Showing 12001 words to 15000 words out of 62089 words

Chapter 5 - Aure Da Karatu Book Complete Rumaisa Sidi

Rumaisa   

18 Jul 2026

533

tsaya wannan keken ma ba tawa bace hayarta nakeyi shiyasa nake
ganin kamar tarayyarmu bazata yuba saboda ke kam sam baki saba da wahala ba"

Wani irin tausayinshi ne ya lullubeni "saboda kana talaka kake tunanin bazaka sameni ba ko
kuma saboda bazaka iya yakin neman soyayyata ba?" murmushi yayi "zan iya gimbiya indai har
kin bani dama wallahi zan iya" mikewa nayi ina gyara gyalen abayar da ke kaina "Allah yaba
mai rabo sa'a"

Aiko daga lokacin lawal ya dunga balbalemin zuciyata ya hanamin sukuni da zazzafan
kalamanshi da suka sa nakejin zan iya komai a kanshi soyayyata da lawal ta canjamin rayuwa
sosai ada duk abinda zanyi to zanyi shine da sanin Ummi amma a yanzu wani abun kafin ma
ummi taji lawal yaji sannan ada can baya duk wanda zai hadu da ni to saidai mu hadu a
gidanmu amma sabanin lawal da har yanzu bai taba shigowa gidanmu ba duk haduwar da za
muyi saidai makaranta

Babban kuskuren da na fara yi shine gwada siyawa lawal sutura domin shima ya rabuda
wayannan kayan da yake sakawa kullum duk dan abinda nasan zai bukata ina siya in bashi
batare da nayi duba da shi ya dace ya kyautatamin tunda nake dashi bantaba sanin wata
kyauta ta hadani dashi ba kuma bantaba damuwa ba don ba shine gabana ba
Kwatsam mai gidan lawal ya karbe napep dinshi bansan abinda ya hadasu ba amma lawal ya
gayamin bazai koma wurinshi karbar napep din ba ya shiga damuwa sosai saboda da ita ya
dogara da ita yake ciyadda 'yan uwanshi da mahaifiyarshi nima na shiga damuwa da tunanin
hanyar da zanbi in taimaka mishi don bazan juri ganinshi a wannan halin ba








Soyayya ruwan.............í ľí´”







Comment & share pls🙏

AURE DA KARATU
NA
RUMAISA SIDI



Page 10

Numfasawa nayi tareda duban maman haidar da ta kashe kunne tana saurarona "kinsan wani
abu wai " kanta ta girgizamin alamun labarin ya fara tafiya da ita numfashi na kara ja

" daya daga cikin sarkar gwal dina na dauka batare da kowa ya sani ba saboda a dakin ummi
suke can take a jiyar su na lallaba na dauko saboda nasan idan na tunkari Abba ko su yaya da
bukatar manyan kudi za su tuhume ni ne kawai ni kuma a yanzu ban shirya bayyanarda lawal
gidanmu ba nafison sai ya dawo hayyacinshi yanda ba zai samu wata matsala ba
Lokacin da na bashi sarkar fada ya dingamin tareda nuna min shi bazai karbi abina ya siyar ba
nikuma kamar sakarya na shiga lallabashi harda kukana ina rokon ya karba indai har dagaske
yana sona dakyar ya karba da sharadin bashi ne zaiyi kokari ya biya ni nace na yarda (hmmmm
har yau ba'a biyani ba)
Kaitsaye hafsat ta nuna rashin goyon bayanta akan soyayyarmu tareda min barazanar zata
samu ummi ta gayamata ba karatu nakeyi ba soyayya nakeyi aiko ba karya ta fada ba don a
yanzu ba yaren da nake ganewa idan ba yaren lawal ba " haba zee da ajinki da komai ki tsaya
kina kula wannan ? me na sama yaci bare ya jefowa na kasa ko haka zaku zauna abinki ya
kare akanshi kullum yazo ko kunya bayaji shi bai kawo miki komai ba amma idan kika siyo abu
kika bashi yana iyayi zai karbe haba zee wallahi jira kawai nake yaya abbas ya dawo daga
tafiyar nan da yayi ya dawo makarantar nan in gani shin zaki cigaba da abinda kikeyi wallahi
baki dace da wannan kazamin ba"

Wani irin zafi kalaman hafsat suka min domin zan jure ta zageni ta gayamin duk abinda zata
gayamin amma bazan juri ta aibanta NISFUL-HAYAT a gabana ba "ya isheki malama cin fuskar
ya isa haka" na fada cikin hargowa ina kara matsawa kusa da ita "Ke kin isa ki gayamin yanda
zanyi rayuwata ko ke zaki gayamin wanda ya dace na kula? tun farkon tarayyata da bawan
Allah nan baki taba furta alkhairi akansa ba kuma da kike kiranshi talaka a haka nakeson abina
kuma a haka naji zan iya zama dashi kije kiyi rayuwarki yanda kike bukata nima nayi tawa
period" na fada tare da zarar jakata nafice daga makarantar tareda jin haushin hafsat sosai duk
da kawatace tun a secondary kuma duk abinda zanyi taga bai dace ba zata bani shawara na
gyara amma yau sai na kasa duba abinda take kokarin nuna min


Tsaye nake a gaban madubi ina kallon kaina so nake na hango kyawun da kullum lawal ke kiran
inada shi nasan ni kyakkyawace duk da kasancewata wankan darza amma ni kyakkyawace
kuma inajin hakan a gurin mutane musamman ya bashir to amma yanda lawal din ke fada ya
banbanta da saura hirar mu na tuna ta dazun " wallahi my zee tunda nake kallon fina-finai daga
bakar fata ke har turawa zuwa indiyawa bantaba ganin tsarin halitta irin taki ba wallahi ke
kyakkyawace kuma ke ta musamman ce kyawunki na dabanne musamman idanunnan naki
masha Allah gaskiya dole na kara kaimi kar late comer yazo yamin abinda ya saba nidai rokona
ki rikemin alkawari kar ki jefa zuciyar marayan Allah a wani hali don Allah" lumshe idanuna nayi

ina murmushi tare da tuna zazzakar muryarshi

"Kanki daya kuwa zee" naji muryar anty halima da ta kwana biyu a a bayana juyowa nayi ina
kallonta har yanzu da murmushi a fuskata " bakomai anty" itama murmushin tayi " ki gayawa
wani ba komai amma bani ba kidaiyi a hankali karki zauce kuma wallahi ki wuce ki kwanta tun
ummi bata shigo ta ganki gaban madubi a tsaye kina murmushi ba takai ga hasaso abinda na
gane" isa nayi nima kan gadon na kwanta ina jan abin rufa tareda kokarin rufe jikina " wai baki
yarda ba komai ba " " na yarda mana ai shiyasa naga dazu kin lake daki kina waya" ta fada
batare da ta juyo ba shiru nayi da bakina gudun in ballowa kaina ruwa


Soyayyar lawal ce ta kawo rashin jituwa tsakani na da hafsat domin kullum kokarin nunamin
aibun lawal take ni kuma banaso ita kuma taki fahimta wannan yasa na fara ja baya da ita
itama sai tayi fushi ta daina kulani ni kuma ban wani damuba saboda lawal ya zamemin
madadinta domin ya siye babbar waya a 'yar sana'ar da ya fara da kudin da nabashi yace akwai
haske sosai samuwar wayar sai muka kara dinkewa da rana muna tare a makaranta da dare
muna makale a waya
Abinda na kasa tsayawa in tantance shin wace sana'a ce yakeyi da kullum muna tare kuma bai
taba gayamin abinda yake siyarwa ba nima bantaba yunkurin sake tambayarshi ba saboda a
ranar da na tambayeshi fushi yayi tare da cewa saboda yana kudina nake tambaya shiyasa tun
farko baiso karba ba
Kwatsam yaya Abbas ya dawo daga tafiyar da sukayi washe gari ya shiga makaranta kuma a
daren ranar maganar lawal ta dira kunnen iyayena da kuma yayyena

Jin muryar ya abbas yana kwallamin kira cikin hargagi yasa hankalina ya tashi duk da yanada
fada amma hakan bai taba faruwa tsakaninmu ba agogo na kalla karfe 9:07 irin wannan lokacin
kowannensu yana bangarenshi to me kuma ya kawo su uzuri na bawa lawal da muke waya kan
zanje in dawo a tsorace na fito
Ya Abbas ne a tsaye jikinshi har tsuma yake sai abba dake zaune da ummi da kai duka ma
mutanen gidan ke har anty halima isa nayi gabanshi na durkusa saboda yanda naji kafafuna
sun fara rawa tun daga kan irin kallon da yakemin dakyar nasamu kwarin guiwar furta " gani
yaya"
" ka zauna abbas sannan kuyi magana" abba ya umurceshi sanin halinshi ko wane lokaci zai iya
rufeni da duka ajiyar zuciya ya shiga saukewa sannan ya watsomin idanunshi masu firgita mai
kunnen kashi irin nawa " me kika ce mana zakije kiyi a makaranta ?" ya watsomin tambaya
tareda tsareni da idanunshi saina samu kaina da rashin gane inda zancenshi ya dosa saida ya
dakamin tsawa " dake nake magana nace me kika ce zakije kiyi a makaranta " cikin rawar jiki
na amsa ina kara matsawa baya " Karatu"

" to da kikaje karatun kikayi" nanma shiru nayi "wallahi idan na sake maimaita miki magana
saina sauyamiki fatar fuskarki da mari " karatun......na...yi" na fada a rarrabe " wayarshi ya janyo
tareda budewa ya dagota yana nuna min " waye wannan" kaina na daga tsuwwwwwww cikina
ya shiga wani kalar kida kamar an kunna disko " na shiga uku tawa ta kare" na fada a raina taya
zan cewa yaya nasanshi ai kasheni kawai zaiyi " idan kika sake kikamin karya wallahi sai na
karya miki hannu zainab" ya tare numfashi na daga karyar dana kammala shiyawa a raina

Hannuwana na hade guri daya "don Allah kayi hakuri yaya wallahi bazan sake ba"
" ka mata a hankali Abbas" yaya isma'il ya fada matsowa yayi yana kallona "meye alakarki da
shi? ki fada karkimin karya" Kallon ummi nayi da ta zubamin ido tana kallona kallon mamaki da
kuma tsoro " wai sona yake yaya" na fada cikin sakalci " sonki yake kuma bazai zo gidanku yayi
magana da ke ba saidai makaranta zainab? wannan wane irin sone kenan ba karatun kike ba
ko" kaina na girgiza hawaye na min zuba " Wallahi inayi yaya"

Mikewa ummi tayi tabar falon abinda ya kara tayarmin da hankali hakama ya abbas sai yaya
isma'il da ya tsaya yimin nasiha tareda nunamin kuskurena da kuma yimin jan kunne kan kar in
kara in rabuda wannan mutumin saboda duk wanda bazai zo gidanku nemanka ba to ba
kaunarka yake ba karin tashin hankalina abba ma baice komai ba
Kuka na dingayiwa anty halima da muka koma daki tareda rokonta ta tayani neman gafarar su
ummi itama nasiha ta shiga yimin tareda nunamin kuskurena muna cikin maganar lawal ya
kirani wani haushinshi naji saboda yanda ta silarshi iyayena suka shiga damuwa kin dagawa
nayi da naga ya isheni da kira na kashe wayar gabadaya







RUMAISA SIDI✍️✍️✍️✍️✍️✍️


Shin an rabu kenan ko ana nan tareí ľí´”

AURE DA KARATU
NA
RUMAISA'U SIDI

Page 11



Washe gari anty halima ta jagoran ce ni wurin ummi na ba ta hakuri haka ma abbana dukansu
nasiha su ka min tare da nuna min kuskuren abinda na aikata duk na ji na tsani kaina da
wannan damuwar da na jefa su har na isa makaranta ba lakka a jikina kuma har lokacin ban
kunna waya ta ba ban iya tuƙa kaina ba ranar saidai driver ne ya kaini
Inda na hango hafsat can na nufa sallama na ma ta kallona ta yi sannan ta amsa "lafiya na
ganku a waje na É—auka ma an shiga lecture" na tambaye ta ganin lokacin lecture É—in ya kama
"kinsan halin malamin wataƙila ma bazai zo ba" gefenta na zauna "ai ko da bai kyauta mi ni ba
wallahi ko lafiya banji a jikina amma haka na zo saboda sanin rashin mutuncinshi" sannu ta
shiga min tare da tayin soyayyar farar da take ci "girgiza kaina na yi ina ya mutsa fuskata "ke
kam hafsa Allah ya shiyaki da shegen kwaÉ—ayi wallahi" lumshe idanuwa ta yi tare da buÉ—e ido
É—aya "bakisan daÉ—i bane malama fara ai ita ce kazar talaka" duk da yanda nake jin zuciyata
amma hakan bai hana ni darawa ba kamar wadda ta tuna wani abu ta É—an dubeni "na manta
kinyi baƙo yace ki same shi inda ku ka saba haɗuwa" daga haka ta kulle bakinta gam tunani na
shiga yi a raina naje ko kar naje daga ƙarshe na yanke shawarar zuwa domin na dakatar da shi
da zuwa gurina don banason abinda zai haÉ—ani da iyayena


Tun daga nesa na hango shi ya na kaiwa da komowa a wurin da ya zama kamar mallakinmu a
makarantar har na kusa isa wurinshi baisan na iso ba sallamar da na mishi da ƙarfi ya waigo
tare da yi cikina kamar wanda zai riƙe ni ajiyar zuciya ya shiga saukewa kamar wanda yayi tsere
"nagode Allah ba abinda ya same ki" wani tausayinshi ne ya shiga tsargamin a zuciya wurin
zama na nuna mishi a sanyaye na ce "ka zauna muyi magana don Allah" zama yayi kamar
yanda na ce nima na zauna na É—au mintuna ina tunanin ta inda zan fara "me ya faru my zee? ko
bakida lafiya?" kaina na girgiza mishi sannan na yi ƙundunbala na fara magana "kayi hakuri
soyayyar mu ba za ta yuba" tsaye ya miƙe yana kallona kamar mai in-ina ya fara magana" Ba
bangane me...ki ke cewa ba"

Kallonshi na yi da idanuwa na da suka cika da ƙwalla hannuwana na haɗe guri ɗaya "don Allah
kayi hakuri abinda zan iya cema kenan" daga haka na miƙe tare da ƙoƙarin barin makarantar
ma gaba É—aya maganar shi ta dakatar da ni "dama an gayamin hakan za ta faru a tsakaninmu
amma na ƙi yarda kinsan ba za mu ci gaba da soyayya ba meyasa ki ka sabamin da soyayyarki
meyasa za ki min hakan laifin mi zuciyata ta miki da ta cancanci wannan hukuncin daga gareki?
saboda kawai na so ki? ko don ina talaka?" kuka na fashe da shi tare da durƙushewa a gurin na
kasa bazan iya ba lawal rayuwata ne wallahi bazan iya ba shima hawaye ya ke gabana ya duƙa
ya na kallona "kiyi hakuri zainab ki gayamin abinda ke faruwa" kamar sakarya na kwashe komai
na gayamishi "ki kwantar da hankalinki insha Allah wannan bazai zamo sanadin rabuwar mu ba
kinji ki kwantar da hankalinki"

In taƙaice miki lawal bai bar makarantar ba saida ya tsaramin kalaman da suka saka naji bazan
taɓa iya rabuwa da shi ba daga ranar kuma mu ka canja wurin haɗuwa saboda gudun ya abbas
ya ganmu a makarantar ashe ba haka kawai ya abbas ya sakeni ba yana lura da kowane
motsina ranar da ya damƙoni a wurin da muka haɗu da lawal ranar yamin dukan da bantaɓa
tunaniba ba kukan dukan da yakemin nake ga a'a kukan rashin sanin halinda lawal ya ke ciki
nake saboda tun a can ya damƙashi ga ƴan sanda ga kuma ummi da naga hawayenta na zuba
nasan duk saboda ni ne

Faruwar wannan abba ya dakatar da ni daga zuwa makaranta ya kuma karɓe wayata bansan
yanda aka yi ba ranar sai ga lawal a gidanmu nidai na yi mamakin daga abba har ya isma'il ba
wanda ya fita har wata rama na yi saboda tashin hankalin da nake ciki kowa ya janyemin a
gurin anty halima kawai na ke samun sauƙi bansan wucewar lawal ba saida abba ya aiko a
kirani

Dukansu suna nan falon abba har ummi gabansu na je na duƙa tare da gaishe su kamar kullum
ba wanda ya amsamin idanuwana da suka bushe kan kuka na lumshe abba ne ya fara magana
"Allah ya sa ni tun tasowar ki da kuma shaƙuwar da ke tsakanin ku na kwaɗaitu na haɗaku aure
ke da yayanki bashir to amma na fahimci hakan bazai sa mu ba saboda wasu sababbin halaye
da kika tsiro da su a ƴan watannin nan bazan so haɗin aurenku ya zama silar taɓuwar zumuncin
mu ni da 6ar uwa ta ba" Numfasawa yayi alamar abin bai mishi daÉ—i ba"Na kira wanda kike so
munyi magana da shi ya je ya shiryo ko gobe ya tashi ya zo a É—aura mu ku aure"

Wata irin zabura na yi kuka na ƙwacemin "Aure kuma abba wallahi ni ba yanzu zanyi aure ba
don Allah ka yi hakuri" ɓallina ya abbas yayi da ƙafarshi da ke kusa dani "za ki mana shiru ko
sai na make ki ai duk hukuncin da aka miki ke kika ja" sannan ya dubi abba "Abba aura ma ta
shi damuwa ce a rayuwarta na gayama nayi bincike kan yaronnan bayada wata sana'a sannan
mahaifinshi ya rasu shi kaɗaine namiji a taƙaice ma har yanzu gidansu ake ciyadda shi saboda
bayada hakuri duk inda yaje" hannu abba ya É—aga mishi "haka ta ke son abinta abbas damuwa
ba ta wuce na zuba musu ido suna zaɓar wurin da su ke son haɗuwa ba wata rana zanga
abinda bama fata shi arziki na Allah ne indai tana son mijinta duk halinda ta tsinci kanta za ta
jure"









Ayi haƙuri da wannan

AURE DA KARATU

NA
RUMAISA'U SIDI




Page 12


Tun daga faruwar wannan karatuna ya tsaya na daina zuwa makaranta ke ba makaranta kaÉ—ai
ba duk wata fita abba ya dakatar da ni daga yinta a kuma lokacinne yaya bashir ya fito da
ƙudirinshi a kaina a lokacin ya diro sokoto da ƙoƙon barar neman soyayyata kai tsaye na
bayyana mishi ina da wanda nake so faɗar tashin hankalin da ya shiga ɓata bakine
A wannan lokacinne kuma ummi ta magantu tun fara magana ta da lawal É—akinta ta ja ni" kiji

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
google.com, pub-9213700357025247, DIRECT, f08c47fec0942fa0