Showing 39001 words to 42000 words out of 92630 words

Chapter 14 - Auren Babban Mutum By Umme Mukhtar

20 Jul 2026

860

amsa aiko
khairat na ganin dadynta itama ta kwasa da gudu tai wajensu """"


ZARAH kam kamar wacce aka dasa ta kasa gane halin datake ciki ,gaba daya bataso dawo
warsa ba hk kurun tana cikin farin cikinta wani zezo yashiga rayuwarta.

Da gudu ta koma ciki Musayyet yaga hakan amma seyai tinanin ko itama murnar take amma
seyaga har anyi mintuna bata sake fitowa ba.



Alhaj Sa'ed ya d'auki khairat yn mata wasa ya shafi jikin Misayyet yace yana ganka a jik'e ?

Smile yayi kawai khairat tace wanka mukai shine momynsa tace wai baze shigoba karya 6ata
waje .

Dariya Alhaj Sa'ed yayi yace ah da gaskiyarta kasan zakai wankan base ka dakko wasu
kayan ka ajeba koda kagama seka saka.

Musayyet ya shafi kansa yace ai dady momyn nan ta fiye rigima d'an duka dady yakai masa
gaba daya sukasa dariya.

Gaba daya part d'in dady sukai basu ganta a palor ba Alhaj Sa'ed hankalinsa nakan ta
sosamune yafara ganinta kafin ya shiga room dinsa amma hakan besamu ba.



Suna shiga khairat ta haye kan bed yayinda suka k'ara gaisawa da dady yai masa ya hanya
yace lfy lau my son ya zaman gidan namu inceko yana mk dad'i ?

D'an murmushi yayi yace eh dady bakinsa yak'i rufuwa dan murna dady yace da magana a
bakinka my son tell me "" smile musayyet yayi yace I didn't say anything """ dady yace nasani
shine nakeso ka fadamin ai .





Ummm dama idan ka huta dady akan maganar nan ne dakace zk nemo mini wacce akeso
yana fad'in hk ya yatashi da sauri ya fita cikin jin kunya. dan


Dariya Alhaj Sa'ed yayi yace my son kenan khairat ya momynki ? Ya fad'a yn shafa kanta
dariya tayi tace lfyarta lau dady.





Musayyet na fita kai tsaye room d'in Zarah ya nufa yai knocking guskarta duk hawaye tataso
ta bud'e nan sukai ido hud'u da juna ta sunkuyar dakaia k'asa yace momy meyasameki?



Babu komai kaina ke ciwo tq fad'a tn kallon gefenta matsowa yai har yn lek'en face d'in ta yace
kinsha magani kuwa ?


Da sauri ta gyad'a masa kai alamun eh yace sannu idan bedena ba se a kira docto ko dama

zamujr ai miki test sbd olcer ki.


Tace to namaji sauki ,, yace sannu Allah yabaki lfy tace ameen.


Har ze tafi ya dawo yace amma kinsan dady ya dawo kuwa?



A abansani ba dg hk ta maida k'ofa ta rufe garam """" tsayawa yayi yarasa gano meke damunta
to.





Yn hawa upstair yai wanka yai alwala ya nufi masallaci koda yadawo neman layin Zarah yai tayi
amma wayar akashe.





Gaba d'aya sun had'u a dining amma banda Zarah,,, dady yacewa khairat taje ta kirawo ta .

da gudu ta tashi suna mata dariya ganin rigar da Zarah tasamata wadda ta tsaya mata iya
gwuiwa .




Knocking tayi zarah ta bud'e tace wai kozo aci abinci """ gaban tane ya fad'i sosai tace to tsaya
mutafi tare.

Seda ta d'akko hijab tasa sannan sk fito "" tin da sk taho Alhaj Sa'ed yaga ta k'ara wani kyau
da haske besan sanda ya aje spoon d'in hannunsaba ya zuba mata ido kawai.


Musayyet ko hankalinsa nakan plate d'in yn cin abinci shikansa daya d'ago yaganta seyaji
wani abu wanda yarasa ko meye shi d'in ,,,so tari idan yaji irin hk baya iya fassara ma'anar
hakan sede kawai ya share abun ransa da zuciyarsa.

Tn zuwa ta zauna kusa da khairat cikin rawar voice tace masa sannu da zuwa ko kallonsa
bataiba.


Shima cikin jin kunya yace sannu ya zaman kad'aici duk da nasan ga my son nan bari barinsa
ma kad'ai yaisheki.


Se anan tai murmushi suma sukasa dariya """" da kansa dady yazuba mata .




Kowa yaraci amma banda ita e juya spoon take kawai a hannu.


Musayyet yace dady ina phone dinka ?


Yace tn room lfy mene '? A a dama number budurwata zan sa maka nasan zaka iya
bincikamin tinda ni yanzu kona buga bata d'auka.



Kallonshi zarah tayi kawai tana mamakin rashin kunya irinta musayyet .




Dariya Alhaj Sa 'ed yayi yace maza jeka dakko insha Allah seta zama mallakinka domin farin
cikinka shine nawa.


Da sauri musayyet ya tashi yn smile gamida d'agawa Zarah eyes yace momy zakusha biki.



Dariya tayi kawai kanta ma k'asa Alhaj Sa'ed kuwa duk hankalinsa nakan duk wani motsi
nata.

[06/09, 16:21] Ummee Mukhtar: *âšœBRILLIANT* *WRTS* *ASSO*�


👳🏻�♀👳🏻�♀👳🏻�♀👳🏻�♀👳🏻�♀👳🏻�♀👳🏻�♀👳🏻�♀

*_AURAN_* *_BABBAN_* *_MUTUM_*

Creting And Written By
_UMMEE _MUKHTAR�__


🅿24



Musayyet na shiga yaga phone d'in kan bed, cikin zumud'i yakai hannu ya d'auka ya shiga sk
number """ meze gani ? Kawai seyaga sunan My one ajikin number , da mamaki yake kallon
number cikin ransa yn cewa toko mistake nak'arayi ?

Amma kuma ai na haddace number batin yanzuba , k'ara saka number yayi amma still abu
d'aya tk nunawa lokaci d'aya ya zube kan bed yn dafe kansa, ya ilahi taya hk zata faru may be
nayi mistake ne ,,,,,

Wayar ya d'akko ya dawo palor jikinsa duk ba kwari """ Zarah ce ta juyo dan jin tafiya abayanta
nan sukai ido hudu da Musayyet ,gaba d'aya sukaji gabansu ya fad'i wanda basu san dalili ba
"""


Musayyet kallonta kawai yk cikin wani yanayi wanda shikansa baze fassara ya yake cikiba.

Zarah tai saurin kauda kanta gefe tana k'aramar ajiyar zuciya-

Yn zuwa ya mik'awa dady wanda shi kuma tin dazu ba abinda yk inbanda kallon Zarah.



Ok karanto min number dady ya fad'a yana kai tea bakinsa ,,,,Kirane yashigo wayar dady yai
pinking call shiko Musayyet da sauri yabar gun yahaye upstair yn waiwayen Zarah"""" da hk
zancen bada number ya shiririce.



Yn shiga room yai saurin d'aukan phone dinsa yashiga sk number irinde wacce yasa d'azun

itace de """ tsaye ya mik'e ya shiga zirga zirga yn shafa kansa yace kumafa dede nk sawa
meyake shirin faruwa ne ?
Amma ba komai I have to way .




A k'asa kuwa Alhaj Sa'ed se jan Zarah yk da hira ita kam tayi shiru batasan meyasa tafison ta
zauna da Musayyet ba idan suna tare yakan mantar da ita damuwarta wacce tk damunta.
Duk hirar da yake bata tanka masa sede khairat da itama take nata surutun .




Se dare sukai shirin tafiya gidan Momy Wanda Zarah taiwa Khairat make up mekyau ta kuma
zuba mata kayam kwalliya a wata bag ,,,,.


Sosai Alhaj Sa'ed yaji dad'i har ransa .



Cewa Musayyet yayi ya shirya suzo suje, amma se yace kansa kemasa ciwo """"Dady yace
nina rasa irinka abu na damunka seka barshi kai wasarere da lafiyarka bk kulawa ,idan anyi
maganar zuwa hospital kace a k'yaleka wai ze dena,,,, what kind is this?



Musayyet yaimurmshi yace to dady barina kira doctor ko""" ..Dady yace yauwa ko kaifa my
daughter mujeko""".Khairat tace to dady amm momyn bata fito ta bimuba na kirawota?


Dady yai 'yar dariya yace no itama zata zone amma ba yauba ,muje karmi dare,,,,. ...gun
Musayyet taje tai masa bye bye """"" shima yn smile ya d'aga mata hannu yace a gaida momy.






Suna fita Musayyet ya kwanta a palor a time d'in 8 :00 pm Zarah na room d'in ta tin datagama
cin abinci ta shige tak'i fitowa.

Jin shirune yasa shi tashi yaje yafara knocking yana tsaye jiyak'e k'irjinsa na bugawa da k'arfi
yai saurin saka hannu ya dafe gun gamida runtse ido .



Zarah tasowa tayi ta tsaya gami da cewa waye? Murmushin k'arfin hali yayi yace nine""" da
sauri ta bud'e dan dama tin d'azu hk kawai ta tsinci kanta da son ganinsa.



Da murmushi akan face d'insu duka tace se yanzu ka sakko?


Yace eh momy hira kawai nakeson miyi """


Tare sk jero kamar wasu masoya aduk sanda ya kalleta seyaji gabansa ya fad'i .






Zama sukai a kujeran dk face d'in juna ya kalleta yace me kika sani gameda da soyaiya ?

Dasauri ta kalleshi ta kalli TV wacce suke haska indian film tace soyaiya aganina halittace
wadda Allah ke sanyawa a zukatan masoya wato mace dana miji yaro ko babba """"",,

Kuma hakan nan lokaci daya jininku kan iya had'uwa dama wanda bk saniba.


Tin data fara magana yk kallon mouth d'in ta harse datai shiru sannan yai ajiyar zuciya """yace
Momy ina cikin matsalane amma kitayani da addu a .

Sedata gyara d'an k'aramin hijab d'in ta sanan tace zan tayama komak zezo da sauki my son .


Murmushi yayi yace ngd momy.

Kallonsa tayi tace me kk gani ga macen da aka aura mata wanda bataso kuma mahaifanta
sukai mata dole sbd wani dalili nasu musamman ma gashi mutumin idan ya kasance babba ne?




Sosai yaji maganar aransa amma wace amsa ze bata?


Kallonta yk da sexy eyes d'in sa yace kawai abinda nasani shine bazata samu duk wata kulawa
ba wadda saurayi matashi ze bawa yarinya wacce tk dedeshi ,,, zatai zaman hkr ne kawai
dashi tinda har bata sonsa .

Amma meyasa kikamin wannan tambayar ?

Gani yai tn hawaye a face d'in ta da sauri ya taso har inda tk ya tsuguna har k'afafuwan su
suna gogar na juna yai saurin janyewa jiknsa har rawa yk yace momy lfy meke damunki
konine na mk wani abun? Ya fad'a muryarsa na rawa.



Da gudu tai room d'inta ta banko k'ofa .



Musayyet ya dafe kai idonsa yaija nan da nan yaji ciwon kai na neman kamashi.





To se wajen 11 dady ya dawo Musayyet a time d'in ya hau upstair amma yn zaune kan wata
chair fara yana shan tea lokaci lokaci yn kallo hanyar room d'in Zarah .





Dady yn zuwa yai room d'in zarah yaita knocking amma shiru , jin knocking yayi yawa yasa
Musayyet d'a lek'owa yn hango dady amma sam Zarah tak'i bud'e wa.

Hk ya koma part d'in sa ransa babu dady, yanzu hk ze zauna batare daya kusanceta ba?

Hk ya kwanta yn tinane tinane.






Da safema hk yaita jiran fitowarta amma shiru gashi ana jiransa domin sunada meeting around
9. Gashi bayason yai mata knocking kartaga yadameta.





Hk ya fita masu rufa masa baya sk bishi da motoci.





Se 12 ta fito cikin riga da atamfa dinkin riga da siket wanda suka matseta se mayafi ruwan
kayan wanda ta d'ora akanta sbd batasa d'an kwaliba.



A dining ta zauna tai tagumi takasa koda motsi ne.


Musayyet ne ya sakko wanda kallo d'aya tai masa taji wani abu a ranta game dashi tabbas
kanada kyau my son duk wacce ta aureka tayi sa'a.

Kananu kayane ajikinsa wanda sukai dede da fatar jikinsa se k'amshi yk face d'insa akantata
har yak'araso gun.





Haka shima yk ayyanata aransa gameda kyawun da Allah yai mata gani yk kamar tafi ko
yaushe kyau.

Zama yayi gefenta yace mng momy ya kika kwan d'an smile tayi snn tace lfy .



Shirune ya biyo baya ta gefen ido yk kallon yanda tai kyau har wani shek'i take yi .





Cen tace dama inason zuwa saloon ne ka tambayrmin dadynka .


Smile yayi yace ok.


Number dady ya kira ya sheda masa cewar momy nason zuwa saloon.


Yace ok seka kaita sekun dawo .




Yace na kaiki momy zami iya zuwa yanzu?



Da sauri tace eh dama yawon takeso """"" dariya yayi yace muje to.



Tare sk fito ta shiga gidan gaba dan yauma cewa yayi shiba drivern ta bane """""" dariya ya
kumayi yace ai grimankine momy.

Fita sukai dg gidan seda suda sk hau kan titi yaji tayi shiru wanda kalamansa na jiyane ke mata
yawo akai nacewa baze sotaba kawai zatai zaman hkr ne.








Lura yai da dogon tinanin datakene dan hk yace momy na baki fad'amin sunanki na gaskiyaba
kawai e inacemiki momy ne ya fad'a yn kallon kan titi.




Kallon shi tai snn tai smile tace sunana ZARAH ,,,,,kaifa?


Wow Momy u have a nice name """ yace ni sunana
Musayyet tace sunan da dad'i, yace ai bekai nakiba .




A haka har sukazo gun saloon d'in zata fita kenan yace ga kud'in gyaran kan ya mik'a mata
ta amsa tace sena fito """ zata kuma tafiya kenan yace samin number ki, zani wani wajene
idan naadawo sena kira .


Smile tayi tace ok

Phone d'in sa ya mik'a amma wata k'arama ba waccen wadda yai saving ba.

Tn gama sawa ta mik'a masa yace sena dawo momy na murmushi tayi kawai ta shiga wajen
wanda ya had'u Sosai .



D'aya wayar ya d'akko ya shiga saka number nan yaga sunan funny gal d'insa ya fito rad'au kan
phone d'in sa ido ya zare yana sake kallon number itace d'in de.


Wani gumi yaji yn karyo masa duk da sanyin ACn motor da sauri ya fito dg motar yn kallon gun
da Zarah ta shiga jiyai k'afafunsa sunkasa d'aukan sa nan da nan hawaye sk shiga zarya a
face d'in sa yn girgiza kai gamida kifa kansa jikin motar.


Zarah dg ciki ta hango matarsa be tafiba dan hk ta lek'o adede time d'in ya d'ago kansa duk
hawaye wanda ita kuma ta juya baya dan komawa ciki """" da hakane besuyi facing d'in junaba
bayanta yk kallo yana ja dabaya yana girgiza kai .



















Love you my fans
[06/09, 16:21] Ummee Mukhtar: *⚜*BRILLIANT* *WRTS* *ASSO*�

👳🏻�♀👳🏻�♀👳🏻�♀👳🏻�♀👳🏻�♀👳🏻�♀👳🏻�♀👳🏻�♀

_*AURAN*_ _*BABBAN*_
_*MUTUM*_

Creating And Wrttn By
_UMMEE _MUKHTAR�__



_SADAUKARWA_ ga Nabeelah Rabi'u Zango.



🅿25




Mota ya bud'e ya shiga yasoma gudu kamar ze tashi sama jiyake kamar zuciyarsa zata fashe
sbd wani mugun zafi dayakeji tana masa.




Ahankali yafara tinanin irin zaman dasukai da yanda yakejinta aransa dama mafarkin dayake
akanta"""" har kawo wasan dasuke tare ,Ashe itace wacce yk nema wannan waca irin
k'addarace ta afka masa ?.



Kuka yafarayi kamar wani yaro yn share hawaye be au neba yaji yadaki wata babbr mota nan
take kansa yabugu da sitiyarin motar """"" take motar takama katan tanwa akan kwalta harse
data kai jikin wani dogon gini sannan ta tsaya ,,,,,,,.


Musayyet ko bema san halin dayake cikiba dan tini ya sume tin da ya bugu akansa.


Nan da nan mutane aka taru gurun suka kaishi wani babban hospital dake kusa dagun""""".

Da sauri doctors sk amshe shi ganin halim da yake ciki ko motsi bayayi ga jini na zuba a
goshinsa.



Alhaj Sa'ed yn cikin meeting wani dg cikin yaronsa yazo yace masa ammasa wayane kan
cewa sir Musayyet yayi Accident.

Da sauri Alhaj Sa'edya mik'e tsaye sauran mutanen dk gun suka mimmik'e tsaye suna
jajantawa lamarin """" da sauri yabar gun sauran jama'ar dk gun wasu dg ciki suka biyo
bayansa dan yin rakiya da kuma ganin halin da Musayyet ke ciki.





Da gudu motocin suka shigo harabar Hospial d'in Alhaj Sa'ed be tsaya an bud'e masa murfin
k'ofa ba da sauri ya fito idanunsa duk hawaye .

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
google.com, pub-9213700357025247, DIRECT, f08c47fec0942fa0