Showing 18001 words to 21000 words out of 74145 words
hannu sukai har yafita...........
Komawa sukai suka cigaba d aikinsu,Jahid yace.
"Don Allah bakaji kunya ba."
Kallon haushi yayi mashi yace,
"Kunya! For what."
Jinjina kai yayi yaci gaba da abunda yake,saida yadauki lokaci sannan yace,
"Ka wulakanta bukatarsa jiya sannan yanxu ko kunyar had'a ido dashi bakayi,meyasa akullum
baka damuwa da damuwar wani sai taka,wallahi Areef ur Always selfishness gay ka gyara
wannan ba rayuwa bane."
Ran Areef yayi masifar b'aci ko kallon da yake ma jahid kad'ai zai tabbatar maka da hakan,cikin
muryarsa data zama so deef yace,
"Duk Akan wannan yarinyar kake gaya mun magana yadda ranka yaso ko jahid,to bari kaji
wani abu wallahi kalma guda da kake fadan marar dadi akan wannan vellege girl din karajin
tsanarta nake cikin zuciyata,don haka ba zance ka daina ba plss continue."
Shi ma cikin tsananin bacin ran yace,
"Uhmmmmm Areef kenan i know u hate her very much,kawai don baka da rabone Allah yajuyar
da lamarin,domin kuwa khairat ta fi karfinka don class dinta bana irinku bane,Amma kasani
wallahi ba ayin shishshigi cikin lamarin ubangiji,ni bansan gaibuba shiyasa bazan yanke maka
hukunciba,Amman insha Allah very soon sai khairat tazamema *dan hakin daka raina* sai
khairat ta saka idaniyarka kuka,sai khairat ta saka ka jinyar da tunda kazo duniya baka tab'a yin
ir......... *stop jahid.......* stop stop Areff ya fada cikin tsananin tsawa da b'acin rai.........takowa
yyi har gabanshi ya daki kafad'arsa yace,
"Stop said that,because har abadan hakan bazai faruba,khairat k'anwata ce kadauka ciki daya
muka fito,aure ya haramta agaremu,plss don't said that again banson b'acin raina yasa nayi ma
yarinyar abunda har ta mutu zata tsaneni akanshi,don haka daga yau karka sake mun maganar
that girl."
Janyewa jahid yayi yafice Areef ya silale kasa jikin bango dafe da zuciyarsa,ya lumshe idonsa
shikad'ai yasan feeling din da yakeji ahalin yanzu,ya dauki almost thirty minutes awajen kafin
yatashi ya fito.
Meenah ce tafito sauri kawai take don ganin goma saura minty goma, kad'an ya hana basuyi
karo da Areef din ba,tayi saurin jaa baya cikin tsoro tace,
"Am sorry yah ban gankaba ne ina sauri,ina kwana."
Saida ya gama kalleta duk da har lokacin fuskarnan turb'une,sannan yace.
"Lafiya,Ina zaki kike sauri."
Kallon agogon hannunta tayi tace,
"Wlh yau muke fara attending lectures shine nake sauri."
"OK u can go."
Har ta juya tayi taku uku ya juyo cikin dakakkar voice nashi yace,
"Meenah"
Saurin dawowa tayi ta tsaya,
"Ke kadai zaki school dinne ina sweetheart."
Jin abunda yace ne yasa tasan bada khairat yake ba yasa tace,
"Ita sai offer monday suke farawa nida khairat ne muke starting."
Shiru yayi kafin yajuyo yace.
"Ta na Ina."
"Bata idasa shiryawa ba shine zanyi gaba,gudun yin let."
Jinjina kai yyi ya shige gidan ciki tafiyarsa ta takama,tasan tasota gaba zai shiyasa ta d'an jira A
little bit.
Wanka na fito inata sauri tsane jikina nashiga yi kafin nafara mulke jikina da cream,idan kuka
ganta sai ku rantse yanga take,Amman nan iyakar iyawarta take sauri,farar powder na saka da
lipstick sai kwalli daya fito da ainahin kyawun idona,sunyi k'ar k'ar kamar farar takada kaya na
fara kokowar cirowa,don aron kayan yah meenah zanyi,kasacewar size dinmu daya har
shoes,kayan sunyi mun nisa yasa na jawo stool na taka,Ina cikin jawo kayan aka banko k'ofar
dak'arfi wanda tsoro yasani fasa k'ara............stool din ta jurgud'e muka taho tare
k'asa...............na sadak'ar karairayewa zanyi kawai.........amman sainajini nafado jikin
mutun,jinai yace washhh..........wata nannauyar ajiyar zuciya na sauke nafara bud'e idona
surprise fuskarshi nayi tozali da ita..........idona cikin nashi ga towel dina ya gama tattarewa
cinya waje,har d'an pant dina ana gani........babu alamun sakin fuska tare dashi,ganin kallon
yaki karewa yasa ya sakeni k'asa timm.......wata kara na saki ta azaba,don k'uguna har saida ya
ansa........kuka nafara ina murza bayana katseni yayi da tsawa.......
"Tashi anan ko in makeki ubanwa kikeyi har yanzu baki fitaba,ok tun yanzu kin fara wasa da
karatu ko,to wallahi kika sake naga spill over ga result dinki kinshiga uku gidan nan,zaki tashi ki
shirya ko saina tattakaki."
Kukana nake silently ina mik'ewa da k'er kayan nake kokarin komawa in dauko,don bankai ga
jawosuba ya kallan yaja tsaki,hannu ya mik'a kurun ya fiddosu ya watso mani ga fuska.........ya
fita yana cewa kisake na sake dawowa."
Haka nasaka na dauko log hijab dina nasaka da takalmi,matching color nayi na pink anda
red........babu wanda nayiwa bankwana nafita......amman kafin na isa compound din gida na
gyare fuskata,kamar komi bai faruba.
Koda muka shiga mota tace me yayi mani cewa kawai nayi fada yayi mun infito.........munje kan
lokaci kowa ya nufi department dinsu,Alhamdulillah lectures din sunyi mani dadi nesa ba
kusaba,don yawancin abubuwan duk i knowing them,Amman fa da alama zamusha lectures
harsai munce masha Allah,ga azumi tafe kuma cikinshi zamu fara test,natsinci kaina cikin
farincikin dana jima banjiba,nayi friend guda husna ladan........d'an zaman da mukai da ita na
lura tanada natsuwa sosai,zanji dadin friending da ita,koda muka samu hutun thirty minutes
mukaje capteria na nemi yah meenah ban ganta ba,na tambayi ko yan department dinsu sun
fito akace sai four,wanda lokacin mu zamu koma sai six zamu tashi.
Husna ta siya mana lemo nikuma na siya mana pizzer da shawarma.......sannan muka koma
muka cigaba da attending,na lura itama hazik'ace wajen karatun,shiyasa zan zage bazan yarda
tafiniba.don inda kishi kan hakan,bazan yarda kafiniba saidai muzo tangal..
Muna class naga miss call din yah meenah,alamun sun tashi,saidai namata text cewar mu sai
six tatafi da motar zanhau taxi.
Husna hostel take sai naji inama nima Abbu zai barni na zauna hostel din da nafi samun
natsuwar karatun.......amman yau zan mashi magana Allah yasa ya yarda.
Koda muka tashi nayi wata irin gajiya,har wata juwa nake gani yasa nazauna na fiddo phone
dina nayi dialing number yah jahid...........muna zaune da husna ta rakoni bakin get.
"Plsss yah don Allah kazo kad'aukeni wallahi bazan iya kawo kaina gidaba,wallahi nagaji."
Dariya yakeyi yana daidai fitowa daga gida yayi wani matsiyacin wankan yamma,dama fita
zaiyyi takira daidai lokacin.
"OK my dear am coming now."
Godiya nayi ina kallon husna tana murmushi,
"Kincika rangwanta kinga mu mun d'an saba tunda tun satin akafara."
"Uhm tunda nake wallahi ban tab'a shan irin wannan wuyarba,lectures fah akwai dadi amman
akwai gajiya wallahi."
Hira muke ahankali tana k'ara nuna man sauran abunda akai ban nan.....har sanda yah yashigo
da motarshi da tasha wanki sabuwar prado dinsu shida yah Areef,don itace gift dinsu sanda
suka dawo daga UK.......sun gaisa da husna tayi mun bankwana tatafi.
Har mukaje gida ina bashi labarin karatun mu yana kara karfafamu guiwa,anata sallah muka iso
gidan yah Areef yana Alwallah bakin get da gani unguwa yaje yau,kafin motar tayi parking yah
jahid yake cemun.
"Dear matsayin yayanki zan baki shawara kinjiko."
Na maida duk hankalina kanshi,
"Karki kullaci Areef akan abunda ya faru kinjiko,ki d'auka hakan damace Allah ya baki kiyi
karatunki cikin kwanciyar hankali,kicire shi daga cikin ranki kidaina kallonshi irin kallon dakike
masa baya,ki kalleshi irin kallon da kikeman kikewa shahid,zaki samu kwanciyar hankali da
natsuwar zuciya kin fahimceni."
Ina wasa DA azurfar hannuna nace,
"Nagode yah Kuma nayi maka alkawrin hakan,daman wallahi yah Jahid tun ajiyan banyi
bacciba saida nayi ma kaina karatun ta natsu,nasan cewa samu da rashi duk na Allah ne,haka
zalika wani baya auren matar wani,nasan cewa wata kila daman badanni akayishiba rabon yar
uwatane,har abadan zancigaba da yi mashi kallon da yakeman matsayin k'anwarsa ciki
guda,nima matsayin yaya shahid zan cigaba damai namaka alkawarin cire wannan feeling din."
Murmushi yayi mani yace,
"That my dear khairat"
ya bani hannu muka tab'a sannan muka fito angama sallah lokacin,har yah Arref yafito daga
masallacin cikin gidanmu....kallonmu yayi yana ma yah jahid alamar baiyyi sallaba,yace"sorry
oga yanzu zanyi ai,dear jeki gida ayi sallah da wanka ahuta ko."
Nace to tare da bin bayan yah Areef har na cinmmashi naji yace mun"ba gaisuwa ta Alkairi."
Mamakinsa ya kasheni amman sai ban nuna bah nayi murmushi nace masa"sorry yah ina
wuni."
Gaba yayi yana cewa"lafiy ya school din".
Answa nayi nima na shige d'akinmi don duk yau banga salma ba,da maah.
Mrs bb ce
09034722970
[5/28, 2:22 PM] Mom Muhseen: í ½í²•í ½í²•í ½í²•í ½í²•í ½í²•í ½í²•í ½í²•í ½í²•
*_ABIN CIKIN RUHINA_*
Written by [Mrs bb]
Mom muhsen ce
*____________________________________*
*í ¼í¼ˆí ¼í·°AINUWA í ¼í·¼RITER'Sâœ�í ¼í¿¼*
*í ¼í·¦SSOCIATIONí ¾í´�í ¼í¿»*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*____________________________________*
17.
Salma ce da k'awarta raihana suketa kwasar dariya cikin d'akin,har basujin sallamar da
nake.......abayar na cire ina cewa,
"Sai Ihu kuke har ba ma kujin sallama ko."
Wani kallo naga raiha nayi mun kafin ta sake kwashewa da dariya,salma na taya ta binsu nayi
da kallo tsayin lokaci kafin na shige toilet,don na lura wanan dariyar dani suke kuma babu
tantama salma labarin abunda yake faruwa ta bata,nasan kuma wannan labarin kaf k'awayenta
ta basu shi........wani takaici ya kamani har naji k'wallah ta taru idona........sharewa nayi nayi
wanka na tare da alwallah nafito har lokacin hirar su suke ta samari,wani zubin sai su yab'oma
gana wanda daji dani suke,ban sake kula suba na hau yin sallata nagama nafara shafa mai inaji
raihana nacewa,
"Saiki kula kinsan ana iyayin komi don aga anrabaki dashi,don kinsan y'anmatan yanzu sun
b'aci da bin maza kina zaune da saurayinki lafiya saidai kiji wuf anfige,kinsan ma wani abun
haushin wallahi nakusa dakai shine zaki samai da wannan hali,kidai kula wallahi."
Kad'an ya hana ban tankaba,saboda maganar takai mani mak'ura don har zuciyata wani irin
ciwo take,haka suka cigaba da hirarsu turarena nashafa duk jikina,sanan na saka kayan
doguwar rigace marar nauyi ina gama wa ana kiran isha,i sai kawai na tada sallah sai lokacin
tayi niyyar tafiya.......fita sukai naci gaba da salla ta ban fito ba sai wajen takwas,d'akin maah na
shiga na sameta suna waya da ummin Dubai........zama nayi gefe injiran su gama har nafara
bacci sannan naji tana gyaraman kwanciya,tashi nayi ina mik'a tare da hamma,hannu tasa
tarufe mani baki"akwai gajiya ko,gashi da ganin wannan cikin baici abinci ba"
"Nayi missing d'inki duk yau maah,wlh school akwai wuya amman fa lectures akwai dad'i
maah."
Murmushi tayi tana shafa kaina tace"oh my angel kibar dai cika baki kwanan nan za kifara mana
kukan kingaji."
Shagwab'e fuska nayi ina sake narke mata nace"maah kinga dai salma ko."
Maido hankalinta tayi kaina tana sha fa kaina tace"mekuma tayi maki dear."
Na gaya Mata abun da ya faru d'azu..........shiru tayi na d'an lokaci kafin tace"my angel karki
biyeta,bake ba harni nan salma ta canza mani daga halin dana d'orata akai,tabbas akwai
abunda yake faruwa,fatana kici gaba dayin hakurin dana sanki dashi,karki ga don na hana
Aurenki da yayanku kiga kamar ban sonki,aa my angel ilove u more than expected,haka kuma
ina duba abunda yadace daku ne,inason har bayan raina Areef ya kasance yayanku mai share
maku kukan ku,koda aure kukai kunada babban yaya da zai kula da lamarinku.........kid'auka
dama babu aure tsakaninku kinji ko angel d'ina.......karki saka damuwar komi cikin ranki Allah
zai kawo maki miji nagari na nuna ma sa,a sannan kiyi kokari ki nuna ma Abbunku cewar komi
ya wuce wajenki hakan zai saka ya daina fushi dani,ko kinason yayita fushi dani."
"Bana so maah insha Allah zan bashi hkr yadaina fushi dake,aman maah kija ma salma kunne
wallahi kar wataran takaini k'arshe,ni wallahi maah tun daga randa akai abun nan nituni na yafe
shi cikin zuciyata,to akan me zata ringa yayatani cikin friends d'inta.........wannan cin
mutuncine.......sallamarsa tasaka nayi shiru ina kwance har lokacin kan cinyar maah tana shafa
kaina...........idasa shigowa yayi yazauna gefen da nake........yadda ya canza fuskarshi daga
shigowar sa yasa ni tashi daga kan cinyar maah,kallon k'asan ido yake mun bansan fassarar da
zanba kallonba.........gyara kallabina nayi har lokacin idonsa na kaina nace batare dana sake
kallon inda yake ba.
"Maah bari naje Wajen abbu inci abinci dama wajenshi zanje na biyo in gaidaki."
Kallon Areef tayi ta b'allamai harara tace"haba my angel daga shigowar yayanki zaki ruga."
Ina nu far k'ofa nace"Aa maah dama yanzu zan tashi idan ya tafi anjima mun ida maganar,saida
safe."
Nafice inajin dukan da gabana keyi yana sassauta,don yanzu wani irin tsoransa nakeji har cikin
k'ok'on raina.....wajen Abbu naje nayi sa,ar kuwa lokacin yake cin Abinci.......zama nayi nasaka
hannuna kamar yadda yasa nashi,kasancewar Abbu baya cin tuwo da spoon muna hira muna ci
har muka gama,nan yake gaya man yah shahid ranar monday zaidawo Anty shida kuma sai
Tuesday zata zo weekend........naji dad'i sosai don nayi kewarsu sosai.....nasiha yashiga yimun
cikin hikima da jan hankali har yazo kan batun shekaranjiya......cikin tattausan lafazi yace"ta
alkairi kinsan cewar duk abuna kaga baka samu ba da hakan ba alkairi bane,don haka kid'auka
cewa yayanku dama ba mijinki bane,kiyi hkr insha Allah mijinki zaizo nagari mai nagarta,fatana
kisaka tawakkali da hakuri kinjiko inhar kinada damuwa kisanar dani karkice kibar abun ga
zuciyarki,don zai illataki karkiji komi ta alkairi na komi kikeso sanar da Abbunki inhar ina dashi
zan maki."
Godiya nayi mashi tare da yi mashi alkawarin cire damuwar,sannan nace yajawa salma kunne
akan abunda takeyi,na gaya mashi abunda ya faru don gudun abunda zaije yadawo.......shima
ransa ya b'aci yace inbarshi da ita,har zan mashi maganar zaman hostel su yah jahid suka
shigo shida dodona don yanzu sunan dana rad'a mashi kenan cikin zuciyata......tashi nayi
nayiwa Abbu saida safe,don banson abunda zai ringa had'amu waje guda.
Mrs bb ceí ½í±Œí ¼í¿»[6/1, 10:22 AM] Anty Ushe: í ½í²•í ½í²•í ½í²•í ½í²•í ½í²•í ½í²•í ½í²•í ½í²•
*_ABIN CIKIN RUHINA_*
Written by [Mrs bb]
Mom muhsen ce
*____________________________________*
*í ¼í¼ˆí ¼í·°AINUWA í ¼í·¼RITER'Sâœ�í ¼í¿¼*
*í ¼í·¦SSOCIATIONí ¾í´�í ¼í¿»*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*____________________________________*
18.
Har nakai k'ofa Abba yace"ta Alkairi zonan."
Kamar in zura aguje haka naji.......Amman babu damar hakan,kamar wadda kwai ya fashewa
aciki haka nake tafiyar,inda na tashi na koma ina jin bugun kirjina yana sake yawa,don har ga
Allah atsorace nake gani nake kamar zai kawo man duka.........
"Kamar kina son fad'an wani abu ko."
Yak'e nayi nace"aa Abbu babu komi."
"Banson gardama kinsani don haka menene."
Lagab'ar dakai nai kamar zanyi kuka nace"Abbu sonake na koma hostel da zama,idan ina can
sai nafiyin karatun sosai,nan gida wani zubin inason yi wani abun zai d'auke man hankali."
Kafinma Abbun yabani ansa yayi zak'al yace"Abbu babu wani hostel da zata zauna,duk salon ta
biyewa abokan banza aringa yawo ga gari,idan ma na sake jin kin anbaci zaman hostel saina
tattakaki,tashi kibamu waje."
Kuka nafita inayi saboda haushin abunda yace.........yauma wajen yah meenah nakwana,mun
raba dare kowa na bin abunda akamana jiya,nice searching ga computer banyi baci ba sai daya
da rabi nayi bacci..yah meenah ta rigank kwanciya............
********
Rayuwar ta mik'a taci gaba da kasancewa yayinda karatunmu yake tafiya successfully,duk da
irin yadda lectures suke zafi hakan bai hana ni jin dadin suba,agajiye lik'is muke dawowa don
yah meenah tana rigana,su sunyi gudun duniya sukai 4:35 pm mukau 6:oo pm wani zubinma
idan abunyayi zafi har lectures din 8:oo to 9:30 muke........kuma haka zan dawo gida sex in yi
wanka da sallar magaruba inci abinci sannan in koma,duk wannan wuyar yah baijin tausayina
na zaun hostel,shiyasa gashinan duk na rame cikin abunda bai gaza 2 to 3 weeks ba.......suma
yanzu ba zaune suke ba kasancewar sun samu aiki yah jahid dama engineering yayi to yanzu
b'angaren yake aiki,cikin wata guda sun sake komawa wasu handsome gays......duk wanda ya
gansu yasan suna kwanta kudi Yah Aareef kuma Act ya yi zane zanen gidaje da
sauransu..........tsakanin sa da salma kuwa bazance komi ba,don wata irin kulawa sukewa
juna,itace abincin safenshi idan zaitai ofis itace lunch nashi itace dinner,gyaran b'angarensu ko
karatunta bata bawa muhimmanci ba kamar yadda take kaffa kaffa da duk abunda ya
shafeshi,zuwa yanzu babu laifi ni da ita muna magana tunda Abbu ya kirata gani gata yayi
mana nasiha da fad'a,har hira munayi babu laifi Amman ba kamar da ba,sosai suke buga
soyayyarsu yah shahid yazo hutu satinsi biyu yakoma don sun kusa kammalawa.......Anty shida
ma tazo kwananta biyar ta koma zuwanta na fahimci wani abu,akwai boyayyar alka itada yah
jahid....nadai yi shiru don nasan basu son asani sai nan gaba,bai wuce kuma kammala
karatunta.
Don inna mahaifiyar Abbu tafara maganar ya kamata a aurar da su yah Areef hakanan,karsu
tsohe agida..........nasan har yanzu ba agaya mata zancen shi da salma ba,sai nan gaba.
Nida yah Areef kamar mage da b'era dana hangoshi zan kama gudu,ko muryarsa najiyo
zanfece wanan abun yana konama shi rai,haka Anni abun yana bata haushi...tayi man fad'an
har ta gaji ta rabu dani,haka maah tayita lallashina tana cewa"haba my angel dina kidaina
gudunshi yayankine badodo bane,kinsan hakan haushi yake bashi,idan ya waiwayoki tau babu
ruwana,kisaki jiki dashi babu abunda zai maki."
Wani zubin ina kuka zance"wallahi maah ko had'a ido mukai hararata yake,tsoran kallonsa nake
bazan iya zama inda yake ba,kiyi hkr maah."
Hardai Abbu Da da dady maah ta gaya mawa aman babu abunda ya canza.
Yau ban samu halin dawowa sex ba,kawai nayi zama na wajen husna har mukai lectures na 8
muka gama lokacin goma saura minty ashirin......duk tsoro ya kamani Abbu nakira nace ya turo
driver ya d'aukeni........"ta Alkairi ai hamza yatafi gida tun d'azu bari naturo maki yayanku."
Ya kashe tunani nafara to wane yayan kenan,Allah yasa yah jahid ne, don nasan shikad yake
zuwa d'aukana.
Hira muke da husna tana cewa ingaida mata yah shashid.
Dariya nayi nace"yarinya takamu da son the handsome din gidanmu,nama manta ai ingaya
maki tun last week yakoma,saidai inbaki no dinsa."
Murmushi tayi tace"uhm kawai dai tun randa naje maki yawo naji ya burgeni,jinina ya had'u
danashi."
"Don't mind friend Zan had'a wannan kaunar insha Alah."
Dariya sukai suna cigaba da hirar.
Abbu suna hira da Dady kairat ta kira yace,
"Bari naje na d'auko khairat,yaran nan nasan basu