolin auren 'ya'yan masu kudi amma kaddara ta riga
fata don aurenki KADDARA CE"

Daga zaunen naji jiri na dibata "Lawal, Lawal ne ke kiran aurena auren kaddara? lawal din?
wayyo Allah na" dishi-dishi nake ganinshi saboda hawayen da ya cikamin ido amma yanda ya
bakanta min nima zan bakanta mishi gorin da yadade yana fadar ina mishi yau daya zan mishi
yasan abinda ake nufi da gori " Aurena ya wuce ka kirashi na kaddara lawal idan har ni ban kira
aurenka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
google.com, pub-9213700357025247, DIRECT, f08c47fec0942fa0