Showing 24001 words to 27000 words out of 54278 words

Chapter 9 - AUREN FANSA BY NIMCY COMPLETE HAUSA NOVELS

ɗaya ne? Ƙilan hakan
zai sanya ta aminci maka, wata zcyar tace "You're mad Ya Heemu, tayaya kake ganin zata
amince maka bayan babu abinda tafi ƙauna a duniya sama da mahaifinta sai mijinta"
Ƙoƙarin cire hannunta take daga ƙirjinsa ko zata samu damar ƙwace towel ɗin
hannunsa, addu'a take Allah yasa kada ya buÉ—e idanunsa.
Runtsa idanunsa Ya Heemu yay sbd zafin da yaji a wajan da Ya Omer ya dakesa, Mannal kam
sai bata san da wani doka ba bare tasan cewa yana jin zafi a jikinsa hakan yasa ta ƙara
murza hannunta dake ƙirjinsa, da sauri ya zame hannunsa dake bayanta cikin rashi Sa'a
gaba É—aya towel ya ware tass, a zabar da Ya Heemu yaji yasa ya É—auki hannunsa yana
ƙoƙarin kama hannunta dake ƙirjinsa domin ya cire kai tsaye hannunsa ya samu
gurbin zama a saman left ƙirjinta, kansa yaji ya sara ta cikin idanunsa ya zare idanunsa ba
tare daya buɗe ba, shidai yaji hannunsa ya riƙe abu kamar balloon abu mai tsayi da kuma
faÉ—i ga taushi, hakan yaji zcyarsa bata yarda da abun ba yana son kuma ya tabbatar dan
haka yasa hannu ya matse ƙirjin wani ihun azaba Mannal ta saka tana sakar masa cizo a
hannu, da sauri Ya Heemu ya buÉ—e idanunsa, idanu ya zare kai tsaye kuma ya sauke
ganinsa a hannunsa dake riƙe da ƙirjinta guda ɗaya, innalillahi wa'inna ilaihir raji'un, a
fili kuma ya furta "Yasubuhanallah" yana faÉ—in hakan ya saketa tai baya ta faÉ—i saman bed
da sauri haɗi da gudu², yabar ɗakin dafe da ƙirjinsa da kansa sai zare ido yake kamar
wanda yaga maciji, yaci Sa'a babu kowa a parlo da É—an gudu yay wajan yana zuwa ya shige
motarsa ya jata da wani irin gudu yabar cikin gidan.
A bakin titi yay parking yana ɗan kalle² kamar me neman wani abu, da sauri kuma ya ware
hannunsa gaba É—aya a É—an ruÉ—e yake sai yarfe hannu yake ji yake kamar yanzu ne abin
yake hannunsa, gaba É—aya ya manta akwai wata halitta a jikin mace makamancin haka.
Rigar jikinsa ya zame ya zame gaba É—aya ya cire singlet É—in ya É—aure tafin hannunsa a
ciki sbd tunanin ko ruwan ƙirjinta ya taɓa masa hannu.
Gaba ɗaya ya marai-raice fuska kamar zai fasa ihu, a fili kuma ya taɓe baki yace "Na aza
balloon ce ashe...," Sai kuma yay saurin yin shiru yana jan idanunsa yana rufewa sai yanzu
dokan da Ya Omer yay masa a ƙirji yake ɗan damunsa domin ko numfashi yaja sai yaji
zafi sosai a ƙirjinsa. Yana barin ɗakin Mannal ta mirgina saman gadon tana sakin kuka tare da miƙewa da
sauri ta isa gaban mirror tare da zame towel ɗin ta kalli ƙirjin ta wanda Ya Heemu ya
matse taga saman yay jaa, kuka ta ƙara saki tana faɗin "Wayyoooo Abba Mamana zafi" ta

faɗa tana ƙara ƙanƙame jikinta gaba ɗaya ta rasa wanne abune hakan, Ya
Heemu na son mayar da ita ƙwallon wasan sa..
Shi ko kunyar haÉ—a ido da ita ba yayi, da wanne ido ma zai kalli Arman ta fahimci Ya Heemu
sam bai san kunya ba, haka kuma gaya gudun abin kunya..
Shi baya son farin ciki a rayuwarsa ne? Banda haka ƙarami yaro kamar Ya Heemu me zatai
dashi, me zai É—auke mata, gaba É—aya nawa yake a shekarun yana jin zai iya É—auke
dukkan buƙatun rayuwarta ne?
Miƙewa tayi bayan taci kuka ta ƙoshi kamar ƙaramar yarinya riga tasa body Short
mara hannu ta fesa parfume tare da É—aure kanta ko dinner ba tayi ba ta haye bed ta kwanta,
tana ƙarasa karanta SIRRIN MU domin Littafin da yazo ƙarshe sai yafi daɗi, tana zuwa
ƙarshen Labarin taga Announcement na sabon littafin Anty Ni'ima mai suna *ABU_MALEEK*
labarin mai tsayi ne domin zai je book 1, 2,3 littafin na kuÉ—i for 500 for vip, 300 for regular,
sosai tai mmki domin a yadda taji tsarin labarin da kuma sabbin abin da yake cikinsa ta
É—auka zai je 1k ko 2k murmushi tayi a fili tace "Nimcyluv i like your attitude kinyi taku"
Sharp-Sharp ta shiga acct É—inta taiwa Nimcyluv transfer 5k just for appreciate, Domin littafin
SIRRIN MU ba ƙaramin daɗi yay ba, amma duk wannan daɗin da yay a hakan Nimcy
tace bai kama ƙafar ABU_MALEEK ba. Ganin bata jin bacci sam sbd tashin hankalin da take
ciki kuma bata ƙaunar damuwa tai tasiri a ranta sai kawai ta fara karanta SAI NA AURETA
littafin Nimcy na farko wanda ta fara na kuÉ—i.
Ya Heemu na zuwa gida ya tarar ba kowa a parlo da kuzarinsa yake taka ƙafafuwansa zuwa
part É—insa har lokacin kuma hannunsa a É—aure yake.
Kai tsaye bathroom ya shiga ya zare singlet É—in ya tara hannunsa a sink ruwa ya fara zuba,
kana ta sanya detol ya shiga wanke hannayensa yana dirzawa, yana gamawa ya sakarwa
kansa shower ruwa ya shiga ratsa jikinsa yana dukan baƙar fatarsa wacce har hasken
baƙi take, yana gamawa ya sanya kayan a washing machine kana ya wanke bakinsa tass ya
shiga busar da gashin kansa da abin gyaran kansa. wasu nightwear masu kyau da taushi ya
É—auka company Panjams White colour, gaba É—aya rigar daya sanya tun daga wuyansa har
zuwa ƙirjinsa a tsage take, wandon kuma gaba ɗayansa iya guiwa ne.
Bayan ya gama ya sanya bedroom sleeper suma white ya nufi kitchen É—in dake part É—insa
ya haɗa coffee mai zafi, yana ƙoƙarin kai coffee ɗin bakinsa yaji wani a zabar zafi,
tsaki yaja kaÉ—an tunawa da Moha da yay he hate her wlh gaba É—aya Yarinyar sam bata da
kunya, kamar wacce aka sangarta. Parlo ya koma ya zauna kana ya É—auki remote ya sauya channel zuwa Aljazeera ya fara
kallon labarai domin abinda yafi kalla kenan, sai kuma kallon Ball musamman idan
ABU_MALEEK ne zai gabatar da wasan gayan ya iya buga ƙwallo.
System É—insa ya buÉ—e yana buÉ—ewa ya samu abinda ya bari da sauri ya fice a wajan a
fili yace "Ƴan iska" kai tsaye ya fara operating system yaci gaba da binciken da yake domin
soon yake son gabatar da komai, domin tuni ya rubuta dakardar sauya muƙami daga Chief
of Army zuwa Captain Khalel Sha'aban. Washe gari tun da safe Mannal ta gama shirinta na barin garin zuwa Kano, domin dukkan
abinda zai sanya ta haÉ—u da Ya Heemu yan zun kam gudunsa take.
A hankali ta fara sakkowa daga upstairs zuwa downstairs tana sanye da wani light purple É—in
lace mai White É—in Flowers, anyi mata nrml É—inkin duguwar riga mata brest_cup sai stones

da aka jera mata a saman wuyan rigar har zuwa baya, rigar ta É—an buÉ—e hakan ya baya
faffaÉ—an west É—inta damar juya son ransa ba tare da takura ba.
Ta sanya nrml passion ɗin neakless da ear-ring fuskarta fayau ba zaka taɓa cewa ta kwana
tana kuka ba, ta murza ɗaurinta na gaban goshi bayan ta sauke gashinta a ƙasan
wuyanta, hannunta riƙe da Iphone 12 max pro.
Cikin nutsuwa ta gama sakkowa tana nufar dinning area, cak ta tsaya sbd jin ƙamshin
turarensa tsoro da fargaba suka saukar mata, haka nan taji bata yarda ba ƙilan abinda ya
faru jiya yasa ta kejin hakan.. kanta a ƙasa ta ƙarasa tare da jan kujera ta zauna, abin
mmkin tana zama taji tamkar ta zauna inda turaren yake, Arman dake zaune yana cin soyayyan
dankali with vegetables source ya kalli mahaifiyar tasa shi kansa yana mmki ace ita ta haifesa
shiyasa da yawan friends É—insa basa yarda sai sun tambayi Ya Heemu, ajjiyar zcy ya sauke
kafin yace "Ina kwana Mumy?" A hankali ta É—aga kanta tare da watsa masa Idanunta wanda
sukai jaa kana ta É—auke tana jan mug domin haÉ—a tea shi kawai take tunanin zata iya sha,
cikin jan ajin daya zama jikinta tace "Yaka tashi hope ba wata matsala" Arman yace "Yes Mumy,
Mgnar matsala kuma kin san akwai" tana zuba milk tace "Ok dear ina jinka" ya marai-raice
fuska yace "Mumy how can you imagine life without you a gidan Abba, and ba wannan ba
tayaya kike tunanin zan iya jure ganinki a gidan wani bana Abba ba, dan Allah Mumy ki koma
sbd ni da kuma soyayyar da kike min" tunda ya fara mgn take shan tea É—inta a hankali tana
rufe idanunta, Yes tana son Abban Arman amma ta ina zata fara? Zata ƙasƙantar da
kanta ne Just sbd she want come to him, this is difficult abu ne mai wahalar gske haka kuma
bashi ya buƙaci hakan ba.
Jin tayi shiru ya kama hannunta ya riƙe cikin nasa kamar zai kuka yace "You're my mother
kinfi kowa sanin soyayyyar da nake maki Mom! Dan Allah sbd ni, ban san mene matsalar ki da
Abba ba, amma koma mene ina son ya zama tarihi ko koma kamar da asalin masoyan Gsky,
Mom! Yanzu duk kwalliyar ki da iya girkin da tsaftar ki sai dai wani ya mura?" Kamar daga sama
taji saukar Muryarsa yana faɗin "Kai kuma kana baƙin ciki" girgiza kai Arman yay yace
"No Ya Heemu is not like that, kai ma zaka tayani kishin Abba ai,dan Allah kasa baki" Mannal
kam tuni tayi suman zau ne, da sauri ta juya ta kalli inda yake no wonder ashe yana left hand
ɗinta shiyasa gaba ɗaya ƙamshin sa ya gana gundirarta, yana zaune kai ba zaka taɓa
cewa shi yay mgnar ba sbd yadda ya É—auke yana duba wayar hannunsa, yana sanye da
wasu blue ɗin suit, wanda sukai masifar haska baƙar fatarsa ya manna wani baƙin
glasa a idanunsa ba zaka taɓa cewa ga halin da yake ciki ba.
ÆŠauke kai tayi Uncle yay dry yace "Ya Heemu baku gaisa da Mumynku ba" idanunsa akan
Wayarsa yana tsotsar strowbeery a bakinsa cikin tattausan Muryarsa mai kwarjinin gske irin ta
ƙasaitattun maza yace "Mrng Mumy" Mannal wani baƙin ciki ya kamata ganin kallon da
Uncle ke mata yasa tace "Ibrahim Ya gida" ajjiye wayar yay gaba É—aya ya juya gareta yace
"Mmy i miss You so much baki ko nemana" ya faÉ—a yana bata side hug kan Uba ta faÉ—a a
ranta lallai Ya Heemu bashi da kunya ji yadda yake acting like duk abinda yake faÉ—a Gsky ne,
Khausar tace "Ya Heemu kwana biyu Mmynka sai addu'a" É—an Murmushi dole tayi kana a
hankali ta É—an rungome sa tare da shafa fuskarsa tace "Sorry Heemu na" tayi hakan ne
domin ta nuna ta fishi iya tsiya, Arman yace "Mmy ni ko kiss É—in da kike min a kumatu kin dai
na" Ya Heemu na É—an É—auke kai tare da juyar da kansa dai-dai fuskarta yana aikata mata
da wani kallo mai kashe jiki kafin a hankali yace "Nikam yanzu za'a rama min" zare ido tayi

shima ya zare mata nasa idon yace "Ohhh!! Mom" runtsa idanunta tayi ta É—ura bakinra gefen
baƙar fuskarsa ta masu small kiss, tana shirin ɗauke fuska yasa tattausan softness hands
ɗinsa ya riƙe fuskarta mai taushi da laushi sai ƙyalli take yace "Ohhh Ya rabb! Uncle
Mom cewa idanu take ne?" Uncle yace "Waya sani, tunda ta rabu da mijinta take cikin damuwa"
Shiru Ya Heemu yay gani ta haÉ—e rai tamau fuska ba walwala dai-dai kunanta yace "Get
ready, Soon you're going to be Mrs Ibrahimul Khalel Sha'aban the richer young man" yana
faɗin hakan ya zame fuskarsa yana taɓe baki kafin yace "Allah ya dai-dai ta" da sauri Arman
yace "Amen Ya Heemu, Abba ma yace kije office ki samesa kuyi mgn" Ya Heemu ya É—auki
wyarsa ya É—ura a kunne kafin ya É—an É—aga Murya yace "Don't ever try to go" sarai tasan
da ita yake kallon Arman tayi tace "Ok My son" tana faɗin haka ta miƙe ko tea ɗin bata
gama sha ba, upstairs tayi Uncle ya bita da kallo kafin yace "ita wannan halan bata san ta girma
bane, shekaru sama da 40 ba wasa ba fa" Murmushi kawai Khausar tayi Arman kuma yay waje
yana faÉ—in "Ya Heemu bari naje" ko inda yake Ya Heemu bai kalla ba sai da ya fice sannan
Ya É—an kalli Uncle yace "zan amshi abu gun Mumy" yana faÉ—in hakan yay upstairs yana
ɗan shafa ƙirjinsa tana tsaye a parlon sama sai kai koma take tana ɗan yarfe hannu.
Buɗe ƙofar yay ya shigo bata juya kamar zata ari baki tace "Ya Heemu ka fita a idanuna,
idan baka da kunya ni ina da ita" waje yaja ya tsaya yana Kallonta yana kuma jin me take
faɗa, wajansa ta ƙarasa inda yake tace "Let's talk Ya Heemu, dan Allah dan Annabi mene
yasa kake haka, kai baka san cewa Namiji ne wanda yake da ikon samun dukkan matar da
yake so ba, look at you Son, kana da kyau hankali ilimi ga kuÉ—i kaga ko Æ´ar sarki kace
kana so billahi zaka samu...," Saurin kai tafin hannunsa yay saman bakinta hakan yasa bata
ƙarasa faɗin abinda tayi niyya ba, matsawa yay sosai kamar zai shige jikinta ɗaya
hannunsa ya ɗura west ɗinta daga baya ganin tana ƙoƙarin faɗuwa, fuskarsa dab
da ta ta, ya shiga sauke mata numfashi yana fesar da iska daga bakinsa kamar bazai ce komai
sai kuma yace "Hate me or love me baya tsarin Khalel ina son amincewar ki, kisan cewa idan
nayi niyar auran ki koda baki so sai nayi, why kike ƙoƙarin wahalar da kanki Mumy? Am
your son, and you're my Mom dan haka period sunayen mu zasu sauya daga haka zuwa miji da
mata, ki dai na wahalar min da kanki" hannu tasa zata hankaÉ—a sa amma ko motsi bai ba, sai
ma ƙara matse ta da yayi yana kallon tsakiyar idanunta wanda ya karanci ƙarancin rashin
baccin dake damunta, ganin bashi da niyyar sakinta yasa ta sakar masa kuka ya riƙesa tare
da tura fuskarta ƙirjinsa shiru yay domin babu wata ƴar mace data taɓa samun so close to
him kamar Mannal, sai Moha wacce sai yaci ubanta yay mata doka taga babu sarki sai Allah shi
ne take maƙale masa, sosai Mannal take kuka tana dokan Ya Heemu shi kam bai san me
ake ba domin bai wani iya rarrashin mace ba, hasali ma kukanta bai damunsa ko kaÉ—an,
ganin yadda take kuka wanda ya tabbatar daman ta daÉ—e tana tara kukan bata samu damar
inda za tayi ba ne, sai yanzu da ƙirjinsa ya zame mata mafaka, sosai take kukan a wannan
lokacin baƙin cikin abinda Abban Arman yay mata ya dawo mata sabu fil, ga rashin kirki da
yaywa Dad É—inta amma duk da haka zuciyarta shi take muradi tasha try kiransa amma kullum
idan ta kirasa dry yake mata yana faÉ—in ta rasa mijin aure tsuhuwar mace like her babu
wanda zai aureta, dan haka idan tana son ta koma gidansa dole sai tazo ta durƙosa akan
ƙafafuwanta ta basa hqr akan idon ɗan ta, hakan zai sanya ya ƙara wanke laifinsa
tunda ya shaidawa Arman cewa ita tace ya saketa.

🤔ANYA YA HEEMU ZAI SAMU DAMAR AURAN MANNAL KOWA? TEAM MANNAL ME
KUKACE?

TEAM MOHA AND YA HEEMU BAN MANCE DAKO BA INA SANE DAKU KUN SAN CEWA
NIMA INA TEAM ÆŠIN KU MANNAL OLD WOMAN CE KAMAR YADDA ABBAN ARMAN YA
FAÆŠA.

*SIRRIN MU*
YA ZAMA COMPLETE DUCOMENT BOOK 1 2, DUK MAI SO ZAI BIYA 500 TA WANNAN
ACCT NUMBER 0116886423 SULAIMAN NA'IMA S UNION BANK EVEDANCE OF PAYMENT
08119237616💃�🌚
11/30/21, 9:04 AM - Ummi Tandama😇: 🌈🌈🌈🌈🌈🌈🌈🌈🌈

*AURAN FANSA*
NA'IMA SULAIMAN SARAUTA
Nimcyluv

🌈🌈🌈🌈🌈🌈🌈🌈🌈


19-20


Wani kuka ne ya kwacewa Mannal Lokacin data gama tuna irin É—ibar albarkar da Abban
Arman yay mata, wani baƙin ciki da take kaici da keji.
Ace mutumin da tafi ƙauna fiye da kowa idan ka ɗauke ta mahaifinta shike nuna mata
rashin daraja, mijinta Uban yaronta Arman gashi dalilin wulaƙanci da yay mata har hakan na
sawa É—an cikinta yace yana sonta?.
Yau Ya Heemu ke mata abinda yaga dama abinta a mafarki bata kawo wannan bare a zahiri?
ÆŠan yaro kamar Ya Heemu har yashe ya gama girman ta gama yi masa wanka ta goyashi a
gadon bayanta, ta bashi abinci yay mata tunbuÉ—i yay mata tsari amma yau shike mgnar yana
son auranta? Ina sam ba zata iya wannan abun kunyar ba ta auri Ya Heemu tace ta auri me?
Yay mata me? Bayan shi kanshi ta raina sa banda shirme shida Arman mene suka iya? Yadda
take kukan sosai iya ƙarfin ta sai riƙe Ya Heemu take sbd yadda take jin zcyarta na zafi
tana harbawa kamar zata fito waje.
Idanunsa ya buÉ—e kaÉ—an yana kallon yadda take kukan kana ganin kukan kasan bawai iya
na yanzu bane, ta daÉ—e tana tarawa kuma tana neman inda zata sanya kanta tayi kukan
wanda zai gamsar da zcyrta, hakan yasa faffaɗan ƙirjinsa ya zame mata mafaka.
Ƙara matsota yay sbd zafin da ƙirjinsa ke masa.
Bai san yaya ake ba bai san kuma ta inda zai fara ba, sam sam bai san yadda zai rarrashi mace
ba, baya ƙaunar yaga kukan mace, amma a yanzu kukan Mumy yaushi ma yake basa, ya
É—auka Moha ce kawai mai baki kuka sai gashi yaga kakar Moha na kuka da Dukkan

ƙarfinta kasa mgn yay sai hannunsa kawai daya sanya a bayanta ya shiga bubbuga bayanta
alamar rarrashi can maƙoshinsa yace "It's okay Mumy na!" ya faɗa yana janyeta daga
jikinsa, hawayen fuskarta ta share tass tai kamar batai kuka ba sai �oyayyiyar ajjiyar kawai
da take saukewa a fakaice. Cikin ƙarfin hali da juriya irin na jarumar mace wacce bata son ko kaɗan aga rauninta ta
tsare Ya Heemu da gajiyayyun idanunta wanda sukai É—an ja kafin ta É—an cije baki tace.
"look at you! Gaba É—aya baka gama kaiwa minzinlin wanda za suce suna son aure ba, bare
har kayi tunanin yi, amma kai ne za kazo kace kana son...," Baƙin cikin ƙarasa maganar
take sai kawai ta É—auke kanta tana

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
google.com, pub-9213700357025247, DIRECT, f08c47fec0942fa0