Showing 45001 words to 48000 words out of 74145 words

Chapter 16 - Abin Cikin Ruhi Book Compelet Mss Bb

Mrs Bb   

05 Jul 2026

834

wani irin haske ga hutu ga ciki,har wani daukar ido nake,daman bana
saka komi ga fuskar sai farar power da liptis saboda bushewar baki,amman duk dahak nai kyau
sai murmushi nake,sanan Dr idan yaganni kilan gaban ummin zai daukeni ya rungume.,don shi
kunya ba isar sa tayi ba bana saka turare tunda na samu cikin nan saidai yar sure danake goga
ma anfit dina da matse matsina saboda smeling.

Fitowa nai da sauri don dauko wayata dake falo naji kamar sadam yana kwalan kira anan
kirana,
Sauri sauri haka nakeyi inje ga wayar nason Dr ne yaketa kira kilan ya iso aje adauko shi,,,,,jinai
kaina da kirjina sunbugi abuu bansan nace washhh Allah na tsaki naja nawuce do k'amshinsa
kadai ya isa yaga yan waye yashigo.

Mikoman wayar yayi yana cewa "Number Dr ne sai kira ake."
Ansa nai ina wucewa karamin falo don induba abunda nasaka ko yayi sanyi yadda nakeso,ina
tafiya ina duba wayar kiransa nakeson inyi still yanzu ma karon mukai sosai,har wayar ta silale
kasa ta fad'i...........wani kululu yazo ya tokare man wuya duk yadda na tsani kwayar idona ta
kallai doke tasaka na zuba mai idanuna dasuka fito waje dukansu,,,,har wata ruwan kwallah naji
suntaru acikin su bakina naji yana fada cikin jin haushi.

"Wai meye hakane ehy d'azu kabanke ni na kyale nai hkr yanzu ma kuma haka gashi kafasan
waya mijina sai kirana yake yaz..........."shut up stupid girl"

Sake dalalo idona nai ina kallonsa tuni kwallah sun cika idon tab,nace"ni ......nice
stupid.....ni...cikin tsawa yace "eh kedin! ba stupid din bace,kina tafiya kamar makauniya bakya
kallon gabanki,,,comon ban waje nawuce nonsence....."
WanI malolon kunci da bak'in ciki suka cika man zuciya.....kafin nayi magana ya janyeni gefe ya
wurgar,bacin bango danai saurin dafewa da sai dai kan cikina zan fad'a.........durkushewa nai
ina kuka bak'in ciki rabona da kuka bazan iya tuna waba.....mimi ta karaso cikin sauri.
"Subhanallahi khairat lafiya,meyafaru mekikamai."
"Mefa me zan mashi kawai zalincine da kuma daman jirana yake....banka ta fa yayi har saubiyu
danme zanyi magana kina gani nan kadan ya hana bai turani k'asa ba da kan cikina zan
fad'a......hakri taban taa tattara man wayata da ta tashi aiki,sim dina nacire na saka cikin wayar
mimi nashiga kiran dr amman ban samu ba,kuka na kubce dashi yanzu haka akwai abunda zai
ce man gashi nan yayi man sanadin rashin samunsa........koda ummi ta dawo banji ko dar ba na

gaya mata ai kuwa ta hau balbalin bala,i kamar zata ari baki.....sadda ya dawo daddare har
lokacin wayar Dr bansamu ba,,,duk nashiga halin damuwa ko yana ina ya iso bai iso ba ina ya
taya oho.....ina kwance kan cinyarta idona saboda kuka har yayi fushi....koda ya shigo shida
imran suna hirar kwallon k'afa ummi tabishi da harara baisan ma tanayi ba, Imran ya wuce dakinsu shikuma ya wuce karamin falo.....inanan kwance kamar ance dago ki
kalli can dagowar dazanyi na hangoshi ya dauko wannan sweet cake d'in ya yanko kusan
rabinshi kan plet,ga spoon dinsa yana yankowa yana saka wa baki.....kamar anzungura man
Allura na tashi afirgice na nufi wajen da yake...... Tun kan na isa inda yake yasha mur kamar bai tab'a dariya ba,yace"ke..... kee.......karki sake ki
iso maninan,wai bakida hankaline "ina zuwa na kab'ar da plet din ina hawaye nace"Wallahi da
kacishi gara ya b'are ai bakai akaima wahalar ba,na rantse kuwa kozai tsutsa da hunhuna inhar
wanda naimawa mijina baici ba kaima kuwa bazaka tab'acin sa ba......."keee............ni ....nikike
gaya ma magana,don kinga ina ragar maki,zan daukeki da mari awajennan........"ummi tace da
kuwa baka kara marin wata mace ba aduniya Ashe baka da hankali Areef,yarinyar da ciki
kakeson kassarawa,oh abunda kayi mata d'azun bai ishekaba yanzu ma gabana kake kirarin
zaka kwad'amata mari,to kafara dani kafin ka yi mata nata."
Juyawa yai yashege b'angarensu cike da b'acin rai......lallashina taitayi tana ban baki,har nahkr
daker nasha maltina da cake din na wuce daki nai sallar mangaruba na kwanta,wayar nake
kallo inajin kirjina yana dukan tara tara hankalina ya gaza kwanciya ......me yafaru da Dr na
hawaye suka silalo man,,,jinai kawai zuciyata tana karkarwa dandanan jikina yafar daukar wani
fitinannan zafi.....mimice tashigo "Khairat ga wayar kisake jaraba kiransa ko za,adace saurin
tashi nai don inaji ajikina zan sameshi insha Allah.....hannuna har wata karkarwa yake ina
danna kiran,jinginanai inajin yadda zuciyata take duka jinai kurun kiran yashiga.........kafin
bakina yaimagana naji wata murya bansanta ba tana cewa *MAI WAYAR GASHINAN ASIBITI
SUNYI HAD'ARI KUYI SAURI KUZO YANA GAF DA RASUWA.*

wata k'ara na fasa wadda tasani rugawa ni ma don kunnena fashewa zaiyyi.........

Mrs Bb Ce
Mom muhseen.
09034722970
[6/27, 9:41 PM] Mom Muhseen: 💕💕💕💕💕💕💕
🌹
*ABIN CIKIN RUHINA*

Writing by mrs bb
Mom muhseen.

Wattpad name
Humaira7531.

DEDUCATED TO ZAUREN MRS BB.

*_ABDOUL-NASSER (ALFAH) COMING SOON INSHA ALLAH,NASAN ZAKU NISHAD'ANTU
DASHI KUCIGABA DA TSUMAYINSA SOON INSHA ALLAH.*

KUYI HKR KWANA BIYU KUNJINI SHIRU WLH JIKINE BANJIN DADINSA FATAN ZAKUYI
MAN UZIRI,ALLAH YAYI MAKU ALBARKA YA KUMA BIYA MAKI BUKATUNKU NA ALKAIRI
AMEEN INA SONKU IRIN BABU IYAKAR NAN.😘😘😘💕💕💕💕🌹🌹🌹


Not edited

40.
Wannan karar dana fasa yasaka gaba d'ayan su kuka runtumo aguje gareni,shashsheka nake
ina dafe da cikina da ya wani irin juyawa............nishi kurun nake hawaye jage jage suna bin
fuskata.......mimi ce a rikece ta d'agoni "kharat lfy maya faru ina Dr bai zo bane ina yasauka me
yace maki." Cikin tashin hankali na dago nakaleta n kalli ummi nace"ummi........numfashina yayi sama
kamar zai dauke daker nace......"yana asibiti hatsari sukai sunce muje da sauri yana gaf da
rasuw.............ban k'arasa maganar ba numfashina ya fizga suduka duk sun gigice afirgice
imran yashigo yana tambayar lafiya,,,,,,,"imran maza maza fiddo mota Dr yayi hatsari wane
asibiti yace ankaishi khairat ki natsu mimi dauko mata ruwa tasha."

Koda na sha ruwan daker ya wuce kuka kurun nake ina shashsheka........"ummi ban sani ba
baigaya man ba,ummi kutai maka man kukaini inson ganinsa ummi banson rashi idan dr ya
mutu yabarni nima mutuwar........"karki sake fad'an haka insha Allah zaitashi bani wayar maza
maza imran sake kira kaji wane asibitine."
Ansa yayi ya shiga kiran number ba jima wa aka dauka,
"Don Allah wane asibitin aka kawo mai wannan wayar."

Mutumen yace"kuyi kokari kuzo yana nan FMB HOSPITAL sai neman makusantanshi yake don
aiki za,a shiga dashi ba lallai ai nasara ba,matarsa yaketa faman kira ita yake son gani kuyi
kokari kuzo kafinan da minty talatin.......wyar ta yanke......tashin hankalin da na shiga bazan iya
kwatan tashiba wani irin rawa jikina yake bansan ma me bakina yake furtawa ba,ga cikina da
yadunkule waje guda ban iya mik'ewa tsaye aduke na isa motar......ummi ke rik'e dani muka
shiga motar dagani sai ita da imran,
Lallashina take sosai har muka isa,,,,,tunda muka doshi emergencybanda karkarwa babu
abunda jikina yake.....yah imran ne yasake kiran wannan mutumen yagaya mashi inda zamu
samai..........ba,a barin kowa shiga d'akin babu inda baya rwa jikina hawayen ma sun k'afe kaf.
Mutumen yayi man iso cikin d'akin.........Idan kaga dr bazaka tab'a iya gane shiba......fuskarsa
tayi kaca kaca babu inda babu rauni,jikinsa gab'a daya nannad'e yake da
bandage...........idanunsa baka ganin komi cikinsu banda jini dake kwance......kuka ya
kubceman "innalillahi wa inna ilaihir raju,un hazbunallahu wani imal wakil,,,,,,,nashiga ukuna
wayyo Allahna dr na kaine haka dr na Allah yasa mafarki nake,Allah ka farka dani daga wannan

mummunan mafarkin,,,,jinai yarik'o hannuna......muryara kanta ta canza ba kajinta yadda ya
kama ta,saida na kanga kunnna saitin bakinsa wanda ansaka mashi oxygen........magana yake
son yayi mni,shiyasa na cire mashi shi.......bakin kanshi babu kyan gani,,,,,

"My love.......ki kula man da yarana,Allah baiyi zamu cigaba da rayuwa tare ba,naso in kasance
dake iyakar rayuwarmu.....amman da alaman burina bazai cimmaba.......kikulaman da abunda
ke cikinki banson hukuncin Allah ba da ya jarabemu da wannan kaddarar,Amman inaji ajikina
zakoyi rayuwa mai kyau.......zaki samu mijin dazai kuka da ke fiye da yadda nakeyi maki,ina
kuma kyautata zaton yadda zaisoki haka zaiso yarana,idan Allah yasaukeki my love in twins din
danake fata kika samu,,,,ina rokon Alfarmar ckinsu kibarwa ummina guda,idan kuma dayane
nabar wasoyyar arubuce nabarmakishi har abadan domin kisamu abun kallo kina tunawa
dani,,,,,kiyi hkr kidaina kuka zakiyi farinciki nan gaba........tari yake kasa kasa kirjinsa yana
d'agawa yacigaba"inarokon ki alfarmar da kidunga man Addua aduk sanda kika kai goshinki
k'asa,my love zan tafi da tsananin kaunarki,zanso ko lahira kizama matata kiyi alkawarin
bazakiyi man kukaba,,,,domin kinsan illar da yakewa mamaci karkiyi man alkawarin
haka........kuka nake ina shashsheka bakina karkarwa yake "Aa Aa Dr na kabar fd'ar haka na
rokeka kadaina cewa zaka mutu,bazaka mutu kabarni ba inhar katafi nima binka zanyi,yazanyi
da kewarka ina zan saka kaunar ka,kataimaka katashi mutai gida kaganifa yaranka najinka
tab'akajisu takai hannunsa saman cikinta.......idanunsa ke kakkafewa yayinda wani uban tari ya
tirnik'eshi babu kakkautawa.....dandanan jini yaringa anbaliya ta hanci tabaki.....afirgice nake
kallonsa yafice daga hayyacinsa likitocin dake kulawa dashi suka iso cikin gaggawa,fita dani
suke ina rizgar kuka,,,,ni subarni naga mijina subarni muyi hirar bankwana......su ummi suka
mik'amani kuka kurun nake ina kiran dr......suna can aka shiga dashi operation don tunda dama
aka kawo masu accident din shine wanda yarayu zuwa yanzu sauran duk babu wanda yarayu.
Don kafarsa guda jijiya kurun ke rik'e da ita dole suka cire ta don bazata tab'a
gyaruwaba,,,,,,akwai wani karfe daya soki hunhunsa sunyi nasarar ciresa tun sadda aka
kawoshi, yanzu aikin cikin zasuyi mashi,aikin yana da had'ari sosai don sai maitsawancin kwana
da rabo yake rayuwa,amman dayawan mutane sun rasa ransu wajen irin wannan aikin.
Nayi kuka har muryata bata fita,su kansu su ummi kukan suke suna share hawaye,,,,,, tun
yamma har dare suna nan suna jiran tsammani har baccin wahala ya daukeni.........su ummi ne
sukajira anfito aikin susan wace akeciki.......tsoranta daya kar dr ya mutu in yamutu ba karamin
tashin hankali khairat zata shigaba,ga cikinta zai iya samun matsala.........likito cin basu fito ba
said wajen karfe d'aya........sunce sukara hkr zuwa safe aga yadda jikin zaiyyi,sun kwantar
masu da hankali sosai sukace suje gida da safe su dawo lokacin ya farka.

Haka mima koma gida har lokacin bacci naked,van farka ba saida mukaje gida.......anan
dadynsu yake tambayar me yafaru nan take sanar dashi halin da ake ciki...........ban iyayin bacci
ba wannan dare tun bayan wanda nafara asibitin,yanzu kuwa ko alamarsa banji saboda tashin
dake kaina......waya mukai da umminsu tace sunana isowa da safe yanzu jirgin zatashi zuwa
shidda na suba sun so.......lallashina take sosai tana kwantarmun da hankali wanda nima nasan
itama tana cikin wanda yafi nawa,saboda ita d'anta ne bata iya sake haihuwar kamarsa,nikuwa
zan iya sake wani mijin.........kuka shine yatayani hira kafin gari yawaye.....saboda kerma har

raui aji aman ba dauba daker nayi sallar asuba na k'agu muje ko naganshi insamu
natsuwa.......zuciyata karkarwa take sadda nafito zamutai jikina kamar ansakani cikin frig
k'arara.......bayadda ummi batai dani ba akan inci wani abu amman nace bazan iya cin komi ba
dole ta rabu dani hada dady muka tai wannan karon a harda Areef. Wanda nakejin wata iri tsanar sa saboda duk shine yayi silar faruwar komi,,,,,,alokacin dabai
bankeniba nasan zan samu dr ya gaya man inda yake aje adaukosa......amman dayake
mugune shi azzalumi gashinan tasilarsa Dr na yasamu mummunan illar dako yarayu balallai ya
zama yadda yake daba........muna isowa kofar asibitin naji wani mummunan fad'uwar gaba ta
riskeni......cikna yawani motsa har saida na dafe marar.
Kamoni ummi tayi na rungumeta inajin jiina amar ansakaman electric.........banda rawa babu
abunda yakeyi.....idona kuwa banda hawaye babu abunda yake fitarwa......ina hango umminsu
da su jalila harda Abbansu durkushewa nai kusadasu ina rizgar kuka........mai tsuma zuciya
d'agoni tayi ta rungume duk da cikina daya turo sosai.......itama hawaue take gogewa su jalila
kam kuka suke sosai itada fati.........adaddafe dai aka gaisa kafin likitan yazo yace "mutun uku
kurun zasu shiga don baison hayaniya..........nida umminsu da Abbansu muka shiga kafafuna
kerma suke hangoshi danai, kuka kurun nake inajin zuciyata tana kakkaryewa........idonsa kurun
yake waje yanzun ma Izzy ne hancinsa da bakinsa........hannu ya mik'oma mu duk muka karasa
gareshi....umminsa kuka tafashe dashi tana cewa,
"Muhd,kaine haka muhd garin yaya innalillahi ya Allah katashi kafad'ar wannan bawan naka
wayyo Allahana idan narasa ka muhd yazamuyi ina zamu saka ran mu muji dadi.......kuka taitayi
Shikanshi Abban kasa magana yayi saidai hawaye dayake sharara daga idonsa.......hannunsa
yasaka daker ya cire oxygen din......muryarsa adishe ta shak'e yace"kudaina kuka ummi,,,,,,,don
Allah ko na mutu karkuyi man kuka hakan zai cutar dani.........ummi koda na mutu nabar
wasiyya arubuce tana dakina cikin drowar na komi na rubuta don Allah ayiman......sannan ina
rokon ku dakuyita yiman Addua,,,,,,,,,kallona yayi yasakarmu wani murmushi zan iya cewa
tunda nake dashi ban tab'a ganin yayi manshi ba,yace"inasonki matata,inasonki zanbarki badan
raina yaso ba,ummi Abba kuyi hkr inata fadan maganganu gabanku,ban da yadda ina iyane
idan ban fad'a yanzu ba banda sauran lokaci dazan sake ganawa da ita........rike hannunshi nai
gagam ina rusa kukana muna cikin haka yafara wata irin shak'uwa.........dandanan na rikice ina
rik'e da hannunsa har lokacin.......aguje likitocin suka shigo,suka roki su Abba dasu fita amman
nace babu inda zanje,,,,,sai dai su dubashi gabana daker da sidin goshi akajani waje kuka
nake kamar raina zaifice.........kowa hankalin sa yayi kololuwar tashi ganin andauki awa guda
babu alamar zasu fito......ina jikin ummina likitan yafito sai uban gumi yake......Abbansu dr ya
fara nufa yajashi gefe amma bama jin mesuke fad'a......Abban mukaga ya silale kasa yadafe kai
nana take naji wani irin duka ga zuciyata.......kaf kaf kaf kawai jikina yake dadunsu yah imran ne
naji yana cewa ma su umminsu dr.

*"sai hkr Allah yayi masa rasuwa......*

Saidai sukajini nazube kasa timmm..........


Mrs bb

Mom muhseen.
Love u my All fans 😘😘😘🌹🌹🌹💕💕💕
[6/28, 2:12 PM] Mom Muhseen: 💕💕💕💕💕💕💕
🌹
*ABIN CIKIN RUHINA*

Writing by mrs bb
Mom muhseen.

Wattpad name
Humaira7531.

DEDUCATED TO ZAUREN MRS BB.

Not edited.

41

Gaba d'aya hankalinsu yayo kaina sadda zasu dagata jinine male male yakebin
kafafunta...........hankulansu suka kara tashi ko kagani wajen kuka yake share share da
hawaye,har su dady hawayen suke........dandanan aka anshita akai emergency da ita........dady
da Abba suka fita don zuwa fara hidimar shirya dr akaishi gidansa na gaskiya............Areef ke
lallashin ummi yana bata baki don shikanshi lokaci lokaci yana share hawayensa,shikenan
Abokinsa ya tafi bai tab'ajin mutuwar data ratsashi irin wannan ba,tausayin khairat ya lullub'eshi
yarinya karama ta zama zajawara,,,ga karamin ciki wane irin ciwo takeji cikin ranta,ai komi tayi
bai wadatar da kuncin da rad'ad'in da zuciyarta kemata,dole zata yake jiki tafad'i............likitoci
uku ne kanta kowa yana aikinsa,domin samun ceto abunda ke cikinta don jinin dake fita idan
yacigaba da fita ba tantama za,a rasa cikin.iyakar kokarinsu suke har Allah ya tai makesu cikin
yadaidaita.....sannan suka shiga nemo numfashinta Amman abun yaci tura,abu guda zai nuna
masu cewar ta da rai shine bugun zuciyarta,inbashi ba babu wata kafa ta jikinta dake nuna tana
da rai.........sunyi mata iyakar abunda zasuyi mata suka kyaleta zuwa wani lokacin.
Koda suka fito daya daga cikinsu yake ma ummi bayani cewar,ansamu nasarar daidaitar cikin
saidai har yanzu numfashinta bai dawo ba,munyi mata allurai insha Allah zuwa gobe ko anjima
da dare numfashin zai iya daidaita,karku damu zata samu lfy shikuma Allah yajikansa."
Areef kurun ya iya ansawa saboda daga unmin dr har ummin yahAreed kuka suke
sosai.........tsawon lokaci sunanan zaune kowa da abunda yake sakawa,,,,,,sun hkr sunbar
kukan saboda yadda yarok'esu kar suyi mashi kuka.........su dady sunzo sun dauki gawar antai
anyi mashi suturra ankaishi gidanshi na gaskiya,sunkira gida sun sanar da rasuwar zuwa safe
zasu juya zuwa nigeria..........jin haka yasa suma su ummi sua koma gida don shirya kayan
su,Areef da imran sun tafi ummin dr da dadynsu sun wuce masauki,ummina ce kurun akabari
tabada sakon asanar da mimi manyan akwatunan su zata shirya masu kayansu,don ita tana
saka ran bama zata dawoba daman don Abbansu yana aiki nan ne shiyasa,to yaringa zuwacan
karshen wata.....kasuwamcinta kuma zata san yadda tai tamayar dashi Abujar....tafison

zamakusada yar uwarta da kuma khairat.

Can cikin dare na farka gaba d'aya nayi losing abunda ya faru,kallon dakin nake ina son tunawa
amman nakasa,idona ya sauka kan ummi dake ta bacci ban tasheta ba na koma na
kwanta,nasan dai na fad'i amman miye dalilin faduwar tawa shine nakasa tunawa........abunda
yasa kuwa shine likitan sukai shawara da Areef kan cewar idan sunyarda zasuyi mata allurar
mantuwa na wucin gadi,yadda za,asamu daidaituwar abundanke cikinta,don muddin ta tatashi
mutuwar zata sake dawo mata sabuwa,kuma cikin yana bukatar hutu da natsuwarta,kuma
hakan zaiyyi wuya karshe arasa cikin,amman idan akai allurar zata manta har zuwa kwana biyu
sannan cikin ya samu sauki don yanzu baida isassar lfy idan tayi abu mai karfi zai iya
fita.........hakan yaa Areef yace suyi mata kawai,yaje yayiwa ummin bayni itama tace ayi hakan
shine samun natsuwarsu,don sun tabbatar tashin hankalin da zata shiga shine nasu tashin
hankalin........kai jama,a mutuwa babban tashin hankalice ubangiji ya kyautata makwancinmu
Amee.

Washe gari ummi ce ta tai maka man nayi sallar asubah,sai dai ta fakaici idona ta share
hawayenta,bayan nayi break da youghout shikadai nasha sannan nayi wanka,riga kawai na zira
kwanta don jikina kwata kwata babu karfi,hakanan nakejin zuciya ta tana kareyewa,,,hawaye
suka ziraromun ina kan cinyar ummin kuka nake can k'asa k'asa.... Batace mun komi ba don
bazasu iya hanani kuka ba. tabbas sadda na farka adaren nan banzan iya tuna komi ba,aman
gari na wayewa komi ydwo ma sabo,jin abunda ummi ke sanar wa da maaah da suke waya
tana gaya mata allurar da akaiman,shiyasa nai iyakar kokarina wajen ganin ban tadawa kowa
hankaliba,kuma ahalin yanzu babu abunda nakejin ina mutuwar so sama da abuna ke
cikina,inajinsa tamkar fitar nufashina shiadaine abunda zan gani inaji sanyi cikin raina,domin
kuwa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
google.com, pub-9213700357025247, DIRECT, f08c47fec0942fa0