Showing 3001 words to 6000 words out of 62089 words
da auren kaddara ba kai kayi kadan ka kirani da hakan wace riba naci a aurenka bayan
'ya'yan da ke tsakaninmu? bayanshi ba komai kai kuma silar aurena ka mallaki gidannan da
muke ciki da motar hawa kai har suturar sakawa lawal" matsawa nayi kusa dashi ina kallonshi
ido cikin ido "Har abincin ci kasamu sanadina lawal nafi karfin ka kirani da auren kaddara" na
karasa ina dukan kirjina jinake kamar in shake lawal sai ya daina numfashi na tsaneshi fiyeda
tunaninku masu karatu
Shima cikin bacin rai idanunshi sunyi jajir ya shiga nuna ni hannunshi na rawa" Wallahi zainab ki
iya bakinki kinsan dai igiya biyu ta rage tsakaninmu" tsaki na buga "to shine me? akwai wanda
ke dannarka game da igiyoyin kayi yanda zuciyarka ke rayamaka akaina lawal"
A fusace ya juya ya fita daga dakin yana banko kofar kamar zai ballata jagwabb na fada kan
kujera tareda dafe kaina da nakejin yana saramin kamar ana dokamin guduma har cikin
idanuna nakejin ciwon da lalube na tashi na wuce daki na dakko magani na tsakiyar falon na
zube ina haki dafe da kaina sunan Allah na shiga kira "Ya Allah ka kawomin dauki Ya Allah ka
yafemin Allah na tuba na tuba ubangiji Allah kayi abinda yake mafi alkhairi a kaina Yarana Allah
ka kawomun dauki ko saboda rayuwar yarana Allah Allah ka......." kuka ne ya kwacemin na kife
kaina kan kafet inayi kamar wata karamar yarinya
Bansan loakci ya tafiba saida naji yarana a kaina ashe wai baccine ya daukeni a hankali na
bude idanuwana da sukamin nauyi na sauke su akan Aysha da ke kallona kokarin tashi zaune
nayi ina tattaro sauran karfina murmushi na musu "Kun dawo? baccine ya dauke ni ashe"
hannuna Amra ta rike "mommy yau baki yi hugging dinmu ba" safwan ma matsowa yayi yana
taba wuyana a razane ya zare idanunshi irin nawa (inji lawal) "Mommy bakida lafiya? jikinki zafi
sosai mommy" sai hawaye " to miye na kuka kuma kamar ba namiji ba dubi kannenka suka
kuka zasu yi common yarana ku kwantar da hankalinku naji sauki sosai" na fada tareda hadesu
na rungume
Indomie na dafa musu ganin lokaci ya tafi dayawa daurewa naci gaba dayi saboda yarana dako
tari nayi zakaji suna hada baki wurin fadin "sannu mommy"
Shareshi nayi nabawa banza ajiyarshi har dare ban kara kulashi ba shima shareni yayi
dukanmu muna falo har shi nidai ina harkar business dina da wayata su kuma safwan na
dubama su Aysha karatunsu shi kuma yana sana'arshi ta chat da kullum ko ya rasa na pure
water bazai rasa na data ba
Ganin dare yayi na kashe data ta tareda tashi na dauke yarana da bacci ya dauke anan falon
kayan kallon da kunna su bayada amfani nazo na kashe ganin yana falon nabar hasken falon
ban kashe ba na wuce daki shirin baccina nayi ina gaba mirrow ina kichaniyar daure gashin
kaina ya shigo
Tsaye yayi yana kallonta a ranshi yace "yarinyar nan fa bata tsufa wazai ganta yace ta haifi
'ya'ya har hudu a cikinta( bayanin ta hudun yana gaba) tun lokacin kuruciya zee kyakkyawace
ajin farko yar kwalisa ba wanda ya taba tunanin zee zata aure shi kasancewar ta fito daga gidan
manya kuma ba wanda baisan irin soyayyar da mahaifanta da 'yan uwanta ke nuna mata ba
Karasowa yayi gaban mirrow yana kallonta ta ciki "Kinyi kyau zee" gira na dage mishi ina
kallonshi ta cikin mirrow " dama can ni kyakkyawace kaima kasan wannan" daga haka ta zame
tareda nufar gadon ta kwanta tareda lullubo bargon har kanta ta rufe ajiyar zuciya ya sauke
"hmmmm bazata canjaba kenan" dakin ya bari ya koma falo ya kwanta
Yau bacci nasha kasancewar weekend ce suma yaran daga sallah suka koma bacci sai
wuraren 11 na tashi saboda kukan Amra "mai yara baya hutu" na fada ina saukowa daga kan
gadon a gurguje na watsa ruwa na fito a jikin safwan na sameta tana shesshekar kuka
mahaifinsu kuma na kwance kan kujera da remote a hannunshi yana canja channel
"Me aka mata" na tambayi safwan "Wayar abba ta dauka shine garin kawomin ta fadi sai....."
hannu na daga mishi saboda nasan kwanan zancen "ku je ku shirya fita zamu yi da munci
abinci" ai dagudu suka ruga har amra dake kuka
Kallo daya na mishi na wuce kitchen na hada mana abinci fitowa nayi jin yara na mishi addu'ar
fita kamar yanda na koya musu "Amm nace abban safwan" na dakatar da shi ganin yana
kokarin fita tsayawa yayi yana kallona karasowa nayi bakin kofar nace "Dama nace zamuje da
yara muje muga babyn salma daga can in wuce gida" annurin fuskarshi ne ya bace da alama ba
haka yayi tunani ba "Sai kun dawo" ya fada tareda ficewa daga gidan "can ta matse ma" na
fada tareda juyawa nakoma inda na fito
A kofar gidansu napep ta sauke mu na sallame shi tareda shiga gidan tareda yarana gidan cike
yake da 'yan uwansu lawal duk yayunshi mata su uku da sukayi aure suna gidan gaisawa nayi
da wayanda ke waje yarana ma suka shiga gaida su cikin ladabi don ba alfahari ba indai a
fannin tarbiyyane banida sanya ga yarana
Dakin mahaifiyarshi na wuce inda mai jegon take sallama nayi suna dakin har mama karasawa
nayi gabanta na durkusa na gaidata kamar yanda na saba kullum har gobe ina ganin kimar
matar "yawwa zainab ya gidan ya kuma yarannaku" sunkuyadda kaina nayi ina fadin "Duk lafiya
lau muke mama ashe salma an sauka Allah ya raya akan sunna"
"Amin Amin zainab" matsawa nayi wurin mai jegon nabar su Amra wurin mama suna zuba mata
zance "Sannu salma barka da arziki" "yawwa" ta amsa a dage kamar wacca akama dole jinjirar
na karba na kira su safwan suma na aza musu kowa ya dauka Amra ma ta sa rigimar sai an
bata "to tara hannun na dora miki ita" da sauri ta miko hannu na doramata ba tareda na
sakarmata 'yar ba
"Kinason baby gashi uwarki ta rufe haihuwar" Anty mariya (yayar lawal wacca yake bi) ta fada
kai tsaye tana kawadda kanta
Sarai na jita amma sai nayi kamar banjiba hirarsu suka cigaba da yi ina jinsu amma bansaka
musu baki ba babbar yayarsu ce ta shigo rike da hannun Aysha Anty A'i (wacca lawal yayiwa
takwara da Aysha) "Anty ina wuni" itama kamar sauran a yatsine ta karba tana zama kan
kujerar dakin
"Shekaranjiya ai nazo bansameki ba nace abu ga gidan 'yan boko lawal kawai na samu nace
Allah ya maka budi kaima ka fita Allah ya rabaka da tsaron gida"
Caraf Anty mariya ta karbe "Ai anty ni ina mamakin matar da take hada AURE DA KARATU
kuma tace duka zatayi wallahi ina tausayawa mijin da matarshi ke KARATU don ba wata kulawa
da zai samu bare kuma lawal da yake cikin jarabawa saidai fatan Allah yasa ya cinyeta"
Mikewa nayi tareda yi musu sallama na hada kan yarana mama na samu a falo don in mata
sallama "zo nan zainab" umurtarsu safwan nayi da su jirani a waje matsawa nayi kusa da ita na
durgusa " ya gidan naku ba wata matsala dai ko zainab"
" A'a mama ba wata matsala" numfashi ta sauke "ki kara hakuri zainab nasan kinmana kokari
zama da lawal ba sana'a amma insha Allah akwai shirin da nakeyi akan hakan da anyi
sunannan komai zai daidaita ki kara hakuri kinji"
Murmushi nayi "Insha Allah mama" ina ganin kimar matar sosai saboda dattijuwar arziki ce sam
su lawal basuyi halinta ba "to ya karatunnaki" murmushi nayi "Karatu alhamdulillah mama wata
1 ya rage mu fara jarabawa insha Allah"
"Masha Allah to Allah yasa a kare a sa'a"
"Amin mama"
Kudi na zaro a jakata dubu 20 kamar yanda na kebesu tun gida na aje a gefen da take "gashi
mama a kara ayi hidimar biki" mikewa nayi tayi saurin rike hannuna "Dau kudinnan zainab tun
ban bata ranki ba duk wannan halin da kuke ciki zaki dauko wayannan kudin ki kawo"
"Wallahi ba komai mama don Allah ki karba" kudin ta dauko ta raba biyu " karbi nan na dau
wannan dai mungode sosai Allah ya miki albarka"
Daga nan kofar gidanmu aka sauke mu a bakin tangamemen get din gidanmu gaida
maigadinmu nayi ya amsa shima yana gaidani cikin girmamawa yana yiwa su Amra wasa
Motar da nahango a farfajiyar gidan ita ta tabbatarmin da YAYA na gidan babban yaya wanda
ke taka matsayin uba a gidan tun bayan da kasa ta rufe idon mahaifinmu
Muje zuwa daiiiiiii
AURE DA KARATU
NA
RUMAISA SIDI
Page 4
Bangaren mahaifiyata na wuce kamar kullum ko ina tsaf-tsaf kamar gidan sabuwar amarya to
akwai masu kula da komai
Tana hakimce akan hadaddiyar kujerar dake falon cike da kauna na karasa tareda rungumeta "
nayi kewarki ummi" 'yar dariya tayi irin ta jin dadi " bansan sai yaushe zaki girmaba Abun abba
ke bakisan kin girma ba wani lokacin ko yaranki basa sangartar da kike yi" gyara zamana nayi
tareda shigewa jikinta "karkiga laifina ummi gurinki kawai nake samun hakan a yanzu" shafa
kaina tayi "Allah ya miki albarka autata"
"To ina kika baro uwayen rigimar kuma" waigawa nayi sai yanzu na lura da bama tare
idanuwana sun rufe da kaunar mahaifiyata "Suna bangaren Yaya don munga motarshi a waje"
"Eh yau bai fita ba kinsan weekend ce"
"Haka ne fa" na fada ina sauke gyalena tareda ajeshi kan kujera
"Asabe Asabe" ummi tashiga kwallawa mai aikinta kira da sauri ta fito "gani um....) maganarta ta
katse tana karasowa cikin falon "Ahhh anty zee sannu da zuwa wallahi banma ji shigowarki ba
ina su Amra" nima murmushin na mata "wallahi munshigo anty asabe su amra suna wurinsu
Nihal"
"Masha Allah" juyawa tayi wurin ummi "gani ummi" nuna ni tayi "je ki kawowa auta abinci ki
zubomata farfesunnan da kika min suma yaran ki tanadar musu abinda za su ci kafin su tuna
dani"
"To ummi" ta fada tareda mikewa waigowa ummin tayi tana kallona " ko akwai abinda kike
bukatar asama miki" girgiza kaina nayi inajin kwalla na neman cika min ido
Allah sarki uwa duk lokacin da zanzo gidan to zakaji tana a girkamin kaza a girkamin kaza duk
abinda take ganin zaimin wahalar samu a gidan mijina to kokari take ta samaminshi nida
yarana
Nan take aka cika gabana da kayan abinci kala-kala da fruit fadi take "ki bude ciki kici abinci
tunda ba bakuwa kike ba" abincin na diba ina ci da kanta ta shiga kitchen ta hadomin fruit salad
ta kawo gabana " kifa buda ciki kici" saida ta sani gaba naci abincin sannan ta kira asabe ta
kwashe kayan
"dubi yanda duk kika rame kindauki damuwa kinsawa ranki bansan randa kika koma haka ba
zainab ada bakida kawa kamata amma daga lokacinda likita ya gayamana kinada hawan jini na
aje wannan tunanin nasha gayamiki duk abinda kike so ki kirani ki sanarda ni ko ki kira yayanki
ba abinda zaki nema a duniyannan indai akwai shi da bazamu nemo miki ba amma kullum abin
inga kina cikowa kina kiba saidai kullum in ganki zuru-zuru da ido sai dogon hanci me kike
tunani zainab? shin ke bazaki kwantar da hankalinki ba kodon yaranki"
Murmushin yake nayi tareda riko hannuwanta duka biyu "ba abinda ke damuna ummi duk
abinda nakeso ba abinda bakumin ba kawai dai may be yawon makaranta ne yasa kike ganin
hakan" ido ta zubamin kamar mai nazari irin kallon da take mana a lokacin da idan tana zargin
muna boye wani abu
"Indai ko zirga-zirgar makaranta ce ta maidaki haka to zansa yayanki ya kaimiki mota daya cikin
ta gidannan"
Wannan karon kasa daurewa nayi saida na rungumeta tareda fashewa da kuka "don Allah ki
yafemin ummi ku yafemin abinda kuka gudarmin kenan na kasa fahimta don Allah ku yafemin"
bayana ta shiga shafawa " kingani ko? kingani ban gayamiki kar ki kara zuwa kimin kuka ba
zainab kodai akwai abinda kike boyemin" kaina na shiga girgizawa tareda kara shigewa jikinta
"bakomai ummi wallahi bakomai"
"To karki kara kuka kinji karkisa mudinga ji aranmu kamar ba mu cika alkawarin mahaifinki ba
Abbanki har ya rasu yana maimaita a kula dake a kyautatamiki ki gayamana zainab idan akwai
abinda muka kasa miki don Allah"
Ganin itama ina neman sakata damuwa yasa na ware na dinga zuba mata shagwaba ita kuma
sai riritani takeyi daki ta shiga ta dakkomin abayas tace gani tayi ana talla suka burgeta tasanni
da son abaya ta siyamin ai kwa nahau murna nashiga gwadawa ina tsalle kamar wata Aysha
Bangaren Yaya Isma'il na shiga (shine babba a gidanmu) matarshi Anty nasma kawai na samu
gaisawa muka yi cikin girmamawa na tambayeta su Safwan
"Sun fita tareda abban nihal rigima suka sakamishi kan teddy shine ya kwashesu ke har yasir
na hada nace duk a tafi"
"Ai gwanda da kika mika su can ko bakinki ya huta"
Sallama na mata na shiga bangaren yaya Abbas (shine kebin yaya babba) shikam yana nan
gida gaidashi nayi cikin mutunci da kaunar juna itama matarshi na gaisawa mukayi ta kawomin
dan abin motsa baki tareda wucewa dakinta ta barmu tare
"Yadai ZEEN ABBA ba wata matsala dai ko" murmushi nayi "ba matsalar komai yaya"
"Idan da wata matsalar kigayamin dubi yanda kika rame ko wani abun yake miki har yanzu"
"Ba abinda yakemin yaya bakomai"
"Idan har kikaga da wata matsala ki dawo gida don bazamu zuba ido ya kashe mana ke ba idan
shi baya bukatarki mu muna bukatarki don haka bazamu zuba ido ya cigaba da wasa da
rayuwarki ba kinji ko"
"Insha Allah yaya" tun dama can yaya mutum ne mai zuciya kuma tsayayye kan ra'ayinshi shine
mutum na farko da ya fara nuna tsanar aurena da lawal tun farkon soyayyarmu baya kaunar
lawal bare kuma abubuwan da suka zo suna faruwa daga baya
"Zan turo miki kudi ta account dinki ranar monday kije asibiti a duba dalilin wannan ramar"
"To yaya" na amsa cikin girmamawa
Sai la'asar nayi shirin barin gidan tareda sha tara ta arziki daga mahaifiyata da kuma 'yan
uwana naji dadin fitar koba komai na kwanta jikin mahaifiyata ta kara kwantarmin da hankali
Banyi girki ba saboda munzo da abinci tun daga gida wanda ummi tasa aka girka mana na
musamman saida mukayi sallar magriba sannan na zuba mana abincin
Muna tsaka da cin abincin ya shigo kallo daya yayiwa shinkafa kazar da muke ci ya kawadda
kai tareda wucewa daki koda ya fito har mun kammala an kwashe kayan ina kokarin jona
wayata caji ya dawo falon yana zama yaran suka dakatarda wasar da sukeyi kowannensu ya
nutsu musamman amra da ta shige jikina
Kallonsu yayi " meye kuma kuka daina wasan" hannu ya mikawa amra data shige jikina "zo
amra na zo inji wa ya taba ki" kafada ta make cikin shagwaba take fadin "Um um ba kaine ka
dakeni ba da safe" kunnuwanshi ya kama "yi hakuri shalelen mommy zo gurin abbanki kinji"
Matsawa tayi ya dauketa ya dora akan cinyarshi wasa ya shiga yi mata tana kyalkyala dariya
sakkowa yayi ya hada kan yaran duka yana musu wasa abinda na dade bangani ba sam baya
cikin iyaye masu jan 'ya'yansu a jiki wani annurin farinciki nake hangowa a fuskokinsu
Iyaye kowane akwai rawar da yake takawa a zukatan yaransu basu rasa komai ba daga gareni
amma kuma yau sai na hango wani bangare na farinciki a tare da su saboda kasancewar
Abbansu kusa dasu kamar a mafarki na tsinci maganarshi " mama tace kunje kinkai harda
gudummawa an gode sosai"
Kallo guda na mishi na kawadda kai " eh wallahi ba komai" hmmmm lawal kenan ai saidai in ba
wani labarinka wallahi a wannan lokacin nasan abinda yake a zuciyar lawal na gama
karantarshi tsaff kudin da mama ta rage yakeso in bashi "kaiii wallahi namiji bayada kunya"
Washe gari saiga mota ankawomin daga gida godiya nakira na musu lawal na daki naje na
sameshi ina murna " abban safwan ga mota can an aikomin daga gida in rika zuwa makaranta"
"Allah ya kyauta" daga wannan bai kara magana ba jiki a sanyaye na juya na koma waje
Da motar nayi amfani na sauke su safwan a makaranta nima na wuce tawa
samuwar motar ya saukakamin sosai da ita nake kai yarana makaranta nima da ita nake zuwa
Tunda muka fito lecture muke zaune muna fira da wayanda muke tare nafisa da kuma maman
ayman sai zee lawal haka muke mu hudu saboda banason tarkacen kawayennan tun dama can
Kallon Nafisa nakeyi da ta dage tana zuba kalaman soyayya a waya ko ba'a fada ba nasan
Ahmad ne saurayinta ko kuma ince mijin da zata aura
kallona tayi "yadai maman amra sai kallona kike ina zuba soyayya da hubby" murmushi nayi "ai
dole na kalleki irin wannan love haka amma dai da zakiji shawarata da kindan rage "
Ido ta zare "me zan rage maman amra? soyayyar? hmmm wallahi bazan iya ba don bakisan
yanda nake kaunar hubby bane shima yake kaunata bazaki gane yanda nakeji ba hmmmm abin
ba'a cewa komai" ta karasa fadi tana lumshe ido
"hmmm da zakiji shawarata da kin rage wannan haukar don wallahi ba abinda zata tsinana miki
sai wahala kinganni