Showing 15001 words to 18000 words out of 74145 words

Chapter 6 - Abin Cikin Ruhi Book Compelet Mss Bb

Mrs Bb   

05 Jul 2026

824

saboda yar cikina in fallasa
wanan abun, yaka keson suringa kallona bazan iya barin wannan abun ya fito bah, khairat tayi
hakuri Allah zai yaye mata, ko salma ba zata aurai ba ta gama haukan nata. "

"Na gode maki saudah, akan wannan kikeson y'ata ta mutu ko, saboda kar Yayarki tace zata
anshi yaronta ko, to shikenan ni zan Sanar da wanna sirrin ga kowa, zan kuma yiwa Areef tayin
Auren khairat, saidai idan shine yace baya sonta bazai aureta ba, zan hakura kuma zan yiwa
khairat Addua Allah ya bata Wanda yafishi Alkhairi, inhar khairat bata samai ba babu Wanda zai
auresa daga salma har shahida da meenah, nagode."

Jin alamun zai fito yasa nafice aguje, kewaye na shige nayi kuka kamar idona zaifita, nayi
kukan da ban taba irin saba, Wanda har saida nayita amai akewayen.......
Mom muhsen ce
Mrs bb[5/27, 8:10 AM] Mom Muhseen: 💕💕💕💕💕💕💕💕
*_ABIN CIKIN RUHINA_*

Written by [Mrs bb]

Mom muhsen ce

*____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S�🏼*
*🇦SSOCIATION�🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*____________________________________*


12&13

Ganin halin dana shiga zai iya saka aganoni, shiyasa nayi iyakar kokarina wajen ganin na dawo
cikin natsuwata, ina nan kwance salma tashigo tana wani taunar cingam cikin yatsina fusma,
mamaki nake yadda salma ta canza sosai daga dawowar su yah Aree zuwa yanzu, kokadan
yanzu salma bata damu da damuwata ba, sai gari ya waye har rana ta koma ga ubangiji, salma
ko kallon banza ban isheta ba, idan ma ni nayi mata magana baza ta kallan ba zata ban ansa,
tabbas ina hasashen wani Abu dangane da ita, salma ba haka take ba inson sanin dalilin
canzawarta.

Wayarta ta ajiye ta shiga wanka ta fito tahau shirin bacci, Amman sai ka d'auka miji gareta sai
kwalliya take yi, tana ta feshe jikinta da turaruka, kallon ta nake ina mamakinta.

Har ta gama bata cemun uffan ba, saida zata fita har takai kofa ta juyo cikin rainin hankali tace,

"Oh na manta fah kifito can babban falon Abbu ana nemanki."

Ta juya bin bayanta nayi da kallo kafin na yuk'ura na tashi, sake wanke fuskata nayi nafito,
tabbas nasan wannan maganarce za,ai gaba na yana fad'uwa na isa kowa nanan har dadyn
yah meenah, dasu Anni da yah jahid kowa dai yana nan banda yah shahid da sai karshen wata
zaizo hutun karshen shekara.
Zama nayi can gefe bakin kofa, saboda irin kallon k'ask'ancin da yayi min muna had'a ido, bacin
tsoronsa da yacika zuciyata ai dana rama.

Yah jahid ne ya bude mana taro da addua,kafin kowa ya shafa muka maida hankalinmu kan
Abbu, gyaran murya yayi ya fara da cewa.

"Alhamdulillah godiya ta tabbata ga Allah subhanahu wata,ala da yanuna mana wannan rana,
ya kuma nuna mana girmanku, Wanda da ba haka kuke ba, an wayi gari kowa ya mallaki
hankalin kanshi, zuwa wannan lokacin nasan wasu daga cikinku kanku yatoshe, abisa wasu al,
amurrah watau abunda kefaruwa shine, azahirin gaskiya Yayanku areef ba mune muka haifeshi
ba, bamune mukashayar dashiba, saidai kuma mune iyayen rikonsa, konace ahalin yanzu dai
Areef namune, watau Abunda ya kawo wanan magana shine babu batun b'oye b'oye, Areef
kanwarka khairat tataso tun bata san kanta ba, take kaunarka Wanda data kara girma ta fahimci
cewar babu aure tsakaninku, tayi kuka tashiga damuwa Wanda wannan damuwar itace ta ja har
aka mata ripeting makaranta, karshe ta kasa rikewa ta sanar da Annin Ku, ganin wannan ba
abunda za, a kyale bane yasa ta sanar dani, bata gaya ma mahaifiyarku ba saboda taji irin
furucin da tayi wa yarinya k'arama, cewar inhar ta sake jin wani yanayi na soyayyarka aranta
bata yafe mata ba, alokacin ta nuna cewar akwai alakar aura tayya tsakaninku, Amman ta
haramta mata kai, saboda wani dalili.
Ban tab'a d'aukar hakan zai kawo ma khairat matsala ba, sai gashi lokacin da ta kwanta asibiti
likita ya sanar dani tana da damuwa, idan da hali a San yadda akai akayi mata maganinta,
saboda zuciyarta ba zata iya d'auka ba, ban d'auki wani mataki ba, saboda ina ganin abari
zuwa sadda zaka kammala karatuka sannan itama tafara hada hadar shiga jamia,sai na
sameka da maganar in ka amunce na aura maka ita."

Shiru falon yayi sai shashshekar kukana dake tashi cikin falon, duk na jike hijabita da majina da
hawaye.

Cigaba yayi da cewa,

"Sanda kuka dawo nayi farinciki saboda ganin kamar abunda nake tunani zai tabbata,saidai
kuma naga kamar ba haka ba, saboda kulawarka kaf akan salma kake yinta, sai kwatsa da
kyara da kakewa khairat, har dalilin haka yaja zuciyarta hau hauwa, Wanda likita ya tabbatar
mun da cewar wanan matakin shine na karshe data sake ta wuce shi babu makawa zata kamu
da ciwon zuciya, shiyasa hankalina ya tashi na kasa natsuwa, gani nake duk sakacina ne,
Amman sai naga wannan damar ce kawai zata warware komi."

"Na samu saudah da maganar hadaku aure Amman Kalmar farko data furta mun itace cewa ta
haramta maku juna kaida ita,saboda alkawarin da tayiwa ummin Dubai cewa cikin yaranta babu
mai auren wani, ma,ana khairat ko shahida bazasu aureka ba, kai matsayin wansu kake uwa
daya uba daya, alakar aure bazata tab'a shiga tsakanin kuba, don haka khairat saidai tayi
hakuri Allah ya bata wani Amman ba kaiba."

"Nikuma nace muddin ka amunce da tayin da nayi maka akan khairat, to kuwa wanan auren
babu fashi saidai idan mahaifiyarka ta Dubai ce tace aa ko mahaifinka, kokuma kai da bakinka

kace bazaka aureta bah."

Shiru ya k'ara yawaita cikin falon zuwa yanzu kukana ya karu, don sonjin ansar da zai bayar,
har ga Allah duk irin abunda yah Areef yake mun banji zan iya hakura dashi ba ina jinsa shine
ABIN CIKIN RUHINA Amman ya na iya da hukuncin ubangiji, muddin yace zai auran, inkuma
har naji sab'anin haka nayi alkawarin yafeshi har iyakar karshen rayuwata, haka zalika bazan
sake tada hankalina akanshi ba zan d'auke shi matsayin yayana uwa d'aya uba d'aya.

Tsawon lokaci baice komi ba Wanda kowa sonjin ta bakinsa yake, har saida dady yace masa.
"Areef dakai ake kayi shiru."

Ajiyar xuciya yayi yace,
"Abbu meye dalilin da yasa maah ta furta hakan."

Baidamu da tambayar da yayi ba yashiga bashi ansa.

"Watau Areef bari nayi maku dalla dallah."

Shekarun baya tun da mukai aure da sauda saida muka shekara goma ko b'ari bayi ba, nan
yashiga sanar dasu halin da suka shiga, da irin takurawar da dangin Abbun suka mata, har
sadda suka bar kasar..........

"Ranar da muka sauka kasar gidan ummin Dubai muka sauka, Wanda aranar aka haifeka
Areef, tun da aka sallamoku asibiti nida saudah muka nuna sha,awar abamu kai, to sanin cewar
suma kaikad'ai garesu yasa bamu rok'aba, to Ashe da saudah suka kebe da hafsat, ta sanar da
ita halin da take ciki na rashin haihuwa, har gashi ance na k'ara aure saboda bata haihuwa. Saboda son juna da tausayin halin da saudah keciki yasa umminku ta nemi iznin mahaifinka,
akan zata barma saudah kai, koda yaji halin da muke ciki baiyyi jaa ba, yace har duniya tatashi
Arref na mune halak makal, wannan yasa bamu dawo ba saida aka gama shayar dakai, ta
dalilinka komi ya canza Duk da saida kaddarar haihuwar salma tasa na sake wani auren, da marigayiya lantana uwa
gareki salma, ranar da aka haifeki ranar mahaifiyarki ta koma ga Allah, saudah ta had'aki da
khairat ta shayar daku batare da banbanci ba, kaji tushe mafari komi yanzu INA son ji daga
gareka, shin zaka auri kanwar ka khairat kokuwa."
Idona akansa hawaye kawai kefita, yayinda kirjina yake wata irin duka, gyara zamanshi yayi
yace.

*"Abbu kamar yadda maah tace nima ina ganin hakan din ne, kayi hakuri ni nadauki khairat
kanwata ta jini ban tab'a jin sonta ba, koda na minty gudane idan nace zan amunce da auren
zan iya kwararta, saboda bana son ta, gaskiyar magana ma SALMA NAKE SO BA KHAIRAT
BA."*

INNALILLAHI WA INNA ILAIHIR RAJU, UN HAZBUNALLAHU WANI IMAL WAKIL.............kala
man da nake ta nanata wa kenan cikin zuciya da kan bakina, duk iyayen AC din dake cikin
d'akin sunkai shidda Amman zuface nakeyi ta fitar sharia, jikina har karkarwa yake gaba d'ayan
falon yayi tsit bakajin motsin komi.
Abbu ne yayi karfin hali yace,
"Salma kina son yayanku."

Kallonta nayi naga ta sadda kai tana wasa da yatsun hannunta, kafin Anni tace,
"Ansarta kenan Abbun khairat alamun ta amunce kenan."

Jinjina kai yayi duk yana yinsa ya canza sosai, daka kalli fuskarshi zaka gane ranshi ab'ace
yake.

"Kowa na iya tashi zan nemeku idan bukatar hakan tatashi."

Daya bayan daya haka kowa kefita jiki babu kwari, maah duk jikinta yayi mugun sanyi, ta kasa
yiwa Abbun magana.

Tashi nayi zan fita don har wata juwa ke kwasata, jinai Abbun yace,

"Yaki nan ta alkairi, kisameni da safe kafin nafita aiki, kinjiko."

Ban iya bashi ansa ba kawai jinjina kai nayi nafita................



Mom muhsen ce
Mrs bb
[5/27, 8:10 AM] Mom Muhseen: 💕💕💕💕💕💕💕💕
*_ABIN CIKIN RUHINA_*

Written by [Mrs bb]

Mom muhsen ce

*____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S�🏼*
*🇦SSOCIATION�🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition isV to entertain & motivate the mind of
readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*____________________________________*


14&15

Basai na kwatan ta muku yadda daren ya kasancewa khairat ba,domin kuwa bacci duk yadda
ya kware wajen sata to fah wannan ranar ya gagara satar khairat,yadda taga rana haka taga
dare,don kasa kwana tayi dakin su itada salmar,kuka tun tanayi da hawaye har ya dawo idon ya
bushe,wani irin zafi takejin kirjinta nayi kanta kamar zai rabe gida biyu,haka meenah tayi
lallashin tagaji tayi bacci ta barta.

Duk wani tashin hankali da na kejin zuciyata aciki, nayi iyakar yina nayi control din kaina kafin
gari ya waye,don nayi wa kaina rantsuwa da alkawarin idaniyata ta gama kukan *SO* kuma
insha Allah zanba marad'a kunya.

Shirin bacci jahid keyi yana yi yana kallon Areef da ya kwanta kasa saman kafet din dake
malale tsakiyar dakinsu,ko combus din dake kafarsa bai cireba balle ya samu damar fara canza
kaya,girgiza kai kawai Jahid keyi don lamarin Areef abun yana kaishi Bango,tsaki yaja wanda
Areef baisan ma yana yi bah..........
"Dallah malam tashi anan,kawani sheme kasa kamar Wanda aka aikowa sakon mutuwa."

Kallon jahid din yayi yana sauke ajiyar zuciya,lumshe kyawawan idanunsa yayi yana sake yin
filo da hannayenshi,baice ma jahid komi ba.

Haushi ne ya sake turnik'e jahid,don ganin yaki kulashi wani tsakin ya sake ja yana hayewa
gadonsu wayarsa yafiddo yana danne danne........tsayin mitina babu wanda ya sake kula kowa
har jahid ya gama abunda yake yayi addua ya kwanta.
Sai lokacin yyi magana.

"Jahid baka ga kamar Abbu ransa ya baci sosai ba."

Cikin kuluwa yajuyo yana cemashi,
"Au sai yanzu kagane haka ashe,ai babu anfanin hakan wallahi kabani mamaki Areef,yadda ka
bashi kunya ka nuna cewar kana bayan maah,kasan me hakan kenufi kuwa.?to bari ni na gaya
maka,kanuna cewar bai isa dakai ba,kuma shi ba matsayin mahaifi yake wajenka ba."

Sai lokacin yayi saurin tashi zaune idonsa ya canza kala saboda damuwa yace,
"Karka fassarani haka jahid,taya zan dauki mutumen da ya haskaka rayuwata irin haka,kasan
matsayin da naba Abbu ciki zuciyata kuwa."

Wani tsakin yaja yace mashi,
"Duk irin matsayin da kabashi baida wani anfani,tunda har ka wulakanta bukatarshi gaban

kowa,kadaina cewa yana da babban matsayi wurinka."

Rutse idonsa yayi da karfi yana jin kamar ya kama jahid da mugun bugu,don jin irin kalaman da
yake anbata mashi.

Cikin muryarsa data canza sauti saboda bacin rai yace,
"Karka sake anbata mani irin haka,na fadi iyakar gaskiyata ne saboda banson ya dauki amanar
ta yabani inakasa rikewa,because i don't love her salma nakeso itace wadda na zabarwa kaina
matsayin abokiyar rayuwata,akanme zanyi karyar yin abunda nasan ba zan yiba,idan kadamu
ne saboda nace bason pls and pls jahid marry her."
Murmushin takaici yayi yana kallonsa kafin ya gyara jinginarsa jikin gadon yace,
"Areef kenan wallahi tallahi kaji rantsuwar dan musulmi ko,da ace babu wata acikin raina ban
riga na furta inasonta ba,jiya dana baka mamaki gabankowa zan ce ni yabani aurenta,saboda
khairat matan dake ma maza wuyar suce,kuma kaima nan gaba am sorry 2 say wallahi u will
regretting."
Wani wawan tsaki yaja ya mike yashige toilet yana cewa,
"U are not in ur sense wlh,nidin zanyi regretting akan wannan yarinyar marar hankali,mtsss
amman babu wanda ya kasheni irinka Allah ya isana wallahi."
.......yashige warshi.

Jinjina kai kawai jahid yayi yana hango yada lamarin zaikaya.

*************

Tun da na tashi da asuba nayi sallah nake karatun qur,ani saboda in kara samun kwarin
guiwa,saida naji zuciyata tayi sanyi sannan na tashi yah meenah har ta koma bacci,fita nayi don
har lokacin banajin bacci sosai saidai kaina da yayi nauyi saboda rashin baccin,kitchen nasamu
anni tana had'a break dinsu Dady don dashi suke tafiya,itada maah idan yau wanan yyi gobe
wannan yyi,tsarinsu gwanin burgewa.

"Annie ina kwana,ai ina cewa sadaqallahul azim nayo nan,saboda k'amshin girkinki d a ya hana
hancina sak'at."

Murmushi a kan fuskarta tana motsa fruit salad da ta gama had'awa tace,
"Lafiya lau yar gidan Annie,Amman dai kinsan ko lashe bazan y'an maki ba ko."

Ansa nayi ina zubawa cikin mazubin da take niyar zubawa nace,
"Ba komi k'amshin ma da naji is okay for me,zai cika mun cikina."

Kallona tayi ina cigaba da idasa hada basket din break din nasu,cikin tausaya wa tace mun.
"Y'ar gidan Annie kallanni."

Banyi musuba na d'ago ina kallonta.

Hannuna ta rik'o dana gama saka komi tace,
"Bakiyi bacci ba khairat,karkice mani abunda yafaru jiya shine ya hana idonki runtsawa,idan
kuwa haka ne to banji dadi ba,khairat shin ko kin manta da cewar yarda da k'addara mai kyau
ko marar kyau imani ne,ladace mai tarin yawa karki soma yin halin irin na marasa ilimi,ke
yarinyace mai ilimin addini dana zamani,zanso aduk sanda kika tsinci kanki acikin wannan halin
kiyi anfani da iliminki,don haka kiyi mani alkawarin wannan shine karon farko kuma na karshe."

Kaina yana k'asa nace,
"Annie nayi maki alkawarin haka insha Allah."

"Yawwa diyar albarka naji dadin haka,nasan kuma tunda kikayi man alkawari bazaki karya
ba,Allah yayi maki albarka ya kuma cigaba da karfafa maki akan komi,dauki break din kikai
falon Abbunku shizai wuce dashi,dadynku sabko yayi don suna da bak'i."

Dauka nayi na nufi cikin fat dinmu,
Kowa bacci yake don lokacin karfe bakwai da rabi,falon na sameshi yana karanta jarida,maah
na zaune gefenshi, yana yin dana gansu ya nuna akwai damuwa.
Sallama nayi na ajiye ina gaida maah,ta ansa cikin kulawa shima na gaidashi.

Nai zaune ina jiran ya fadan abunda yasa yace in sameshi da safe,jinai yace mum.
"Ta alkairi kije zuwa dare mun hadu,amman ki tabbatar kiyi baci isashe don idonki ya nuna jiya
bakiyi bacci ba."

Ina wasa da hannuna nace,
"Insha Allah Abbu,saika dawo Allah ya kiyaye."

Cikin kulawa yace,
"Amen Allah yayi maki albarka."

Nace"ameen"na baro falon

Mom muhseen ce.
Mrs bb.
[5/27, 8:12 AM] Mom Muhseen: 💕💕💕💕💕💕💕💕
*_ABIN CIKIN RUHINA_*

Written by [Mrs bb]

Mom muhsen ce

*____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S�🏼*
*🇦SSOCIATION�🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*____________________________________*


16.

Daki na koma nayi dakin yah meenah na sameta tashin ta kenan,tana mik'a da salati.
Murmushi nayi mata ina hayewa gadon nace,

"Morning my dear."

Hararata tayi kafin ta sauka daga gadon tana cewa,

"Mai kukan banza kawai,wallahi saboda kuka wataran sai kin makance rab'o kawai."

Dariya nayi don yadda ta dage sai hararata take tana fad'a,
"Kinyi dariya mana ni kinga shigata wanka,kinsandai yau muke fara attending lectures ko."

Kwanciya nayi ina jan bargo tare da cewa,
"Wallahi yah meenah ko bature bazai nuna maki biting time ba,kiga fa kwata 2 eight muda keda
lectures ten thirty."

Ta na daga cikin barth room din tagama wankeshi tana hada ruwan wanka tace,
"Kanki akeji don wallahi bazan ringa let ba,dana gama inhar baki tashiba saidai kisaman
can,don na lura nawarki is too much wlh."

Dariya nayi nashige bargo don sanyi akeyi kwanan kamar kamarme.
Dandanan bacci yayi gaba dani don dama idon sai lumshewa yake saboda tsabar baccin dake
cina.

**********

Areef ne da jahid suna wajen exercise dinsu,don wajene keb'entacce wanda aka k'awatashi da
abubuwan more rayuwa,babuce babu awajen Abbune yafito zaiwuce ya hangi k'ofar wajen
abude,yafasa shiga ya cewa driver yasaka mashi jikarshi baya yana dawowa.

Shiga yayi ya samesu duk sunyi gumi,jahid na kan machine din gudu Areef na gefe yana kan na
keke......hira suke jefi jefi saida yagama kallesu sannan yayi gyaran murya,duk juyowa sukai

suka kallo wajen...........da sauri areef ya sauko daga inda yake ya iso inda Abbun yake,ya dan
rugumeshi yana cewa.
"Good morning Abbu."

D'agoshi yayi yace,
"Morning."
Jahid ma yazo ya rungumeshi ya gaidashi,don wannan salon tun suna yara sukeyinshi kuma
Abbun ne ya koyar dasu hakan,don yanajin dadin jin yaransa ga jiki,Allah kadai yasan irin son
da yake masu.

Duk suna zaune kasa shi yana tsaye,
"Ya kamata dai kamar yanzu kunfara zuwa office,ai kun huta haka nan ko."

Areef ya langab'ar dakai zaiyyi shagwabar da ya saba,Abbu yace.
"Karkace komi,sarkin son jiki kaikuwa wata macen ma tafika jarumta,don haka banason korafi
idan na dawo am talking about that issue OK."

Duk suka ce yes Abbu tare suka fito suka rakoshi har mota,Areef ya bude mashi baya yashiga
sannan yarufe,daga mashi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
google.com, pub-9213700357025247, DIRECT, f08c47fec0942fa0