Showing 51001 words to 54000 words out of 62089 words

Chapter 18 - Aure Da Karatu Book Complete Rumaisa Sidi

Rumaisa   

18 Jul 2026

515

ba" ta sako ƙarafi kamar
yadda ta saba


"Ai nima naga ina buƙatar kulawar nan ko?Ko don kinfini baki,tun daga Kaduna har Sokoto ki
kasa ɗaga waya ki kira mijinki ki tambayeshi ya hanya,sai ni zaki ga laifina kan naƙi kiranki,ke
shikenan kullum ƙorafi dai ba randa za a miki daidai" daga haka ya buga tsaki tare da kashe
wayar

Da kallo tabi wayar bayan ta sauketa daga kunnenta,leɓonta na sama ta ciza tana ƙoƙarin
haɗiye kukan da ke taso mata.


Wai meye laifinta? Ina ta kuskure? Me ta rasa? Kyaun fuska ko kuma kyaun jiki?









*RUMAISA'U SIDI*✍️✍️✍️



AURE DA KARATU
NA

RUMAISA'U SIDI

FARAR ANIYA WRITERS


page 35


Number Ya Bashir ta ƙara dannawa kira bugu biyu ya ɗaga "Ya dai"ya tambaya kamar wanda
aka yiwa dole.A sanyaye tace "Inaso ne inje gidan Anty Maryam idan ka bani dama"


Jikinshi ne yayi sanyi jin yadda muryarta ta sauya "Allah ya tsare amma ki dawo da wuri saboda
nima ina hanya" amsa mishi tayi da "To"tare da kashe wayar ba wata addu'a ko fatan
dawowarshi lafiya.


Shiryawa tayi tsaf sannan ta shiga ɓangaren Mama tare da gaidata,amsawa tayi ba yabo ba
fallasa ta gaya mata fita zata yi,tace Allah ya tsare hanya.


Driver tasa ya kaita saboda ita batada Mota,ba yadda batayi da shi kan ya siya mata Mota ba
amma yaƙi sai yace ga driver nan duk inda zata je ya kaita,har ƙarar shi ta kai wurin
mahaifiyarshi kan ai ga Zainab nan da mota,amma sai ya kafa hujja da ai bashi ya siyawa
Zainab ɗin ba.

A bakin get ɗin ta sauka tare da faɗawa driver lokacinda zai zo ya ɗauketa.Sallama tayi bayan
ta isa tsakiyar falon,murmushin yaƙe ta saki bayan fitowar Antyn daga kitchen tana amsa
sallamarta.


"Ahh sannu da zuwa Zubaida,ki zauna mana"ta faɗa tana nuna mata kuhera,zama tayi kamar
wata munafuka sai murmushi take dokawa kamar sabon kamu,saboda abu ne wanda bata taɓa
kawo wa a ranta ba wai zata zo wurin wannan matar da tunanin neman taimako.


"Yawwa Zubaida ɗan bani 5minutes please na kammala abin da nake yi"ta tsinkayi muryar
Antyn tana faɗi tare da jera mata lemu da kuma cups.


Tana nan zaune har Antyn ta fito ɗauke da manyan kuloli haɗaɗɗu,mayafi ta ɗora a kanta
sannan ta fita da su,bata jima ba ta dawo,mayafin ta ajiye sannan ta koma kitchen nan ma ba
jimawa ta dawo ɗauke da wani abincin da aka zuba a plate "Kiyi haƙuri na barki kina ta jira

na,Kinga bismillah matso kici abinci,tun bai huce ba" ta faɗa tana tsiyaya ruwa ta sha


Sha'awar da abincin ya bata da kuma ƙamshin da ke tashi yasa ta fara cin abincin da niyyar yin
cokali 2 ko 3 sai gashi ta zarce,batasan ta cinye abincin ba saida taji Anty na faɗin "Bari in ƙaro
miki"girgiza kanta tayi cikin kunya "A'a wallahi Anty na ƙoshi"


Zama Antyn ta gyara tana fuskantar Zubaida"Ina jinki Zubaida,tun jiya da kika kirani hankalina
ya kasa kwanciya,ina fatan dai lafiya" ajiyar zuciya Zubaida ta sauke idanuwanta na tara ƙwalla


Hannunta Antyn ta kama tare da nufar sama inda inda ɗakinta yake,zaunar da ita tayi bakin
gadon sannan ta jawo kujerar da ke gaban mirrow ɗinta ta zauna tana fuskantar ta "Meke
faruwa ki gayamin"


Numfashi taja tare da ɗauke ƙwallar da ta tarammata a ido "Ina cikin matsala Anty,na rasa da
wa zanyi magana in samu mafita,duk wanda na tunkara da matsalata abinda nake ganin bazai
yu ba yake kawo min a matsayin mafita,shi ya sa nazo gare ki da fatan in samu warwarewar
matsalata a wurinki Anty"ta ƙarasa tana ɓarkewa da kuka.

"Subhanallahi Zubaida me ya faru?Ki sanarda ni damuwar ki ni kuma na miki alƙawarin matuƙar
inada dama zan samo miki mafita da yardar Allah"


Idanuwanta ta zuba mata sannan sannu a hankali ta fara jero mata halinda take ciki "Da farko
dai Anty zan alaƙanta duk wata matsala da nake ciki da shigowar Zainab cikin rayuwar mijina a
karo na biyu,kamar yadda kika sani Ya Bashir ya so Zainab a lokacinda take budurwa,rashin
samunta yasa Anty tayiwa Abba magana akan ai gani nan,ba don Ya Bashir naso ba aka yi
aurenmu.Duk da ba shi ya zaɓeni ba,amma ya zauna dani zama na amana,yana ƙoƙarin
faranta min a koda yaushe,duk shirmen da zan mishi baya fushi dani.Rashin girkina bai canja
da yadda ya saba yi min ba,saidai ya shaida min nayi ƙoƙari na koya ni kuma na gaya mishi
bazan iyaba gaskiya.Dama kuma ni gani nake idan na roƙeshi abu baya saurin bani wannan
yasa idan inason abu saidai naje na faɗawa mahaifiyarshi ta mishi magana ya bani,yasha faɗa
min na daina yi mishi haka idan ina son abu na dinga faɗa mishi da kaina,ni kuma ganin kamar
idan ita tayi magana yafi saurin bani yasa naƙi dainawa.Ana haka na samu cikin Zee,nasha
gata a wannan lokacin daga shi har mahaifiyarshi da Abba ba wanda baya kula dani.Ƙauna
suka nunawa cikin kamar me,haka ma mahaifiyata da duk wani masoyinmu.Cikin kuma ya sako
min fushi da saurin faɗa wanda kai tsaye zan fara cin mutunci ko da kuwa da shi ne,kuma a
gaban kowa.Sosai muka yi rigima lokacin da na haihu na samu ƴa mace,tun a asibitin ya faɗa
mini yayi wa yarinya huɗu ba da suna ZAINAB a gaban kowa na hau rigima nace ni ban yarda

ba,saboda sanin muhimmancin Zainab ɗin a wurinshi.Duk haukar da nayi wannan bai canja
komai daga sunan da ya sakawa ƴarshi ba.Rago Anty ta siya da nufin canjawa yarinyar suna
amma Daddy ya hana.Bayan haihuwar ne Anty ta samo min yara ƴammata biyu,ɗaya mai shara
da girki,ɗayar kuma wadda zata riƙa kula da Zee,saboda ni ko sakamata pampers ban iya
ba,mahaifinta ke saka mata,to bayan zuwan mai aikin sai komai ya koma hannunta.Kullum Ya
Bashir na faɗa min na rage yawan ƙorafi,bayan kuma duk abinda nayi magana to tabbas naga
an tauye min hakkine,kinga ko bazan zuba ido a tauye min hakki ba.Bayan tasawar Zee ne na
sallami ɗayar mai aikin,na bar wadda zata ci gaba da kula da gidan da kuma girki,mun fara
samun matsala da shine bayan ya min gargaɗin kar in ƙara tura mai aiki ta gyara mishi ɗakinshi
ya fi son in gyara da kaina,ni kuma a gaskiya bazan iya ba.Na shiga tashin hankali lokacin da
naji mutuwar auren Zainab,saboda nasan abinda ke tunkaro ni,ban ƙara gigicewa ba saida tazo
garinnan naga yadda yabi ya ruɗe akanta,har kashedi na mata amma baiwar Allah nan ta kasa
barmin mijina"ta tsagaita tana share hawayen idonta sannan ta ci gaba.


"Na roƙe shi kar yayi aurennan amma saida yayi,ina raye Ya Bashir ya auro Zainab ya kawota a
cikin gidanshi,wanda a wannan lokacin ni ina gida bisa shawarar Anty Amina da tazo ta tafi da
ni.Zamana gida ba abinda ya ƙaramin sai tashin hankali saboda biris da Ya Bashir yayi dani tun
bayan komawata gida sau ɗaya yaje nace bazan koma ba daga nan bai ƙara dawowa ba.Ni da
kaina na maida kaina ɗakina Anty bayan da naji Anty ta tubure akan sai Ya Bashir ya sakeni,ni
kuma har ga Allah ina ƙaunar mijina.Ko da na dawo ɗin ma ba abinda na tsinta bayan
takaici,saboda a fili Ya Bashir ke nuna kulawarshi ga Zainab,duk abinda tayi zai yaba,saɓanin ni
da kullum banayin daidai,har video girki nayi downloading a wayata don in mishi nima in
burgeshi amma da ya ci sai ya furzar ya kirata ta kawo mishi nata.Anty yanzu komai na yiwa Ya
Bashir banyi daidai ba,komai nayi bana burgeshi,na rasa ya zanyi,har wata ƙawata tace nazo ta
kaini wurin wani malami da yake bada taimako naƙi amincewa saboda ina tsoron faɗawa wata
halakar.Abinda yasa nazo wurinki saboda kece mutum ta farko da ta fara ƙoƙarin nusar da ni
akan gidana amma naƙi saurare,a yau nazo ina roƙon ki taimakamin Anty ki faɗa min yadda zan
yi yaƙin ƙwato mijina a hannun Zainab" ta ƙarasa tana saukowa daga kan gadon ta zube gaban
Anty tana rera kuka.



Hannunta Antyn ta kama tare da zaunar da ita unda ta tashi,fita tayi daga ɗakin,ba jimawa ta
dawo da gorar ruwa a hannunta,tsiyaya ruwan tayi a kofi sannan ta miƙawa Zubaida.Karɓa tayi
tashi tana sauke ajiyar zuciya.



Komawa Antyn tayi ta zauna tana kallon yadda Zubaida ke shan ruwan,tausayi ta bata har wata
rama tayi alamun tana cikin damuwa sosai ga kishi da ke cinta.

"Da farko ina so ki janye alhakin shigar ki wannan halin akan kowa,ke kika cuci kanki
Zubaida,duk abinda ya same ki ke kika ja,maganar gaskiya ma Bashir yayi haƙurin zama da ke
tsawon wannan lokacin.Haba Zubby sai kace ba ƴar zamani ba,ke shikenan ba abinda kika iya
sai yin ɗinki ki matse jiki,bayan gyaran jikin ma baki iya ba.Ace mace da mijinta Zubaida amma
ace bakya gyara?To ina mace anan,bari in faɗa miki ba wai ki shiga toilet ki bugo wanka ki saka
sutura mai tsada ne kawai gyara ba a'a,ke gyara dai da zai janyo miki daraja da kuma
girmamawa a idon mai gida,taya miji zai miki abinda kike so bayan ke baki mishi abin da zai ji
daɗi? Ɗan turarennan ma mai ƙamshi bakya sakawa Zubaida,ba wai sai kina wari zaki saka
turare ba,ke da kanki idan kika saka turare zaki jiki cikin nishaɗi,to bakya yi Zubaida,magana
mai daɗi wannan bata fitowa daga bakinki a lokacinda kike magana da mijinki,namiji da kike
gani tamkar jariri haka yake,duk yadda kike ganin idan ya fito yana muzurai to zaki samu
ƙaramar yarinya ke juyashi a cikin gida,da zarar kin san kanki,kina gyara kanki ta ko ina,kin iya
magana mai siye hankalin ɗa namiji,kina girmama iyayenshi da ƴan uwanshi,to wallahi da izinin
Allah zaki same shi a tafin hannunki.Irin ku ne mazajenku ke faɗawa tarkon matan waje,saboda
ku na cikin kun kasa yi musu abinda na wajen ke musu.Kinada kyau Zubaida,kinada ƙira da
komai ma,to meyasa da ƙuruciyarki kike nema ki kashe kanki?Sannan da kike maganar Zainab
ta ƙwace miki miji,yo ai dole ta ƙwace tunda ta samu sakarar kishiya,kinyi zaune kina kuka,kin
barmata mijin,wallahi nan gaba kaɗan idan baki gyara ba har dukanki sai yayi.Saboda shi namiji
zai iya yi miki uzuri a lokacin da yake tare dake ke kaɗai,amma da zarar kun zama ku biyu to
bazai ƙara yi miki uzuri ba saboda zai yi tunanin dama rainashi kika yi tunda ga wata halitta
irinki na mishi,daga nan ne wulaƙanci zai shiga,idan kika cika ƙorafi ya sallame ki saboda yana
ganin ko kin tafi ba wata damuwa zai yi ba tunda ga wata yanada" tsagaitawa tayi sannan ta
tsiyaya ruwa tasha tana kallon Zubaida da ta mayar da hankali tana saurarenta.


"Abinda na fahimta manyan matsalolinki sune rashin gyaran jiki,rashin iya girki,rashin iya
magana,da kuma rashin riƙe sirri,dukkan waƴannan abubuwane da rayuwar aure ke lalacewa
matsawar aka samu ɗaya daga cikin waƴannan.Dole sai kin gyara,kin koyi girki,kinsan yadda
zaki yi magana da mijinki,ba da kalar harshen da zakiyi magana da Amina za kiyi da mijinki
ba,a'a muryar da kike amfani da ita idan kina tare da shi ta banbanta da wadda aka sanki da
ita,kar ki kuskura muryarki tafi taki ɗagawa a lokacin da yake magana wannan haramunne,kar
kiyi musu dashi,ko saɓani kuka samu kar kiyi ƙoƙarin fahimtar da shi a lokacinda yake cikin
fushi,ki barshi sai ya huce tukunna sannan ki mishi bayani,kar ki ƙara kai ƙararshi wurin
mahaifiyarshi ko taki mahaifiyar duka waƴannan biyun kuskurene babba.Ita dai mahaifiyarshi
ƙimarki zata rage a idanuwanta,zata daina ganin girmanki za ta ga kamar kina tonawa ɗanta
asirine a idon duniya.Mahaifiyarki kuma zata tsani mijinki zata ga kamar yana musguna miki,ke
har ki manta ma da kunyi wani faɗa amma ita bazata manta ba zata ci gaba da kallonshi da
wannan abun.Duk lokacinda ya kasance a rayuwar ma'aurata akwai third party to akwai
matsala,kar ki kuskura ki bada wata kafa da third party zai shigo tsakaninku,duk wani saɓani da
ya shiga tsakaninku ki rufe shi ki bari ku sasanta kanku,kar ki yarda wani ya fahimci akwai
matsala a tsakaninku bale kuma har kishiya,wallahi dole ma Zainab ta rainaki"Anty ta ƙarasa
tana buga tsaki tana jin kamar ta shaƙo wuyan Zubaida

"To yanzu yasan kin fito ko haka kawai kika fito"ta tambaya ganin kamar harda hauka ke cin
Zubaidar.Kanta ta gyaɗa "Ya sani saida na kirashi na fito"


"Baya nan ne?"Anty ta tambaya kanta ta ƙara gyaɗawa "Eh ya rakata Sokoto,amma yace min
yau yana hanya"hannu Anty ta buga a ƙirji tana salati "Yanzu mijinki na hanya ƴarnan amma
kika biyo hanya kika zo? To idan ya dawo wurin wa zai sauka"ta faɗa tana riƙe haɓa.Shiru
Zubaida tayi tana jin tausayin kanta

"Idan miji na hanya ba'a fita Zubby,kuma ki kwantarda hankalinki zan kaiki wurin gyaran jiki da
turarukka masu ƙamshi zan kuma koya miki abinda ya samu na girki,In sha Allah sai kin ƙwato
Bashir ɗinki a hannun Zainab,sai kin karkato hankalinshi ya dawo kanki,ke sai ya koma ko zama
zaiyi sai ya tambayeki"ta ƙarasa tana ƴar dariya

Dariya Zubaida keyi itama tana share ƙwallar da ke mata zuba "Na gode sosai Anty,In sha Allah
zan aje hankali in koya yadda ya kamata"






RUMAISA'U SIDI




*AURE DA KARATU*

*NA*

*RUMAISA'U SIDI*

*FARAR ANIYA WRITERS*


*Page 36*

Ƙara gyara zama Anty tayi tana fuskantar Zubaida "Ki kwantar da hankalinka da yardar Allah
zan kaiki inda za a share miki hawayen, ki daga yanzu kin daina zubar da hawayen ki akan
kishiya,kuma zaki ciri taki tuta a idon Bashir" wayarta ta ɗauko dake ajiye akan mirrow sannan
ta ƙasa dubin Zubaida
"Zan haɗa ki da shahararriyar mai ingantattun magunguna da turarukannan wato MEERAH_B
HERBS.A wurinta zaki samu duk abubuwan da ki ke buƙata,tsafta zata gyara ki da sahihai
kuma ingantattun magungunan ta, har Amar'e take gyarawa ,ke uwar gidan ma ba'a barta a
baya ba.Kin ganni nan lokacin da na haifi Marwan wurinta na siye kayan da naji daɗin su,nima
wata ƙawata ce ta haɗani da ita,har yau ban daina sakawa wannan ƙawar tawa albarka ba
kuma jima ban daina siyayya a wurinta ba.Kinga wannan tumbin da kika fara radawa
sanadiyyar haihuwar Zauna,tsaf zai ɓata idan har kina amfani da magunguna ta.Maganin sanyi
da na haihuwa duk tana yi.Don haka ki kwantar da hankalin ki"


Ajiyar zuciya Zubaida ta sauke "Na gode sosai Anty wallahi har naji daɗi" murmushi Antyn tayi
"Yanzu zan kira ta zata haɗa miki kaya masu kyau" wats number ta lalubo ta dannawa Kira
bugu biyu aka ɗaga


Cikin mutunta juna suka gaisa bayani ta mata akan kayan da take so a haɗa mata ta faɗa mata
ba matsala.


"Ki saka number ta idan kika tashi ki dinga kiranta"


Wayar Zubaida ta ɗauka tana saka number da Anty ke karanto mata "08142800199.Wannan
ita ce number MEERAH-B HERBS ki riƙa siyayya a wurinta za kiji daɗi"


Kaya Anty ta duba mata masu kyau ta haɗa mata "Kiyi amfani da wannan kafin naki su iso,don
Allah Zubaida ki maida hankali,ki cire wannan sakarcin,kisan ciwon kanki.Idan muka bi daki daki
kema zaki ciri tuta a idon Bashir"


Sauri-sauri ta dawo gidan,tana fatan wannan ya zamo silar warware war damuwarta.


Kitchen ta shiga bayan tayi download ɗin video yadda ake kallon.Step step ta dinga bin abin har
ta samu ta kammala daƙar.

Toilet ta wuce ta feso wanka da wani sabulu da Anty ta haɗo mata a cikin kayan,turaren ta
murza a jikinta tana jin wata mutuwa na shigar ta.Ƙamshin na daban ne,kayan ma na daban ne.


Kallon kanta tayi a madubi bayan ta gama kafa ɗaurin ɗan kwalin atamfar ta.Ita kanta ta san
tayi kyau.


Turaren ta ƙara ɗaukowa ta fesa tana jujjuyawa gaban madubin.Wayarta ta ɗauka tare da fita
falon, talabijin ta kunna sannan ta koma kan kujera ta ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya tana danna
wayarta.


Bataji tsayuwar motar shi ba sai sallamar shi taji a bakin ƙofar,da sauri ta juya tare da tashi a
hankali tana ƙawata fuskarsa da kyakkyawan murmushi.


Sanarwar yayi a wurin yana kallon ta,saboda irin kyaun da ta yi a cikin atamfar.Kallonta ya ke
Yadda take takowa a hankali kamar mai tausayin ƙasa.


Ya shagala da kallon ta yaji tana mishi magana cikin wata sanyayyar Muryar da bai santa da ita
ba"Sannu da zuwa Hubby"ta faɗa tana wani karairaya tare da zare jakar da ke hannunshi.


"Bismillah muje ko"ta faɗa tana yin gaba ganin yadda ya zuba mata ido.Ɗakinshi suka nufa
kallon ɗakin yake shima duk da ba wani gyara na musamman aka mishi ba amma sai ƙamshi ya
ke.


Toilet ta shige ba jimawa ta fito tare da samar da shi ga ruwan wanka can.Saitin zuciyarta ta
dafe bayan ya shige,bata taɓa aza zata iya abinda Anty ta koyar da ita ba,amma

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
google.com, pub-9213700357025247, DIRECT, f08c47fec0942fa0