Showing 30001 words to 33000 words out of 62089 words
yaƙi matsalata da ƙarfin
addu'a da yardar Allah.
Tsaf na shirya domin ina so yau in shiga makaranta a falo na sami ummi tare da yi mata
sallama.
Ina tuƙi naji wayata ta yi ƙara ban ɗauka ba saboda akwai ni da tsoro in dai har ina tuƙi to bana
ɗaga waya sai in wayar daga Ummi ne ko su Yaya to shine zan yi parking sannan in ɗaga.
Sai da na isa makarantar ban fita daga mota ba na duba ashe Hafsat ce ƙawata ta amana
murmushi na yi tare da danna mata kira
"Uwar gida a gidan Dr"
"Kuma Amarya ba,Faɗi ki ƙara nice dai ba wata" dariya na yi "Allah ya shirya ki,na ga kiranki ina
tuƙi"
"Eh wallahi kwana biyu na jiki shiru,ya su Safwan"
Numfashi na sauke "Su Safwan suna can tare da mahaifinsu"
"Ban gane ba, to ke kina ina?
"Ina makaranta Hafsat bari idan na koma gida zan kiraki mu yi magana"
Sallama na yi da ita sannan na wuce in da muke ɗaukar darasi.
Sai da na koma gida na kira Hafsat ina faɗa mata abin da ya faru
"Amma wallahi mutuminnan ya ji daɗin shi,ki kwantar da hankalinki In sha Allah hakan shine
mafi alkhairi a gare ki,Ki na kammala idda za ki samo mana wani handsome.Allah na tuba ban
da ma ƙaddarar aure ai ke ba sa'ar shi ba ce"
"Ni fa yanzu Hafsat na cire wani aure a raina,ki dubi ko Lawal yadda muka buga soyayya da
shi,amma dubi yadda abin ya ƙare.Ni dai kawai karatuna na ke so na kammala"
Tsaki Hafsat ta buga "To saboda Lawal za ki cire hope ɗin miji na gari? Ayi sha'ani kawai
Hajiyata.In sha Allah kwanannan zamu shigo sokoto da na dawo za ki ganni"
Wuraren ƙarfe 5:00 sai ga Amna ya kawo tare da kayanta.Bai shigo gidan ba Baba mai gadi ne
ya shigo da ita,na yi farin ciki sosai da dawowar Amna wurina duk da dukansu na so,saboda
bansan ya rayuwar su zata kasance ba.
Da dare muna tare Amna na bani labarin ruwan da suka sha a matsayin breakfast na tausaya
musu sosai shi ya sa da safe da zan kaita makaranta na dafa abinci har su Aysha.
Ko da na isa makaranta su Safwan ba su je ba parking nayi ina jiran zuwan su.Sai 8:30 sannan
ya shigo kamar wani almajiri ya na jaye da hannun Aysha Safwan na gefen shi.Har yaran suka
shiga ina kallonsu sai bayan sun wuce nima na dawo.
Kuyi haƙuri yau biki muke yi ku karanta wannan kafin gobe
*Na gode sosai*
*RUMAISA'U SIDI✍️✍️✍️*
*AURE DA KARATU*
*NA*
*RUMAISA'U SIDI*
*FARAR ANIYA WRITERS*
*Page 23*
Tsaftataccen zawarci na keyi saboda sam Ummi ba ta bari na yi wata shiga da bata kamata
ba,duk abin da nasan bai kama ce ni ba ban yin shi.
A kwana a tashi har na kammala iddata na ci gaba da sha'ani na,yarana suna zuwa duk lokacin
da suka buƙaci hakan sai dai ba yanda nakeso na ke ganin su ba,daƙyar su ke komawa idan su
ka zo.
A kwanakinnan duk fitar da zanyi to sai wani ya biyo ni,tun ina damuwa har na ƙyalesu na shiga
sabgata don ni yanzu lamarin rijalu tsoro ya ke bani.Musamman wani maƙale matan lecturer
abokin ya Abbas da ya ke damuwata.Ni dai saidai in saurare shi kawai domin ni yanzu kalaman
soyayya sun daina tasiri a zuciyata.
Yajin aikin da aka tafi a makarantar mu yasa na yi shirin zuwa Kaduna wurin Gwaggo na.Wurin
Ummi na bar Amna saboda su basu yi hutu ba.Na so inje da ita to amma su ma suna gab da
fara exam.
Driver aka haɗa ni da shi saboda Ya Abbas yace bai yarda na yi tuƙi har Kaduna ba.
Cikin zumuɗi na shiga falon ina ƙwala kiran Gwaggona "Miƙewa ta yi daga zaunen da take da
wannan murmushin ƙauna da ke kasancewa a fuskarta duk lokacin da muke tare hannuwanta
ta buɗe min alamar nazo gareta.
Da sauri na ƙarasa tare da shigewa jikinta ina jin wata ƙaunar ta ta musamman "Tun ɗazu nake
dakon isowar ki,yayanki ma da wuri ya dawo office yana jiran isowar ki"
Sakin ta nayi ina raba idona a falon "To ina Yayan,shine kuma bai jira ni ba?
Hannuna ta ja ta kaini ga kujera "Yanzunnan ya shiga sashenshi,amma tunda ya san kina
hanya yanzu zai dawo"
Kitchen ta wuce bata jima ba sai ga ta tafito tare da mai aikin ta,kaya aka shiga jerawa a
gabana kamar wata sarauniya.
Shagwaɓe fuska na yi "Gwaggo hutawa zan fara yi sannan in ci abinci,wallahi bacci na ke ji"
Hararata ta yi "Zaman awa nawa kika yi? kisha ko ruwane sannan ki je kiyi wanka kizo ki ci
abinci"
Lemun da ta zuba min na kurɓa tare da sanar da ita a kaiwa driver ahinci yana waje don juyawa
zai yi.
Ɗakin da zan sauka ta kaini,komai an gyare tsaf.Wanka na yi tare da ɗauro alwala kaya na saka
mara nauyi.Gyara kwanciyata nayi kan daddumar da nayi sallah ina jin yadda ƙassan jikina ke
amsawa na gaji sosai.
Wayata na tuna da ita,tashi nayi tare da buɗa hand bag ɗita na ɗakko.Missed calls na samu na
Ummi da su Yaya bansan me ya hanani jin ringing ɗin wayar ba.
Number Ummi na danna "Kin kyauta Zainab,wato daga zuwa wurin dije har kin manta da ni ko?
Zama na yi gefen gadon ina bata amsa "Haba dai Ummina,kema kin san ba yadda za'a yi in
manta da ke koda na second ɗaya.Ba uwa irinki ake mantawa ba Ummin Zainab"
Ina jin sautin murmushinta ta wayar "Allah ya shirya min ke Zainab,kun sauka lafiya ina dijen?
"Lafiya lau muka sauka Ummi,gwaggo ma tana lafiya" na faɗa ina kallon Gwaggo da ta shigo
ɗakin.Matsowa ta yi kusa dani suka gaisa da Ummi tana tsokanar ta na har ta fara kewata.
Jin Ummi na neman kashe waya yasa na cire kunya na tambayeta Amna
"To rasa kunya,ƴar ki na wurin su Nihal ki kwantar da hankalinki ko kewarki ma bata yi ba"
Sallama muka yi tana jaddadamin na kira yayyena sun damu da rashin ji na" Sai da na kira su
muka gaisa sannan na fita falon.
A falon na sami Yaya Bashir da Gwaggo da kuma Sister Zubaida matar Yaya Bashir
"Na yi fushi tunda sai yanzu za ka zo tarbata"
Hararata yayi "Haka ma zaki ce,bayan kinsa na baro office tun ban tashi dawowa ba,hala dai
tata drivern yayi?
Dariya na yi sannan na dubi Matar tashi "Sannu Anty Zubaida,Na same ku lafiya,ina Takwara
ta?
Abin mamaki sai naga ta ɗauke kanta duk uwayen tambayoyinnan da na mata cemin kawai ta yi
"Lafiya" daga haka ta rufe bakinta gam.
Zama na yi kan kujera,miƙewa naga Ya Bashir yayi ya fara ƙoƙarin haɗamin abinci "Wai me
zaka yi?
Na tambaye shi ganin abinda ya ke shirin yi " Abin da annabi ya umarce mu da muyi,mu
karrama baƙin mu.Shi ya sa zan zuba miki"
Matar shi na kalla da ta kafa mana ido,plate ɗin na karɓe daga hannunshi "Ka bar shi zan zuba
da kaina,ai ni na wuce ka kira ni baƙuwa Yallaɓai"
Har na kammala cin abincin ina jin idanun matar shi na yawo a jikina,duk hirar da muke yi ko
ɗaya bata saka bakinta ba,ban jima ba na musu sallama kan zanje in kwanta.
"Ina gayyatar ki karin kumallo a gidana da safe"
Waigowa na yi na dube shi "To sannu masu gida,gayyata bata karɓuba" na faɗa ina ƙoƙarin
shigewa ɗaki,ban daɗe da shiga ba,bacci ya ɗauke ni.
*WASHE GARI*
Tunda na yi sallah na koma bacci saboda gajiyar da nake jin har lokacin bata fita jikina ba.Na
daɗe ban yi irin tafiyar nan ba,auren Lawal ya hana mini zuwa ko ina iya kata kula da shi da
ɗiyanshi.
Sai ƙarfe 9 na tashi shima ba don na gaji ba,wanka na yi na zuba doguwar rigar abaya ta ban
damu da shafa komai a fuskata ba saboda tun dama ni ban cika yin kwalliya ba.
Ban samu Gwaggo a ɗakin ba shi yasa na wuce bedroom ɗinta a can na same ta gaida ta nayi
ta amsa tana tambayar yadda na kwana
"Tun ɗazu yayanki ke yawo nace baki tashi ba,kuma ba za a tada ki ba.Muje ki gaida Abbanku
jiya ko da ya shigo kin yi bacci,sannan ki wuce ɓangarenshi tun bai dawo min neman ki ba"
Sai da muka je na gaida Abba dattijon arziki,cikin nuna ƙauna muka gaisa da shi yana tambaya
ta su Safwan.
Na fito ɓangaren Abba na hangeshi tafe,murmushi na yi tare da tsayawa wurin da nake "Kin
wahalda ni da yawa Zainu,tun ɗazu kin hana mu cin abinci ni da madam"
Girata ɗaya na ɗage "Na hana ku cin abincin ne? Kuma ai bance muku nayi accepting wannan
IV na cin abinci ba"
Hararar wasa ya min "Wallahi ba ki isa ba,ko kina ci kina amai sai kin ci shi,baki isa ki hana
matata cin abinci ba sannan kice ba za ki ci ba"
Jerawa muka yi har ɓangaren nashi yana tambaya ta makaranta ina bashi labarin yadda abin
ke tafiya.
A ƙofar kitchen muka samu madam ɗin Ya Bashir da alama magana ta ke da mai aikinta,kallo
ɗaya ta min ta kawadda kanta.
Ina kwana na mata tare da isa ga Zainab da ke wasa a tsakar falon,ƴar Yaya Bashir wadda ya
min takwara shekarar ta 2 yanzu,bayan haihuwar Amna yayi aure,shima saida suka shekara
sannan aka samu cikinta.Dariya ta shiga ɓingilamin tana min gwaranci kallon Yaya Bashir da ya
zuba min ido na yi.
A bazata na ji maganar shi "Wallahi yau na ƙara ganin kamanninki da sweet heart da kullum
Mama ke faɗa,kamar ke kika haifeta"
"To da wa ya haifeta? Ni na haife ki ko Zainab" kamar ta san abin da nace ta shiga ɓingilamin
dariya tanawa ubanta gwaranci.
Dinning ɗin da aka shirya muka nufa ina ɗauke da Zainab abin mamaki matar gidan ma
kamewa tayi a kujera tana ƙwalla kiran mai aiki ta zo tayi serving ɗinmu.
Miƙewa nayi ina cewa ta barshi ni zanyi,ita na fara zubawa sannan na zuba mishi na zuba wa
kaina.Zama na yi ina ci ina baiwa Zainab da ta maƙale min kamar ta saba da ni.
Saida na kammala na tashi na koma falo tare da Zainab ina nan ya wuce sama yana cemin in
jirashi ya fito.
Ganin mutum kawai na yi a kaina tana girgiza jiki kamar wadda aka kunnawa disko "Bari kiji,
wannan ya zama na ƙarshe da zaki ƙara shigewa mijina ehe,ni dama tunda naji aurenki ya mutu
na san ba za ki barni na samu kwanciyar hankali da mijina ba,kin kashe aurenki nima kina
nema ki kassaramin nawa,to nikam mijina yafi ƙarfinki saidai na wata don................"
"Keeeeeee......." ya daka mata tsawa yana saukowa daga matattakalar benen da zata sadaka
da ɗakinshi.Nuna yi yayi
"Kin san muhimmancin ta a wurina? Kin san alaƙa ta da ita da za ki zo kina faɗa mata
maganganu akan wani banzar haukanki da kike kallo a matsayin kishi"
Ƙara tubure wa ta yi kamar sabon kamu "Eh ai dama tare mata faɗa za ka yi,tun da ƙaunar ta
kake yi,ƙaunar da bata ma amfanin komai ba tun da ta tsallake ta ɗauki wanin ka saida ya gama
gurgunta rayuwarta za ta zo tana neman tarwatsamin farin ciki,wallahi ba zan yarda ba"
Kallon mamaki nake ma ta kishina ta ke kenan ƴarta na dire mata a kan kujera sannan na
tunkari ƙofa don wannan faɗan ba nawa ba ne.
Ganin yadda Zubaida ta ke da zafin kishi akan mijinta sai na shiga ja baya da shi duk da shi
sam ya ƙi fahimtar hakan,a wurina Zainab ke wuni mun saba sosai da ita duk da mahaifiyar ta
bata ƙaunar hakan.
Ina kitchen muna haɗa abincin dare ya shigo "Tunda na jiyo wannan ƙamshin na san kece a
kitchen ɗin" Murmushi na yi "Kenan girkina har wani ƙamshi ne da shi na musamman"
Shigowa ya ƙara yi kitchen ɗin tare da haye gefen cabinet ɗin "Ai tun kina ƴar ƙaramar ki nasan
ƙamshin girkinki,kamar na Ummi haka ya ke,don haka yau bazan bar kitchen ɗinnan ba sai an
kammala an zubawa ɗan almajiri" Aikina na ci gaba da yi muna ƴar hira shima ya na riƙe da
wayarshi ya na latsawa.
Kamar wadda aka jefo ta shigo kitchen ɗin raba idanuwanta ta shiga yi tsakanin Ni da Shi
"Me kake yi a kitchen" ta tambaya kamar itace mijin shine matar "Laifine don kin same ni a
kitchen ɗin mahaifiyata?
"Ai da can baka shigowa sai yanzu da aka shigo da kai" ta ƙarasa tana bankawa bayana harara
"To kenan kema shigo da ke aka yi"
Tsaki ta yi wanda a ɗan zaman da muka yi na fahimci ɗabi'ar ta ce" Ka tashi mu je an kammala
haɗa abinci" hannunta ya jawo "Yau girkin Zainab za mu ci,kiji kema ki huta da ganin laifina idan
ina baki labarin yadda na ke santin girkinta"
Ba tare da na waigo ba nace "Gara dai ka je ka ci wanda aka saka da kai don wannan babu
rabonka a ciki"
Hannunta ta ƙwace "Allah ya kiyaye ni,kaima kuma ba za ka ci shi ba" ta faɗa tana jawo shi
kamar wata mai ƙarfi,ganin haukar ta ta fara yawa yasa ya daka mata tsawa "Wai ke a komai
sai kin yi hauka?
Nan ta ke idanuwanta su ka tara ƙwalla "Ai dole kace min mahaukaciya tunda ga ƴar so a
gabanka,ni kuma matar cushe ce,wallahi tun mutuwar aurenta ban ƙara samun bacci mai daɗi
ba saboda nasan abin da ke tunkaro ni"
Girkina na sauke sannan na bar kitchen ɗin ita ma bayana ta biyo tana ƙara sautin kukanta
kamar wata ƙaramar yarinya.
"Lafiya Zubaida"Gwaggo da ke fitowa daga bedroom ɗinta ta tambaya.Nuna ni ta yi "Tun da
wannan ta zo ya canja min Mama,komai za. a mishi sai dai yace ita za ta mishi,yanzu ma abinci
na haɗa mishi wai ba zai ci nawa ba na ta zai ci"
Kallon tuhuma ta mishi "Zo ku wuce,ba za ka ci min abinci ba kuje ku ci wanda kuka girka" Kaɗa
su ta yi suka tafi sannan ta same ni a ɗaki ina zaune kamar mai tunani
"Kar ki damu da Zubaida har yanzu akwai sauran ƙuruciya a cikinta,kuma ban cika son saka
baki a lamarin aurensu ba tunda mahaifiyar ta bata ganin laifinta idan nayi magana kuma Alhaji
zai ga dan ta na ƴar ƙanwar shi yasa na ke haka, amma shi kanshi ba daɗin zama ya ke ji da ita
ba.Matar da bata san ta shiga kitchen ta girkawa miji abinci ba ai muna mata ce"
Numfashi na sauke "Allah hay kyauta,bari in zubo miki abincin" Na faɗa tare da miƙewa nabar
ɗakin.
Duk kishin matar shi baisa ya fasa abin da ya ke min ba,ganin ina neman haɗa rigima ya sa na
fara shirin barin garin.
"Yanzu ke Zainab har kin gaji da zama kusa da ni,ko dai wani abu aka miki"
Kai na na girgiza "A'a wallahi gwaggo ni ba abin da aka min sai alkhairi,kuma na ji daɗin zama
tare da ku"
"Kar ki yarda da ita Mama,kawai dai wani bazawarinta ne yayi kewar ta shi yasa ta ke son ta
koma ya ganta" ya faɗa yana tsare ni da ido
Murmushi ta yi "Dagaske Zainab surukina ne ya damu?
Fuskata na rufe da tafin hannuna "A'a wallahi,ni ba wani bazawari da nake kulawa"
"Ai ko gwanda ki kula,don ba za mu zuba miki ido a hakan ba.Miji za ki fitar musha biki don
haka tun yanzu a cikin masu nemanki ki darje ki fiddo ɗaya.Ko Abbas kwanaki mun yi maganar
da shi yace har da wani abokinshi ke son ki"
Ajiyar zuciya na sauke "Ku ci gaba da taya mu da addu'a Gwaggo,In sha Allah zan fitar.
Ina ɗaki ina shirya kayana domin gobe da sassafe na ke son tafiya naji ƙarar wayata,Ya Bashir
ne ɗagawa na yi tare da sakata hands free na ci gaba da aikina
"Wai dagaske tafiya za ki yi Zeen Abba"
Wani abu na ji ya tsirga min jin sunan da ya kira ni da shi bayan tsawon lokaci,na tafi wata
duniyar na ji maganar shi a kaina "Zainab" Ya kira ni kai tsaye "Na'am" na amsa cikin sanyin
murya
"Zainab yanzu ma bari za ki yi in rasa ki?
Ya tambaya kamar zai yi kuka "Ban gane ba" na faɗa ina dakatawa daga ƙoƙarin rufe jakar da
nake yi "Kin gane komai Zainab,ba abin da baki gane ba,sai dai ina son ki sani bana jin wannan
karon zan haƙura ina kallo wani namiji ya ɗauke ki.Haba Zainab ki taimaka min mana,tsawon
shekarun nan ina