Showing 48001 words to 51000 words out of 62089 words
abin da bai kamata ba.
Ina nan kwance naji ƙarar wayata,ɗaga wa bayi batare da nasan mai kiran ba,a hankali naji
muryarshi "Baby idan akwai abinci wurinki ki zubo min ki kawo min ɓangarena"
Har naji kamar nace babu amma sai naga rashin dacewar hakan shiyasa na amsa mishi da "To"
tashi nayi na shirya mishi abincin da na dafa na kasa ci.
Ɓangaren nashi na nufa dashi tare da yin tsaye a wajen na kira shi "Ka buɗe ka karɓa" na faɗa
bayan ya ɗaga kiran "Ki shigo a buɗe ta ke" ya amsamin shima
Ba don naso shigar ba na buɗe tare da shiga falon,yana zaune da remote a hannunshi sai
kuma abincin da aka zuba wanda da alama ba'a ci cibi biyu a ciki ba gabanshi na dire kayan
"Yawwa Baby Allah ya miki albarka"
Amsawa nayi da "Amin" ina ƙoƙarin tashi "Ki zuba min mana" ya dakatar da ni.
Zuba mishi nayi tare da janye wanda ke saman center table ɗin nakai gefe "Ki kaishi kitchen
kawai"ya umarceni kaiwa nayi tare da wanke hannuna na fito wanda yayi daidai da fitowarta
daga bedroom cikin shirin bacci.
Ƙugunta ta riƙe tana kallonshi "Kam balastinnnnnn wato nawa abincin ne ba zaka ci ba kenan"
*RUMAISA'U SIDI*✍️✍️✍️
*AURE DA KARATU*
*NA*
*RUMAISA'U SIDI*
*FARAR ANIYA WRITERS*
*page 33*
Takowa tayi har gabanshi tana kallon abincin da na zuba mishi,maida kallonta tayi a kaina
ƙwalla na taruwa a idanuwanta "Yanzu saboda tsabar wulaƙanci ranar girkina zaki kawo mishi
abinci"
Ji na nayi wani iri saboda nima sai yanzu nake jin ban kyauta ba domin kuwa idan nice ba zan ji
daɗi ba duƙawa nayi da niyar tattara abincin "Kar ki taɓa komai,za ki iya tafiya"
A sanyaye na bar ɗakin,koda na koma ɗakina daƙyar bacci ya ɗaukeni ina mai addu'ar Allah ya
kareni daga shiga haƙƙin matar nan,saboda a duniya ba babbar asara kamar ka bari haƙƙin
wani ya kaika wuta.
Kuka ta fashe da shi bayan Zainab ta bar ɗakin "Wai Ya Bashir me na maka da ka tsaneni har
haka? Ance ban iya girki ba na fara koya saboda kai amma yanzu na maka girkinnan kace bai
yi daɗi ba,ai sai kace in dafa ma wani abun amma shine zaka kirata ta kawoma abinci saboda
ka tozarta ni,ka nuna mata banida wani girma a idonka"
Hannunta ya riƙo tare da zaunar da ita gefenshi,hawayenta ya shiga sharewa yana jin ba daɗi a
ranshi "Shikenan kiyi shiru,tunda bakyaso baza a ƙara ba yanzu bari in dafa mana ko indomie
ko?" kanta ta gyaɗa mishi.
Shi ya dafa musu indomie ya zubo a plate suka ci tare,nan take sai ga Zubaida ta saki ranta
suna zuba hira ita da mijinta.
Washe gari a sukwane na tashi na gyara gidana tare da dafa ruwan shayi sai ƙwan da na
soya,kamar dole haka nake shan tea ɗin saboda yadda nakejin bakina yana ɗaci,na rasa me
yake min daɗi.
Ina breakfast ɗin ya shigo yayi kyau sosai cikin coffe colour ɗin yadi,sallamar shi na amsa ina
ƙara kurɓa ruwan tea ɗin da ke hannuna "Ina kwana" na gaida shi da ƙyar
"Kin tashi lafiya,ya jikinki" ya tambaya da kulawa tare da ajiye briefcase ɗin dake
hannunshi,zama yayi kan kujerar da ke fuskantata "Har yanzu jikinne" ya tambaya ganin yadda
take cin magani.
Kofin na ajiye tare da girgiza kaina "A'a naji sauƙi Alhamdulillah" tasowa yayi daga inda yake
zaune ya dawo inda nake,hannuna ya riƙe "To meke damunki? Ki faɗa min don Allah" kuka na
ɓarke da shi tare da ɗora kaina akan kafaɗarshi,lallashina ya shiga yi.
Saida ya ga na ware sannan ya bar gidan,ɓangaren gwaggo na shiga acan ma nayi rabin
yini,na warwarewa Zainab kanta na mata sabon kitso.
Haka zaman namu ya ci gaba da kasancewa,Zubaida bata daina shigar min hanci ba,wani
lokacin na ƙyaleta wani lokacin na kulata,kuma ina ƙoƙarin nusar da Ya Bashir akan kwatanta
adalici a tsakaninmu.
A ɗan zaman namu na fahimci Zubaida sam bata san wani kula da miji ba,ɗan girkin ma da ta
fara yanzu ta daina,mai aikinta ke yi kamar yadda take yi tun farko,ba ruwanta da ƙamshi za dai
tayi wankanta tsaf ta fito ƴar ƙwalisa ammafa ba ƙamshi,bata sarrafa harshenta lokacin da zata
mishi magana,ko rigima suka yi bata ɓoye hakan ko a gaban waye zata nuna sun sami
matsala,kuma ba ruwanta har gurin mahaifiyar shi za ta kai ƙararshi wanda wannan yana ɗaya
daga cikin abinda ya ƙara kada ƙimarta a idon Gwaggo.
Ƴan uwanta ma idan suka zo indai zamu haɗu to sai an yada min habaici,ni wani zubin ma
dariya suke bani don kusan har na haddace abin da suke gaya min duk lokacin da muka haɗu
"Bazawara kawai mai ƙwacen miji" shine kawai abin da suke faɗa.
Result ɗina ya fito Alhamdulillah kuma na samu nasara,a lokacinne nayi shirin zuwa sokoto don
ganin ƴan uwana da kuma ƴaƴana,duk da kowannensu muna waya don ko Safwan idan ya sami
dama yana kirana da wayar tsohuwar maƙociyata Maman Haidar.
*LAWAL*
Zaune yake a ƙofar gidan yana ƙoƙarin sallamar yaran da ke miƙo mishi kuɗi don ya sallame
su.Dakatawa yayi daga ƙoƙarin saka tattasan da ya ɗebo da niyyar zubawa a leda ganin wani
mai irin uniform ɗin makarantar secondary ɗin da ya kai Safwan bayan ya kammala primary ya
sauko daga napep ɗin da ta faka.Sai ga Safwan ɗin shima ya fito,sakin ledar hannunshi yayi
tare da miƙewa ganin yadda yaron ya riƙo Safwan alamar bayada lafiya.
"Subhanallahi me ya same shi" ya faɗa yana kama Safwan ɗin ya shige dashi cikin gida,akan
kujerar falon ya kwantadda shi tare da sheƙawa da gudu kamar wani yaro yayi kitchen,bai jima
ba ya fito da ruwa a hannunshi tare da zama kan kujerar ya ɗaga Safwan yana ƙoƙarin saka
mishi kofin ruwan a bakinshi amma ya ƙi karɓa
"Wai me ya same shine"ya ƙara tambayar yaron kamar zaiyi kuka "Wallahi Abba ban sani
ba,kawai an tashi daga makaranta mun fito har mun ɗanyi nisa naga ya faɗi nayi ta tada shi bai
tashi ba,shine na tari mai adaidaita na kawoshi gida"
Nusaiba ya shiga ƙwallawa kira yana girgiza Safwan ganin jikinshi ya fara saki saɓashi yayi a
kafaɗarshi ya nufi ƙofar fita a harmutse.Wani abokinshi da ke zama wurinshi ya roƙa da ya
kwashe mishi kayan asibiti zai je.
Da sauri likitoci suka karɓe shi ganin halin da yake ciki,kaikawo ya shiga yi a ƙofar ɗakin da aka
shiga da Safwan,ji yake kamar ya sa kuka,me ya samu yaronnan? Me zai cewa Zainab,kardai
shima Safwan mutuwa zai yi kamar yadda Aysha ta mutu,kar dai dagaske bazai iya riƙon
ƴaƴanshi ba"Allah ka kawo min ɗauki" ya faɗa yana goge zufar da ke wanke mishi fuska.
Magunguna aka rubuto da allurai da ruwan da za a saka mishi da sauri ya haɗa ƴan kuɗaɗen
da ke aljihunshi ya nufi wurin siyen maganin saida aka haɗa komai akayi lissafi kuɗin kayan sun
kama 16k aljihunshi ya shiga lalabawa bayan ya lissafa dubu bakwai da ɗari biyar ɗin da ke
hannunshi kallon mai saida maganin yayi "Don Allah ka taimaka min,na duba kuɗina basu kai
ba,kamin alfarmar bani maganin na maka alƙawari yanzu zan je na kawoma kuɗinka"
Girgiza kai mai maganin yayi"Kayi haƙuri wallahi nima kaga maganinnan ba nawa bane bazai
yu in baka maganin mutane ba" ajiyar zuciya ya sauke tare da juyawa yana tunanin tafiyar da
zai yi gida ya ɗauko kuɗi duk yaronshi na cikin wannan halin.
"Kawo takardar"mai maganin ya faɗa cikin tausayawa "Kamin alƙawarin kawo min sauran
kuɗinnan don Allah"
"Na maka alƙawari yanzu zan je in kawo ma"
Sai da Mama ta iso asibitin bayan Lawal ya kirata sannan ya koma gida don ɗauko kuɗi.
Bayani ya kewa Mama bayan dawowar shi daga wurin likita"Kinji wai sun ce zafinnan da ake yi
ne yanzu,sanƙarau ne yaso kamashi amma abin bai yi tsamari ba.Ina ganin zan canja mishi
makaranta saboda yawan cinkosu tunda yace wajen su 100 suke a aji guda zan yi ƙoƙari in
duba wata mai ɗan damar kuɗi in saka shi"
Kallonshi kawai Mama ke yi a ranta tana ƙara godewa Allah da ya shirya mata Lawal,wai yau
Lawal ne ke nema da kanshi batare da ya duba ƙarancin sana'arba,yau shine ke nuna kulawa
kan ƴaƴanshi abin da bata taɓa gani ba,ko wani abune ya same su na rashin lafiya sai dai kaga
tashin hankali a fuskar uwarsu amma shi "Tirmisisi tusar gaba ga miji"inji hausawa.
Ƙarfe 3 na rana muka shigo garin sokoto tare da Ya Bashir da ya kawo ni,rungume Ummina
nayi ina jin wata kewarta ta musamman.Amna ma riƙeni tayi tana gaya min bazan ƙara tafiya na
barta ba.
Mama ce ta kira Ummi ta faɗa mata Safwan na asibiti,don basu san na shigo garin ba.
Ya Bashir ne yace na shirya muje don shi a gobe zai koma,shiryawa nayi jiki a sanyaye na fito
yana motar na same shi ɗaure fuska yayi yana kallona "Kije ki saka hijabi ki aje wannan gyalen"
duban jikina nayi gyalen nake sanye da shi amma babbane ya rufe jikina ko ina.
Fita nayi kamar yadda yace na canjo hijabin,kallona ya dinga yi kamar shima hijabin bai yi mishi
ba.
Har muka isa asibitin bai ƙara magana ba,ina ƙoƙarin fita ya dakatar da ni"Wai meyasa kika
daina saka liƙab ɗinnan naki?" ya tambaya yana wani ɗaure fuska
Murmushi na mishi "Ka kwantar da hankalinka,Zainab taka ce,kuma mallakinka ce don haka ka
daina damuwa da mutanen da bai kamata kana saka damuwa akansu ba kaji mijina"ta faɗa
tana leƙen fuskarshi.
Dariya yayi sannan suka fito suka tunkari inda aka kwantar da Safwan,sallama suka yi Safwan
ɗin na zaune kan gadon Lawal na ɓare mishi ayaba,Mama kuma na zaune kan tabarmar da ke
shimfiɗe tsakiyar ɗakin.
*RUMAISA'U SIDI✍️✍️✍️*
*AURE DA KARATU*
*NA*
*RUMAISA'U SIDI*
*FARAR ANIYA WRITERS*
*page 34*
Miƙewa Lawal yayi tare da jan kujerar da yake zaune baya,gaida Mama nayi tare da tambayarta
mai jiki sannan shima Bashir ɗin ya gaidata.
Hannu Lawal ya baiwa Ya Bashir suka gaisa yana tambayarshi mai jiki "Jiki Alhamdulillah ya
samu sauƙi gashi nan sai sangarta yake wa Mama"ya ƙarasa yana ƙoƙarin ɗora murmushin
dole a fuskarshi.
Matsawa nayi kusa da gadon ina kallon Safwan da naga ya ƙaramin girma a ido,kamar ba shi
ba "Mommy" ya kirani da murmushi a fuskarshi
"Na'am Safwan,ya jikin naka?" na faɗa ina zama kan gadon saitin ƙafafunshi "Na samu sauƙi
Mommy,yaushe kika zo?Ina Amna?" ya tambaya yana raba ido.
"Yau ɗinnan na iso,Amna kuma tana gida tare zasu zo da Ummi"
"Ya jikin My boy"Ya Bashir ya faɗa yana shafa kan Safwan,shima murmushi ya mishi "Naji sauƙi
sosai uncle"
Hira muka ɗan taɓa da Mama da kuma Mariya dake ɗakin,saboda Lawal tun shigowarmu ba
jimawa ya bar ɗakin,yanzu ma Ya Bashir nake jira da yace in bari yazo.
Hira Safwan ya shiga yi min,akan makarantar da mahaifinshi ya kaishi,da yadda yake gane
karatunu.
Muna nan zaune wata matashiyar mace ta shigo riƙe da ƴar ƙaramar kula a hannunta kallo
ɗaya na mata na mayadda hankalina kan Safwan da ke roƙona wai in siya mishi waya.
Ƴar ƙaramar dariya na mishi sannan nace "Wallahi Safwan ka gama raina ni"ƙara kallon matar
da naji Mama ta kira da NUSAIBA nayi wadda nake kyautata zaton itace amaryar Lawal don
kamar na taɓa jin sunan a bakin Safwan har na mishi faɗan kar in ƙarajin ya kira sunanta kai
tsaye.
"Ga Maman su Safwanu nan"Mama ta faɗa mata tana nuna ni.Wayata na ci gaba da dubawa
ina jin idanuwanta a kaina sai can tace "Sannu" ɗago kaina nayi a hankali na dubeta "Sannu" na
maida mata nima.
Shigowar Ya Bashir ɗakin yasa na ɗago kaina,uwayen ledodi ya shigo dasu na kayan fruit da
kuma ice cream daban,Safwan ɗin ya baiwa ai ko ya shiga murna yana godiya.
Gaban Mama na isa tare da duƙawa ina mata sallama,kuɗi na dunƙule 20k na aje gefenta nace
asiyi ko ruwa,godiya tayi tare da muna fatan zaman lafiya.
Ɓata fuska Safwan yayi kamar bai so in tafi ba,har nakai ƙofa naji maganarshi "Mommy don
Allah ki dawo kafin ki tafi"kaina na gyaɗa mishi tare da mishi addu'ar samun lafiya.
Ziyara nasha har gidan Hafsat da ake ƙoƙarin kawo ma Amarya,kwana uku ya bani shima
daƙyar.
*ZUBAIDA*
"Wallahi baki ji haushin da kike bani ba idan naji kina ƙorafi kan matar nan,tun yaushe nake
gaya miki ki ɗauki mataki amma kika ƙi,kina tsammanin ita a banza tabar Bashir ɗin ne" Laila
ƙawar Zubaida ta faɗa bayan Zubaidar ta gama yi mata ƙorafi akan Zainab
Ajiyar zuciya Zubaidar ta sauke "Ba zaki gane ba Laila,ni fa duk harkar malaman nan ba
ƙaunarta nake ba,duk da bamu yi Islamiyya ba amma naji ana faɗar duk wanda yaje wurin boka
to kamar ya kafirta ne.Ni ko bazan yadda naje wuta a dalilin Zainab ba"
Taɓe baki Laila tayi "To Allah ya yafe mana kawai za a ce,amma gaskiya banjin zan iya bari
kishiya ta kawo min matsala,ke da kika ji zaki iya sai kiyi tayi,ke kuma kullum bazaki rabu da
kayan takaici ba"
Zaune take a falon bayan wucewar Laila a ranta take tunani "Wai me yasa Ya Bashir ke nuna
wa Zainab ƙauna a gaban kowa? Me yasa su basa faɗa? Me yasa ko magana ake yi da zaran
ta fara magana za a ce tayi kuskure amma idan Zainab tayi magana sai a dinga yaba mata? Me
yasa ƴarta ta cikinta ma yanzu nuna take tafi ƙaunar Zainab?"
Jifa tayi da filon dake gefenta tare da yin watsi da ɗan kwalin kanta "Why Zainab,me yasa komai
Zainab?"ta ƙarasa tana yamutsa gashin kanta.
Kuka take yi sosai,ita kaɗai tasan azabar da take sha a cikin zuciyarta,ita kaɗai ta san yadda
take jin tsanar Zainab a cikin ranta.Ta rabata da mijinta,a da idan ta mishi abu yana mata uzuri
amma yanzu baya mata uzuri ko kaɗan da tayi ɗan kuskure zai hauta da faɗa.
Yau bata masan tare zasu yi tafiyar ba saida ya shigo yake faɗa mata Sokoto zaije "Amma ai ba
adalci bane da zaka rakata ni kuma kayi tafiyarka ka barni"tayi maganar kanta tsaye.
A fusace ya ke kallonta "Kema idan zakije to ki shirya sai mu tafi,Nasan dai damuwarki kwanaki
ko? To karki manta gobe ma kwanan Zainab ne don haka daidai zan dawo bazan shiga cikin
haƙƙinki ba" daga haka ya ajiye mata kuɗi tare da barin ɗakin.
Har taji tashin motar tasu tana nan tsaye inda ya barta,wannan damuwarce ta hanata
walwala,kuma har suka kwana bai kirata ba,ballantana yaji lafiyarta.
Share hawayen da suka zubo mata tayi,tare da ɗauko wayarta,danna wurin kira tayi bayan ta
samu ganin Number da take nema sallama tayi bayan wadda ta kira ɗin ta daga "Anty barka da
yau"ta gaidata bayan sallamar da suka ƙare
Da mamaki sosai a muryar Antyn lokacin da take amsawa "Barka dai Zubaida,ya gidan ina
Zainab"
"Tana nan lafiya Anty,am anty nace don Allah gobe zan same ki a gida? Ina so in shigo don
Allah"
Shiru Antyn tayi sai can tace "Lafiya dai Zubaida?" Murmushi tayi mai sauti "Lahhh lafiya lau
Anty akwai maganar da nake so muyi ne"
Anty matar mahaifin su Zubaida ce,wayayyace sosai mai son mutane.Sam basa ga maciji
saboda irin tsanar da su Zubaidar suke nuna mata da sunan suna taya mahaifiyarsu kishi.
Tun bayan aurenta da Bashir Anty ta taɓa zuwa gidan ta mata nasiha kan irin zaman da taga
suna yi ita da mijin,a lokacin bata saurareta ba sai ma cin mutunci da ya biyo baya wanda har
takai ga mahaifiyar Zubaidar wato Husaina ta shiga tace kar ta ƙara yi ma ƴaƴanta shisshigi a
lamurran gidan aurensu.
Wannan ne ya katange Anty da zuwa gidan,tun da abin ya faru bata ƙara yunƙurin zuwa wurin
Zubaida ba,saboda duk abin da zai janyo mata matsala bata sonshi bale kuma har ya kawo
ɓacin rai a zuciyar mijinta.
Number Bashir ta danna da tun jiya da ya tafi bata ƙara jinshi ba,saida ta gama ringing sannan
ya biyo bayan kiran gaida shi tayi ya amsa tare da tambayarta Zainab.
"Kenan Ya Bashir da ban kiraka ba,ba za ka kiramu kaji lafiyar mu