Showing 33001 words to 36000 words out of 92630 words

Chapter 12 - Auren Babban Mutum By Umme Mukhtar

20 Jul 2026

871

kira aiko tasame shi yace hello my blood ya kk""" cikin jin kunya tace
ina lfy dama so nake zan d'an fitane inason naga gari "" . Murmushi yayi yace ok my son yana
gidane ?

Tace eh gashi""" yace bashi wayar , ta mika masa suka gaisa yace kufita tare duk abinda
takeso kasiya mata koda kuwa kullum tk son fitar """ musayyet yace to Dady """ gud boy ku
kwana lfy ina saurine kasan saura 3days na dawo so yanzu a kwai inda zani bata wayar"""
Musayyet yace nayi murna dady gara ka dawo kanemomin masoyi yata ""murmushi sukai duk
kanninsu Zarah tai saurin kallonsa ya kad'a mata ido ya kuma mik'a mt wayar """" ok seda
safe da sauri Alhaj Sa'ed yace baza acemin I love you din ba?
Musayyet na jinsa ya sunkuyar da kai zarah ita kam duk kunya takamata ta kashe wayar har
tana k'ok'arin su6ucewa dg hannunta.





Musayyet yace ki shirya idan anyi magriba semuje """"" tace to hanyar bangarensa yai ta bishi
da kallo tn kallon yanda yake tafiya abun sha 'awa .






Seda sukai sallah sannan sk fito mota ya bud'e mata gidan gaba ya tsareta da idonsa masu
kashe jiki """ rigace doguwar riga ta material ajiknta dinkin yamata kyau sosai"""" smile tayi
tace gidan baya zan zauna kaine driver na""".. dariya yayi yana shafa kai yayinda ya zura
hannunsa cikin lallausan yadinsa fari cikin aljihu yace haba k'aramar momy na so kike mufita
ace ni driver ne? Dariya tayi sosai tace eh man """" hannunsa ys a duka kunnensa 2
yanayinsa kamar na yaro zeyi kuka alamun tai hkr ta shiga """" smile tayi ta bude gidan gaba
ta shiga suka fita masu gadi suna kallon su .

Dayan yace oh sude 'yan boko baruwamsu wlh """" .wanda ake kira da musa yace meka gani?

Yace ah bakaga yanda Sir Musayyet suka fita da Amaryar Abbansa ba""" kuma wlh se sukai
macin kai kace matar sace.



Musa yace kaga ka iya bakinka inaruwanka hk Al'adarsu take a kwai wayewa aciki.


Yace ba wata wayewa Amma de kusan hakanne su suna daukan kowane abu dasauki.




Tafe sk amota ya saka music na masoya yana tashi kad'an kad'an ta kalleshi tace da alamu
kanason soyaiya """" be kalle ba yai smile yace sosai ma Momy na a kwai wacce nakeso amma
bansan ina takeba tamin yawo da hankali ban ta6a ganin taba amma tabbas inajin sonta
acikin jinina """... ..face d'inta na kallon kan titi tace bakasan gidansu ba ?
Tsaida mota yayi gefen titi ya kalleta face d'insa harda k'wallah yace bansani ba Momy amma
kimsamme ?

Ta kalleshi ta girgiza kai """ yace senakeji kamar tana tare dani hakan nakeji araina.

Murmushi tayi tace idan harso dama yazamana na gaskiya koda wanda kk so baya tare dakai
aguri to zaka dingaji kamar yn tare dakai.

Karka damu zaka gantane insha Allah zamush biki ranar nice uwar biki.



Dariya yayi yace Allah ya akaimu yaja mota sk tafi.



Seda sukaje gidan abokin sannan sk nufi wani mall sukai shopping me yawan gaske dan hk
yadinga dibar mata kaya kamar hauka ,komai yaga ni seya debo yace ze mata kyau.

Kayan ciye ciye dana sha se mayuka turaruka kayan sawa dogwayen riguna da kananun kaya
wai tasawa dady """" sede tai dariya ta kar6a ta aje waje d'aya .


Koda suka fito wani restaurant sk biya sukaci snacks da juice sannan sukayo gida.

A hanyane suna tafe Zarah harta fara bacci yn kallonta yn tuki'i yai smile cikin ransa yace
beautiful sleep kenan.


Ahankali ta bud'e idonta dede nan wata mage tazo giftawa kan titi Zarah ta kwallah ihu ganin
kamar Musayyet ze bige magen """" dariya yayi yace kai momy magen kike tsoro koda yk hk
fa na dinga tsorataki a gida bakisani ba.

Da sauri ta kuma sa wani ihun Musayyet yai saurin taka burki gamida zaro ido yace momy
ya akai ?


Motor ta bud'e ta fita taci kunu alamum fushi da sauri ya fito dg motar hasken fitilun kan titin
suka haske masa face ' duk zarah na cikin fishi dashi sedata kalleshi cikin ranta tace su kuma
hk suk kyawawa dasu """" gunta yayo yn smile tai saurin tamke fuska yace menayi wayyo
Allah na karki kaini k'ara gun Dady.


Baya ta juya masa ta fara magana cikin alamun fishi tace dama ashe kai kake tsoratani?

Ajiyar zuciya ya saki yai dariya ya juyo gunta ya tsuguna har k'asa yn dariya yace sorry my
mom I will ņt repit it again """ idan na sake ki zane ni ..koki hana ni zuwa ko ina .

Dariya tayi har fararan teeth d'inta suna haske shiko kansa na face d'inta yn kallon yanda take
dariya shima smile yakeyi cikin ransa yana cewa Gaskiya Dady ya iya za6e

.


Seda ta gama dariyarta sannan tace na hkr idan kasake kuma sena fadawa dadynka.





Da sauri yace bazan sakeba gaba daya sukai dariya suka shiga mota ko wanne cikin ransa
yana mamakin yanda sukai sabo da juna cikin k'aramin lokaci.

I love you my fans kumin âfuwa I'm lazy writter 🤣 se ammin uziri�🏻�🏻�🏻
[31/08, 16:19] +234 905 934 3174: 👳🏻�♀👳🏻�♀👳🏻�♀👳🏻�♀👳🏻�♀👳🏻�♀👳🏻�♀


_*AURAN*_ _*BABBAN*_

_*MUTUM*_

Creating And Written By
_UMMEE_ _MUKHTAR_�


My fans Muna tare🤞🏻😊 I'm Lazy writter�🤣 se hkr.








🅿21




Wajen 10:30 suka dawo masu gadi sk bud'e musu gate ""' a tare sk fito suka d'auki kayan
yace ta barshi ze shigo da sauran """"" tace to sukai ciki yn kallon bayanta kamar wata
macijiya hk take tafiya cikin sanyin jiki """" koda suka shigo a palor suka zauna kowanne ya
zauna a kujerar dk fuskankantar dan uwansa """"... Kallonta yai ya cire hularsa waje daya wacce zatai 20k ya shafi sumar kansa yace sannu momy
na na gajiyar dake ko
?

Zarah tace nagaji duk da bani nai driver ba amma jinake kamar nayi wani aiki .



Murmushi yayi yace aiko kinyi aikin, irin wannan ihu da kika dinga min a hanya kamar na
satoki ya fad'a yn dariya.


Kallonshi tai ta turo baki tace ai lefin kane bana wani ba "''. Yace is ok ki hkr bazan sakeba

dama nima ramawa nayi.


Da mamaki ta kalle shi tace menai mk ?

Matsowa yai daga kan kujera yn kallonta yace kin tina wanda yata6a zuwa gidan nan ranar Da
aka kawoki a time d'in kina tare da k'awarki?




Kallonshi tai cikin ido tn murmushi tace dama kaine ?

Exactly ina tinanin na ta6a jin muryarka amma sena manta ko a ina ne""" smile yayi yace
gskiya ne yakamata ki kwanta kinga dare yayi """" .


A tare sk tashi sk jera har k'ofar room dinta ya rakata ya tsaya dede bakin k'ofa 'itama tsayawar
tayi suna kallon juna sukai murmushi yace ki addu'a kafin ki kwanta karki manta ''''' mayafinta
ta gyara duk motsin datai idonsa akan jikinta " da yaga zt juyo se yai saurin kauda kai dan
wani irin abu yakeji namasa yawo ajiki """ tace zanyi kodan Aljanun gidan nan .


Dariya yayi yace Momy nine Aljanin? Itama dariyar tayi tace bada kai nkb seda safe '''...ciki
tayi abinta da sauri yace momy bakiji ba"""" .Zarah ta juyo face dinta akan tasa tai shiru
tana jınsa """""" .kansa ya shafa ya kuma kafa mata ido yai smile yace koda yak barshima
mu kwana lfy have a nice dream my mom dg haka ya hau upstair yn mata bye bye ,,,,
murmushi tayi itama ta d'aga ms hannu tana yaba kyan da Allah yai masa.



Kai inama miji nane dana more tafada tn shirin yin Alwala .


Seda tai sallah tasa kayan bacci ta kwanta.



Musayyet hk yaita tinanin Zarah da siffarta tn mai gizo sede yai murmushi yace yarinyace me
saurin sabo da shiga rai.

Shima sallar yayi yasa singlet da karamin wando ya ware AC yai addu'a se bacci cike da
mafarkin zarah.





A cikin baccinsa ne yai mafarki gashi ga Zarah ga wani kyakykyawan baby wai dan sune
suna cikin fairin ciki "" da sauri ya mik'e zaune yn kalle kalle tsorone yakamashi cikin ransa
yace taya hk zata faru ?
Aiko sede a mafarkin bade zahiri ba yafada yana me Addu a da sake komawa wani baccin.





Hk suka zauna koda yaushe cikin raha da wasa da dariya har tsawon kwana 3 yayinda sukai
wani irin sabo da juna na ban mamaki .


A kwanakin nan kullun se sun fita yawo kamar yanda Alhaj Sa'ed yacewa Musayet da
hakane shak'uwa me k'arfi ta shiga tsakanin su.







Musayyet da yamma ya shirya zefita Zarah na kwance a d'akinta cikinta na ciwo se juyi take
akan bed""""


Zama yayi tsawon mintuna beji motsin taba hakan yasa yatashi har bakin room d'inta yai
koncking amma beji maganar taba .




Kunnensa yasa ajikin door d'in seya jiyo kamar ana nishi " da azama ya bigi k'ofar ya shiga
ciki ,, ya salam da sauri ya juya yana shirin fita domin dg ita se mini pant iya cinya se
k'aaramar best iya cibiya kana hango shafaffen cikinta a kwance kamar batacin abinci.

Juyawa yayi ze fita tai saurin jan bargo gamida rufe ido cikin murya me kasala tace ina zaka?
Katemakan my son banda lfy """" jikinsq har rawa yk be juyowa bå yace mk damunki momy?


Olcer ne ta fad'a cįkin rawar murya """ gumin har keto ms yake sbd ganin d yaimata sosai ta
tashi hankalinsa ,,,seda ya gyara tsayuwa sannan yace ki daure kisa kaya doctor na zuwa
yanzu yana fad'a ya fita yn danna phone d'insa


Ba afi 20mns ba family doctor su yazo Musayyet yai masa iso zuwa palor """" komawa
d'akinta yayi sameta kwance amma tasa doguwar riga mara nawi me karamin hannu baqa
se ratsin fari """".



Tana ganinsa ta fara shirin tashi shiko tsayawa yayi yn kallonta ganin kayan dk jikinta """jiyai
kishi yakamashi yace amma ina hijab d'inki?


Nuni tai masa da wardrobe yai dariya yace nan kuma kika wullashi?


Ita kam dafe ciki tayi ya dakko mata tasa suka fito.



Doctor na zaune yn ganinsu ya mik'e tsaye yn murmushi yace sir Misayyet yaushe kai aure
bansani ba gashi da alamu har an samu k'aruwa?



Kallon juna sukai tsakanin Musayyet da Zarah yai smile yace inda nayi ai zk sani wannan
Matar Dady nace .




Oh sorry wlh bansani bane,,,,, Zarah na kwance kan sofa tn jinsu """ cikin ranta tace rainin
hankali

Doctor ya gaidata yace mk damunki? Zaune ta tashi tn cije lips Musayyet ko jiyake kamar
ciwon ajikinsa yk tace olcer ce nan ta fad'a masa yanayin datakeji ajikinta"""" magani ya
rubuta sannan yace ko gobene suzo za ai mata skining And urine test"" .amma tadenacin
yaji da maik'o da abu me tsami pls asa ido kan hakan dan yanzu olcer tana rashin kyautawa.
To kawai tace cikin ranta kuwa tace ba inda zata'°.




Tare suka fita da musayyet da kansa ya siyo mata magani tace tea zatasha ya hada mata
sannan tasha maganin ta kwanta yn kallonta tausayinta duk yakamashi """". A time d'in
gidan Momy yai niyyar zuwa amma yafasa sb jikin Zarah.





Bata farkaba se bayan Magriba a lokacin yaje sallah yadawo yn zaune kujerar dk fuskantarta
ya zuba mt ido"""""





Tana tashi suka had'a ido yai mata smile yace sannu ya jikin ?


A hankali ta mik'e tace da sauki ngd fa.


Mene ne a ciki danna temaki kaina inaga kaina nayiwa ai ko?

Smile tayi tace hakane zanje nai wanka nai sallah idan na kintsa zn dawo """"" yace ba
komai.

Se bayan isha suka zauna a palon cen ciki suna kallon cartoon ""' kallon ta yai yace nifa
nagaji da ganin wa'yan nan watsatstsaken """ dariya tayi tace ni kuma sena gani sede ka
koma wancen ka kunna abinda kk son gani.



Murmushi yk yace to anan nai niyyar gani kuma sena kalli abinda nakeso """" tace kamo
za6inka kana kamowa zan tashi kuwa ta fad'a tana juyar dakai .




Oh sorry Momy wasa nk yi muga abinda kikeso d'in nima inaso.



Ko kaifa my son tafada tanai masa gwalo "' dariya yai a hankali cikin ransa yace ynz zan
koraki yarinya.





Seda aka gama cartoon yakai AMC MOVEIS sun haska wani film lord of the ring """
ZARAH ido ta zaro ganin wani harrow tasa k'ara ta zura d'aki da gudu shiko ysa dariya harda
gyara kwanciya yaci gaba da Kallonshi yace ai gashi nan kin gudu ynz nayi kallo na ai yagada
yana dariya gamida waigen hanyar datayi.



Tana zuwa d'aki tasaki ajiyar zuciya harda dafe k'irji """' gani nai tayi shiru cen tai smile kawai
tace zk sani ne"""",,,, farin mayafinta ta d'auka ta lanyace dukkan jikinta har kanta dashi ta nufi
palon .

Musayyet na kwance hankakinsa kwance yn kallon jiyai ance kaiiiiiiiiii cikim murya tabada
tsoro """ A hankali ya juyo da kansa aiko yaga mutun tsaye da farin kaya ko motsi ba yayi ai
da gudu ya hau upstair har yn bigewa da gwiwarsa yn zuwa ya banke k'ofa yn haki .




Zarah dariya tasa tace kaima bazakai kallonba .



D'aki ta koma ta kwanta cike da nishadi da jin dadin tsoratar da Musayyet datai.



�������

[06/09, 16:21] Ummee Mukhtar: 👳🏻�♀👳🏻�♀👳🏻�♀👳🏻�♀👳🏻�♀👳🏻�♀👳🏻�♀👳🏻�♀

*AURAN*_ _*BABBAN*_

_*MUTUM*_

Sadaukarwa ga dukkan masoya wannan Novel inasonku Allah yabar k'auna🤗 .



Creating And Written By

_UMMEE_ _MUKHTAR_�



🅿22



Da Asubah Musayyet tsaye yake bakin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
google.com, pub-9213700357025247, DIRECT, f08c47fec0942fa0