Showing 18001 words to 21000 words out of 62089 words

Chapter 7 - Aure Da Karatu Book Complete Rumaisa Sidi

Rumaisa   

18 Jul 2026

517

ya kammala
sannan ya tashi yana gyatsa ya kwashe kayan ya wuce ɗakinshi da kallo na bishi ina kissima
yanda zan rama abinda ya min saboda na sanshi tun dama ba dai kwaɗayi ba duk abinda
yasan zaiyi ɗanɗano to yana ƙaunarshi "nasan maganinka" na faɗa a fili tare da tashi na wuce
ɗaki

Duk abinda nasan zai ƙarawa girkina ɗanɗano ko ƙamshi saida na zuba shi a dahuwar
lafiyayyar kazata da nake wa farfesu harga Allah ban tashi cinta ba amma saboda lawal na
ɓanɓarota daga freezer na shiga mata haɗin da nasan ba'a bawa marowaci daga yanda ya fito
ya zauna falo nasan ƙamshinne ya fito da shi dama can hakan yake ko ya nake girki indai yana
ɗaki sai ya fito yace bazai iya haƙurin jira a ɗaki ba kamewa yayi a kujera yana canja channel
saida na ganshi sannan na shiga kitchen na zubo wa yara safwan na kira "ka ɗauka ku je ɗaki
ku ci" ba don komai na tura su ciki ba sai don za su iya canko wani abu zubawa nayi a wani
plate na ɗauka na nufo falon


Da gayya na yi saitin lawal kamar wurinshi zanje saida naje dab dashi sosai sannan na duƙa na
ɗauki remote ɗin da ke kan cinyar shi ƙiris ya rage dariya ta ƙwacemin ganin har yana ƙoƙarin
ɗaga hannunshi kamar zai karɓa ganin na goce sai ya fara muzurai yana raba ido ba ƙaramin
ƙoƙari nayi ba wurin taushe dariyata saboda nasan ƙiris ya rageyawunshi su zubo
Tun dama Allah ya sa mishi son kaza ni kuma na fi son kifi ina da tabbacin shiyasa ya min
abinda ya min jiya saboda har ga Allah kifin ya burgeni ga yanda aka gasa shi kuma nqce sai
na rama don yanzu na daina yarda ina bar mishi bashi da ya min zan rama na daina ajiyar
wutar damuwarshi zan riƙa fitarwa ta shafi kowa
Har na kammala suɗe dabgena ban ragawa komai ba kai hatta ƙassa ban ragawa ba sai
lumshe ido nake ina tanɗar baki a fili kuma ina faɗin "Allah ka ƙara mana lafiyar cin dajaja" tsaki
ya buga tare da tashi ya shige ɗaki dariya na tuntsire da ita har ina dafe cikina saboda yaban
dariya wallahi lawal ba dai kwaɗayi ba yaran nasa suka shirya na ce Amna taje ta ce idan
abbansu zai fita ya biya da su wurin mama saboda sun ɗan jima basu je ba

Ban ɗauka zai fita da su ba saida ya shiryo ya fito cikin dakakkiyar shaddarshi sai maiƙo ta ke
ya ce su fito hannu su ka shiga ɗagamin nima na ɗaga mu su har ya kai ƙofa ya ɗan dakata
batare da ya waigo ba yace "Nifa mashin zan hau ko napep"na fahimci abinda ya ke nufi ya
ɗauka tunda na haɗashi da yarana in bashi key ɗin motata yayi yanda ya ke so da ita kawadda
kaina nayi sannan na bashi amsa "ko a baro za ka tafi ai ba matsala bace yaranka ne kai ko a
ƙafa ka jasu dai-dai ne" bai ƙara yin magana ba yayi fuuuuuuu ya fita

Ina bedroom ɗina naji sallamar maman haidar sai yanzu ma na tuna da mun haɗu shekaranjiya
tace za ta zo nace kar ta zo ta bari sai yau kai wannan matar badai son gulma ba fitowa nayi
muka gaisa ta zauna a ɗaya daga cikin kujerun falon lemu na kawo mata sannan na zauna
gyara zamanta tayi tana fuskantata "tun lokacin da kika ban labarinki hankalina ya kasa
kwanciya inaso inji yanda rayuwar aurenku za ta kasance duba da irin soyayya da kuma
halaccin da kika nunawa abban safwan" dubanta nayi sannan na ɗan ya mutsa fuska "to ai ni
nama manta inda na tsaya" da sauri ta katseni "yanda rayuwar aurenku ta kasance keda abban
safwan" gyara zamana nayi sannan na ci gaba da bata labarin yanda rayuwar aurena ta
kasance

Da farko rayuwar auren mu da lawal..............












Hhhhhhhhhhh Allah sarki lawal😄


Shin kuma kun iya gulma kamar maman haidar😂





AURE DA KARATU

NA

RUMAISA'U SIDI


Page 15

Da farko rayuwar aurena da lawal rayuwa ce irin ta soyayya kamar yanda muka daɗe muna
tsarawa ina samun kulawa da kuma tattali daga gare shi zallar soyayya na ke gani a wurin
angona

Matsalar mu ta fara ne daga lokacin da garar da nazo da ita daga gidanmu ta ƙare buhu ashirin
mahaifina ya baiwa lawal tare da naira dubu ɗari na cefane a matsayin kayan GARAR AURE
na(littafina na farko) bayan an kai kayan gidansu buhu biyu ne kawai su ka shigo gidana bansan
inda sauran su ka shiga ba
Tunda naga kayan abincin sun yi ƙasa na gayamishi yace min zai siyo yau koda muka wayi
gari bamuda ko ƙwarar shinkafa a gidan yana ɗaki yana shiri na same shi gefen gadon na
zauna ina kallonshi "Nisful yau fa kayan abincin duk sun ƙare ko abin kari babu bale kuma

shinkafar da za mu dafa anjima"

"ohhhhhhhhh wallahi kina da matsala my zee ko jiya kin gayamin maganar nan nace miki zan
siyo da inada kuɗi zan ƙi siyowa ne? kina kallon yanda nake fita kasuwar nan haka nake
dawowa wallahi ni in banda mama bazan koma wurin mutumennan ba malam mutum don yana
ganin kamar kana ƙarƙashin shi sai an tashi kasuwa ya ɗauko wata banzar dubu biyu ya baka
kamar almajiri"

Raina naji baimin daɗi ba yanda naga ranshi ya ɓaci akan maganar da na mishi"kayi haƙuri
nisful ba wai don in ɓata maka rai yasa nayi maganar ba"miƙewa nayi na isa ga wadrobe ɗita
ƴar ƙaramar jaka na ɗakko a ciki kuɗin da ke ciki na fiddo za su kai dubu hamsin ko ma su fi
kusa da shi naje tare da miƙa mishi " ga wannan yaya mu'azzam ne ya bani su lokacinda za a
kawo ni gidannan ka siya mana koda taliya ce kafin ka samu"

Idanu ya ƙuramin sannan ya girgiza kanshi "bazan karɓi kuɗinki ba my zee saboda nauyin
ciyarda ke akaina ya ke ba a kanki ba na fara tunanin ko in siyar da mota ta in siya mana kayan
abinci saboda bazan juri ganinki a wani hali ba banaso kiyi nadama a aure na da kika yi"

Wata ƙaunarshi ce naji ta ƙara cikamin ruhi "duk abinda na mallaka naka ne nisful ka daina
tunanin sayar da motarka insha Allah komai zai dai-daita a shirye nake da naci duk abinda ka
kawo a gidannan kuma idan har kana ƙaunata kamar yanda kake faɗa to ka karɓi kuɗinnan"

Karɓa yayi ya shiga jujjuya kuɗin"ina ƙara gode ma Allah da ya bani ke a matsayin matata
nagode sosai matar rufin asiri Allah ya nuna min nima na kyauta ta miki fiye da yanda kike min"
wani daɗi ne ya lulleɓeni jin kyakkyar shaidar da nake samu daga mijina rakiya na yo mishi har
tsakar gidan sannan na koma falo
Ina ƙoƙarin zama na ji wayata da ke chaji ta na ringing sance wayar nayi tare da duba mai kiran
murmushine ya faɗaɗa a fuskata ganin number ummina na yawo akan screen ɗin da sauri na
ɗaga ina karawa a kunne

"Umminaaaaaaaaaaa"naja sunan sosai ina jin kamar nayi tsuntsuwa na ganni gabanta saboda
yanda nayi kewarta tun aurena banzo gida ba amsawa tayi na gaisheta a tsanake "magana
nakeso na yi da ke" daga yanda naji tayi maganar nasan maganace mai muhimmanci gyaran
murya tayi sannan ta ci gaba da magana "idan kina tare da mijinki ki keɓe magana za muyi
kuma banaso kimin ƙarya"

"ba kowa tare da ni ummi" na faɗa cikin sanyayyar murya "yawwa jiya da dare abbanki ya siyo
mana sarƙa da ni da ke nace bari in haɗe inda nake ajiyar sarƙoƙinmu amma abin mamaki koda
naje ba sarƙarki a ciki bayan kuma nasan duk suna tare kuma nasan ba ta hannunki sannan
idan ɓarawo ne bazai ɗauki sarƙa ɗaya ya bar saura ba shine nakeso ki gayamin gaskiya
zuciyata tana gayamin kinsan wani abu akan lamarinnan"

Dakan lugude gabana keyi ni shaf na manta ma da na ɗau wata sarƙa" kar ki kuskura kimin
ƙarya" ta katseni daga abinda nake shirin yi" ni naɗauka ummi" na gayamata gaskiya ganin
ƙaryar ba abinda za ta tsinana min "me kika yi da ita" ta jefomin tambayar cikin taushin murya
yanda bazan tsorata ba
"Lawal na baiwa yayi jari kuma yace ranta yayi da zaran ya samu zai maidomin kuɗina sai in
siyi sarƙar" shiru tayi na mintota na ɗaukama ta kashe sai can tace "kin kyautawa kanki kuma
nagode sosai" daga haka ta katse wayar tsorone ya shige ni don ga dukkan alamu fushi ta yi
kuma nasan illar fushinta akaina kiranta na shiga yi amma ta ƙi dagawa
Kuka na shiga rerawa wata nadama na shigata number lawal na shiga nema saita muryata nayi
jin ya ɗaga izini na nema inje gida ya tambaye ni lafiya na ce lafiya lau kawai naji ina kewar
gidane yace in tafi amma kar in kai dare don ya yo mana siyayyar kayan abinci

Gani nayi gidan yamin nisa ko da na isa ko baba mai gadi da ke tsokanata bayan mun gaisa
ban tsaya kulawa ba saida naje tsakiyar falon sannan nayi sallama "keee lafiyar ki" ya mubarak
ya faɗa ganin yanda na shigo a hargitse kallo ɗaya na mishi na ƙarasa gaban ummi na zube
guiwowina ƙasa hannuwana na ɗora akan cinyoyinta "don Allah ummi kiyi haƙuri kar kiyi fushi
da ni" ba ta min magana ba sai ma ya mubarak da ta kalla "kaje kawai" magana zaiyi ta dakatar
da shi "kaje nace"

"Don girman Allah ummi kiyi haƙuri wallahi fushinki akaina babbar matsala ce a rayuwata nasan
nayi kuskure wallahi kuma bazan ƙaraba" janye hannuwana tayi daga jikinta sannan ta miƙe
tana ƙoƙarin wucewa bedroom ɗinta ƙafafunta na riƙe ina kuka ina mata magiyar ta yafemin
"Yanzu har aure ya miki daɗin da za ki ɗau dukiyarki ki bawa miji? namiji? namiji kike wa
wannan rawar kan? ba baki nake miki ba zainab amma ina ji maki tsoron ranar da zai nuna miki
butulcin ɗa namiji in za kisan ciwon kanki ki sa ni in kuma duk abinda kika mallaka za ki miƙawa
lawal ɗauka ki bashi Allah ya bar ƙauna"

Na sha kuka na sha magiya kafin ta sauko hankalina bai kwanta ba saida naga ta haƙura
sannan na yi shirin komawa gida ɓangaren yaya isma'il na shiga nayiwa anty nasma sallama
sannan na wuce na yaya abbas ita ma na mata sallama sannan na ja motata na lula titi

Ko da na koma gida ya dawo da siyayyar da yace yayi katin ɗin taliya ne sai mai da kuma ƴan
kayan magi sai da na gama dubawa sannan na dube shi ina so inyi magana kuma ina tsoron
yayi fushi daurewa dai nayi nace "Nisful da ka sa ni shinkafa ka siyo ma na"

Wani kallo ya mini sannan yayi fuuuuu ya wuce ciki kayan na kwashe na kai kitchen sannan na
wuce na same shi ɗaki waigowa yayi ya dakata daga ƙoƙarin cire rigar da yake yi" bari in
gayamiki bazan ɗau wannan ɗabi'ar ba idan ke san don ki sakamin doka za ki bani kuɗinki to
nagode ki riƙe abin ki"
Tun daga ranar taliyar ce ta zama abincinmu kuma bantaɓa yi mishi ƙorafi ba saboda ina tsoron

yayi fushi bansan ya saida motarshi ba saida aka kwana biyu ban ganta ba na tambaye shi
"Nisful lafiya kwana biyu banga motarka ba? ko lalacewa ta yi"

Wani kallo ya min "saboda an bani motar daga gidanku shiyasa kike sakamin ido a kanta? to na
siyar ne? ko akwai magana" kallon mamaki na ke mishi "meyasa za ka siyar da motarka nisful?
wallahi banji daɗi ba"

"Dole in siyarda mota in nemi kuɗi saboda na gaji da wulaƙancin mutumennan bazan ƙara
komawa wurinshi ba" inaso inyi magana to amma ina tsoron abinda maganar za ta haifar

Gyara zamana nayi sannan na sako mishi maganar da yaya abbas ya kirani ya min kan
karatuna yana gayamin ƙyaleni ne abba yayi ya ga iya gudun ruwana nima kuma sai na ji ina
sha'awar karatun yanzu

"Nisful maganar KARATUNA ina so in koma makaranta" baya na ja ganin yanda ya wani zabura
"makaranta kuma? ni sakarai ne da zan sakeki wasu mazan na kallonki? A'a wallahi ba da ni ba
karatunnan dai ana yin shi ne don tara wani abun duniya to na miki alƙawarin nema har iyakar
ƙarfina don na huce miki takaici "
Haka ya ci gaba da tsara ni har na yadda naga ba amfanin wani KARATU da zanyi ya sa na kira
ummi nace mata yace zan koma amma sai na haihu kamar yanda ya tsaramin

su kuma jin maganar ciki sai suka jingine maganar karatu ashe ko mun sara bisa gaɓa domin
lokacin ina ɗauke da cikin safwan da ko ni bansa ni ba






Uhmmmmm


AURE DA KARATU
NA
RUMAISA'U SIDI



Page 16


Ba mu amfana da komai ba cikin kuɗin motar da ya siyar, don ɗaukar kuɗin yayi, ya baiwa

abokinshi wai ya jujjuya mishi su raba riba.Lokacin da ya gayamin haka, na gayamishi sam
wannan ba dubara bace, amma ya nuna min ai mai amana ne.

Sai ga shi ya dawo ya na gayamin, kuɗi sun lalace na nuna mishi baiwa wani kuɗi da sunan ya
ma sana'a ba mafita bace shi kuma ga yanda na lura sana'ar ce bazai iya ba ina mamakin
yanda namiji ke ƙyamar sana'a to idan baiyi sana'a ba me zai yi?

In taƙaice miki sai da duk abinda na mallaka ya ƙare wurin cefanenmu tun ina yi har nazo na ka
sa domin ko banida komai wallahi akwai ranar da muka kwanta haka nan ba mu ci komai ba
saboda ni banida komai haka ma shi ga ciki na rame duk na fita hayyaci na gida ma na daina
zuwa don duk abinda zai sa aga laifin lawal banason shi
Bikin anty halima da ya matso ya sa dole naje gida kusan firgicewa nayi yanda ummi da su
yaya suka sakani gaba da tambayar meke damuna? bansan me zan ce musu ba kaitsaye yaya
abbas ya turani mota sai asibiti gwaje-gwaje su kamin suka ce in rinƙa cin abinci mai gina jiki
faɗa ya dingayi tun a mota yana gayamin ga abinda ake gudarmin
Kayan abinci ya siyamin da kuma kayan fruit ma su yawa shi ya maidani gida yana tambayata
me ya hanani zuwa da motata? nace mishi kawai bazan uya tuƙi ba saida ya kawoni nazo futa
ya ɗakko kuɗi masu yawa ya bani yace in sa mai wataƙila ya fahimci rashin mai ne yasa ban fita
da ita ba
Lokacinda lawal ya ga kayan faɗa ya dingamin wai na je gidanmu nace ya barni da yunwa ta
inda ya ke shiga ba tanan ya ke fita ba nidai bance mishi komai ba don abin ya fara kaini
maƙura abin haushi kuma kayan da yake faɗa a kansu da shi aka cinye

Haka akayi bikin anty halima na shiga bikin duk a muzance yanda na lalace kamar ba ni ba
cikin garinnan aka kai anty halima saboda mijinta ɗan sokoto ne kuma itama anan za ta ci gaba
da aiki saboda har yaya isma'il ya samo mata aiki a inda yake aiki

Tun da na doshi watan haihuwata na fara mishi maganar ya kamata a rage siyayyar wasu
abubuwan to nima ina faɗane kawai don ko cikina ban cikaba bale kuma akai ga ajiyar wasu
kaya

A ranar da zan haifi safwan shi ya kaini asibiti da kayanshi aka rubuto kayan da ake buƙatar a
siya abin baƙin ciki haka na kasance cikin wani hali har zuwa lokacinda ya kira gidanmu ya
gayamusu ina asibiti

Faɗa yaya Abbas ya dingayi ganin asibitin da ya kawo ni ganin halinda na ke ciki yasa ya biya
komi cikin ikon Allah sai ga shi na haifo santalelen ɗana

Tunda na haihu ba wani abu da ya fita daga aljihun lawal komai ƴan uwana ke yi ba abinda aka
nema daga gareshi mahaifiyarshi sun zo da ƴan uwanshi

Sai daren suna aka kawo kayan barka kala huɗu ya min dukansu ƙanana sai jaririn kala goma
ban wani damuba saboda duk yayyena har yaya mubarak ba wanda bai min sha tara ta arziki
ba cikinsu na fantama na kuma fita kunya

Zamana gida sai gani na dawo hayyacina daga abbana har ummi wata kula suke ba ni sai gani
na zama ƴar lukuta na yi wani kyau na musamman har banso inji ana maganar koma wa ta

Haka na koma gidan lawal muka ci gaba da gurgura rayuwar a haka ba wata sana'ar arziki da
ya ke yi taimakon da nake samu daga yayyena da iyayena da shi muke amfani

Shekarar safwan uku na ƙara haihuwa na haifi Aysha (baiwar Allah) haihuwar aysha

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
google.com, pub-9213700357025247, DIRECT, f08c47fec0942fa0