Showing 27001 words to 30000 words out of 62089 words
*RUMAISA'U SIDI*
*FARAR ANIYA WRITERS*
*Page 20*
"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un"Ummi da Yaya Isma'il su ka shiga maimaitawa "Allah ya sa
hakan ne mafi alkhairi a rayuwarki Zainab,Allah ya baki juriya,ya kare mi ki yaranki a duk in da
suke. Don Allah kar ki ɗaga hankalinki don kin rabu da Lawal ba shi ke nufin kin rabu da farin
ciki ba,ki duba ga ni ga kuma ƴan uwanki masu son farin cikinki,don haka ki kwantar da
hankalinki.Saki nawa ya miki?"
Ɗagowa na yi daga jikinta ina kallonta hawaye na ƙara zubo min "Saki biyu ya min Ummi"
"To ki kwantar da hankalinki ta shi muje ki samu ki kwanta kar ki jawowa kanki wani ciwon
kuma"
hannuna ta riƙe ta kai ni har ɗakin baccinta sai da na ce mata bacci na ke ji sannan ta
fita.Amma inaaaa,ba na jin yau duk satar ɓarawon zai sa mu nasarar sace ni,mutuwar Aure fa
ake magana,duk da ba abin da Auren Lawal ya tsinana min amma kasancewa ta inuwa ɗaya da
yarana ya fi min daɗi fiye da rabuwa da su.
Yanzu fa su na can hannun Lawal,ko sun yi bacci? shin ya mu su addu'a? Zaune na tashi tuna
yadda na barosu su na kuka nasan in dai Amna ce sai ta raba dare ta na wannan kukan ba abin
da ya dame ta,da ma can ni ce mai lallashin kayana to yanzu ga shi za mu kwana ba a tare
ba,bansan a wane hali su ke ba.
*FALO*
"Wallahi Ummi sai ya yi nadamar wulaƙanta Zainab,zan nuna mi shi na fi shi ɗanyen kai"Yaya
Abbas ke faɗa cikin matuƙar ɓacin rai miƙewa ya yi ya tunkari ƙofa
"Abbassssss" Ummi ta kira shi da ƙarfi sanin abin da zai je yayi ba zai wa kowa daɗi ba"Dawo
ka zauna"da ido Ya Isma'il ya bi shi har ya zauna
"Haba Abbas da iliminka da komai,da ma Aure rai ne da shi to su nasu ya ƙare yau addu'a
kawai za ku mata Allah ya zaɓa ma ta abin da ya fi alkhairi a rayuwar ta" Ya Isma'il ya tunatar
da Ya Abbas
Numfasawa Ummi ta yi sannan tace "Damuwa ta ɗaya yarannan da ke hannun shi,mutumin da
ya kasa kula da kanshi ma ballantana wasu ƴaƴa.Idan har zai yu ina so a karɓo yarannan ko
don kwanciyar hankalin mahaifiyar su,ni zan fitarwa da Abbas kono tun da ya yi rantsuwa amma
ban lamunta da zamansu a can ba"
A kan wannan su ka tsaya,kowa ya bada goyon bayan karɓo yaran ko don lafiyar Zainab.
*LAWAL*
A kan idanuwanshi ta ja jakarta ta bar gidan,ga ihun yaran da ya cika mishi kunne,bai san me
ya sa ba shima ji ya ke kamar ya ɗora hannu a ka ya yi ta ihun.Yaran ya kalla tausayi su ka ba
shi ganin yadda su ka makure gefen kujera Safwan na rungume da su,tausayi su ka ba shi ta
shi ya yi ya isa in da su ke,hannu ya sa ya ɓanɓaro Amna da ihun ta ya fi na kowa
Rarrashinta ya shiga yi ta na tuburewa "Wai za ku yi min shiru ne ko sai na haɗe ku na zane" ya
da ka mu su tsawar da ta ƙara firgita Aysha,jikin Safwan ta ƙara shigewa ta na danne bakinta
kar kukanta ya fita
Ƙwacewa Amna ta yi daga jikinshi ta nufi ƙofa miƙewa Lawal ya yi tare da cafkota,zillewa ta
shiga yi "Ni wallahi wurin Mommyna zan je,ni wallahi sai na je" gajiya ya yi da rarrashinta ya da
ka mata tsawar da ta ya kamata ta sa tayi shiru amma sai ta faɗi tsakiyar ɗakin ta na
shure-shure "Ni wallahi sai na je wurin Mommy,Ni wurin Mommy zan je,Abban tusa kawai"
Kan shi ya dafe ya na jin kamar zai watse wannan bala'in da me ya yi kama,Zainab ta bar mi shi
jaraba,Daga shi har yaran falo su ka kwana.
*ZAINAB*
Yadda na ga rana haka na ga dare,ba wai saboda mutuwar aurena na kasa bacci ba A'a
saboda ƴaƴana ne da na san yadda na shaƙu da su.
Ƙwarin guiwa na baiwa kaina na fita kitchen ina taya Anty Asabe aiki saboda ya ɗebe min
kewa.Muna yi muna fira jefi-jefi har Ummi ta fito,daga yanayin fuskar ta na fahimci ta ji daɗin
yadda na ke ƙoƙarin danne damuwata.
Lokacin da na zo yin breakfast ɗina yarana na tuna shin sun ci abinci? To ko shi ba daƙyar ya
ke samu ya ci ba ballantana ya ba su "Ya Allah ka zama gatan yarannan a duk in da su ke"
*LAWAL*
Bai ƙara raina kan shi ba sai da aka wayi gari ba ya da ko sisin da zai siyawa yara abin kari ga
Amna ko yau ta tashi da rigimar ta wata dabara ce ta faɗo mishi ya tunkari kitchen sanin komai
ana kawo ma ta daga gidansu.
Ruwan Zafi ya ɗora har su ka tafasa ya juye,wurin da yasan tana ajiyar kayan shayin ya tafi sai
dai ga sugar amma ba madara.Kayan ya kwaso ya fito da su,ɗakin yaran ya shiga dukansu su
na kwance Safwan ta duba "Kai ina Mommynku ke aje madara?
Ba tare da ya tashi ba ya bashi amsa "Madara ta ƙare ko jiya sai da ta bamu kuɗi mu ka siyo"
ajiyar zuciya ya sauke tare da barin ɗakin Yaran ya ɗaga murya ya kira ya zuba musu ruwan
zafin da ya zuba sugar a ciki
"Abba haka za mu sha shayin ba madara kuma ba breadi" Amra ta faɗa tana ɓata fuska "Eh
haka za ku sha idan kuma ba za ku sha abinda na baku ba to ku bari"
"Ba kayanka ba ne,duk abinda ke kitchen ɗin na Mommy ne,kuma mu Mommy ba ta taɓa ba mu
ruwa a matsayin breakfast ba" Safwan ne ke maganar,cikin wani sauti da ke bayyanar da tsanar
mahaifinshi ƙarara.
"Kai rashin kunyar ta ka har ta kai can? Ni za ka nuna wa ka girma? To wallahi ba zan siye
madarar ba,duk wanda bai sha ya bari"
Haka ya kwankwaɗi ruwan su kuma kowanen su ya kasa sha maganar makarantar su Safwan
ya mi shi "Lokaci ya tafi ku bari sai gobe,yanzu ku tashi in kai ku wurin Mama don ni fita zan yi"
A tsakar gidan su ka sami Mama ta na jawo ruwa a rijiyar da ke gidan,jawo gugar ta yi tare da
zube ruwan da ta ɗebo a bokiti ta na kallon su cike da mamaki,saboda duk zuwan da su ke yi
ba su taɓa sammako irin yau ba.
"Wa'alaika salam,yau su mai gida ne tun da sassafe" durƙusawa ya yi a gabanta ya na gaida ta
amsawa ta yi tare da wucewa ɗakinta Lawal da kuma yaran su na bayanta.
"Lafiya na gan ka da yara tun da sassafe kuma na ga jakar kaya a hannunka?
Kallon yaran ya yi "Ku je waje kafin in fito" sai da su ka fita sannan ya mayadda kallonshi ga
Mama "Za su zauna ne na ɗan lokaci kafin in samo mafita"
"Ban gane za su zauna ba ina mahaifiyar su? ta tambaya tare da fatan Allah ya sa ba gajiya
Zainab ta yi da zaman ta yi yaji ba
"Mun rabu da Zainab ne jiya Mama"
Hannunta ta buga ga ƙirji "Kun rabu da Zainab? kana kuwa da hankali Lawwali?Zainabun ka
saka? Matar da ta rufa ma asiri Allah ya rufa ma,ka na buƙatar ci gaba a rayuwar ka kai
kam,innalillahi wa inna ilaihi raji'un"
"Ita ce ta kai ni bango Mama,kullum nema ta ke ta mayadda ni sakaran namiji kuma................."
"Dallah yi min shiru,to miye kai in ba sakaran namiji ba,hotiho wanda ba ya da aiki sai
bacci,wallahi idan akwai abin da ya fi sakarai to kai ne.Kuma wallahi ba baki na maka ba sai ka
yi nadamar wannan sakin da ka yiwa Zainab.Kuma wallahi ka yi gaggawar ɗaukar yaranka ku
bar min gidana don bazan riƙa su ba sai ka san inda za ka kai su" daga haka ta tashi tare da
shigewa ƙuryar ɗakinta ta mai da ƙofa ta rufe.
A sanyaye ya kaɗa yaran su ka fita,tsaye ya yi bakin titi ya na tunanin yadda zai yi da
yaran,Allah ya gani shi ya san bazai iya kula da su ba don ko abincin da zai ba su baya da shi
ko na cikinshi wuya ya ke mishi ballantana na yara har uku.
Gidan Anty A'i (yayarshi) ya nufa da su,tunda ta ganshi ta ɗaure fuska don ta ɗauka ya zo
roƙonta ne kamar yadda ya saba.Sai da su ka gaisa ta sa aka zubowa yaran masa da miyar da
ta ke siyarwa sannan taje ta samu Lawal da ke jiranta a falo.
"A gaskiya Lawal idan na ce ma zan riƙe su Safwan na yi ma ƙarya,ka na kallo nima yadda na
ke gurgura rayuwata da ƴan yarana duk da mijina ya na bani amma dole sai na ƙara saboda ba
ya bamu abin da zai wadace mu,wallahi idan na ce zan riƙe su na tauye kaina.Ni da za ka ji
shawarata da ka kaisu wurin mahaifiyar su kawai don ban tunanin za ka samu mai riƙe ma su a
ɓangarenka.Ka na kallon halin da Mariya ta ke ciki,Allah ya haɗa ta da maƙetacin miji ba ya
bata abinci sai dai ta nema ta ci,ni dai shawarar da zan baka ka miƙa su ga Zainab"
Tafe ya ke yana tunani daga jiya zuwa yau ya tsinci kanshi a halin ƙaƙa ni ka yi ga shi sai yawo
ya ke da yara kowa ya ƙi amsa a fili yace "Ke ki ka ja Zainab,da baki tunzura ni ba da yanzu
kina nan tare da ƴaƴanki"
*MAMA*
Bayan wucewar Lawal hankalinta ka sa kwanciya yayi wallahi tayi baƙin cikin wannan asara da
Lawal ya tabka.Wayarta ta jawo ta shiga neman layin Ummi mahaifiyar Zainab bugu uku ta
ɗaga,gaisawa suka yi cikin mutunta juna
"Hajiya ashe abin da ya faru kenan,wallahi ban sani ba yanzu ya zo da yara ya ke faɗa min.Don
Allah ku yi haƙuri wallahi ban ji daɗin wannan al'amari ba sam"
"Ba komai Hajiya ai dama aure rai ne da shi,zaman su ya riga ya ƙare sai dai dukansu mu yi mu
su fatan alkhairi"
Haƙuri Mama ta ci gaba da bawa Ummi kamar ita ta yi sakin sai da su ka yi sallama sannan
Ummi tace
"Am ni ko nace Hajiya idan ba damuwa don Allah ina neman wata alfarma a wurinki"
"Wace alfarma Hajiya"
"Don Allah ina so idan ba damuwa a bata yaran ta riƙe idan kuma ba zai yarda ba ko da
ƙaramar ce ta dawo hannunta"
*RUMAISA'U SIDI*✍️✍️✍️
08104445106
*AURE DA KARATU*
*NA*
*RUMAISA'U SIDI*
*FARAR ANIYA WRITERS*
*Page 21*
Numfashi Mama ta sauke "Kar ki damu Hajiya In sha Allah ba matsala,zan yi magana da shi"
daga haka suka yi sallama.
*LAWAL*
Kukan Amna ke ƙara ruɗashi tana kiran Mommynta.Tsawa ya buga mata a karo na barkatai
amma ko gezau ba ta yi ba.Kanshi ya dafe ya na jin kamar shima yayi ta ihun ina zai saka
kanshi? tunda suka dawo gidan ya ke tare da su.
Ko abinci farar shinkafa kawai ya dafa musu saboda ita kaɗai ya iya itama kuma da ace babu
shinkafa a kitchen ɗin da bai san yadda zai yi da yaran ba.Don bayada ko sisi dama da kuɗin
Mama ya ke fantamawa to suma ƙalilan su ka rage kuma ta karɓe ba ya da wata madafa yanzu
wani sashe na zuciyarshi yace "Yanzu da Zainab na nan da ita zata yi komai"
Saurin kawadda tunanin yayi don sam ba ya son ya na tunawa da wata Zainab ballantana har
yaji a ranshi ta na tare mishi wani abin.
Wayarshi yaji ta na ƙara ɗagawa yayi tare da karawa a kunnenshi "Mama barka da dare" ya
gaidata cikin girmamawa kamar yadda ya saba kullum
"Ina su Safwan?Ka ba su abinci? Kallonsu yayi sannan yace
"Ga su nan Mama kuma sun ci abinci"
"Yayi kyau ina so gobe ka ɗau Amna ka kaita wurin mahaifiyar ta sauran kuma ka riƙe su"
"Gaskiya Mama ni bazan iya baiwa Zainab ɗana ko ɗaya ba,zan iya riƙe abina"
"Za ka iya riƙesu amma ka bar mata ragamar su? Banson shirme umarni na ke baka ka kaiwa
Zainab yarinyar nan,idan kuma ba haka ba wallahi duk abin da na maka kai kaja" Daga haka ta
katse wayarta goshinshi ya shiga murzawa.Sam ba haka ya so ba don bayason Zainab ta yi
tunanin ko ya kasa da yaranne,dama haka ta ke gani kullum ,ranar ma bai yi wani baccin kirki
ba.
Tunda Asuba yaran suka hana mishi bacci saboda Zainab ta riga ta saba musu da tashin Asuba
dole ba don yayi niyya ba shima ya tashi yayi sallah.
Kamar jiya yau ma ruwan da suga ya dafa Safwan da Aysha kuma suka shirya Amna.Yau ma
ƙin shan ruwan su ka yi dole ya fitar da ƴar ɗari biyun da ta rage mishi a aljihu ya baiwa Safwan
yace ya karɓo madara ta naira 50 wani kallo Safwan ɗin ya mishi "Abba tun yaushe aka daina
saida madarar naira 50? Sai dai ɗari,ita ma wallahi ko Amna ba za ta yiwa shayi ba"
Zabura yayi "Bani kuɗina,in za ku sha haka kusha in ba zaku sha haka ba ku bari"
Haka suka yi shayin da Madarar naira ɗari abu kamar ruwan banza haka suka sha shayin ba
don daɗi ba.Gidan ya kulle sannan yace su jirashi ya tunkari wurin mai shagon da yake zama
"Laminu don Allah ɗari biyar za ka ranta min in kai su Safwan makaranta"
Wani kallo ya mishi "Da me za ka biya ni idan na ranta ma? Da shekarunka ko da ƙaton kanka?
To bari kaji wallahi dama jiranka na ke inga kana da kunya ko ba ka da ita? to na gani don in
banda rashin kunya banga dalilin da zai kawo ka wurina rancen kuɗi ba bayan ina binka kuɗi
sun kai dubu biyar"
Ran Lawal ya kai ƙololuwa wurin ɓaci "Kar ka faɗa mini magana malam,kuma yadda ka samu
kuɗinnan nima zan samu da yardar Allah"
"kana zaunen za ka samu? Ko kuɗin fiffike ne da su da zasu sauka kanka? To bari ka ji bazan
bayar ba" Fuuuuuu Lawal ya bar wurin ya na ji kamar ya kashe kanshi ya huta don baƙin cikin
wannan tozarcin da Laminu ya mishi
"Haba Laminu bai dace ka mishi haka ba,ina laifin wanda ya zo neman wani taimako a wurinka
da tunanin za ka taimaka mi shi amma sai ka mishi haka,bai dace ba sam kuma banji daɗi ba"
wani da yazo siyayya a shagon ya faɗa
Tsaki Laminu yayi "ƙyale shi kawai Aminu,haka ya ke kullum shi dai a ranta mishi,ko kaɗan bai
san zafin neman kuɗi ba yana kwance matar shi ke nema ta ciyadda shi da ƴaƴanshi.Ba ya da
aiki sai rance kuma bayada abin biya don ba wata sana'a ya ke ba duk sana'ar da ka nuna
mishi zai nuna ta mishi ƙanƙanta"
Kuɗi Aminu ya fitar daga aljihunshi "Nawa ka ke binshi?
"Dubu biyar da ɗari huɗu"
Kuɗin ya bashi sannan ya fita daga shagon.A bakin titi ya samu Lawal a tsaye riƙe da hannun
Amna sauran yaran na gefenshi hannu ya bashi su ka gaisa sannan ya fitar da kuɗi dubu biyu
daga aljihunshi "Gashi Malam Lawal a siyawa ƴan makaranta alawa,shima mai shagon ba sai
ka bashi kuɗin ba na bashi.Kuma ina roƙonka don Allah ka tashi ka nema ko don future ɗin
yarannan"
Godiya ya mishi sannan ya samu adaidaita suka shiga ya sauke yaran makaranta sannan ya
wuce gida wurin Mama
Kuyi haƙuri da wannan
Wallahi yau saboda farin cikin ku kawai na yi typing ɗinnan, Ina muku ƙauna lodi-lodi
*RUMAISA SIDI*
*08104445106*
*AURE DA KARATU*
*NA*
*RUMAISA'U SIDI*
*FARAR ANIYA WRITERS*
*Page 22*
*ZAINAB*
Wani sanyi na ke ji a cikin raina matsalar rashin yarana ne kawai a gabana,duk wani ƙunci da
nake ji akan mutuwar aure na ya kau saboda na mayadda hankalina ga addu'a abin da na yi
sakaci tun farko.
Idan ƙuncin Lawal ya sako ni gaba maimakon na na tashi na gayawa Allah matsalata, sai dai na
shige ɗaki na dinga kuka.Amma yanzu In sha Allah wannan ya kau,zan