Showing 33001 words to 36000 words out of 74145 words

Chapter 12 - Abin Cikin Ruhi Book Compelet Mss Bb

Mrs Bb   

05 Jul 2026

825

kaga mu isa in fesa mata albishi.
Har bakin get din hostel ya kaimu muka tsaya fiddo kaya,don suna da yawa saboda kayan yah
meenah.
Kin tafiya yayi yana ta danna waya,zuwacan yace "kikirata ta taya ku daukar kayan mana."
Wayyo dadi haka naji aikuwa nai maza na shiga contact dinta na danna mata kira.
"Besty nah gamu bakin get pls kizo ki taya mu kwasar kaya tare muke da yah meenah."
"Besty ina hangenku ganin bayanku yanzu nadawo daga cefane bari in karaso."
Dadi kamar yayi yaya dani don inson wannan kaunar ta jone,
Kamar wasa sai gata sai fara,a take tunma kafin ta san waye amotar,
"Yah meenah oyoyo,wallahi naji dadin zuwanku zaman nika dai ya isan,kewa tayi mun yawa."
Rungume juna mukai ina mata oyoyo.
A kunne nayi mata rad'a nace"kalli gefenki pls."
Juyawa tayi ta ganshi zaune cikin mota,kirjinta yabada rassss duk ta diririce daker tace tana yar
fara,"yah shahid ur welcome."
Dagowa yai ya kawata fuskarsa da murmushinsa mai kyau yace"Asma,u ykk ya makarantar."

Tana wasa da hannunta tace"dasauki makaranta yah angode Allah."
Jinjina kai yayi yace"Allah ya bada sa,a ga friend dinki nan na maido maki na fita ko."
Dariya tayi kadan ta kalleni na kashe mata ido guda tace"ka kuwa kyauta wallahi thank you."

Murmushin yayi mata yana tada motar,
"Ga wannan akara kudin siyen garin rogo."
Dariya tayi ta ansa tana godiya tace"ai mu bama cin irin wadannan yah mu fa inkaga dish din
damuke ci zakaso kazauna dakinmu."
Yana dariya yace "ok zan gani wataran zan maku shigar bazata."
Matsowa mukai muka mashi sallama yayi mana jan hankali kan karatu sannan yafita.

Ihun murna nake harda taka rawa,bada dariya babu abunda suke man har mukaje
daki............nan fa na sata gaba da tsokana badai tace komiba wai kunyar yah meenah take,
"Nace bur wallahi lallai kin ma daina wallahi,wai besty ya kuka kare rannan."

Mikewa tayi zatabar dakin nai saurin rikota,
Yah meenah tana dariya tace"husna ya haka mun zama daya fa ki bar jin kunyata ni banajin
taku,inkuwa haka ne daki zan canza."
Dole ta dawo na matsa mata saita gaya man yadda sukai.
"Wallahi besty kinfi ciwon ciki katsawa,bafa wani abu ya faruba kawai ya na ta jana da firar
school ne tare da cewa kardai na biye samarin makaranta su hanani karatu,shikenan fah."
Murmushi nayi nace"soon zakiji ya kiraki yana cewa Asma,u in bakeba sai rijiya mai kwalabe."

Gaba daya muka saka dariya,tun tana nokewa taki sakin jiki da yah meenah har ta sake,ranar
munsha fira don babu mai lectures cikinmu sai tomorrow morning.

💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕

A hankali rayuwar take gurgurawa har gashi fara shirin exams,saboda nayiwa dr magana
yayiwa Abbu magana yabarni na gama aji uku na,ya kuma yi mashi yayarda ga shirye shiryen
biki ga na exams,dole dr ya hakura da takura man kan kira da kuma zuwa,don ma ba sosai
muke haduwa ba ko acikin schol din. Saidai koran weekend yazo ya dauke mu muje yawo da shopping.

Duk abunda nakeyi ba wai na mance da *ABIN CIKIN RUHINA* ba ne Aa babu second ko awa
da zuciyata bata bugawa dashi,daidai darana guda bai tab'a barin zuciyata da *ruhina* huta wa
ba,banda wani abun tunawa dashi,illa kalaman sa na karshe nidashi airport.

_ina maki fatan Alkairi matar muhammad kaseem,sai wata rana bazaki sake ganina ba,kiyi hkr
dani mun haramta ga juna har abadan,domin bazan iya karya wa maah Alkawarin taba,zanje
nayi jinyar zuciyata kikula da kanki And plsss forget About Areef farouk,good by ummulkhair._

Wadannan kalaman sun zamar mani kamar fatiha cikin sallar farillah,duk daren duniya sune

suke amsa kuwwa cikin kunnena,juriyace da karfin hali kawai suke rike dani,don nayiwa Abbu
Alkawarin hakuri da kaddarata,yace man na tai makeshi karya rasani,in nabiye shiga damuwa
komi zai iya faruwa dani,don ciwon zuciyata zai iya tashi kuma likita ya sanar da su cewa inhar
nasa ke irin wannan kwanciyar,komi zai iya faruwa dani don haka inyi hakuri kowa da kalar
jarabawarsa ke kuma taki haka tazo,don haka ki yi wa Allah godiya tare da kokarin ganin kin
cinye jarabawar.
Kalaman Abby kenan ranar dazan dawo makarnta,naji nasihar sa sosai don inason Abbu na ba
zanso ya shiga wani hali ba saboda ni.

Zuciyata ta azalzaleni akansa har nakusan shiga wani yanayi,kalamnasa da ya gaya man ranar
kafin mufita mota sune suke tunzura bacin raina,har ma inji to miye na kwallafa raina dashi
tunda koda babu dr nasan yadda ya fadi kalaman hakan nanufin nai mashi kadan.

_k'wailaye daku berori da bakusan kanku ba._

Wadannan kalaman sunfi komi kona man rai,har nakan kalli kirjina dake cike masha
Allah,wanda nasan idan za,a tara mata goma cinkinsu da wuya asamu biyu masu irin breast
dina,shine yake ceman k'waila,to nayarda dai salma k'walarce Amman ni wallahi ba ita bace.
Haka dai nake ta abuna abu wanda yasan halin nake ciki,illah yah meenah da besty husna.

Suma ba suda abun yi man face lallashi da ban baki,insuka na yini daki ko lecteres ban jeba
nakicin abinci sosai sun san abunne ya tukoni,zasuyita lallashina suna gaya man kalamai masu
kwatar da hankali,sai inji nasamu natsuwa.

Rannan dai nazauna nayi wa kaina karatun ta natsu,nace shifa wanda nake wannan haukan
donshi yana can yana rayuwarsa cikin kwanciyar hankali,wata kila man ya shafe babina ya
bude wani sabon shafin,kilama yayi budurwa ko ince yayi yanmata don nasa shi gwanin farin
jinine akansu. Tunda natuna haka nacire ma raina yah Areef,ganin gamai sona kamar yayi mani sujada
saboda tsananin kaunar da yake mani,to akan me zan dorama kaina damuwar wanican da ko
kirana mu gaisa baiyi,saidai najishi suna waya da yah meenah amman ko agaidani baicewa,to
kan wane dalili wata jotter ta sabuwa da ban fara komi cikin taba nayi rubuta kamar haka.
*_NI UMMULKHAIR FAROUK,NAYI ALKAWARIN SHAFE BABIN SA CIKIN RAYUWATA,NAYI
ALKAWARIN MAN TASHI CIKIN RAYUWATA,NAYI ALKAWARIN DAINA YIN CIWO SABODA
SHI,BAZAN SAKE SAKA YAN UWANA DA IYAYENA CIKIN HALIN DAMUWA BA SABODA
SHI,ZAN FARA SABUWAR RAYUWA DA MASOYINA KUMA MIJINA INSHA ALLAH._*
na jefata cikin tarkacena ban sake bai takan taba,don promise ne bazan karya ba zanba marad
kunya inaha Allah.
Cikin yardar Allah muka gama exams,kuma muduka muna fatan samun sakamako mai
ktau,daga wannan hutunne zamutai pratical sai munyi six months sannan mudawo makaranta.
Shirye shiryen bikinmu ake babu kama hannun yaro,duk kullum husna nagidan mu sai dare yah

shahid yamaida ta,kasancewar yanzu babu laifi sun saki jiki dajuna amman ban tunanin yafurat
mata yana sonta,suduka dai idan kagan su tare kasan akwai soyayya mai karfi,amman kowa
jinkai dajan class ya hanashi,amman inanan ina hada masu tarko sai yah shahid yafurta da
tsiya ma bada arzikiba.
Mrs bb ce😉👌🏻
[6/12, 6:28 PM] Mom Muhseen: 💕💕💕💕💕💕💕
🌹
*ABIN CIKIN RUHINA*

Writing by mrs bb
Mom muhseen.

Wattpad name
Humaira753.

DEDUCATED BY ZAUREN MRS BB.

NOT EDITED.

30

Komi aka sama rana sai yazo,cikin ikon lillahi gashi dai bikinmu yarage saura kwana uku,yau
mutanen dubai suka sauka,da iyalanta yah imaran da kanensa saifudden,sai yar auta mimi taci
sunan mahaifiyarsu maah watau zahra,u shine ake kiranta da mimi.
Ummi kamar ta goyani don tsananin murnan ganina,nima haka nakeji don yinin ranar muna tare
da ita,sai jana take wai ina surukinta yazo ya kawo gaisuwa.
Nace metake ci nabaka na zuba zaizo,har sata gaji dashi.

Wasu irin kayan kitcheen tazo man dasu new moden,kai daka gansu kasan an narkar da kudi
waken,kuma abun jin dadin bani kadai ba harda sweetheart dina salma.
Naji dadin kayan sosai naita mata godiya, dun gureman kai tayi wai ai miye na godiya bacin
hakkinta ne matsayinta na uwa,kuma haka batunta yake saboda ummi na sonmu tana kaunar
maah batajin tsadar abu inhar mune zata yiwa alkairinsa.

Mimi tsararmuce amman mun dan girmeta da shekara guda,amman inka ganta zakace itace ta
girmimu.
Don girman jikine da ita sosai,banyi mamakin rashin ganin *ABIN CIKIN RUHINA* ba don
daman naji ajikina bazai halarci daurin aurena ba,ganin kamar zanji babu dadi yasa nai saurin
kawar da tunanin hakan cikin raina,

Dadaddare Dr yazo gaida ummi sai nokewa yake tana masa dariy,don ummi babu ruwanta da
jin kunya,maah cema kejin nauyinsa sosai Annie ma batajin kunyarsa sosai.

Gida ya dauki harami don yan gidansu Annie sunzo hada hajiyarsu,da kanwarta da yayarta sai
hidima ke dasu,dangin maman salma kuwa basu zo nan gidaba sunacan wajen Inna,hakan yafi
don sai anyi rigima yadda nasansu basuda hakuri kona kwabo.

Gyaran jiki muke zuwa tunda yarage saura sati biyu,shiyasa gamunan ko ince ganinan nayi
wata irin canzawa,don salma bansan wace take cikiba,taki shigowa cikinmu ko kadan,itada
kawayenta su raihana kurun suke hidimarsu,har kararta nakai wajen Abbu yace in kyaleta tunda
ta janye daga gareni nima injanye mata,idan nacigaba da cusa kaina wajenta zata yi kokarin
ganin ranki ya baci,nikuma bazanso abunda zai taba rankiba har agama bikinku ta Alkairi.

Rungume Abbu nai ina fashewa da kuka,don tun yanzu nafara jin kewarsa inajin sa har cikin
kokon raina,yadda yake tattalina yake gudun duk abunda zai shigar dani cikin
damuwa,lallashina yake sosai daker nayi shiru.
Kallona yake yana murmushi yace"Kinyi kyau ta Alkairin Abbu,Allah ya kawo ranar da ta
alkairina tazama babba zata tai gidan miji itama."
Sadda kaina nayi inajin kunyarsa.
Dagoni yayi yana dariya yace"kiyi man alkawarin kulawa da mijinki da danginsa da yan uwansa
abu mai muhimmanci ma ace mahaifansa,don hakan zai kara maki daraja da kima ga idon su
da idon duniya,hakan yasaka mahaifiyarki kullum Allah yake daukaka darajarta akan sauran
mutane,saboda tsaye take kan dangina da mahaifiyata,sujjada ce kurin bata yi masu,don haka
kizama jaruma mai jajircewa acikin gidanta,hakuri shine babban jigo ga rayuwar Aure idan kika
rikeshi kingama dacewa,sannan kizama mai rike sirrin gidanki,sirrin mijinki bakomi akeji da
bakin matar gidaba,nasihata kenan wajenki ta Alkairi,ubangiji yasaka Albarka acikin rayuwar
aurenku,Allah ya kareku daga sharin masu sheri,kiyi riko da Addininki kirike ibada,duk Abunda
ya dameki ki gayawa Allah shi zai jibanci ramurranki."

Kuka nake don hakika nasihar shi tashigeni,naji duk wata natsuwa tashigan,naji hankalina ya
natsu da auren saboda kalaman abbu,yayi man addua ya sakaman Albarka wannan ma kadai
ya isheni,don kowace amarya konace budurwa zataso ta rabu da yayenta lafiya yayinda zata
gidan miji,su rabu suna samata Albarka.
Haka na fito ina share hawayena.

Yah imran tunda ya kyella ido yaga yah meenah shikenan ya zama kamar bindinta,saita boye
idan zamu fita yo wani abun,don duk ya hanata samun sukuni,ga yah imran badai iya love ba
duk yarudar man da yah meenata.

Yaune akagama man gyaran jiki,gobene daurin aure,don nidai nace banason kowane irin
event,sai angama daura Aure sai ayi dinner gidan iyayen dr.

Mun shigo gidan kenan mukai karo da yah shahid,duk ya fita natsuwarsa murmushi nai don duk
yau banbari sun hadu da mutuniyarba,kallonmu yai yasha mur.

"Ina Asma,u."
Da yake sunsan kanun zancen sainai saurin cewa,
"Au nafa manta,yah shahid wannan wanda nace maka yana sonta din nan, yah kamal cousin
dinta.
ya samemu wajen gyara,ana gama mata ya dauketa inajin sai anjima kadan zaka ga tashigo."

Gani kawai nai yadafe kai cikin masifa yake ceman,
"Donme zaki bari wani yatai da ita wani waje,bayan kinsan amana mominsu tabaki,ehye maza
kirata yanzun nan ta dawo."

Mimi da yah meenah sabewa sukai suna dariya kasa kasa,don sun san idan ya kama su suna
mashi dariya ran sune zai baci.

Sake shan mur nai nadanne dariyata nasake tun zurashi da cewa,
"Yah nace maka cousin dinsu ne,ansanshi gidansu,ko ita momin nasan bazatai fad'a ba don
antsayar da ranar aurensu bayan sallah babba."
Wayyo kuzo kuga tashin hankali karara kan fuskar yah shahid,
Cikin tsawa yace.

"Sa ranar banza da wofi, aure akai masu dazai bita wani waje ya dauke ta ehy,laifin kine da
kikajata.
maza maza nace kikirata yanzun nan tabaro duk inda take ta dawo,inba haka ba daga ke har
itan sai rayukanku sun b'aci."
Ya bar wajen kamar zararre.

Saboda dariya har duke wa nake lallai yah ya kamu over,haka nakeso daman,dole ya sauke
girman kanshi yafurta tunda shine namiji,wayata na fiddo ina cigaba da dariyata nakirata,
"Plan dinmu yayi Husna maza kishigo kafin yah shahid yasama gidan nan bom yatashi.....ina
dariya."
Itama dariyar takeyi tace,
"Ganinan tahowa ina cikin taxi,dama nasan za,ai haka saina iso kiban insha."

Kashe wayar nai ina dariya sakon dr ya shigo man.

_AMARYAR GOBE YAUDAI D'AYA ABARNI NAZO NAGA KWALLIYARNAN DA AKETAYI
KUSAN WATA GUDA._

Murmushi nai inatura mashi sakonsa cewa saikazo.

Dakin yah meenah nanne madaddalarmu,can nanufa,.
Ina shiga kofar falon Annie naji munyi mugun karo da wani abu,har wayana tana
faduwa.......duka wanai na daukota ina murza kaina,saidai sadda zan d'ago banga
kowaba........kirjina naji yace dammm saboda wani k'amshi da ko mutuwa nai nadawo bazan iya

mance shiba,..........bin hanyar nayi da kallo jikina yana wata irin rawa.............

Taufah.🤔

Wani irin sanyi jikina yayi kamar ansakani cikin frig,ina waigen hanyar na karasa cikin
daki,hayaniyar suce kurin ketashi,daki suna kyalkyala dariya suna maida yadda kai.
Kamar wadda akazarewa kuzari da lakkar jiki haka naji,ina sando na shiga dakin ina bin bango.
Silalewa nai kasa bakin kofar shiga bayi,wani irin kerma jikina yake...........wayata na ajiye kan
madubi babu wanda ma ya lura dani saboda daroyarsu suke suna ta hirarsu.
Rungume kafafuna nayi ina dora kaina saman guiyawuna,ina sauraren bugun zuciyata.
Bazan iya cewa ga halin da zuciyata take cikiba,runtse idona nayi ina dauke numfashina na
wucinngadi kozan daina jin wannan mayataccen kamshin,amman ina kamar ma hade yake da
numfashina,duk sanda zan shakesa tare nake jinsu.
Husna ce tashigo tana sauke numfashi,duk suka juyo suna kallonta,mimi ce tai saurin jawota
"Ya kuka kare husna na matsu inji wannan dramer."
Harararta tayi tana dariya yah meenah tace"Ai da kin jima baki dawo ba kilan yah shahid bulala
zaisa ya zanemu tas har amaryar."
Cu dariyar suke husna tace,
"Ina Amaryar take.......shiru tayi ganina zaune bakin toilet na kudundune kafafu,duk wajen suka
kalla.
Husna ta ajiye jikarta ta iso wajena.

"Khairat,meye haka lafiya kike,yanzu fa muka rabu dake awaya lafiya lau,meya faru daga baya."

Duk sun shiga damuwa kowa so yake yaji abunda ya saman,taya zan iya yi masu bayani
mezance masu,karo nai da wani mai kama dashi,koko kamshin sa naji,wane daga ciki zan fada.
Nashiga ukuna miye haka zuciyata ya ina cikin farin ciki zaki yiman haka,gobene fa daurin
aurena inkikamun haka kin zalinceni kin cutar dani da masoyana,plsss na rokeki kifitar mun da
wannan masifar,bazan iya cigaba da jurewa ba,inason cigaba da ganin farinciki afusar
iyayena............ji sukai kurun na fashe da kuka maitsuma rai,suduka duk jikinsu duk yayi
sanyi.......don dajin kukan kasan maiyinsa nacikin kunci da damuwa.

Mrs bb ce👌🏻

Love u All 💋💕😉
[6/13, 8:47 PM] Mom Muhseen: 💕💕💕💕💕💕💕
🌹
*ABIN CIKIN RUHINA*

Writing by mrs bb
Mom muhseen.

Wattpad name

Humaira7531.

DEDUCATED TO ZAUREN MRS BB.

Not edited

31&32

Saida nayi iyakar yina sannan nayi shiru,shigewa toilet nayi nashige cikin ruwan sanyi,ko
sirkashi banba,shaya ce keta zuba bisa kaina nafi minty goma haka.........injin karar wayana yah
meenah na cewa,
"Wannan wankan ya isa haka ga dr nan nata kiranki yanzu haka zowa yayi."
Wani kulutu ne ya tokare man ga makoshi,jinai banson ganinsa bana son jin
sunansa..........zafin da zuciyata keman harga jikina don wata irin masassara nakejin tana
saukoman.
Dole na jawo towel na daura nafito,kowace ta kama waya sai yitake......tsaki naja nafara
shiryawa.
Doguwar rigace nariza nadan shafa lotion,da body spray na zuba abayata har kasa,don inason
dogon hijab rayuwata,kocikin lefena da aka kawo akwatinsu daban wajen kala goma
shabiyar.......wayar na dauka nafito compound din gidan,motarsa nacan gefe guda kasancewar
filin wajen badai girma da fadi ba,mota goma saita shige har asamu sauran waje.
Fitilar ya kunna don nagane shine,tafiya nake kaina kasa inajin babu dadi,bazanso yaga
damuwa tare da niba don ban san mezan ce mashi ba,dole na kakaro murmushi nasa ma
fuskata........
Budeman gidan gaba yayi yana murmushin sa mai kyau,yasha shadda gizner sai daukar ido
take.
Shiga nai ina sallama.

"Wa alaiki salam,gimbiya Amarya da girman kujerarki,Amarya bakya laifi koda kin kashe dan
masu gida."

Bansan sadda dariya ta kucce man ba yana tayani,
Nace"irin wannan kirari haka,karkasa kaina ya fashe sir."

B'ata fuska yayi kamar karamin yaro zai kuka,
"Ba nace banson wannan sir dinba,nace maki da munbar school to sir ta kare,saidai my only."
Murmushi nai ina jin nauyin sunan sosai,shiru nai ina wasa da tsuna da suka gaji da kyau,don
mai kunshi musanmman yayar Annie tazo mana da ita,ta zane mana kafafu da hannuwa,sai
daukar ido suke.
Hannun ya kalla yace"bakiji wani miyau daya wuce man ba,inso samune wannan yan yatsun in
tsotsesu."
Bansan sadda nasa abayata na boye fuskata ba.

dariya yake sosai yana sake karkacewa yana kallona yace,
"Aini ban maga kwalliyarba my love,kidan cireman abayar ingani mana,wallahi tunda kikashigo
kamshinki yaketa dukan hancina,ni ko wuyanki kibani in shinshina........."

Wayyo kunya kamar zan nitse don kunyar kalamansa,
Shagwabe fuskanai nace"pls si........"

Wallahi dakin ida saina cinye wannan bakin tunda baijin magana.
Shiru nai inajin kunyar fadar sunan da ya keson in fada,jinai yace inajinki.

"Cewa nai pls kabari inkana irin wannan guduwa zanyi Allah ni kunya kake bani."

Juyowa yai gaba daya gabana,ya riko duk hannayen nawa yace"sa idonki cikin nawa,yau
kwana nawa rabon dana saki idona,kullum kina man wayau gyaran jiki kike,to tunda angama
yau kibarni na mora ganina pls."
Ya karashe maganar yana sunbatar hannayen,har wani lumshe ido yake.
Wani iri naji don dr akwai iya salon kauna.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
google.com, pub-9213700357025247, DIRECT, f08c47fec0942fa0