Showing 24001 words to 27000 words out of 62089 words

Chapter 9 - Aure Da Karatu Book Complete Rumaisa Sidi

Rumaisa   

18 Jul 2026

532

ina ɗauke ƙafafuwana na ɗauke na mayar kan kujera na
kwanta sannan na bashi amsa yana gab da barin ɗakin dariya nayi a raina "ga tsoro ga ban
tsoro"shine taken lawal

Ashe yasan abinda ya ke wa ƙarfe 12 sai ga mama gidan takan jima ba ta zo ba saida
ƙwaƙƙwaran dalili lemu na kawo mata da sauran abincin da na girkawa ƴan makaranta bayan
na gaidata

"kiramin mijinki kice na iso na gayamishi ganinan zuwa yace idan na zo a kirashi"

"To mama" na shiga laluben number lawal da anty halima ta canjawa saving daga Nisful ta
mayaddashi Abban safwan bugu biyu ya ɗaga "ga mama na jiran ka" daga haka na kashe ɗan
katina

Ba jimawa sai gashi (wata ƙila kasuwar ta su ba nisa😂) gaidata yayi ya na tambayarta gida
tace komai lafiya zama yayi a kujerar da ke fuskanta ta

"Na zaɓi na zo nanne muyi magana saboda tunda na baka kuɗinnan ban ƙara ganinka ba
bayan kuma kace za ka zo da zainab kumin bayanin kalar sana'ar"

Hankalinta ta mayar kaina "ke zainabu gayamin wace sana'a ce ku ke yi" kallon lawal nayi da ya
zubamin ido ina ganin yanda ya ke ƙiftamin ido na yi banza da shi "bansan sana'ar da ya ke yi
ba mama" na bata amsa kai tsaye

"ban gane ba kai lawwali kace min tare ku ke sana'ar"ta faɗa tana tsare shi da ido nima
kallonshi na ke yi sai raba ido ya ke murtuƙe fuska ya yi kamar wani zaki "da kai fa nake
magana" ta daka mishi tsawa ganin ya na maisheta sakarya

"Ni fa mama bazan iya wata sana'ar takalmi ba na bincika ba wata riba ake samu ba"

"to ba ni kuɗina" ta faɗa tana miƙa mishi hannu "kai wane irin sakaran namiji ne da baisan
kanshi ba? kamarka da iyali da komai ka naɗe hannu ka dawo gida ka kwanta don ma Allah ya
ba ka mata ta gari mai rufin asiri ta na iyakar ƙoƙarinta akan ka duk wani nauyin yaranka ta
ɗauke amma saboda zamanka sakarai ba wani alamun damuwa a tare da kai yanzu saboda
kai na siyarda ɗan filina da na ke kallo a matsayin ƙadarar da na mallaka na baka kuɗin amma
kake gayamin ba za ka iya sana'ar takalmi ba to ka bani kuɗina don ni ba sakarya bace irinka in
rabawa ƴan uwanka su da za su iya sana'ar na baka nan da gobe ka kawomin kuɗina"miƙewa

ta yi nima na miƙe ina bata haƙuri

"ke za'a ba haƙuri zainabu ke da kike tare da sakaran miji wanda baisan inda ke mishi ciwo
ba"rakata na yi sannan na dawo falon yana nan zaune kamar zane wayata na ɗauka ina ƙoƙarin
barin falon

"kinyi farinciki kin haɗani da mahaifiyata" waigowa nayi na kalleshi "saboda ni na cinye mata
kuɗi" na mayar mishi da mai zafi don na kunna shi aiko ya kunnu don tashi yayi yana nuna ni
"karki gayamin maganar banza naji ni na cinye kuɗi ai dai na mahaifiyata na ci ba na wani ba
naga ai ke kinada kuɗin amma ba su da amfani tunda an makkale an hanaki ana yanda ake so
da dukiyarki"

"Dukiyata tana hannun waɗanda ya dace kuma waɗanda ba su damu da abin duniya ba da ma
wanda ake tunanin zai cinye ake bibiya wanda aka san dama ya saba da su sai dai fatan
alkhairi da kake faɗar an mallakemin dukiya kasan dai duk cikinsu ba wanda cefanen gidanshi
ya fi ƙarfinshi" daga haka na cikawa sket ɗina iska ganin yanda ya harzuƙa kar ya cafkoni ya
fara kirɓa

Ina shiga na maida ƙofa na rufe da key ina sauke ajiyar zuciya don dama duk maganar da nake
yi a tsorace na ke yinta ina maganar ina kallon motsin hannunshi ina tsoron saukar wannan
gudumar a lallausan kumatu na


Sai da naji hayaniyar yara sannan na fito ba ya falon da alama ya daɗe da fita

Haka muka ci gaba da zaman bansan yanda ya ƙarasa da mama ba don ban ƙara kula shi ba
ganin shima ya ɗau fushi da ni kamar ni na kama muka cinye kuɗin

Karatuna na ci gaba da yi da kuma kula da tarbiyyar yarana ta ɓangaren kasuwancina
Alhamdulillah ina samun ci gaba ina harkokina cikin iyawar uban giji

Jarabawar da muka fara ita ta ƙara ɗaukemin hankali daga shiga harkar lawal sosai na duƙufa
ina fatan cika burina da lawal ya ɗau aniyar tarwatsawa har muka kammala cikin nasara aka tafi
hutu

Yau tunda na wayi gari nake fama da faɗuwar gaba abin ba daɗi sunan Allah na shiga kira ina
fatan ya bani ikon ɗaukar abinda ke tunkaro ni aiki nake yi amma sam ba ƙarfi a jikina

Ina ƙoƙarin sauke abinci naji kukan amna abincin na sauke sannan na fita ina tambayar abinda
ya faru "mommy Aysha ta zaga shine na buge mata baki"

"Zagi? ina kika iya zagi? ai gwanda da ka doke mata baki" ƙara buɗe baki tayi tana min ihun
kuka "za kimin shiru ko sai na ƙara miki" na daka mata tsawa wanda yayi daidai da shigowar

lawal tashi ta yi da gudu taje ta riƙeshi tana shessheka

"me ta miki da za ki doketa"ya tambayeni yana tsareni da ido kamar wanda ke son turkeni
"zagin Aysha tayi kuma ba ma ni na daketa ba safwan ne ni yanzu zan mata nawa"

"Saboda jakar ku ce?" ya tambaya cikin masifa kallon mamaki na bishi da shi "zagi fa aka ce
maka ta yi ba wani abin kirki ba"

"To ke bakya zaginne? ko shi da ya doketa baya zagin" wurin safwan ya isa kamar wani
sa'anshi ya dinga dukanshi ido na zuba mishi tare da tunanin "anya saboda dukan da safwan ya
yiwa Amna ne lawal ke mishi wannan dukan sam abin bai kai haka ba amma kuma ɗanshi ne
banida halin dakatar da shi" juyawa nayi na koma ga girkina ina danne abinda ke tasomin
Ɗaki na same shi bayan na bawa safwan magani saboda zazzaɓin da ya taso mishi .wataƙila
harda kukan da yayi abinci na zuba musu sannan na wuce ɗaki yana rungume da ita sai wani
narkewa ta ke idona na zuba mata ina nuna mata ƙofa "ki wuce ga abincinku can kafin ranki ya
ɓaci" sauka tayi daga jikinshi ta bar ɗakin kallona na mayar wurinshi

"ba haka ake hukunci tsakanin yara ba abban safwan ko ba komai shi babba ne a gurinta kuma
hukunci ya mata kan abinda ta yi bai kamata ka dokeshi kan wannan ba dukansu ƴaƴanka ne"
miƙewa yayi kamar yanda ya saba shi kullum ba za'ayi magana da shi a zaune ba


"to sannu ƴar iya ai dama komai ban iya ba ke kika iya to bazanyi yanda kike so ba dama ba tun
yau ba na fahimci duk cikinsu ba wanda kike so kamar shi ba ya laifi a gurinki to ni ba irinki ba
ce son ƴaƴa bai rufemin idon da zan iya komai a kansu ba" galala na saki baki ina kallonshi wai
kodai ya fara kurɓe-kurɓe? to nikam yaushe abin ya kai na ɗaga murya

"Allah ya baka haƙuri"na faɗa tare da juyawa ɗakin na bar mishi na koma falo na kwanta ina
kwance sai ga yaran sun fito wurina suka yo dukansu hannu na miƙawa safwan ya tako wurina
gefena na zaunadda shi tare da kwantarda kanshi akan cinyata jin har lokacin jikinshi akwai
zazzaɓi kallon amna da ke matsowa wurina tana kallona na yi harara na watsa mata "kar ki
kuskura ki matso wurina tunda bakya jin magana"


Kuka ta sa tana riƙe kunnenta kamar yanda suke yi idan sun min laifi "kiyi haƙuri mommy bazan
ƙara zagi ba" tausayi ta bani na janyo hannunta "to ki ba yaya haƙuri kinga akanki abba ya
dakeshi" matsawa tayi tana leƙen fuskar safwan "yaya kayi haƙuri bazan ƙara zagi ba"

Faɗa na ƙara yi mata sannan su ka zauna muna hirarmu kamar wasu sa'anni na muna nan
zaune ya fito ya murtuƙe fuska kamar wanda bai taɓa dariya ba kuɗi ya fitar daga aljihunshi 200

"kai karɓi amsomin sugar wurin idi" ya faɗa yana kallon safwan


Dubanshi nayi "ka baiwa ko Aysha ta karɓoma zazzaɓine sosai a jikinshi wallahi" zabura yayi
"zazzaɓinne zai hana mishi karɓo min sugar a waje? kai zaka tashi ko sai na ɓallaka munafuki
kawai wallahi daidai na ke dakai yanzu" shiru na yi har safwan ya karɓi kuɗin ya fita miƙewa na
yi na koma ɗaki ina ƙoƙarin shiga toilet maganarshi ta tsunduma kunne na

"kar ki ƙara sakamin baki idan ina magana da yarana tarbiyya nake basu don bazan sake su
haka kawai yanda ake so ba"











HMMMMMMMM✍️✍️✍️



*AURE DA KARATU*


*NA*

*RUMAISA'U SIDI*




*FARAR ANIYA WRITERS*




*Page 19*

Gajeriyar dariya na yi sannan a fili na ce"Su tarbiyya manya" na doshi toilet ɗina da shigowar
shi ta dakatar da ni "Me kike nufi da su tarbiyya manya? ba nida tarbiyyar kike nufi ko me"


"Wai don girman Allah Abban Safwan me ya sa kake son mai da masassara ciwo ne? na lura
kwanan nan magana kaɗan ka ke jira in yi ka hayaƙo min, wai me ke faruwa don Allah" na
tambaye shi ina so ya faɗa mini laifin da na mishi da ya ke jin haushi na.Wannan zaman ya ishe
ni ta ya za a ce ke da mijinki amma ba wata magana mai daɗi da za ta shiga tsakanin ku?
Shikenan mu ba mu da aiki sai gasawa juna magana kamar ba Auren soyayya mu ka yi ba?


Magantuwa na ƙara yi ganin ya zuba min ido ya na kallona"Ka faɗa mi ni laifin da na maka sai
in baka haƙuri,wannan abin ya ishe ni,da me kake so inji,da KARATUNA,ko da yarana,ko kuma
da rigimarka?


"Au wato ma rigima na ke yi ko?tunda ga ɗan ki ko? To bari ki ji,yadda ki ke ɗauka ta ba haka
na ke ba,ni ba sakaran namiji ba ne da mace za ta riƙa juyawa yadda ranta ke so ba.Ki bar
ganin kina da ƴan canji a hannunki hakan bazai canja matsayina na miji a gare ki ba,waƴannan
yaran kuma ba za ki canja mu su wani uban ba ni ɗinne dai idan kuma za ki canja mu su to
bismillah"


Yadda ya ke fitar da maganar kaɗai ya isa ka fahimci haushina da ya ke ji,wanda ni har ga Allah
ban san laifin da na mishi ba,wallahi ban sani ba ganin tsayuwar ta wa ba ta da wani amfani ya
sa na shige toilet ɗina ina cewa "Allah ya kyauta"


Abin mamaki har na kammala abinda zan yi na fito yana ɗakin kuma bakinshi bai huta da
masifar da ya ƙirƙirowa kan shi ba.

Ƙofa na dosa da niyar bar mishi ɗakin na ji an janyo bayan rigata da ƙarfi waigowar da zan yi na
ga ya ɗaga gandamemin hannunshi alamar jikina zai yo na yi saurin kaucewa.


A fusace nima na fara magana "Kar ka kuskura,wallahi kar ka kuskura hannun ka ya sauka
jikina da sunan duka,wancan ma na baya na raga maka ne saboda igiyar aurenka da ke
kaina,amma wallahi tallahi yanzu duk ka kuskura ka taɓa lafiya wallahi za ka yi nadama marar
iya ka"

Kallona ya ke sandare da hannun da ya ɗaga da niyyar shararamin mari jikinshi ne ya fara rawa
idanunshi su ka rikiɗe "Ni kike faɗawa wannan maganar? Nufin ki idan na mare ki ramawa za ki
yi?

Ya na maganar ne bakinshi da kuma harshenshi na harɗewa alamar ya kai maƙura ga ɓacin
rai.Nima kuma haka,don har ga Allah tsayin da na gyara na gyarane da shirin da ya mare ni zan
rama don ni ba jakar shi ba ce.


Zuwa da komowa ya fara yi a ɗakin,nima ina tsaye ina jiran duk abinda zai faru ya faru don ya
na dukana wallahi ramawa zan yi.Dakatawa yayi tare da kallona "Na samo mafita,wannan ne
kaɗai hanyar da za ki gane har yau ina gaba da ke...."shiru ya yi na ƴan sakanni sannan ya ci
gaba da magana "Kije *NA SAKE KI SAKI BIYU*, ba sauran Aure tsakani na da ke,na katse
igiyoyin da kike tunanin akwai sauran mutunci a tsakanin mu.Kuma kar ki kuskura ki ɗaukar min
yara saboda ba da su kika zo ba,ki bar su gidan ubansu don ban faɗa miki na kasa ba"



Kamar wadda ta hau lilo haka na ga ɗakin na juyawa da ni,kunnuwana kuma kamar an jona
lasifika a ciki haka na ke jin shigar kowace kalma da ke fitowa daga bakin shi daƙyar na samu
na fara kiran "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un"na shiga maimaitawa jin gani na neman ɗaukewa.


Zagaye ni yayi ya bar ɗakin,bakin ƙofar na kai zaune daɓass tare da dafe capet ɗin da ke
malale a ɗakin nawa na sauke kaina ƙasa.Na rasa me zan yi?Shin kuka zan yi ko ihu? Me yasa
ya min haka? Tabbas ya na da dalili,ko ya na tunanin ba zan iya rayuwa ba sai da shi? Ya sha
faɗa min hakan "Zee irin wannan soyayyar da ki ke min wallahi da wahala ki iya rayuwa babu
ni"


To kenan haka ne? Me yasa kullum na ke bari Lawal ya na galaba a kaina? Duk abin da na sa
mu ba ya wuce lawal, a kan shi na guji zaɓin iyayena.Tabbas sakamako na ke gani akan
bijirewa shawarar iyayena.Na san da ace abin da na suke so na bi, da ban haɗu da wannan
ƙalubalen ba.Idan kuma dama can an rubuto hakan zai faru da ni to Allah zai kawo min sauƙi ko
don biyayyar da na yiwa iyayena.


Amma ko yanzu ban makara ba,zan nuna wa lawala a da ne na mishi wannan mahaukacin
son,amma a yanzu tsaf zan yi rayuwa ta ba tare da shi ba.


Wani ƙwarin guiwa ne na ji ya na shiga ta miƙewa na yi na shiga haɗa tufafina da ƴan ƙananan
kaya na da na ke amfani da su kullum a babban akwatina.Ɗakko hijabin sallah ta na yi da ya ke

har ƙasa na zuba,agogo na kalla 8:47pm na san ba matsala zan iya tuƙi da yardar Allah.


Falon na fito ina janye da akwatin kayana,shi ma ya na nan zaune rungume da Amna,Aysha
kuma na kwance akan center capet da drawing book a hannunta.Tashi zaune ta yi tana
kallona"Mommy fita za ki yi" idanuwana na zuba mata tare da jin wani irin tausayinta da ya
lulluɓe ni,saboda duk cikin ƴaƴana ta fisu ƙulafucin uwa,ba ta ƙaunar ko nan da can na matsa
na barta.


Jin maganar da Aysha ta min ya sa Amna da mahaifinta waigowa kallon kallo muka shiga yi ni
da shi,ni na fara janye idanuwana na mayar kan Amna da ta riƙe min ƙafafuwa "Mommy zan bi
ki,kin san ranar da Aysha kika tafi,ki ka ce idan za ki ƙara fita za ki je da ni" hannuna na sa na
janyeta sanin da na buɗa bakina kuka zai iya ƙwace min.

Kanta na shafa tare da ɗaukar akwatina na tunkari ƙofar barin ɗakin,da ƙarfi na ji an rungumeni
ta baya,zafin da naji ya fara ratsamin jiki ya sa na fahimci Safwan ne.Juyowa na yi ina kallonshi
hannuwana ya riƙe idanuwanshi na zubar da hawaye "Mommy don Allah kar ki tafi ki
barmu,kinga Aysha kuka ta ke yi,Amna ma kuka za ta yi,duba ki gani Mommy nima kuka zan
yi,don Allah kar ki tafi"


Rungume shi na yi da ƙarfi ina jin kamar in maida shi ciki saboda ƙaunar da na ke mishi.Da
gaskiyar Lawal da yace duk cikin ƴaƴana na fi son Safwan bai faɗi ƙarya ba sai dai ban taɓa
kuskuren nuna hakan a gare shi ba ballanta hakan ya raba min kan yara.


"Ka kula da ƙannenka,Ku ci gaba da karatu,banda shiririta Allah ya muku albarka kai da
ƙannenka" sakin shi na yi na ɗauki akwatina na bar ɗakin ina jin yadda sautin kukan yarana ke
shiga kunnena ina gab da isa motata na ji sautin kukan Amna ta na kirana
"Mommmmmmmmyyyy" har cikin kwanyata na ji sautin,Ina tuƙi ina kiran sunan Allah,da fatan
ya kaini gida lafiya.



Kamar ƴar maye haka na shiga falon na mu ina layi,Ummina da Yayyena suna zaune a falon da
alama wani abu suke tattaunawa.Yaya Isma'il ne ya taro ni ganin ina neman faɗuwa ƙasa "Ke
lafiyarki,Me ya same ki?


Zaunar da ni ya yi a kujera kusa da Ummi,matsawa na yi jikinta tare da rungume ta ina goga
kaina a jikinta kaina ta shiga shafawa a hankali,sai lokacin na samu na saki wani marayan

kukan da na daɗe ina nema ko zan samu faɗawar ƙololon da ya tokare min maƙoshi da ƙyar na
samu na fizgo maganar da na ke son fitarwa "*Ya SAKE NI*,Ummi Lawal ya sake ni,yau Aurena
da lawal ya ƙare,komai ya ƙare ummi"








Uhmmmmmm😢






Follow this link to join my WhatsApp group:
https://chat.whatsapp.com/D84KccWmLGj6Iw3z7tTAh3



*AURE DA KARATU*


*NA*

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
google.com, pub-9213700357025247, DIRECT, f08c47fec0942fa0