Showing 54001 words to 57000 words out of 62089 words

Chapter 19 - Aure Da Karatu Book Complete Rumaisa Sidi

Rumaisa   

18 Jul 2026

531

ga dukkan
alamu akwai nasara daga yadda taga ya fara canja wa yana bin ta da mayen kallo.


Koda ta zuba mishi abincin ma kallon mamaki yake mata yadda take mishi fira mai daɗi kuma
cikin natsuwa.


Ba laifi tayi ƙoƙari wurin dafa abincin.Kallonta yayi bayan ta dawo daga kai kayan kitchen
"Abincin yayi daɗi Babu,kin yi ƙoƙari sosai,haka ma wannan ƙamshin ya tafi dani sosai,wannan
ma ya min kyau"ya faɗa tana shafa dogon gashinta da ta taje ta shafe da mayukka.

Murmushi tayi tare da riƙo hannunshi ɗaya"Na gode da yabawar ka,idan har zaka ci gaba da
min hakan ni kuma zan ƙara ƙaimi don in ga na farantama.Don Allah Ya Bashir kar ka daina so
na,na maka alƙawari zan canja,duk abinda baka so zan daina,Ni dai fatana ka soni fiye da
yadda kake son Zainab"ta ƙarasa ƙwalla na taruwa a idanuwanta.

Hannunta ya ƙara damƙewa yana jin wani kalar tausayinta na ratsa shi,hannunshi yasa yana
ɗauke ƙwallar da ta zubo mata "Bana son kina saka damuwa a ranki,ko kiyi tunanin bana
sojoji,wallahi ina sonki Zubaida matsawar zaki ɗore a yadda na dawo na same ki yau,to zakiga
zallar ƙauna"

Wani daɗi ne ya ratsa ta,yaushe rabon da ta sami irin waƴannan kalaman daga mijinta.Tun
zuwan Zainab komai ya canja,tana fatan wannan ya zama silar warwarewar matsalolinta.


Wata kalar duniya take jinta a kwana ukun nan da tayi da mijinta ba Zainab tsakani.


Zaune take tsakiyar gadon tana kallon yadda yake taje sumar shi "Gaskiya Ya Bashir kana ji da
suman nan taka kamar wani gaye"ta ƙarasa tana sakin dariya


Juyowa yayi ya dubeta tare da mata hararar wasa "Na san dai wata harda suman nan tawa ta
jata ta ƙara soma,har take kuka idan bata aure ni ba zata mutu"ya ƙarasa yana mata gwalo.


Ɓata fuska tayi tare da doddoka ƙafarta akan gadon"Ai kaima haka kace"


Rakoshi tayi har bakin ƙofar,har ya saka ƙofarshi da niyyar fita sai kuma ya dakata tare da
juyowa"Am nace Zubaida kar kiyi girki dani, kin san yau Zainab zata dawo"


Shiru tayi tana binshi da ido,tana jin kamar ta saki ihu.Daƙyar ta iya jawo ƙafafuwan ta ta dawo
falon,zubewa tayi kan kujerar falon tare da sa hannu biyu ta dafe kanta "Innalillahi wa inna ilaihi
raji'un"ta samu ta faɗa daƙyar.Ba ta so Zainab ta dawo yanzu ba,taso ace ta samu koda sati
ɗaya da mijinta amma wannan makirar bazata bari ba.

Number Anty ta dannawa Kira,gaidata tayi bayan ta ɗaga "Ya dai Zubaida,komai lafiya dai ko"

"Lafiya lau Anty,ina murna farin ciki na ya dawo gare ni amma matar nan bazata bari ba
Anty,yanzu yake faɗa min wai yau matar nan zata dawo"


"To shine me?"Antyn ta tare numfashin ta "Ko baki san da ita ba?Dama ai kin san zata dawo,to
miye abin damuwa?Ina magungunan da kika siya?"


"Suna nan Anty ina amfani da su,kuma suna da kyau sosai"


"Yawwa to ki ci gaba da harkokin gabanki kawai,matsawar zaki gyara to wallahi kin fi ƙarfin wata
Zainab.Ke dai kawai ki ci gaba da gyara kuma ki dinga addu'a shine kawai"


Bayan la'asar taji shigowar Zainab ɗin,tana zaune kan kujerar ta ko ɗaga kanta bata yi ba.Jin
Muryar Bashir yasa ta miƙe tare da fita tsakar gidan tana kallon shi yadda ya tattalo jakar kayan
Zainab ɗin.


"Sannu Maman takwara mun same ku lafiya"Zainab ɗin ta faɗa tana duban Zubaida.Ƙyaleta tayi
kamar bata ji ba tayi tsaye tare da riƙe ƙugu tana kallon Bashir


"Bakiji tana gaida ki ba"Bashir ɗin ya faɗa ganin kamar bata ji ba.


Tsaki ta buga sannan ta zubda yawu "Na jita,sannu ta min ko? To ni asibiti ce da zata min
sannu?Ko kuma wata nakasa ta gani a jikina?"ta juya wurin Zainab ɗin tana nuna ta "Na gaya
miki ki fita harkar,ba ruwana da ke,kiyi rayuwarki inyi tawa.Mijine dai kin aura ko? Kije ke da
Allah,kuma wallahi duk wani hakki nawa da aka ci ban yafe ba"daga haka ta juya tare da
komawa sashe ta.








*RUMAISA'U SIDI*✍️✍️✍️

*AURE DA KARATU*

*NA*

*RUMAISA'U SIDI*

*FARAR ANIYA WRITERS*


*Page 37*


Guntun murmushi na saki bayan ɓullewarta,Allah ya gani na tsorata da irin kyaun da naga
jikinta yayi,ga wani fitinannen ƙamshi da ke fita a jikinta.


Amma daga lokacin da ta buɗe bakinta sai hankalina ya ɗan dawo.Shi ya jamin jakata har cikin
gida,sannan ya fita bayan ya tambaya idan akwai abin da nake buƙata nace babu.


Gyaran gidan na shiga yi,nan take na ƙalƙaleshi tsaf na watsa turaren da nazo dashi a cikin
burner sai gashi gida ya game da ƙamshi.


Kitchen na shige duk da na gaji,amma haka na daure na girka muna sauƙaƙƙen abinci.Wanka
na ɗanɗasa bayan na ƙare sannan na jiƙe jikina da turare na fesa kwalliya ta.


Dogon hijabi na ɗora akan kayan jikina sannan na ɗauki wata ƴar ƙaramar jaka na nufi
ɓangaren gwaggo.


Tsaraba ce da nayo na kaimata,tare da ta Zubaida "Ki kaimata da kanki mana,ai mun gode
sosai wallahi kinyi ƙoƙari"ta faɗa tana miƙo min na Zubaida


Ba zan iya musu da ita ba,wannan yasa na karɓar tare da yi mata sallama na fito.


Ɓangaren na nufa,tsayawa nayi a bakin ƙofar falon ina doka sallama,daga ciki naji an amsa min
saida na shigo na samu ƴar aikinta na wurin dinning tana zuba mata abinci,ita kuma tana

hakince kan kujerar tana jira a kawo mata.


Ƙara sawa nayi wurin da take zaune na ajiye mata ledar sannan nace "Maman Zainab ga
wannan aci da haƙori"daga haka na juya ina ƙoƙarin barin falon


Ƙiiiii naji an janyo hijabi na da ƙarfi,ban shirya wa hakan ba shi yasa kai tsaye nayi baya cikin
iyawar Ubangiji na dafe kujerar da ke kusa da Ni.


Miƙewa tayi a fusace ta watso min ledar da na kawo mata,nan take kayan miyar da na kawo
mata suka zube ƙasa.


Yatsunta ta buga suka bada sauti sannan tace "Wannan ya zama na ƙarshe da zaki je gida
kuyo barbaɗe-barɗenku sannan ki dunƙulo ki kawo min.Su dai da kika shanye sun shanyu
Amma wallahi ni nafi ƙarfi ki"


Juyawa nayi da sauri don barin ɗakin don a yadda raina ya ɓaci komai zai iya faruwa.Amma
me?Ina juyawa naji maganar ta ƙasa-ƙasa "Banza kawai Karuwa"cak na tsaya tare da juyowa
da ƙarfi wanda ko ita saida ta zabura tare da yi baya kaɗan


Wurinta na matsa "Maimaita abinda kika ce"na faɗa ina juya hannuna


Cike da rashin kunya ta ƙara faɗi "To tsoron ki nake da bazan maimaita ba?Nace banza Karuwa
mai ƙwacen.........."



Tasssss na ɗauke ta da mari batare da jiran ta ƙarasa ba,dafe kunci tayi tana kallona "Ni kika
mara"ta faɗa tana nuna kanta


"Wannan ya zama na ƙarshe da ƙazamin bakinki zai ƙara faɗa min magana irin wannan,idan
can gidanku ba a miki tarbiyya ba to ni nan zan miki.Kar kiga ina ƙyaleki,wallahi na fiki iya
rashin mutunci.Amma idan kina musu ki ƙara magana ki gani" daga haka na bar falon zuciyata
na tafasa sosai,na tsani wannan kalma.

Ina zaune falona ina latsa wayata don ta ɗan ragemin abinda nake ji ya shigo kamar wanda aka
koro.



"Me Zubaida ta miki da zakije har gidanta ki mare ta"ya katse numfashi na daga gaida shi da
nake ƙoƙarin yi


"Ita da ta turo ka,bata faɗa ma abin da ya jawo hakan ba" na faɗa ina ɗauke kaina abin da ya
ƙara tunzurashi


"Ba zan ɗauka ba,wannan ya zama na ƙarshe da zaki ƙara ɗora mata hannu da sunan duka,ko
ni da nake mijinta ban taɓa dukanta ba.Don haka kema wannan ya zama na ƙarshe"


Zuciyata ce ta kawo wuya nima na miƙe a fusace "Wallahi muddin ta ƙara shiga gonata sai nayi
fata-fata da ita,idan har kana gudun wani abu ya taɓa ta to ka maida ta ciki ƙarewar ƙauna"daga
haka na ɗauki wayata don in wuce ɗauki


"Wato ina miki magana wuce wa ma zaki yi ko? Tafiyar kwana uku duk ta canja ki, ni bazan
ɗauki wannan abin ba gwanda ki sani tun yanzu"


Idanuwana ne suka cika da ƙwalla na dube shi "Tafiyar da nayi ai kasan inda naje,wata ƙila can
aka koyo min baƙin halin"daga haka na shige ɗaki na.


Nasha kuka sosai a wannan ranar,ko da dare yayi nayi shirin bacci tsaf na gyara kwanciyata sai
gashi ya kirani in kawo mishi abincin shi.


Haɗa kayan nayi na kai,koda naje tana kwance akan kujerar ɗakin,gabanshi naje sannan na aje
tiren abincin "Yawwa ƴar albarka" Zuba mishi nayi sannan na miƙe tsaye,kujerar ya nuna min
"Kinga ƴar uwarki zazzaɓi ke damunta saboda kukan da ta sha.Don Allah Zainab ku dinga
haƙuri da juna"

Ko gefen da take ban kalla ba nace "Ai tunda kana nan zaka kula da ita"daga haka na bar falon.

Kwana biyun nan nawa haka suka tafi ba daɗi,duk da idan muna waje ba wanda zai fahimci
abinda ke faruwa a tsakanin mu.


Shima kuma shareni yayi suna zuba soyayyar su shi da sabuwar Zubaidar shi.


A tsaye na fara rashin lafiya,bana cin abinci,ga jiri,nan take na rame.Gwaggo ce ta fara ankara
da halin da nake ciki "Zainab ki faɗa min damuwarki,duk gidan nan baki da kamata.Ni kamar
Mahaifiya nake a wurinki.Na daɗe da fahimtar akwai abin da ke faruwa a tsakanin ku da yaron
nan,ki faɗa min kinji"

Murmushi nayi mai ciwo sannan nace "Ba komai Gwaggo, kawai banjin daɗi ne kwana biyu,
amma ba wata damuwa"ido ta zuba min alamun bata yarda ba


Ajiyar zuciya ta sauke sannan tace "Shi kenan,idan ma akwai abin da kike ɓoyemin Allah ya
yaye miki damuwarki.Kuma gobe Kiyi ƙoƙari kije asibiti ba a zama da ciwo kinji"


Kaina na gyaɗa "In Sha Allah zanyi ƙoƙari in je"


Washe gari text na mishi nace ina so inje asibiti ko minti biyu banyi da tura saƙon ba sai gashi
har cikin ɗakina.


Wurina yayo da sauri ya shiga taɓa wuyana "Ba kida lafiya Zainab?Me ke damunki?Innalillahi
wa inna ilaihi raji'un"


Idanuwana na lumshe abinda ya baiwa hawaye na damar zubo wa,nayi kewar wannan kulawar
tashi,ƙara ruɗewa yayi "Don girman Allah ki daina kuka Zainab"


Kaina na girgiza hawaye na min zuba "Izini fa kawai na nema ka bani,naje na dubo lafiya,bance
ka baro matarka ba"


Rungume ni yayi da ƙarfi"Don Allah ki daina wannan maganar, wallahi ji nake na tsani kaina da
faruwar wannan al'amari,ki yafe min Zainab"lallashina ya shiga yi da kalamai masu daɗi tare da
neman yafiya a wurina

Shi yasa na shirya tsaf muka fito, ɓangaren Gwaggo muka shiga muka faɗa mata zamuje
asibiti.Alamu sun nuna taji daɗin yadda ta ganmu.


Gambu ya buɗe min ina ƙoƙarin shiga muka ji Muryar ta tana magana "Ya Bashir kaifa nake
jira"ta faɗa cikin shagwaɓa.


Ko da muka dawo asibitin ƙin binshi ɓangaren gwaggo na yi na wuce nawa ɓangaren.


Koda maganar samun cikina ta fita ba wanda bai yi murna ba.Kullum da kalar ƙwalamar da
Gwaggo zata min,kuma ina jin daɗi sosai.


Haka ma uban gayyar,wata kulawa yake bani ta musamman,kamar wanda za a yiwa haihuwar
fari.


A fili Zubaida ta nuna hassadar ta akan cikin,inda ta bi ta tada hankalin ta.Wannan yasa basa
kwana biyu basu samu matsala da shi ba.


Ni dai fatana Allah ya raba ni da shi lafiya.


*LAWAL*



Tunda aka sallamo Safwan daga asibiti,Lawal ya canja mishi makaranta.Ya maida shi mai
sauƙin cunkoso.


Kulawa yake baiwa yaron ta musamman,duk abinda yake so yana siya mishi.Haka ma Amna da
ke gidansu Zainab duk wata yake siyayya yaje ya ganta.


Nusaiba ma ganin bazata samu riba a Safwan ba yasa ta shafa mishi lafiya.Ta fita harkar
shi,duk da mugun haushin yaron ta ke ji.

Yau tun safe da Lawal ya tafi kasuwa bai dawo ba,har Safwan ya dawo makaranta ba a dafa
abinci ba.


Sai bayan la'asar ya dawo ya jigata sosai ya shigo gidan,da gudu Safwan ya rungume shi "Baba
Ina ka tafi, nayi ta neman ka"kanshi ya shafa yana jin wata ƙaunar yaron na shigar shi.


"Wallahi ina kasuwa Safwan,kayanne sai yanzu suka samu,idan nace na dawo ban siyo ba to
ko gobe ba zan samu ba.Kaci abinci dai ko"


Girgiza kanshi yayi "Aa banci ba Abba"


Nusaiba da ke hakince ya duba "Yanzu Nusaiba shine kika kasa ranta min kuɗi ki dafa abinci ko
don yaron nan"










*RUMAISA'U SIDI*✍️✍️✍️




*AURE DA KARATU*

*NA*

*RUMAISA'U SIDI*

*FARAR ANIYA WRITERS*


*Page 38*

Wani kallo ta watsa mishi sannan ta ɗauke kanta "Ina naga kuɗin da zan ranta ma?Kuma kenan
ta ɗan ka kawai kake ni kuma ko oho"ta ƙarasa tana girgiza jiki.


Wani baƙin ciki ne ya turnuƙeshi a ƙufule yace"Yanzu saboda tsabar rashin tausayi kika bar
yaron nan haka?Ina kuɗin da na baki jiya?Allah sarki Zainab,wallahi ta banbanta da matan
zamanin nan"



Tsaki ta buga cikin jin haushi "To amma duk wannan bai sa ta tsira a wurinka ba,kaga malam ba
fa zaka zo ka saka ni gaba ka dinga min masifa ba ehe,na gaji wallahi"daga haka ta murguɗa
baki tare da buga zane ta wuce ɗakinta.


Idanuwanshi ne suka rine,jikinshi ya ɗauki rawa.Hannun Safwan ya kama ya fita dashi daga
gidan.


Abinci ya siyo mishi ya aje gabanshi "Kaci kaji Safwan,kayi haƙuri,na bar ka da
yunwa"murmushi yaron yayi sannan ya riƙo hannun mahaifinshi ya zaunar da shi "Kar ka damu
Abba, kaima ka zauna ka ci"



Shafa kanshi yayi cikin tsantsan ƙauna yace "Allah yayi ma albarka Safwan"


Sai da ya tabbatar yaron ya ƙoshi sannan shima ya samu ya siye abincin yaci,daga nan wurin
mama suka wuce.


*ZUBAIDA*


Tunda taji samuwar cikin Zainab tabi ta addabi rayuwarta,ta hana kanta farin ciki,ta daina cin
abinci kullum cikin fitina ta ke da Ya Bashir.


Tsaye take gabanshi shi kuma yana zaune kan kujera ya ɗora laptop akan cinyarsa yana aiki.

"Magana fa nake maka,amma ka ƙyaleni"


Kallo ɗaya ya mata ya ci gaba da aikin da yake yi "To me kike so in Miki?"


"Au wato baka ma san me zaka min ba ko? To wallahi dole ayi wacca za a yi"ta ƙarasa tana
ɗaukar filon da ke gefenshi tayi jifa da shi.


Haka ta dinga jifa da duk abin da takai hannunta.Miƙewa yayi ya riƙo ta da sauri kuma a fusace
"Wai kina da hankali kuwa?"


Kamar mai shafar aljanu ta juyo da ƙarfi tana watsa mishi idanuwanta da suka rine "Eh bani da
hankali,ni mahaukaciya ce Bashir"ta ƙarasa tana dukan ƙirjinta.


"Wallahi bazaka taɓa samun kwanciyar hankali ba har sai ka haɗani da likitan da zai duba
ni,nima na haihu kamar yadda zata haihu"


Tureta yayi ta faɗa kan kujera ya nuna ta yana faɗin "Wallahi ba likitan da zan haɗa ki dashi,
lokacin da kike yin allurar ki kin shawarce ni?Har nuna miki fushina nayi akan hakan amma kika
yi biris, kika ce ke bazaki iya haihuwa kamar akuya ba.To yanzu na samu wadda zata haifo min
ƴaƴa miye matsalata da ke"

Zaburowa tayi da ƙarfi ta cakumo wuyan shi "Wallahi Bashir baka isa ba,kai kayi kaɗan ka
tozarta ni.Mugu kawai maci amana Allah ya isar...................."



Tasssss ya ɗauke ta da wani marin da saida ta tangaɗa,nuna ta yayi hannun shi na rawa "Na
gaji da matsalolin ki,haukar ki ta isheni,wallahi idan kika kaini ƙul komai zai iya faruwa"daga
haka ya ɗau kayanshi ya barta nan yashe tsakar falon.



*ZAINAB*

Na tsorata sosai da yanda ya shigo ɗakunan,tashi zaune nayi ina kallon shi cikin mamaki
sannan na dubi agogon ɗakina ƙarfe 12:08.


A hankali nayi magana ganin yadda jikinshi ke rawa "Lafiya dai Ya Bashir"


Kanshi ya girgiza tare da dafe kanshi "Haɗa min ruwa toilet please idan zaki iya"


A gurguje na haɗa mishi tsoro na ƙara shigata saboda ban taɓa ganin shi a irin wannan halin
ba.


Ina nan zaune har ya fito,cikin kayanshi da ke ɗakin ya ƙara shirin bacci ba tare da ya dube ni
ba yace"Bani key ɗin ɗayan ɗakin"


Idanuwana na zaro sannan nace "Lafiya dai,me ya sami ɓangaren ka"


Tsaki ya buga tare da dafe kanshi "Don Allah ki bani"


Washe gari ma anan ya shirya Amma yau koda ya fito ba wannan fushin na jiya,saima tsokana
ta da ya shiga yi.


A kwanakin da suka biyo baya na fahimci sun sami matsala da Zubaida ne,saboda kwana biyu

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
google.com, pub-9213700357025247, DIRECT, f08c47fec0942fa0