Showing 9001 words to 12000 words out of 62089 words

Chapter 4 - Aure Da Karatu Book Complete Rumaisa Sidi

Rumaisa   

18 Jul 2026

513

haifa daga shi babana UMAR sai kanwarshi khadija mahaifiyata ma 'yar
asalin jihar sokoto ce auren hadi aka musu da babana saboda iyayensu aminan juna ne Itama
mahaifiyata 'yar bokoce domin a gidan mijinta ta hada digreen ta na biyu

Mu biyar iyayenmu suka haifa kuma ni kadaice mace a cikinsu yaya isma'il shine babba kuma
kwararren likita ne yanada mata daya anty nasma da kuma 'ya'ya biyu sai yaya Abbas shine

mai zafin zuciya a gidanmu yanada fada sosai shi kuma lecturer ne a usmanu dan fodiyo
university shima yanada mata anty yasmin da yara uku sai yaya mu'azzam shi ma yanada mata
daya da yaro daya kuma yana aiki da gidan man NNPC sai yaya Mubarak shi kuma soja ne
yana ibadan sai kuma ni shalelen abba da ummi
Kasancewata nikadai mace yasa na taso cikin gata da kulawa ta iyaye da kuma yayye gata na
musamman nake samu a gidanmu ba abinda na nema na rasa kai hatta gwaggona da take
aure a kaduna to duk lokacinda za tazo ita da yaranta yaya bashir da kuma anty halima to suma
burinsu su sakani farinciki zan iya cemiki nice farincikin gidanmu gaba daya bansan yanda zan
misalta miki kaunar da nake samu daga gidanmu ba wallahi bansani ba

Tun lokacin kuruciya nakeda burin yin karatun masscom inaso sosai sanin burina iyayena da
'yan uwana suke kara bani kwarin guiwa duk da ba haka suka so ba burin abbana nayi karatun
likita hakama 'yan uwana lokacinda yaya abbas yaji karatun jarida nakeso nayi fada ya
dingamin na bazan yishi ba na tsorata sosai kuma naji karatun yana neman fitarmun arai
saboda ana nema a dakushemin burina saboda a lokacin nake rubuta jarabawar fita daga
secondry saida babanmu ya taka mishi birki da gayamishi a barni nayi ra'ayina tunda shi nake
kauna

Banida kawa sama da mahaifiyata da ita nake shawara hakama yayyena komai tare mukeyi
idan fita nayi saurayi ya biyoni ita zan fara gayawa ke zan iya cemiki a wurin mahaifiyata na koyi
komai ta sakani a jikinta sosai ta yanda kaitsaye zata gane gaskiyata ko akasin haka

RAYUWATA ta fara canzawa ne bayan haduwata da lawal dan wanka kuma dan kwalisa saurayi
irinsu lawal ne akewa lakabi da (bakyau gareku ba shiga rai) mun hadu dashi ne bayan
kammala secondry dina a bikin yayar kawata hafsa wankan lawal ne ya jani na kulashi a
lokacinda ya fara min magana cikin yanga na tsaya na saurareshi bayan tsayuwarmu kuma
labari ya sauya


" banga laifinki ba don kinki kulani a karon farko domin kin cancanci hakan kyakkyawa saidai ina
rokon don girman Allah ki aramin koda minti 3 ne cikin lokacinki" cikin wata sabuwar yangar da
naji tana tasomin na fara magana "ina jinka minti 2 na baka saboda inaso in koma gida da wuri"
tsayuwarshi ya gyara "nagode sosai Beauty tun lokacinda kika shigo idona ya sauka akanki
ganin shigowarki na kara godewa Allah da ya sanya ina cikin wayanda aka gayyata a bikinnan"
kallonshi nayi "saboda me?"


"Saboda na hadu da beauty wanda bansa ran haka ba" kallon wayata nayi duk da yanda
zuciyata ke ingizani da son sauraren yanda yake fitarda sautin kalamai kamar wani mawaki
"zan wuce lokacinka ya cika" daga haka na fara tafiya har na isa wurin motata shi ya budemin
na shiga " kiyi tuki a hankali beauty Allah ya tsaremin ke ya kaiki lafiya a gaida mommy ace
sabon danta na gaishe ta" motata na rufe na shiga kokarin kunnata ba don wulakanci ba sai

don yanda naji zuciyata na karbar sabon sako daga wannan mai zazzakan kalaman Ina tuki ina
tunani to shi haka ake soyayyar? kofa number ta bai nema ba duk da bana raba number ta
amma ina jin da ya tambaya shi zan bashi


A bakin tangamemin get din gidanmu na shiga doka horn da sauri aka shiga wangalemin shi
sauke glass nayi ina wa dattijon mai gadin namu murmush " barka da dawowa shalele kuma
farincikin gidan gaba daya"
"barka da aiki baba" shima da murmushin a fuskanshi yake fadin"Allah ya huce gajiya" amsawa
nayi da "Amin tare da wucewa da motata na kaita ma'ajiyar motocin gidan kashe motar nayi
tareda fitowa farinciki naji ya cikamin zuciya ganin motar yaya bashir a gidan sauri-sauri na
karasa falon tareda kwalla mishi kira shima kamar kullum da murmushi a fuskarshi ya mike
yana mini waka kuma yana tafi lokaci daya "ga shalelen abba ga shalelen ummi kai ga shalelen
gwaggo kuma itace shalelen yaya"( ku rera wakar da kanku)


Rausaya na shiga yi kamar kullum dariya suka shiga min saboda inda sabo sun saba indai yaya
bashir yana sokoto to kullum muna tare ko wani gurin zaije to saidai mu tafi tare ko su yaya
abbas bamuyi shakuwar da mukayi da shi ba bayan ummi da abbana shine mutum na uku da
yasan sirrina kamar yanda zan nemi shawarar abba ko ummi haka zan kirashi in nemi
shawararshi


Tambayarshi su yaya halima nayi dasu gwaggo yace duk suna lafiya sunce a gaisheni "ga
tsarabarki can da suka baki sai na huta zan baki" kafata na shiga dokawa kamar wata karamar
yarinya "nidai wallahi aba ni abina yanzu tun ba'a min danwaken zagaye ba" na fada ina kallon
ya mubarak (wanda nake bi) tsaki yayi " nasan tsarabarki bata wuce chocolate ko sweet tunda
har yanzu kallon kanki kike a wata jaririya wallahi malaman university ne maganinki" baki na
murguda " eh naji dai ai nasan haushi kakeji saboda ba kaine auta ba kuma da kake cewa
hakan ai dai nima kwanannan zan fara jami'ar nan kuma zan baku mamaki" wata harara ya
bankomin " wallahi har na matsu na ganki a jami'a" wannan karon ya bashir ne ya taremin fada
"mubarak sai mun baka mamaki zakaga shalele a jami'a hankali kwance tana karatunta wata
rana saidai mu ganta a gidan tv tana karanto news kamar baturiya"
Tsallen murna na buga tareda riko hannunshi wata harara ummi ta bankomin abinda yasa nayi
saurin sakin hannunshi tareda wucewa dakina don in rage kayan jikina inyi wanka


Ina zaune gaban mirrow ta shigo dakin wurina ta nufo tana hararata kunnena ta kama ta murde
"banhanaki taba mutum ba idan kina magana ban hanaki ba?" kara na saki saboda yanda naji
zafin rikon "ummi bazan kara ba" kunnen nawa ta saki "nasha gayamiki ba kyau amma kinki
daunawa kedai wuyarta fira tayi dadi yanzu zaki cumuimuye mutum ko su mabarak na hanaki
yiwa haka bare kuma bashir da zai iya aurenki "aurena kuma ummi" na fada ina zare ido dakin
ta bari tana gayamin in fito mu shiga kitchen

Da dare kamar kullum bayan mun kammala cin abinci muka dawo falo har Abbana kusa dashi
na zauna ina nuna mishi system din da nakeso ya siyamin " duk abinda kikeso zan siya miki
Zainab indai zaki aje hankali kiyi karatu naso kiyi karatun likita sosai amma burina bai kai ya
dakushe naki burinba shine kuskuren da iyaye ke tafkawa akan karatun yaransu yarinyarka
tana sha'awar fanni kaza kai kuma kaza kakeso tofa ka sani idan har ka tursasata tabi naka
ra'ayin to bazata taba maida hankali ba don ba shi takeso ba na barki kiyi ra'ayinki fatana ki
maida hankali a karatunki banda kule-kulen samari ko tarkacen kawaye ki rike mutuncinki da
kuma muruncin gidanku kece farincikinmu kema kinsan hakan to don Allah karki watsa mana
kasa a ido" jikina naji yayi sanyi sosai bana cikin 'yan mata masu tara samari saboda a ganina
hakan zai hanani cika burina abba yasha gayamin ko ina makaranta miji ya fito to za'a yi auren
sai in hada biyu inyi AURE DA KARATU

Ummi ma nasihar ta shiga min kamar ance gobe zan fara zuwa jami'ar nan tana gamawa shima
yaya isma'il ya dora hakama su yaya bashir kuka na saka musu ina nuna ya mubarak" yaya
shima ku mishi fada wallahi baya karatu kullum saidai yasa littafi gaba yana chat da ya jiku tafe
ya aje waya" harara ta ya shiga yi " wa zaki yiwa sharri? kedai in kinsan bazaki iya karatunnan
ba ki fada kar ayi hasarar na man mota" kuka nasa ina daddaga kafafuna kasa lallashina yaya
bashir ya shiga yi yanawa ya muby fada abba na dariya

Abin mamaki koda nazo kwanciya sai tunanin bawan Allah nan ya hanamin bacci ya iya tsara
zance daga yanda yake fitarda kowace kalma cikin tattausan lafazi juyi na shiga yi da mamakin
wannan sabon al'amarin da ya sameni tunanin wani namiji bai taba hanamin bacci ba saboda
koda munyi magana da kai nan gurin zan barta bana sakawa raina barema abin ya dameni
amma wannan mak'ale-matan ya hamin sukuni


Jin wayata tayi kara alamar shigowar sako yasa na mika hannu akan bedside drower ta na
janyo wayar zaune na tashi ganin sakon da ya shigo wayata "Barka da dare Beauty na fatan kin
isa gida lafiya a yau zanyi bacci da wayata akan kirjina saboda number mai daraja da wayar ke
dauke da ita mu kwana lafiya kiyi bacci cikin aminci"

Sakon na shiga maimaita karantawa kamar wata hadda tabbas mutuminnan ne na dazu
gurinshi kadai na taba jin kalamai irin wayannan wayar na rike ina kara kallon sakon daga nan
wani bacci mai dadi ya daukeni sai asuba da naji ummi na tadani tareda yimin fadan kwanciya
da waya ina kan dadduma ina azkar bayan kammala sallar asuba naji shigowar sako "MAYE"
na fada a raina ganin yanzu ma number jiya ce "Barka da asuba Beauty fatan kin tashi lafiya
Allah yasa haka Amin kar ki manta nima kimin addu'a sako daga MAYENKI" murmushine ya
subuceminn "sai maye kam" na fada ina nade dardumata tareda komawa kan gado na gyra
kwanciyata

HMMMMM✍️✍️✍️✍️✍️

AURE DA KARATU
NA
RUMAISA SIDI



Page 9




A bun sai ya zama kamar ibada kullum zai min text da safe da rana hakama da dare amma bai
taba gwada kirana ba nima bantaba yunkurin yi mishi reply ba duk da abin ya riga ya zamemin
jiki kullum na saba da karanta shi kuma kullum da kalar kalaman da zai turomin

Yau haka na ke aiki ba k'wari saboda rashin ganin sakon MAYENA kamar yanda na radamishi
suna na riga na saba da shi yau sai naji daban girkin kawai nakeyi amma hankalina sam ba ya
wurin na damu sosai na rashin jinshi ashe haka na shaku da sakonshi

"Lafiyarki kalau kuwa zainab" naji ummi ta daka min tsawar da ta sa na dawo hayyacina "dubi
abinda kike yi" ta nunamin abinda nakeyi sanwar miya zanyi ashe na cika tukunya har ga baki

Bakina na dafe ina kallonta "wallahi ban lura bane ummi" tsaki ta buga "ya za'ai ki lura? na dade
da lura akwai abinda kike boyemin ki gayamin meke damunki" murmushin yake na mata "ummi
dagaske ba abinda ke damuna" hanya ta nunamin "fice bani guri inyi girki na" hakuri na shiga
bata sannan ta kyaleni muka dora sabuwar sanwa
Har muka doshi kwana uku ba sakon MAYENA har wani daci-daci nakeji a bakina kamar wacca
tayi zazzabi a daren ranar ne na kasa hankuri zuciyata nakeji kamar zata buga wayata na
dauko na shiga laluben numbershi da nayi saving da sunan da na rada mishi

Jinai kamar na samu baturiyar da ke gayamin wayarshi a kashe take na makure mata wuya
tunani na shiga yi "to idan ya daga me zance mishi? ince na daina ganin text dinshi ko me? ko
ince nayi kewarshi? kaii inaaaaa" wayar na aje tareda kokarin yaki da abinda zuciyata ke sakani

Kawadda tunaninshi nayi kokarin yi daga raina naci gaba da harkokin gabana da kuma
shirye-shiryen makaranta ta da nida yaya bashir muke komai kamar wata baby zata je boarding
school haka mukayo siyayyar uwayen kayan biscuit sweet dasu chocolate ya gama kwanakinda
zaiyi lokacin komawarshi yayi rigima na samishi " nidai wallahi ya bashir bangaji da ganinka ba
don Allah ka dawo garinnan gaba daya ni banson komawarnan taka" ido ya zubamin yana
kallona " dagaske kike shalele? dagaske bakyaso na koma? indai har hakan kikeso wallahi zan
nemi transfer in dawo nan" washe baki nayi ina murna " wallahi inaso" hannuwanshi ya watsa
"angama shalele" murna na dingayi

Sai dare bayan munkare cin abinci ya sami abba da maganar fada ya dinga mishi wanda wani
na fahimta wani ban fahimta ba "Wannan ai shashanci ne saboda tace kayi abu sai kace
zakayi? ita yarinyarce zata gayama abinda za kayi to hakan za'ayi zaman ita ke bada umarni
kenan ba haka nakeson ganinka a gidanka ba tsayayye nakeso na ganka shiriritarku ni ta isheni
hakan nan kusa zanyi maganinku" wannan ne ya dakatarda ya bashir da dawowa sokoto


Na fara karatuna cikin aminci a USMANU DAN FODIO UNIVERSITY da motata nake zuwa duk
da yaya abbas yaso ya hanani tuki yace a hadani da driver amma na tubure na ce ni zan iya
karatu nakeyi amma har yanzu wannan mutumin yananan makale a cikin zuciyata har yau na
kasa goge sakonninshi dake cikin wayata kusan kullum sai na maimaita karantasu kamar wata
hadda

A hanyata ta komawa gida motata ta tsaya fitowa nayi gashi wurinda nake ba mutane ko ina tsit
wayata na dauko na shiga kokarin kiran ummi cikin shagwaba na fara magana jin ta daga "
ummi gani nan a hanya motata ta tsaya kuma ko ina tsit ba mutane"

"Gashi ba kowa a gidan ko driver sun fita da su Antynki Nasma bari in kira bakaniken yazo inda
kike ya duba motar ke kuma kisamu ko napep ki dawo gida zamanki a irin wurarennan
hadarine" tsoro na rikaji nima ina kallon gabas da yamma ina nema inga napep

Sai can ga bakaniken ya iso barmishi key din nayi idan ya kare ya kaimin gida na dawo dubin
napep can na hangeta tafe taro na shiga yi cikin iyawar ubangiji ya tsaya "malam Arkilla
za........."maganar ta makale a bakina ganin yanda shima yayi saurin dagowa yana kallona
"Shine wallahi shine" na shiga nanatawa a raina dakewa nayi na karasa maganata " Arkilla zaka
kaini" shima kawadda kai yayi " bismillah to" shiga nayi ya fara tuki a hankali mun danyi nisa
naga ya tsaya kifa kanshi yayi akan keken sai can ya dago batare da ya kalleni ba ya fara
magana " Na dauka zan iya na dauka zan saba ashe bazan iya ba na ga kamar ina takura ki
tunda na hadu dake bankara bacci cikin kwanciyar hankali ba ranar da na ganki hankalina bai
kwanta ba saida na koma wurin taron nabi duk hanyar da zanbi na samu number ki naci gaba
da neman soyayyarki ina kaunar jin muryarki amma bana fatan hakan ya zama abinda zai bata
ranki shiyasa na zabi na tura miki text da fatan watarana ki kulani kwatsam mahaifina ya rasu a
wurin makokin aka dauke 'yar wayar ban san kuma inda zan kara samun number ki ba kullum

fatana ina zan kara haduwa dake" juyowa yayi yana kallona " Ina sonki zainab wallahi ina sonki
saidai naga kamar abinda nakeso bazai samu ba saboda ta kowane bangare kinfi karfina
zainab"

Abin mamaki sai nasamu kaina da cewa "dama mace tana fin karfin namiji" zama ya gyara
"sosai ma kuwa" sai a sannan na fahimci bada kaina da nayi kallon wayata nayi " muje please
ina bukatar isa gida da wuri" murmushi yamin wanda ya dakarmin zuciya "angama ranki ya
dade"
Sai kofar gidan yayi parking ina kokarin fita maganarshi ta dakatarda ni "Am Zee don Allah
inaso idan ba damuwa mu samu lokaci muyi magana" hmmmmm abin takaici ban musaba "
Kasameni a UDUS gobe karfe 12:00"

"An gama ranki ya dade nagode sosai" kudi na zaro masu yawa bansan ko nawa bane na mika
mishi girgiza kanshi yayi "Allah kiyaye ko karen gidanku na dakko bazan karbi kudinshi ba bare
kuma ke" ganin zamu tsaya bata lokaci yasa na aje mishi kudin tare da shigewa gida bana son
haka sam alakarmu daban sana'arshi daban kuma ni har yanzu ma ban gama tantance abinda
ke tsakanina dashi ba Yinin ranar har dare ina cikin walwala ta musamman

Washe gari da zanje makaranta sai na samu kaina da tsayawa zaben kayan da zansa inje
makarantar daga karshe bakar abayata data sha adon stones na dauko saiko na fito fes dani
ankare nake da agogo sai 12 muka gama lectures can na hangoshi zaune cikin napep
kafafunshi da jikinshi suna waje Hafsat kwasare na kalla "ina zuwa hafsat nayi bako ne" baki ta
dafe "Ahhh lallai wannan wane handsome ne mai wannan babbar sa'ar bantaba jin ko ganinki
tare da wani ba" dube-dube ta shiga yi tareda riko hannuna "wai ina yake? ko tsoron amiki
snatching kike" nuna mata shi nayi "kinganshi can kuma nifa bance miki saurayina bane kawai
nace miki bako nane" fara'ar fuskarta ta bace "Aiko shi akayi kenan har na fara murna" dariya
ma ta bani takawa na shigayi na isa wurinshi da isata ya mike tsaye yana kallona da murmushi
a fuskarshi "barka da isowa gimbiyar mafa" murmushi na mishi nima "barka dai mu dan isa can
ko" na nuna mishi wurin zama

"Sunana Lawal muhammad kuma ni haifaffen garinnan ne maganar gaskiya tunda na ganki
Allah ya dasamin kaunarki a raina sai kuma nake ganin kamar abin bazai yuba saboda ni dan
talaka ne zainab a halin yanzu mahaifina ya rasu kuma ni kadaine namiji a gidanmu 'yan uwana
duk matane kuma ni ke dauke da nauyinmu gashi banyi wani dogon karatu ba bare ince zan
nemi aiki daga secondry na

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
google.com, pub-9213700357025247, DIRECT, f08c47fec0942fa0