Showing 6001 words to 9000 words out of 74145 words

Chapter 3 - Abin Cikin Ruhi Book Compelet Mss Bb

Mrs Bb   

05 Jul 2026

801

shahida sauran yah mujahid yakoma dasu,salma hada kukan ta
bazata tafi ba saida Yah Aree yayi mata jan ido sannan.
Shima d'in bai tafin ba zamanshi yayi duk yadda Anni ke fama dashi yak'iya,dole ta kyaleshi
haka sukai ta zaman zuru har ten thirty,sannan nurse din ta lek'o tace shishiga na tashi,Amman
wani Cikin su yaje doctor nason ganinsa.

Areef ya tafi Anni da Anty shahida suka shiga,

Gaisawa sukai da likitan sannan ya zauna,
Bayani yayi mashi akan abunda ke damunta.
"cewa damuwa ce ta sakar mata masassara sannan da alama ma andoketa ne hada wannan
dalilin yasa fever d'in tayi zafi, sannan dole akula da cin abincinta don bata cin abinci sosai,idan
ba haka ba ciwon ulcer zai iya kamata, ga magani kasiya can phamercy."

Godiya yayi mashi sannan ya fito yaje yasiyo maganin ya jiyo zuwa d'akin da aka kwantar da
ita,jiya ke kamar ya kama dukan kanshi haushin kansa yakeji sosai akan abunda yayi wa
sweetheart d'insa, tsoro yake kar tayi dogon fushi da shi, don yasan halinta akan
rik'o.......sallama yayi Yashiga Ya ajiye magungunan gefe ya kalli Anni,
"lafiya dai ko Anni."

"da sauk'i dai tunda muka shigo ta k'iyiwa kowa magana, sai kuka da take duk lallashin munyi
Amman taki yin shiru."

Kallona yayi nayi saurin kawar da idona, Ina shashshekar kuka k'asa_k'asa yana son lallashin
ta Amman Idan ya yiwa Khairat saku saku babu tantama raini zai shiga tsakanin su, so yake ya
koya mata tsoransa wanda nan gaba baza ringa yi masa taurin kai bah,ya nason bata hakuri

dukan jiya da yayi mata, Amman ya girmansa zai kasance a wajenta ba makawa raina shi zatai,
Wanda shi bazai so haka ba zai nuna yama manta da abunda ya faru, Shan mur yayi wanda
dole idan ta ganshi haka tashiga fargaba...... Cikin dakakkar murya yace,

"jiyo nan nace."

Jiyowar tayi gabanta na fad'uwa yace,
"goge wannan kwallar banzai, me akai maki yanzu da zaki kama yiwa mutane kuka, kin ma
gaidasu tukun koko islanci ya hanaki."

Bani kad'ai ba su kansu sunsha mamakin Areef d'in,don basu tab'a ganin yayi mana irin
wannan kakkausan lafazin, sab'anin y'an kwanakin baya ko fad'a zai mana cikin taushin murya
da lallashi yake yi mana, baison ma wani yaji idan kuwa d'ayan mu tana kuka kamar ya taya ta
saboda baya son kukanmu,amman yau shine ke d'aga mani murya yana kwatsata dole kowa
yayi mamaki katseni yayi da cewa.

"maza ki goge wannan kwallar ki gaidasu Idan kuma na dawo baki saki jikinki kamar da ba nida
ke ne."

Ya maido dubansa ga Anni yace,
"Anni bari naje na kawo maku abun break, zo muje *shidah*."
sunan da shikad'ai yake ce mata kenan.

Fita sukai suka barni da Anni, matsowa tayi jikin gadon da nake ta rik'o hannun da aka cire mani
drip, tana kallona kallon da ban tab'a ganin Anni tayi Mani shiba jinai tace mun.

"y'ar gidan Anni yajikin naki."

idona ya ciko da kwalla nace,
"Anni Ina kwana."

Murmushi tayi tace,
"lafiya lau yajikin naki."

"da sauk'i Anni saidai inda yah ya dokeni jiya Anni ciwo yake mun ko zaki gasa mun."

tausayi ta bata Amman ta danne bata nuna hakan sosai bah tace,
"Ayya sannu kinji bari Antynku ta kawo ruwan zafi sai agasa maki."

"nagode Anni nah ke kad'ai ke sona ko."

Murmushi tayi mata tace,
"Aa y'ar gidan Anni kowa yana sonki, meyasa kikace haka. "

"Anni yah Aree baya *kaunata* yafison salma akaina."

Gabanta ya fad'i meke faruwa haka, Khairat yarinyar da bazata Gaza shekara 13 ba tasan kishi,
danne fargabanta tayi tace,
"Haba y'ar gidan Anni Waye yace maki haka, aduk cikinmu in banda Abbu da Maah babu mai
son farincikin ku sama da Areef."

Hawaye suka zubo mani nace,
"no Anni wallahi yah baya sonah jiya naga haka yau ma naga haka, nidai daga yau babu ni
babushi, Anni kinsan abunda yasa na fad'i jarabawa ta."

Tana kuka take maganar hawaye share_share ga fuskarta,Anni gabanta banda duka babu
abunda yake, sunan Allah kurun take anbata,don wannan lamarin na Khairat to saidai akira
sunan Allah kurun.

sake danne yanayin da take ciki tayi tana yak'e tace,
"Ina jinki y'ar gidan Anni,meyasa kika fad'i exam dinki har kika bari aKai maki repiting."

Wani kukan ta rushe dashi saida tayi iyakar Inda take so sannan tace,
"Anni don Allah karki gaya ma kowa kinjiko idan yah yasani sake dukana zaiyyi."

Ai Anni jitake kamar ta zura Aguje,
(😂😂😂😂 yo baki bari Kiji komiye tun yanzu har kin shiga rud'u.)

"Namaki Alkawarin babu Wanda Zaiji wannan maganar sanar da ni kinjiko."

share hawayena nayi nace,
"Anni tun daga ranar da Abbu yace su Yah zasu tai wata k'asa karatu nashiga cikin bak'in ciki,
kullum saidai na b'oye toilet nayi ta kuka, ko idan naje makaranta inyi, har Cikin dare yi nake
Anni saboda banson ya tafi, gashi maah tace idan suka tafi sai sunyo shekara shidda ko bakwai
zasu dawo, Anni banson yah yayi mun nisa inaji kamar inbishi ko ince karya tafi, Anni kinsan
abunda yake bani tsoro har yasa naki sanar da kowa."

Anni tayi Wata irin zufah duk AC din dake sambad'owa ad'akin kuwa, daker ta had'iye wani
kakkauran miyau amak'oshin ta tace,

"Aa ta Alkhairin Abbu meke baki tsoron."

Sake share hawayena nayi Ina cewa,
"akwai ranar da sweetheart bata je makarantar islamiya ba, malamin mu ya gama mana darasin
sa akan mutanen da ya halitta ka aura, da kuma wanda bai halatta ka aura bah, ban fahimce
shi sosai bah Anni sai na bari da aka tashi naje har office d'in Su nasa meshi nayi masa

tambaya,

"malam don Allah ko mutun zai iya Auren yayansa wanda suka fito ciki d'aya."

Kallona yayi yace Meyasa nai masa wannan tambayar nace,
"wata ce tace na tambayar mata Kai."

Jinjina Kai yayi yace mun,
"Aa Khairat haramun ne babu aure tsakanin su har abadan."

Banjira sauran bayanin sa ba na tashi na taho,
Ko drivern mu banjira ba ranar nataho ina kuka, gida ban bari ko salma tasan me yafaru bah."

"kinsan me yasani kukan Anni."

Kallonta take tana jinjina kaifin tunani irin na Khairat,kafi tace"Sai kin fad'aman."

Wani kukan ya kucce mani Nace,
"Anni ba komi ne ya sani kukan bah illah yadda nakejin yah Areef acikin raina, Anni ni Yarinyace
nasan da hakan, Amman nima ina mamakin yadda akai har nasan *so* Anni bansan tsawon
lokacin da na samu kaina tsundum cikin *kaunar yah Areef* ba, wallahi ban saniba kuka yaci
k'arfina naci gaba da cewa, wannan abun da nakeji yasa nayi ma malam tambaya, sai kuma
naji cewar babu aure tsakani da shi har abadan,kinji dalilin fad'uwata jarabawa na gaza sanar
da kowa saboda dai wannan Abun kunya ne awajen kowa............kuka yaci k'arfina Anni kiyiwa
Allah da manzon sa karki gaya ma kowa, don nayarda dake ke bazaki dakeni ba shiyasa na
sanar dake.........."

Tabbas wannan lamarin ya hargitsa kan Anni, duk ta diririce Lallai Allah mai hikima tunda har
hakan tafaru akwai abunda da Allah ya b'oye,amma Duk da haka yarinyar na buk'atar lallashi da
ban baki,zatayi wannan k'ok'arin Insha Allah.

lallashina take cikin kalamai masu kwantar da hankali,tare da cewa"ki fawwala ma Allah tunda
shine ya sanya maki hakan, kiyawaita sallar dare nasan ki da wannan k'ok'arin,to kici gaba
sannan kiyi yak'i da zuciyarki akan shi kiringa jarumtar danne komi kikeji Akansa, Allah zai yaye
maki kinjiko y'ar gidan Anni,ki rage kuka ki rage taurin kai sannan yanzu so nake ki janye daga
gareshi,ban kuma ce kidaina gaidashi ba Amman kijanye mashi idan bashine yakiraki ba
karkije,hakan zai saukaka maki komi kinjiko y'ar gidan Anni."

"to Anni nah Nagode zanyi Insha Allah daman ina tsoran gaya ma wani ya bigeni shiyasa nace
bari ke in gaya maki, dama na yanke shawarar janye mashi."

Haka taita lallashina har naji duk damuwata ta ragu sosai.

Bajima wa Anty shidah ta shigo da Kayan break tayi mamakin ganina cikin walwala, har ina
yimata dariya ruwan zafin Anni ta had'a ta d'age mun rigata na yi kwanciyar rufda ciki take Gasa
mun, tana cewa ai dole yamaki zafi duba kiga yadda ya fasaki.......tana Cikin gasawar Ya
shigo....... Lumshe idona nayi inajin dadin gasawar.
Gabansa ya fad'i duk ni nayi mata wannan dukan, innalillahi dole kiyi fushi dani
sweetheart,amman afili sai dai yace mun sannu kawai, tunda nace Yawwa ban sake ko kallon
shiba komi Anni tayi mun, brush da wanka ta kuma bani abinci naci, Zuwa can saiga Maah da
Dadyn meenah sai Abbu, sunjima kafin Su tafi sunata tsokana ta.
Har aka sallameni ba muyi wata magana da shiba, haka muka koma gida salma sai nan nan
take Dani, idone nawa kawai.............

Na warke sumul Amman na shigo da Wata sabuwar d'abia ta rashin magana, bana shiga shirgin
kowa haka duk maganar da zakai mun zan tarasu in baka one ansa.

Anni ce kurun nake hira da ita ko salmar na banzatar da ita,duk Inda hankalin Areef yake yakai
k'ololuwar tashi saidai duk maitarka bazaka gane halin da yake ciki bah.

Kwamci tashi ba wuya wajen Allah har Gashi jibine tafiyarsu UK.............

mom muhsen ce
Mrs bb 👌🏻
love u fan's 💕💕�
[5/27, 8:10 AM] Mom Muhseen: 💕💕💕💕💕💕💕💕
*_ABIN CIKIN RUHINA_*

Written by [Mrs bb]

Mom muhsen

*____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S�🏼*
*🇦SSOCIATION�🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*____________________________________*


3.

Alhamdulillah gida ya tsaru iyakar tsaruwa,babban gidane mai fat Kala Kala wanda saboda

girman Abota irin ta su Alhaji farouk yace da Amininsa jafar yazo su zauna tare,har kuka yayi
saboda farin ciki haka suka dawo gidan rana guda, komi sabo aka loda masa yayinda tuni
angyaare ma Inna wancan gidan ba zaka tab'a cewa shine bah.

Rayuwar ta cigaba da kasance masu Cikin jin dad'i da kwanciyar hankali,yayin da Wata irin
shak'uwa mai K'arfin gaske ta shiga tsakanin *AREEF* da k'annensa *khairat da salma* idan
Sun dawo makaranta shine wankansu ya shiryasu ya zubo abinci yaringa basu har sai sun
koshi, sannan assessment d'insu zai zauna ya tusasu gaba yana guarding d'insu yaga Sunyi shi
lafiya lau, Areef saboda k'annensa ko fita baya yayi, Duk nacin *mujahid* haka zai rabu dashi,
haka shahid da shahida Duk yadda suka so Cikin weekend ya ringa binsu shopping sai yace
bazai bisu bah, saboda suna cin zalin sweetheart dinshi,dole sukai hakuri saidai driver ya kaisu
shikuma Ya ware rana ya kaisu da kanshi.........wata guda kenan da kammala secondary
d'insa,tunda twince suka girma Maah ta hana yaringa masu wanka da shiryawa,tunda yanzu ko
wacece zata iya yiwa Kanta wanka da shiryawa, yanzu suna js one yayinda shahid da shahida
Suke ss2, Muhajid tare sukai graduation da Areef, Neenah ce take js3.

Shirye shiryen tafiyar Areef da Muhajid ake zuwa UK jamia,wanda idan suka tafi baza su dawo
bah sai Sunyi har masters d'insu........

Motarsu na tsaya wa suka fito Aguje suna kyalkyata dariya,kowa so take ta riga y'ar uwarta isa
cikin gida wajen yah Areef kafin Su shiga saiga su sun fito shida mujahid Aguje sukai kanshi,
dariya suke masu shida mujahid......kafin ya ankare *salma* ta mamuk'eshi tana dariya har da
yiwa *khairat* gwalo aikuwa me zatayi banda kuka, bilhakki da gaskiya ta shige gidan tana rera
kukan shagwaba,duba Maah tayi bata ganta ba yasa ta nufi b'angaren Anni tana shiga sukai
kacib'is Anni ce ta tatareta.

"lalalala kairyn Anni waya tab'aki zo zo taho muji."
Ta jata jikinta Maah tace,
"Uhm bai wuce rigirmarsu ita da salma, yanzu haka riganta tayi isa wajen Areef."

Annin tace,
"wai haka ne yar gidan Anninta."
Wani kukan ta sake fashe wa dashi tana cewa,
"Anni kingani salma ko, kullum sai ta ringa rigana wajen Yah Aree,kuma nace mata yau ta
barmun in rigata shine ta k'iya,gasu can suna mun dariya."
..........ta sake rushewa da kuka.

Dariya Maah tayi tace,
"ai na gaya maki kullum rigimar kenan, salma ta rigani,salma ta rigani tunda ke lusara ce komi
babu hanzari,ba dole komi salma ta rigaki ba ko wanka da shiryawa sai bakina yayi tsawo kike
gama wa inhar Areef baya nan."

Anni zatai magana Areef ya shigo rik'e da hannun salma, har tayi wanka da ga dawowar ta ga

lollipop nan Areef ya bata tana ta sha.

"Ayya sweetheart gamu munzo biko,ke baki yin zuciya kiringa riganta kema, Amman kullum sai
Kinyi kuka, Kinga zo zo mu shirya."

Maah dai ficewa tayi tabarsu Inda sabo sun saba wannan fad'an basu wuce d'an lokaci kad'an
sun shirya.

Anni ta mik'e tace,
"sorry y'ar gidan Anni kije yayanku zai shirya ku,sanan kiyi wanka anjima ma zaku rakani
unguwa."

Salma tace,
"Anni irin wannan gurin da kikaje damu rannan,har aka bamu chocolate."

Dariya tayi tace,
"shazumamu sarkin Shan zaki bacan ba,wani wajene kama hannun y'ar uwarki kuje ki taya ta
shiryawa. "

Kan ma salma ta iso wajenta ta fashe da kuka,
"ba zanje wajensu bah."
Ta ruga can cikin gidan Annin ta barsu sake da baki."

Don irin hakan bai tab'a faruwa ba, Duk yadda suka b'ata da juna to kafin anjima sun shirya
kansu, ko kuma wata sa, in Yah Aree ya shiryasu.

Salma tace kamar zatayi kuka, don idan sukai fad'an duk rud'ewa take ko kau itace aka kwara.
"Yah Kaga sweetheart ko."
Idonta ya cika da kwallah
Murmushi yayi ya d'an sunkuyo yace"kar kidamu my Angel, sweetheart dinki zata huce zo muje
muci abinci."

Anni tace,
"zan lallasar maki ita kinjiko salma yar albarka."
D'aga Kai tayi tana sake goge kwallarta,janta yayi suka fita, Annin ta wuce wajen Khairat d'in.

💕💕💕💕💕💕💕💕

Wasa wasa Khairat ta k'i shirya wa da salma, haka Shima Areef d'in ta daina shige masa,tama
koma gaba d'aya wajen Anni bacci ne kurun yake maido ta cikin gidansu, hakan ya saka salma
cikin damuwa saboda tunda suka taso irin haka bata faruwa tsakaninsu.
shi kanshi Aree ya shiga damuwa ba kamar k'iriniyarta da tsalle tsallenta, da rigimar ta.

Amman duk yadda yaso ya jawota jikinsa ta k'iya,don da ya tunkarota zata fashe da kuka,dole
zai barta don subiyun baya son kukansu.

shahida ce ta sameta b'angaren Annin tace tazo Yah Aree yana kiranta,
Dole tataso suka taho shahidar nayi mata fad'an fushin da take da salma, wadda gata can bata
da lafiya saboda taurin kanki Khairat.

Cikin muryar kuka tace,
"da gaske kike Addah."

"gata can ma tak'icin Abinci har yah Aree yayi yayi Amman ta k'icin komi. "

Aguje ta k'arasa cikin gidan falon farko ta same su,
Zube wa tayi gabanta tana kuka tace,
"sweetheart Miye haka, don kawai Ina fushi shine zaki wani sheme kina wani pretending,kinga
ki tashi na huce bazan sake fushi da sweetheart d'ina ba,tashi kici kinjiko inhar baki son na
cigaba da fushin."

Kamar almarah haka suka ga salma ta Mike tana cin abincin,suna hirar su cike da so da kauna.
Areef wani sanyi yaji don ko kad'an baya son fushin ko wace cikinsu.
Cikin k'an k'anen lokaci komi ya daidai ta, saidai fah Khairat ta canza salo ta daina shigewa
Areef, ko assignment ne ta k'asa yah mujahid shine zata je ya koya mata, ta daina rigima da
salma akan Areef, ko k'iriniyarta da take masa ta daina Magana ma sai ta Kai makura take
masa........gashi lokacin tafiyarsu ya taho don yanzu bai wuce 2 weeks masu zuwa.
Amman gefe guda Khairat kullum cikin lissafin tafiyar take, duk kwanan duniya sai tayi kuka
ahankali ta fara ramewa duk ta fice hayyacinta,haka akai jarabawa tashiga js3 aman saboda
rashin maida hankali saida aka mata repiting......wannan dalilin ya jawo b'atawar *Khairat da
Areef*

Taufah ana wata ga wata.

Mrs bb ce
Mom muhsen [5/27, 8:10 AM] Mom Muhseen: 💕💕💕💕💕💕💕💕
*_ABIN CIKIN RUHINA_*

Written by [Mrs bb]

Mom muhsen ce

*____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S�🏼*
*🇦SSOCIATION�🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*____________________________________*


6.

Nasan da labarin tafiyar su Amman ko Anni ban nuna ma halin da zuciyata take ciki ba, tabbas
inajin babu dad'i ba kamar jin danai wai salma zata yi masu rakiya har can, ita da Abbu da
Dadyn meenah.

Wanda da sanda ana maganar tafiyar Abbu cewa yai hada ni za,a rakiyarsu shine yanzu don
banyi k'ok'ari ba za,atai abarni basu san yanzu duk abunda zai had'ani da Yah Areef ba bana
sonsa, ko sunyi mun tayin zuwa zance bana zuwa.

I think kun san yadda feeling d'in missing yake, Wanda da kaji wannan yana yin gara kayata
rusa kuka, to haka Khairat takeji,duk yadda taso yin kukan abun yayi mata wuya saidai zafin da
takeji cikin ranta, haka tak'i bari Anni ta fahimci komi akan tafiyar tasu,wanda hakan halin
Khairat ne inhar bakaso gane abu ba is hardly ka fahimci yana yinta.
tana kwance kan gadon meenah wanda yanzu d'akin ya koma nasu su biyu,karatun English
novels nake na soyayya, jin abud'e k'ofa yasa nayi saurin b'oyewa don yah mujahid ya hanani ni
kuma sun shiga jikina bazan iya daina waba.
Ganin salma ce yasa nafiddo naci gaba daga Inda na tsaya, suna rage mun k'uncin da nake
ciki,zama tayi kusa da ni ban kulata bah ganin kuma ba kulatan zanba yasa tace,

"sweet............"
Katseta nayi da cewa,
"pls idan kinsan takura ce ki barni don Allah."

Shiru salma tayi don iya wuya yau Khairat ta kai salma, wannan halin ko inkulan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
google.com, pub-9213700357025247, DIRECT, f08c47fec0942fa0