Showing 30001 words to 33000 words out of 54278 words

Chapter 11 - AUREN FANSA BY NIMCY COMPLETE HAUSA NOVELS

murya yay sosai cikin sigar
rarrashi yace "Me kike so yanzu"
Tana ƙara birgima kamar yarinyar goye tace
"Kawai kaje wajan waccan baƙin mugun mai baƙar zcy kace masa ka sauya makaranta"
Zaro ido Ya Omer yay shikam ko yasha giyar wake ai bai isa yaje wajan Ibrahim É—in Baffa ba,
kallon ta yay cike da soyayya yace "Shalele kina ganin baya kulani"
Turo baki tayi tana ƙara fasa ihu wanda har sai da Inna taji tace
"Yau mun shiga uku fa"
Moha tana kuka tace
"ai dai kai ma baka kyauta ba, meyasa zaka dakesa"
Da mmki Ya Omer ya kalleta yaga iyakar gskyar ta kenan, kamar zai kuka sbd yadda yaga ta
ɓata rai yace
"To me zanyi Shelele? Kina kallo dokanki zaiyi, ni kuma bazan iya jurewa ba"
Miƙewa tsaye tayi kamar mai aljanu ta shiga goge Idanunta kamar ba ita ga gama kukan ba
tace
"To basai ka rabu dashi ya daken ba, ni kuma sai na haÉ—asa da Ummi kaga yana son
Umminsa sosai yana jin mgnarta haka kuma yana son Mamana sosai (Anut Meera) ko kuma kai
ma ka buÉ—e masa ido kamar yadda yake zaro wannan manyan idanun nasa kamar na mage"
Kallon baki san yaya na keji a zcyta ba Ya Omer yay mata, yana da aiki sosai dole ya zama
mutum na farko kuma na ƙarshe daya samu waje a zcyar Moha amma ta yaya, da sauri
yace "Shalele akwai wani labari mai daÉ—i"
Da sauri ta matsa kusa dashi sai kuma taja baya kaÉ—an tana washe fararan jerarrun teeths
É—inta tace "Dan bani labarin na cartoon ne"
A zcyarsa yace "Ikon Allah"
A fili kuma yace "A'a, novel ne mai daÉ—i na marubuciya Nimcyluv"
Shiru tayi sai Idanunta ta zuba masa wanda yake ƙara dagula masa lissafi yace "Zan baki
wayata ki sauke application É—in wattpad, kiyi searching sunan marubuciyar kisa F@y@l ko
Nimcyluv, saiki follow daga nan saiki duba littafin SIRRIN MU ko UNCLE NE ki karanta after nan
sai muyi mgn" Wayar hannunsa ya bata bayan ya zare sim ɗaya, karɓa tayi da sauri tai waje da sauri yace.
"kee! Shalele!! Shalele!!"
Amma tuni tayi waje, tana zuwa wajansu Inna taga lodin siyayyar tafiya makarantar su, wacce
yanzu Ya Areef ya sauke masu ita a mota tare da sabbin uniform da school bag da littafai da
system, wacce duk siyayyar Ya Heemu ya bada kuÉ—in.
Hannu tasa aka ta kurma ihu tace "Na shiga uku" sai kuma tayi É—akin Inna da gudu tana
sakin sabon wani ihun.
Yana kwance lubb saman gadon Inna da sauri ya runtse idanunsa sbd bugun da zcyarsa tai
masa kamar zatai tsalle ta faso ƙirjinsa.
Ƙara narkewa yay jikin gadon tare da ƙanƙame idanunsa yana jin zcyarsa yana buga
duk abin Ya Heemu baya son ihu da É—aga Murya a kansa ko mgn mutum yay yanzu sai ce
yana masa ihu, bare yanzu da take kurma masa ihu a saman kansa dake barazanar

tarwatsewa gida biyu.
Moha sam bata kula da Ya Heemu ba,ta faÉ—a gadon ta hau birgima tana ihu tare faÉ—in.
"Wlh ko kafi ƙoda naci ba zani ba gidan Baba Haroon (Mahaifin Hannah Yaya ƙani a
wajan Mahaifin Ya Heemu).
Marai-raice fuska Ya Heemu yay kamar zai sanya kuka sbd ihun da take masa, gashi a dai-dai
saitin kunansa take haushin nata.
Mirginawa yay kaÉ—an yana danne kunansa da pillow.
Jin motsi yasa tai saurin juyawa domin Allah yay mata tsoron mage
Tsitt tayi sbd ganinsa kusa da ita idanunsa a lumshe, duk da kasancewar sa baƙi amma
hakan bai hana fuskarsa sauyawa ba kana hango wani jaa da tayi na ɓacin rai.
Ga jijiyoyin kansa sun Miƙe sosai.
Sai huci yake jikinsa duk tsoma yake gargasa jikinsa ta miƙe sosai.
Kuka tasa tana ja baya tana faÉ—in
"Dan darajar Annabi kayi hqr wlh suɓutul kalam nayi, dan Allah kada kai min komai dan son da
kakewa Ummi"
A hankali ya shiga buÉ—e nauyayyen idanunsa wanda sukai jajirr.
Ya sauke a kanta tsanar da yaywa Yarinyar yasa yake ganin fuskarta nada munu a idanunsa.
ÆŠauke idanunsa yay hakan yasa ganinsa ya sauka akan wayar hannunta zare ido yay.
A hankali kuma ya miƙa hannunsa da sauri tai baya zata sauka yay saurin cafke Hannunta
ya shiga kallon wayar hannunta kafin ya kalleta fuskarsa kamar hadari babu walwala.
Kallon da yake mata yasa tace "Wlh ba ruwana Ya Omer yaban wai nai karatun littafi.
Baice mata komai ba ya kama hannunta tare da sauka daga saman bed É—in jikinsa duk rawa
yake, Moha kam gaba ɗaya ta firgita da Ganin Ya Heemu bata taɓa ganinsa a haka ba.
A waje ya samu Ya Omer da Ya Areef suna Mgnar gidan gonar Ya Heemu, tun daga nesa Ya
Areef yaja baya domin shima ya tsorata duk da cewa shi ne gaba da Ya Heemu gaba É—aya
Ya Heemu shi ne ƙarami a cikinsu.
Shima Ya Omer gyara tsaiwa yay domin yasan kwanan zan can tunda yaga wayarsa a
hannunsa ga Moha daya riƙe kamar zai ɓalla ta.
Idanun Ya Heemu har ruwa yake sbd zallar bala'i yana zuwa bai tsaya jiran komai ba yasa ya
zabgawa Ya Omer mari zafi da ƙarfin marin yasa Ya Omer yin baya yana dafe kunci abinka
da mai Zcy shima ya nufi Ya Heemu zai mara Moha na ganin haka tai saurin ƙanƙame Ya
Heemu tana sakin kuka tsayawa Yay cak yana kallon Mmki. Baffa da Baba Haroon da Kawo Shuriem (Mahaifin Shoona da Areef) suka tsaya cak suna
kallon ikon Allah domin basu taɓa sanin akwai saɓani a tsakanin Yaran nasu ba.
Baffa kam Murmushi Yay sbd abinda Moha tayi ga wanda ta saba dashi ta shaƙo dashi an
maresa batai komai ba amma wanda ta tsana anzo marinsa ta hana.
Ya Omer yace
"ka maran?"
Ya Heemu ta huci yana son zare Moha daga jikinsa amma tai masa mahaukacin riƙo yana
fesar da iska yace "Sai na mallaka yanzun nan, ashe girman banza gareka ashe baka da
hankali yarinyar da an zuba mata ido wacce Allah ya kaya bare ka É—auki waya ka bata, abin
takaicin bama karatu makaranta zatai ma wai Hausa novels ka bata ta karanta, what the fuck?
Heeee!! What's this answers my questions OMER ALIYU AL'AMEEN?" Murmushi Baffa yay

yace "AL'AMEEN sunana ke nan"
Bai ko kalli inda Baffa yake ba yace "Baka da amsa ko? Sbd kana son ka gina soyayyyar ka a
zcyrta shi ne baka son komai ka bata waya tai karatu may be she understands very well ko?
Well-done Omer Aliyu Al'ameen"
Ya faɗin hakan yana buga wayar a ƙasa ta watse nan take.
Baffa ne ya samu damar faÉ—in "Malam Ibrahimul Khalel meya faru kai da waye jikalle?"
Hucie kawai yake ganin hakan yasa Kawo Shuriem ya ƙara so wajan tare dasa hannayensa
ya riƙe hannun Moha kuka tasa tace "Kawo dukansa Ya Omer zai yi haka kwanaki ya
dakesa a ƙirji"
Kallon juna sukai wato faÉ—an bana yanzu bane kenan.
Ya Omer kam duk ihun da Ya Heemu yake baya fahimta fargaba da tsoro suka kamsa, ganin
yadda Moha take nuna kariya ga Ya Heemu.
Da sauri ya zube gaban Baffa yana riƙe ƙafafuwansa yace "Baffa dan Allah dan Annabi
kayi min rai ka aura min Aysherh idan duk akanta yake wannan abun zan kawo ƙarshen
abun yazo, dan Allah Baffa nai maka al'ƙawarin duk abinda za kace amma ka fara aura min
ita wlh zan iya rasa rai na idan ban sameta ba" Baba Haroon ne yace "Omaru baka da hankali amma dai ko, wannan yarinyar zaka aura gaba
É—aya nawa take?"
Baffa ne yace "Haruna kira min Aliyu yanzun nan, sannan ka kira min Al'mustapha yanzu
shima"
Da mmki Baba Haroon yace "Amma Baffa kiran na mene?"
Baffa yace "Bana son mgn" yana faÉ—in haka ya kama hannun Khalel da jikinsa ke rawa kana
ya riƙe na Ya Omer yace "Kawo min matar nan" ya faɗi hakan yana nufar cikin ɗakinsa.

Driving daya É—auko Mannal nayin parking ta fito daga cikin motar a nutse take tafiya amma
hankalinta gaba É—aya baya jikinta tana shiga cikin babban parlo Dad É—inta na fitowa da
sauri ta nufi inda yake yana ganinta yasan akwai matsala, tana zuwa ta faÉ—a jikinsa tana
sakin kuka tana riƙe tana faɗin "Dad!! Dad!! Dad Abban Arman" sai kuma ta ƙara saka
wani kukan, janta yau zuwa wajan kujerar ya shiga rarrashinta sai da tayi Shiru tana manne
jikinsa tana sakin ajjiyar zcy kamar wata yarinya Dad yace "Ƙara zuwa kikai ko? Ashe kin
girma ba zaki hankali Ba Daughter na? Kinfi son ki zauna da wanda zaici mutuncin ki yaci
mutuncin mahaifin ki? Ke kika hanani kaishi Court da al'ƙawarin ba zaki sake mgn dashi ba
yanzu shine kika karya al'ƙawarin ko?" Waya ya ɗauka ba tare daya janyeta daga jikinta
ba ya kira yace "Kamal kazo kai da Jamil" yana faÉ—in hakan ya da É—a kiran wata number
yace "Yace Sufyan har yanzu kana sha'awar Auran Daughter?" Kai ya jinjina kana yace "Ok
meet me right now" gaban Mannal ya bada sauti rasss rasss dam! Miƙewa tayi tace "Dad?"
Hannu ya É—aga mata yace "Kinyi abinda ki kaga dama yanzu nima zanyi abinda naga dama a
matsayi na mahaifinki"
Wayarsa tayi ƙara bayan sun gaisa ya tsaya yana jin abinda ake cewa shiru yay sai kuma
yace "Ikon Allah"

Baffa ya kalli yaransa, Baba Haroon da kawo Shuriem sai kuma Uncle Aliyu, da kuma
Al'mustapha mahaifin Moha wanda dawowarsa daga ƙasar kenan, Baffa ya kalli Ya Heemu

dake gefen damarsa wanda har yanzu jikinsa rawa yake, kana ya kalli Ya Omer sai kuma ya
kalli Moha yace "Aysuhtul humaira wa kike son Aura tsakanin Yayanki Ibrahimul Khalel da
Omaru?".
Narkakkun idanunsa Ya Heemu ya É—aga ya sauke akanta yaci Sa'a suka haÉ—a ido tsuro
tayi tana kallonsa kamar yadda shima yake kallonta a lokaci na farko da tasan cewa shi É—an
uwanta ne kuma jininta domin Moha Æ´ar wajan Al'mustapha shi kuma Al'mustapha É—an
uwan Ummi ne, Anut Meera kuma Æ´ar ce wajan Baffa, sai yanzu take ganin kamar su sosai da
Ya Heemu hatta dimples teeths gave da tusar jakinsu duk iri guda ce, kallonsa take kamar
yadda yake kallonta hawaye ya sakko mata bata taɓa sanin kalmar aure ba sai a bakin Ya
Omer dan haka ta juya ta kalli Ya Omer kana ta kalli mahaifinta mutum mai karamci da kuma
alkunya muryarta na rawa tana son sakin kuka tace "Baffa Ya Omer na keson ya auran"
Da sauri Ya Heemu ya miƙe yana haɗa hanya ya bar ɗakin yana ɗan sakin gajeran
tari.


MASOYA NA MASOYA LITTAFAI NA, NESA TAZO KUSA, ABINDA KUKE ZAMAN JIRA YA
KUSA ZUWA GAREKU, SOYAYYAR KU KAWAI YA JIRA, LITTAFIN *ABU_MALEEK* KADA
KU SAKE A BAKU LABARI, DOMIN DUK WANDA YACE ZAI BAKU LABARI TO TABBAS YAY
MAKU ƘARYA, DOMIN LABARIN *ABU_MALEEK* YA HUCE TUNANIN MAI TUNANI, DA
HARSHASHEN MAI NAZARI, DUK YADDA KA KAI DA FAHIMTA LABARIN *ABU_MALEEK*
ZAI MAKA WAHALAR GANEWA, SOYAYYA CE MAI ƊAUKE DA SARƘAƘIYYAR
ƘIYAYYA DA KUMA ZALLAR MULKI DA IKO TA *MASARAUTAR KANZAF* KU NUNA MIN
SOYAYYA KO FARANTA MIN KAMAR YADDA NAKE FARANTA MAKU KUZO KUYI PAYMENT
NA ABU MALEEK AKAN #500 KACAL ZAKU SAMU BOOK 1 2 3, KUN KARANTA MOON,
UNCLE NE, THE NEW EMIR, JIDDAH, JUYAYI DUK KUNJI UWA UBA SIRRIN MU TO ABU
MALEEK YA HUCE DUK SANINKU, BAZAN FARA POSTING BA SAI AN GAMA PAYMENT
KUMA ZAN FARA POSTING NE BAYAN NA KAMMALA BOOK 1 KA SANCE MUTUM NA
FARKO WAJAN BIYI HAKAN ZAI BAKA DAMAR SHIGA VIP POSTING SAMA DA ÆŠAYA
KULLUM TARE DA KYUATAR LITTAFIN *SAI NA AURETA* VIA 0116886423 SULAIMAN
NA'IMA S UNION BANK EVEDANCE OF PAYMENT 08119237616 GA ƳAN NIGER ZA SUYI
MGN TA NAN 84506476 KADA KO MANTA NAIRA 500 NE.




SARAUTA
11/30/21, 9:05 AM - Ummi Tandama😇: 🌈🌈🌈🌈🌈🌈🌈🌈🌈
*AURAN FANSA*
NA'IMA SULAIMAN SARAUTA
Nimcyluv


23-24

Baffa ne yabi bayan Grandson É—in nasa da kallo yana mmki hali irin na Ibrahimul Khalel.
Not too long Ya Heemu ya dawo cikin É—akin É—auke da gorar ruwa yana kafawa a bakinsa
tare kwankwaÉ—ar ruwan da sauri da sauri kamar zai janye gorar ruwan zuwa cikinsa.
Yana gama sha yaja ya zauna dab da Baffa kansa a ƙasa amma jikinsa har yanzu was
vibrate amma ko a fuska baza ka taɓa gane ai nayin abinda yake cikinsa a zcy ba.
Huci kawai yake yana fesar da iska hatta gashin kansa wanda suke a murmurÉ—e kamar anyi
masa (Dada)
Sai da suka miƙe tsaye.
Baffa ya gyara zama yana É—an daidaita nutsuwarsa cike da kamala da kuma haiba irinta
kamilallun maza Baffa ya kalli Al'mustapha yace.
"Al'mustapha ina neman amincewar ka akan ka bawa jikana auran Æ´ar kuma jikata idan babu
damuwa"
Wanda aka kira da Al'mustapha yaja gajeran numfashi tunanin halayyar Moha yake.
Yarinyar tana da wahalar sha'ani mai gane mata sai ya shirya.
Bata da tsoro sam ga tsaurin ido haɗi da zallar ƙuruciya, bata sanin dai-dai da abinda
yake ba dai-dai ba, sai dai ita É—in abin tausayi ce sosai.
Musamman idan ciwonta ya tashi ko da yake duk zafin ciwonta bai kama ƙafar na (Hawwa'u
Jidderh, kulu kuma Julde Æ´ar makauniyar Abu Maleek ba).
Tana da rauni sosai amma shi kansa bai san mene rauninta ba, har gobe kuma abu guda yake
sawa ta saduda shi kansa baya gane wannan lamari nata domin abun yana masa kama da
JUYAYI.
rawar kai yay mata yawa over nutsuwarta É—aya Ya Heemu gashi wani dalili na sawa ya cire
dukkan wani hope nasa akan É—an Æ´ar uwar tasa.
Idan Khalel baya kusa mgnar wa Mamansa za taji? Wazai mata tsawa É—aya ta samu
nutsuwa?
Baffa ne yay gyaran murya yace
"Alhj Al'mustapha kai muke saurare"
Numfasawa Alhj Al'mustapha yay kafin ya É—aga kai ya kalli Aysuhtul humaira yaga taiwa Ya
Heemu ƙuri da idanu kana ya mayar da kallonsa ga Ya Heemu yaga hankalinsa kwance
kamar ba shi ya shiga tension É—in daya shiga yanzu ba.
Kansa a ƙasa yana latsa Wayarsa mai ƙirar Iphone 12 max pro.
Cikin sanyin nutsuwa haÉ—i da kamala da kuma kamewa irinta mazan jiya masu sanin darajar
na gaba dasu yace.
"Baffa Nima kamar É—a nake gareka to bana da haufi akan dukkan wani shawara daka yanke
akan wannan sabon al'amarin, yadda Jikar ka Aysuhtul humaira zata amince da sharaÉ—in ka
haka nima zan amince da sharaÉ—in ka Baffa, ka amince É—ari bisa É—ari Allah yasa Albarka
ya kaɗe fitina" Ya ƙare maganar yana sunkuyar da kansa ƙasa yana mai tausayin yarinyar tasa, wacce
har yanzu bata san abinda yake mata ciwo ba, girman jiki ne kawai da Ubangiji ya bata.
Jinjina kai Baffa yay cike da gamsuwa da kuma girmama girman karamcin da Al'mustapha yay
masa.

Kullum yana buƙatar kasancewar da yarinyar sa, amma baya samun damar haka.
Domin dashi da Baffa ba'a san wanda yafi son Moha ba, ƙarfin soyayyar da Baffa ya kewa
Moha yasa gaba É—aya ya dawo da zamanta wajansa, ganin haka yasa sauran jikokinsa
dawowa wajansa baki É—aya, Shoona, Hannah Sai kuma Sunaina ita wannan tana karatu waje
sbd tana ɗan gaba dasu, Murgayiya Safa kam ƙulafucin uwa gareta kamar dai SARAUTA
haka take, sometimes shike ɗaukan ƙafa yaje wajanta yana cewa yaje biko.
Tuna wannan karamcin na Al'mustapha yasa Baffa faÉ—in.
"duk da cewa ina da iko akan abinda zan aiwatar amma dole dai na nemi amincewar ka domin
kai ka haifi Aysuhtul humaira, Ina gdy ƙwarai da wannan karamcin ka nuna min nima mahaifi
nake gareka kamar yadda nake mahaifi a wajan Matarka (Aunty Meera)".
Casbahar hannunsa ya ajjiye tsohun yasan me yake duk da cewa ya tsufa ainun amma sosai
yake da himma da kuma saurin fahimtar abubuwa masu muhimmanci.
Yaransa ya kalla sannan ya kalli jikokin nasa a nutse yace.
"Haruna fito min da dukkan abinda yake aljihun ka"
Baba Haroon ya sanya hannunsa ya É—auko harfar kuÉ—i ta 500 wanda ya kasance 50k ne,
kuÉ—in ya ajjiye gaban Baffa da sauri kuma yasa hannu ya É—auki zoben daya faÉ—a daga
cikin kuÉ—in.
Zoben Ya Heemu yabi da kallo sai kuma ya janye idanunsa yana maida kallonsa ga Wayarsa.
Baffan yace
"A bisa abinda yake faruwa ga yaran nan ni kuma na yanke nawa hukuncin da nake ganin shine
dai-dai da abinda nai nazari, dan haka na bawa Omaru auran Aysuhtul humaira, bisa sadaki
dubu hamsin Allah ya sawa Auran albarka"
Gaba É—aya suka amsa da Ameen.
Nan Baba Haroon ya zama waliyin Ango Ya Omer sai Kawo Shuriem ya zama waliyin amarya.
Ya Omer wani hawayen farin ciki ne ya sakko daga cikin idanunsa ya rungome Baffa yana masa
gdy.
Moha kam shiru tai sai zare fararan Idanunta masu sheƙi wanda kamarsu ya ƙara fita sak
dana Ya Heemu.
Ji tayi abu mai girma da kuma nauyin gske ya danne mata kai.
Yayinda bugun zcyarta ya tsananta, ƙarfi da harbawar ko wacce ƙofa da take jikin zcyrta
ya ƙaro fiye da ko wanne lokaci.
Cikin rashin makamar abinyi da kuma rashin gane ainahin abinda yake faruwa idanunta ya fara
fidda wasu zafaffun hawaye mai fidda zafi da kuma kala, yadda hawayen suke gudu a saman
farar ƙyakkyawar fuskarta zai sanya ka tabbatar hawayen bana jin daɗi bane sam-sam ko
kaÉ—an. Duk wannan abinda ake idanunta yana kan Ya Heemu ita kanta ba tace ga kallon da take masa
ba.
Wasu abubuwa na shekarun baya suka fara dawowa gareta da tunanin, Shadow'n photon abin
ya fara yawo cikin ƙwayar idanunta masu fidda ƙyallin zaiba.
Ya Heemu ya ajjiye wayarsa ba tare daya kalli kowa na wajan ba ya mayar da ganinsa kan
Baffa yace
"Baffa ina da buƙata"
Shafa kansa Baffa yay yana mai jin so da kuma ƙaunar Ya Heemu na ƙara huda ƙofar

jijiyoyin zcyarsa.
Cike da kulawa yace
"Haba zakina, faɗi ko mene indai maifi ƙarfina

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login