Showing 36001 words to 39000 words out of 74145 words

Chapter 13 - Abin Cikin Ruhi Book Compelet Mss Bb

Mrs Bb   

05 Jul 2026

803


Jaye hannun nayi inacewa"pls mekakewa sauri gobene fah."
Murmushi yayi yace"shikenan,aidai daga gobe andaina man iyaka da halalina."

Hira mukai tayi dashi duk wata damuwata dana taho da ita ya kawar mun ita,dr mutunne mai
sanyin hali,hakurinsa mai girmane tsawon tarayyar mu ba taba ganin bacin rans ba,ko abu nai
mashi na bacin rai bazai taba nunaman ba,zaidai ce kibaryin abu kaza babu kyau.
Any time ever moment fuskarsa dauke da murmushi,tabbas nasan na auri dr na gama
damuwa,duk irin halin da nake ciki muddin mukai waya or muka hadu ban sanin inda damuwar
take rugawa,tabbas maganar Abbu gaskiyace da yace dr shine ya dace dani,nima nayarda na
amunce kuma ashirye nake nayi zaman aure dashi mai dadi,nayi damarar faranta mashi har
iyakar karshen rayuwarmu.
Zamu yi rayuwa mai kyau da yardar Allah,hakika 100% na yarda dr ya zama mijina uban
y'ay'ana.

💕💕💕💕💕💕💕💕

*RANA BATA KARYA SAIDAI UWAR DIYA TAJI KUNYA*
*RANAR WANKA BA,A BOYON CIBI,ALKWARIN ALLAH YA TABBAT,UMMULKHAIR FAROUK
TA ZAMA MATA GA DR. MUHAMMAD KASEEM,TAREDA MATA GA SHAZALLI YUSUFA DA
AMARYARSA UMMUSALMA FAROUK.*

dubunan mutane da bazan iya kwatan ta maku iyakar adadinsu ba suka shaida wannan
Auren,Amare sunyi kyau har sungaji.
domin khairat musanman ummi tayo hayar maiyin kwalliya daga dubai,khairat tahadu iyaar

haduwa,saidai muce Allah ya tabbatar da Alkairinsa........tunda labarin daurin auren yazo ga
kunnena nake kuka,badan komi ba sai don kawai cewar yanzu fa nazama matar Aure,wacce
zata tashi daga gidansu zuwa wani gidan,zan fara sabuwar rayuwa da sabbin mutane,shin
wace irin rayuwa zamuyi. Shikenan babuni babu zama gidanmu kenan saidai nazo yawo,lallai Aure abune maigirman
gaske,kaduba abunda zai raba uwa da yarta yaraba uba da yarsa,wane abune wanan inbada
mutuwa da Aure.
Ina falon Abbu ankirani na gaisa da bakinsa,nasamu kyaututtuka har basan iyakaba,vanyi zaton
friend dina zasuzo ba saigashi harda mazan department dinmu sunzo man daurin aure.

Durkushe nake nasha wani dankareren less,sky blue da pink color,nasha takalma na da jikkata
duk farare sai mayafina babba da aka rufaman bisa kaina har fuskata.......majina kurun nake
gogewa don kukan tunyaa zuwa da sauti har ya barfita da sautin,falon yarage mutane Abbune
da daddy,sai maah Annie da ummi,sai yah jahid da yah shahid..............wanine daga can bakin
kofar shigowa,takalmansa sawu ciki kurin nake gani farare tasss,tabbas shine yanayin da
zuciyatabtake bugawa ya tabbatar mun shine......hakanan banji dadin zuwansa ba hakika rashin
zuwansa sai yafimun kwanciyar hankali,domin samun natsuwar zuciyata.
Alamu dai ya nuna fada za,aimun salma akejira tun dazun.
Abbune yake waya da driver da ya aika gidan inna dauko salam,
"Kashiga kace nina turo azo adaukota za,ai masu fada ita da khairat,..........muryar innar mukaji
tafito sosai ciki wayar.

"Faruku kafita idona,dolene fad'a tace mun tsoron zuwa take kana iya dukanta,to nima na hana
anan za,a dauketa akaota gidan mijinta,ruwanka ne kasamata albarka ruwankane ka tsine
mata,inace saudah ce mai yinfadan itada yar uwarya,to itama ga nata dangin uwar nan suna
mata,bazata zoba."
Baice komiba ya sauke wayar,ummi ranta yabaci don daman ummi badai fada ba,inhar
akatabota.
Yo ba,a tabota din bama wace allah ciki balle antabo........cikin banbami tace,
"Wace irin yarinyace wannan kahaifa farouk,ace yau aurenki zakitai dakin miji bazakizo kiyi
sallamar mutunci da iyayenkiba,idan ita wannan ta nuna maah,sannan tacigaba idan ita bata
haifetaba kai aikaine ubanta,tazo kasamata albarka.
Kumaninda kara da mutunci saudah ba itace tashayar da itaba tsawon shekara
biyu,tatarbiyantar da ita,amman dayake nonon datasha fitsarar dashi tayi ta nuna maku cewar
itafa diyar lantana ce Allah yajikanta,ai saudah uawartace idan tasan kanta tasan mutunci,kuma
inna saita biyeta inbacin kurun dama jiranmu take......" Maah ce tai saurin katseta dacewar,
"Don Allah yaya kiyi shiru hakanan,kowa yaza ma nagari don kanshi,ni wallahi taje nayafe mata
duk abinda tayi man,Allah yasa Albarka cikin auren."

Magana zata sakeyi ummin dady yace"pls hafsat abar maganar kaima kuma kayi hkr duk yadda
ranka yakai gabaci dole zakayi hakuri kabisu da Allah yabada zaman lafiya shi ake fata,shine

kawai."

Nanfa suka rufu kaina kowa da abunda yake fada,kukana kurun nake don jinake baza iya barin
maah da abbuna ba.

Cikin yayyaena akace idan damai magana yayi mani ga mototci can zuna jiranmu.
Yah jahid yayi man nasiha sosai akan hakuri,yac"nasanki indai akan nan wajenne to kikara
domin zamane baa yauba bana gibe ba,Allah yayiwa rayuwarku Albarka yakuma kareki daga
makiya."
Kowa yace ameen,yah shahid ma yayi man Anty shidah kiwa kwallah take tayi tama kasa cewa
komi,duk ta kwakwumeni,itada yah meenah.

Har yanzu yananan inda naganshi,bai motsaba bai kuma tashiba kuma baice komiba,
Ummi ce tafita don wasu baki da sukazo mata biki,tare da maah suka fita tana cewa yah imran
yaje yacewa masu daukar amaryar sukara hakuri gatanan za,afiddota.
Wannan kalamin yasake tunzura kukana har muryata bata fita,sumabyah meenah kukan
suke,don Anty shidah yah jahid yajata sunfita.
Abbu da Dady daman suma bakin garesu dayawa zasu sallamesu,don yama tayi wajen biyar
harda rabine.

Husna ce taje tasake tattaro man kayana danayi using dasu,babu kowa dakin dani sai yah
meenah saishi dake can zaune har lokacin.

Munanan zaune tsawon lokaci banda shashshekar kuka bana yin komi wata irin kewar yan
gianuce akejin tana kamani,sonake yayiman magana yakiya,yaki motsawa yaki kallona,yaki
zuwa inda nake kowa yana furta albarkacin bakinsa akan aurena,Amman shi ko tanke baice
komiba,hankalina bai sake tashiba saida naga ana jana za a fitar daga cikin gidan.......kua nake
ina rike Maah da Annie amman babu mai saurarena,Abbu dakanshi ya kamani yasa
motar,sanan yashiga gaba dady shike tukamu,sauran motocin suka rufa mana baya.......inaji ina
gani nabar gidanmu zanfada wata duniyar daban,bansan kuma wace rayuwar
zanyiba........lallashina kirun Abbu keyi har muka isa,baibari nasaka kafata ba saida nayi addua
sosai,har yana aranto man ina ansawa sannan adagaafatta dama asakatare *BISMILLAH.*

Mrs bb ce👌🏻💕💕💕😘😘😘ina Alfahari daku
[6/16, 11:11 AM] Mom Muhseen: 💕💕💕💕💕💕💕
🌹
*ABIN CIKIN RUHINA*

Writing by mrs bb
Mom muhseen.

Wattpad name
Humaira7531.

DEDUCATED TO ZAUREN MRS BB.

*I need ur prayers Am not feeling fine.*

Not edited.

33.

Iyayena maza sune suka kawoni har cikin gidan mijina,nayi kuka kuka mai sunan kuka har
jinake kaina zai rabe gida biyu,dandanan zazzabi ya rufeni ruf rawar sanyi kurun nake su yah
meenah da suka shigo motocin Abokan ango duk sun rude da halin dana ke ciki,don jikina har
wani siraci yake fitarwa.......hakika ban taba dauka haka ake jin dacin rabuwa da iyaye ba in
aure ya tashi,lallai ajinjina ma Aure.

Anty shidah bata kwana ba yah jahid ne yazo ya dauke ta,Husna dai nan zamu kwana da ita da
yah meenah.........sauran kawayen mu duk sun tafi gida suna cewa sai sun dawo gobe walima.

Ganin jikin nawa yayi tsanani yasa suka kira dr suka sanar dashi,aikuwa sai gashi kamar daga
sama duk yarude.......waya ya ciro ya shiga kiran dr su ganin dr baima ganin su yah meenah
rungumeni yayi abunsa babu abunda ya damai,dole suka bar dakin suka koma daya daga cikin
bedroom dina,don babu karya iyayena sunyi matukar komari,Abbu gado biyu duk yayi mana da
set din kujeru biyu,amman ni maah da annie da ummi suka hadu suka kara man kala guda,duk
da halin da nake ciki hakan bai hana ni ganin kyan bedroom din da nake ciki ba.
Komi maroom dakin sai walwalin fitilu yake,gadon kanshi cycle ne kuma juya wa yake,kana iya
tsayar dashi kana iya barinsa.
Abun gwanin burgewa da ban sha,awa.

Ina jikinsa nayi lamo sai ajiyar xuciya nake,kaina kurin yake shafawa yana jeraman sannu,tuni
dama ya rabani da gyalena.......saida likita zai shigo ya rufa man shi.

Dubani yayi sosai yace"damuwa ce da kukan da tasha suka sakar mata wannan zazzabin,da
tasha pen relief zai sauka kuma tayi kokarin cire damuwa insha Komi zaizama successful."

Godiya yayi mashi ya tafi kwance nake na kudun dune wuri guda,na lumshe idona ina jin
kamshinsa kusa dani.

Waya yake idonsa akaina don inajin su suna sakani takurewa.

"Ummi jalila ta hado abinci maidan saukin ci sai taci kafin a kawo na sauran,eh ummi to insha
Allah, jikin ai da sauki gata nan oky to."

Ajiye wayar ya yayi yana tab'a goshina........ajiyar zuciya nai yace,

"Sorry my dear tashi ga abinci nan sai kici kisha magani,bazan so wannan ciwonba muna tsaka
da farinciki,kokin manta yau wace rana ce bari na tuna maki,yau ranace ta farin ciki agaremu da
duk masoyan mu baki daya,burin mu ne ya cika na mallakar juna Allah ne ya nuna mana don
haka plss my love,ki tashi mu fuskanci sabuwar rayuwa."
Sake lafewa nai cikin gadon mai dauke da wata irin katifa mai laushin tsiya.
Kofar aka bude aka shigo tare da sallama,

"Wayyo Antinmu kina nufin wannan dinner ba za,ayitaba gaskiya kitashi ki wartsake gidan
masoyinki fa aka kawoki..........muryarsa cike da annashuwa yace"Jalila kin raina niko."
Tashi nai ina gyara kallabina dana rufa ma kaina shi,kokarin sakin fuskata nai nace mata.

"Inayini."
Dariya tayi tace"lafiya Anti tunda kinbarmun girman."
Harararta yayi yaceman
"Karki sake gaidata inba haka ba rainaki zatai,kanwarki ce itace zata ringa gaidaki."

Murmushi nake bance komi ba,
Tace"ga Abinci nan Anty amarya aci awartsake mutai party."

"Jalila babu wani party da za,ai matata bata lafiya kibari inkingama ruwan idon zaben saurayi
inbikinku yazo saikuyi koma miye ko love dina."

Wayyo kunya kamar tasan yadda zatai dani,
Sunkuyar da kai nai ina wasa da gefen kallabina.
Dariya tayi tace"ashe kuwa zaki sha kunya don bakiga komiba wajen Dr sai ya rungumeki
gaban ummi."
Zaro ido nai ina kallonta mezasuyi ba dariya ba har suka bani dariyar nima.
Mikewa tayi tace"nayi nan amarya Allah yabada lafiya,ummi na miki sannu."

Muryata tayi wani irin sanyi sosai nace,
"Nagode kice mata ina ansawa sosai."

Kallona kurun yake duk naji na takure shagwabe fuska nai nace"plss d........jin lips dinsa kurun
nai kan bakina........daskare wa nai kamar nayi kankara saida ya tsotsa iyakar yinsa sannan ya
dago yana kallona,
Murmushi yayi yace"Aina gaya maki duk randa kika sake ceman wani dr ko sir saina cinye
baki,to yanzu ma arzikinki daya baki daafiya da kinsha mamakina tunda bakijin magana."

Juya mashi baya nai kamar zan kuka saboda wallahi rashin kunyar dr tayi yawa,
"Nidai kadaina bana so."

"OK naji wannan juyo maza nabaki inada baki nabarosu ban sallamesuba.,"

Yada yayi alamun babu wasa dole yasa na juyo yana bani yana man hira,yana gaya man irin
mutanen da suka halarci bikinmu.........ashe daman yunwar nakeji sosai don kwana biyu bana
cin komi sai dan abu me ruwa,saida yaga ina shirin sheka mashi amai yasa ya kyaleni.........ya
sunbaci goshina yace, "Sai da safe ko in dawo mukwanta tare."

Jifarsa nai da filo ya cab'e yana dariya yace"ohodai duk wayon amarya sai ansha
manta,kishirya gobe anagama walima zanfara kora don nan gidan zanyi magrib."

Dalalo ido nai baki bude dariya ya kwashe da ita yafice bayan ya jehoman filon.

Komawa nai jagwaf kan gadon,ina ajiyar zuciya tunda nake ba,a tab'aman kiss ba sai yau har
yanzu jinake kamar bakin nasa yana kan nawa,numfashi na sauke ina jinjina soyayyar dr,ya iya
tafiyar da ita yadda ya kamata.........tashi nai na gama kalle bedroom din sannan nafito na shiga
wanda su husna suke ciki ita da yah meenah.
Hira suke konace kowace hira take awaya da masoyinta,don yah meenah tuni tayi nisa wajen
kaunar yah imran,love kurun suke bugawa mimi ce keta chat tana ganina tarungumeni.

"Allah sarki Amaryarmu sannu kinjiko yajikin,yayi sauki."
Murmushi nayi nace"nasha magani na samu sauki,kunci abinci kuwa."

Tace"yanzu muka dawo daga cikin gidan,munci mun koshi wallahi khairat kinyi dacen dangin
miji kowa maganarki yake,yana yabon halinki ki zauna dasu lafiya kinga wai yadda sukaita
hidima damu,abincin nan nama yafishi yawa ferfesun naman kai,gasassun kaji,yan ciki
soyayyen naman rago sai wanda mutun yaga damar ci.......mahaifiyarshi tana ta tambayar jikin
naki."

Wata natsuwa ke shigata "tabbas ina fatan hakan ya dore,Allah ya kawar da shedan tsakanin
mu nidasu."

Tace "ameen muje na rakaki kiga gidanki khairat,wallahi su Abbu sunyi kokari sai fatan Allahb
yabiya su."
Tare muka fita dayan bedroom din dake tsakiya muka shiga,Italian bed ne golding color komi
golding har fentin kanshi,sai daukar ido yake don yama fi wanda aka saukeni ciki,wanda su
Husna keciki kuma komi purple ne da dark pink.........palona biyune babba da karami babban
set biyu na royel chairs aka saman,karamin kuma wasu kujerune yan gaske har wani malatsi
garesu inzaka zauna zaka danna,wanda zai bakujerar wani irin sanyi ni,ima har haske suke
fiddawa da daddare.......saboda farinciki har kuka nai ina gode wa iyayena.
wani abun mamakin shine wadannan kujerun wai yah Areef ya siya man su cewar mimi.

"Bawan Allah gaskiya Khairat yah yayi jarumta yayi karfin hali sosai,kinsan tunda yabaro nigeria

yazo nan gida wlh baida lfy in takai ce maki yah baya cin abinci tsawon sati baici komiba,amai
dai kurun karshe saida ya kwan ta asibiti,da fadan ummi da hargaginta ya daure ya karfafa
zuciyarsa,amman har gobe ke har abadan yah bazai taba son wata mace kwatankwacin wanda
yake makiba,ina rokonki kiringa mashi Addua Allah ya sassauta mashi yana cikin yanayi,don
baiso zuwa bikin nan ba ummi ce kamar zata cinyeshi danye yasa dole yazo,to gashinan zuwan
ya tado aiki don yanzu haka yana asibiti,gobe zasu koma don yaga likitanshi dake dubashi."

Silalewa nai na zauna kan kushin din dake tsakiyar babban falona,hawaye masu zafi suka shiga
zubarmun inajin wani ciwo cikin zuciyata.

Zamatai kusa dani ta dafa kafadata tace"kiyi hkr ban gaya maki bane don kiyi kuka ba ko
kishiga damuwa ba,nagaya makine don kisashi addua Allah yaba shi lafiya ke yanzu kinriga kin
zama ta wani tunanin wani ma inkikai haramunne,ki fawwalama Allah komi shikadai yasan me
hakan yake nufi,Amman wallahi nidai idan nice koza,a mutu sai an aura man wanda nakeso,ni
banson irin wannan rayuwar taya Allah bai haramta abuba amman mutane su maidashi haramci
wannan badaidai bane,ana shiga hakkin mutane wallahi."

Ina share hawayena nace mata"mimi wannan abun babu wanda keda laifi cikinsa
saishi,saboda gaban kowa Abbu yake sanar dashi halin da nake ciki akansa,Amman ya sha
mur yace wai shi bama ni yake so ba,shibazai iya aurena ba wannan dalilin shine duk ya jawo
komi,har mai aukuwa ta auku,wallahi bazan tab'a yarda da cewar ba laifinsa bane mimi,don
haka ni kibar ma yiman maganarsa,don nariga na shafe babinsa zanyi sabuwar rayuwa da
maisona."

Murmushi tayi tace"kiyi hkr Amman wallahi duk duniya inbanda iyayenmu bakida mai kaunarki
sama da yahna,ki dauka haka kaddararku take wani baya auren matar wani."
Mikewa nai nace "nayi nan inje nai sallah na kwanta goma saura,"
Biyoni tai tana cewa"karki tsani yaya ba laifinsa bane."
Afusace na juyo kanta nace"nawaye inba shiba nace laifin waye,inda yana sona da gaske mai
yahana shi furtawa tun kafin atsayar mun da mijin aure,plsss mimi karkija najuye maki haushin
da bana kiba,kibarni haka kibarni na jida kuncin da nake ciki ehy."
Bata wani ji haushiba don ko itace wanda ma yafi haka zatai,don bata yarda da auren da babu
soyayya ba imfact inta sai wanda ma take masifar so yake masifar sonta zata
aure.......tace"Allah ya huci zuciyarki nabari,ammafa duk sanda mukai wya dake ko bayan mun
tafi zan ringa baki news din halin da yake ciki."
Banza nai mata nashige dakin na banko kofa.

Mrs bb ce👌🏻💋💕😘😘
[6/19, 12:43 PM] Mom Muhseen: 💕💕💕💕💕💕💕
🌹
*ABIN CIKIN RUHINA*

Writing by mrs bb
Mom muhseen.

Wattpad name
Humaira7531.

DEDUCATED TO ZAUREN MRS BB.

*Nga sakonnin gaisiwarku gareni Allah yasaka maku da Alkairinsa*

Not edited.

34.

Alhamdulillah biki ya tashi anyi walima lafiya amarya tasha kyau,anyi hotuna kala kala har kuka
nai da su ummi suka zo yiman bankwana........lallashina taitayi tana shiman Albarka nan akabar
mimi wajen maah zata kara mata sati biyu,yah imran kamar yayi kuka baison tafiyar,sai tsogumi
yake mata har ya kureta ta haushi da fada, dama ummi abu kadan zai tun zurata taita masifa,
"Tun yaushe kake man maganar inace maka dan uwanka ne zaiga likita amman kaki fahimta,ko
so kake ya mutu anan ne."
Hakuri yaita bata don ya manta shaf da batun ganin likitan Areef din.

Kowa ya watse dagani sai husna da yah meenah,suna jiran Ango sai su wuce gida.

Hirarsu suke nikuwa nayi tagumi,duk na firgice nasan dr bazai daga man kafa ba yau,yadda
yake wannan rawar kafar tun kan akawoni abun tsoro yake ban,duk jikina yayi sanyi harga Allah
inason dr Amman banson making love dashi,hakanan nidai zuciyata bata son bashi
kaina........jinake kamar ace ba yau banezai tare,sai kuma naga ai koma yaushe ne dole zai tare
ni nabani wlh bana so.
Hawaye na share husna ta ankare dani tayi murmushi tace,
"Yah meenah mutuniyarfa da alamu dai atsorace take,wallahi nikaina tausayi take ban,ganin
yadda dr ba sauki ne dashiba."

Murmushi tayi ta matso kusa dani tace,
"Sorry my qanwa,babu fah wani abu idan baki saki jikinki bane zakija har wani abun ya
sameki,amman inkin sake lafiya lau dan zafin baida yawa."

Kallonta nai idona yana zubar da kwallah nace,
"Yah meenah ni wlh banson ya kusanceni kwata kwata,nidai bana so wlh."

Ajiyar zuciya tayi tace"bakison shi kenan."

Girgiza kai nai "aa ina son shi kwai banson making love dashine pls ya zanyi wlh ina iya
mutuwa akan hakan."

"Subhanallahi!khairat kina cikin hankalin ki kuwa,kinsan mekike fada,mijinki nefa halal dinshi ce
ke komi yayi dake baida zunubi sai tarin lada,kifitar da duk wani tunani cikin ranki kicire son
zuciya ki cire wani can kisaka mijinki cikin zuciyarki,
Na riga na ganoki khairat kina son ki kaurace ma mijinki saboda wani

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
google.com, pub-9213700357025247, DIRECT, f08c47fec0942fa0