Showing 30001 words to 33000 words out of 73884 words

Chapter 11 - Dangartakar Zuci Book Compelet

01 Sep 2026

507

sai da safe, dan gobe ne xa'a kai amarya gidan mijin ta dake Abuja.


Fitar ta a mota ta fara yima Safwan bye bye, duk a idon Yah Abdullah , Cikin sauri Husna ta
nufi part d'in su dan chanja kaya dan taji alamun period dinta yaxo, tana shiga corridor d'in da
xai billa da ita dakinta taji an rike hannunta, xatayi ihu taji an tushe bakinta, sosai ta tsorata ta
fara kiciniyar kwatar kanta. Jin kamshin turaren Yah Abdullah yasa hankalinta ya kwanta. Yah
Ibrahim ka cikani please, cikata yayi ya xuba mata mayattatun idanunsa da suka rine, cikin
sarkewar murya ya fara magana.

"Husna ashe dama akwai ranar da Allah xai nuna mini kina tarayya da wani bayan ni, duk
soyayyar da muke wa juna ina chan ina fama da sonki amma Husna ashe kina nan kin
mallakawa wani xuciya ki? Husna ina sanki, wallahi baxan iya rayuwa ba idan bbu ke........"
"dakata Yah Abdullah , kasan me kake cewa kuwa, aure ya riga ya haramta tsakanina dakai,
Ilham itace matar ka, ita take bukatar kulawarka, ita take bukatar ka firta mata wadan nan
dad'ad'an kalaman ba Husna ba, Yah Abdullah ban taba son wani d'a namiji ba sai kai, ban taba
mallakawa kowa zuciyarta ta ba sai kai, akanka na fara so, naso ace munyi aure dakai, sai dai
kaddara ta riga fata, "hannu tasa ta share hawayen ta," Safwan malami nane, kuma yana debe
min kewar rashin ka," please Yah Abdullah , ka manta mun taba soyayya dakai, ka rungumi
matarka ka bata kulawa please" fashewa tayi da kuka ta wuce ciki tabar Yah Abdullah a tsaye,
gaba d'aya jikinsa ya mutu, sosai ya hango zallar kaunarsa a idon Husna, sai dai yasuyi, hajia
maamaa ta gama cutarsu, ta tarwatsa farin cikin su.


Husna na shiga daki ta baje akan bed dinta ta fara kuka mai cin rai, soyayyar Yah Abdullah
ce take nukurkusarta, shi yasa tunda ya dawo taki yarda su hadu, sai da tayi kuka mai isarta
sannan ta nufi toilet.
Washe gari

An kai amarya Ilham dakin mijin ta bayan nasihohi da fad'a da itayenta sukayi mata, shima
Yah Abdullah yasha nasiha akan ya rike Ilham bisa amana, ya manta duk abinda ya faru, hajia
maamaa harda kukan farin ciki wai yau burinta ya cika,(ni da sister mukace kaji wannan
tsohowar, suna kukan bakin ciki tana kukan murna) lol. Sosai nasihar ta ratsa Yah Abdullah ya
kuma dauri aniyar kula da Ilham.

Husna da Safwan kam ana tare, dan har Abuja shi yakaita dasu rauda, sosai soyayyar da
Safwan ke nuna wa Husna take basu mamaki, lallai Husna tayi sa'a, Allah yayi mata chanji na
alkhairi, dan suna ganin indai ta auri Safwan to tagama mure jin dad'in dunia sai dai ta nemi
lahira. Soyayya da shakuwa tayi malemale a xuciyar masoyan, har suna jin baxasu iya rayuwa
ba batare da juna ba.





Sumayya salees sadeeq
&
Aishat A Muh'd
[25/07, 09:36] Aishat A. Muhd: 🍃 *DANGARTAKAR ZUCI*🍃



*written by*
Aishat A muh'd

*&*

Sumayya salees sadeeq




*Page 43-44*



Haka rayuwa ta cigaba da tafiya har akayi wajen wata uku da bikin Yah Abdullah da Ilham,
yanxu husna ta cire Yah Abdullah gaba d'aya a cikin xuciyar ta soyayyar su kawai suke xuba wa
da safwan din ta, a yanxu kusan kowa na gidan yasan da soyayyar safwan da husna kuma sun
amince dashi sosai saboda mutum ne na gari ga hankali da nutsuwa, mamee taji dad'in ganin
shi a matsayin wanda xai auri erta.

Ana cikin hka safwan ya sanar da husna ta fad'a wa su dady xai turo iyayen su ayi magana,
husna bata yi k'asa a gwiwa ba ta sanar da mamee maganar ita ma mamee ta fad'a wa daddy a
lokacin da ta sanar dashi a lokacin yana kok'arin shiga part d'in hajia maamaa don hka bayan
ya shiga part d'in ya tarar da yayun shi Abba 1 da Abba 2 bayan sun gaisa sai yake cewa
"maamaa daman yaron da yake son husna na ne yake son ya turo iyayen shi "

Cikin rashin fahimta hajia maamaa tace "wane yaro kuma daman husna ta tsayar da wanda
xata aura ne? "

"Ehhh tabbas mun sha gaisawa dashi yaron yana da kirki malamin su ne ma" Cewar Abba 1
wato abban su Yah Abdullah.

"Humm ae kuwa abin baxai yiwu ba saboda husna na riga da na xa6a mata wanda xata aura
kuma kada wanda ya fad'a mata, su dai iyayen yaron xaku fad'a wa Idan lokaci yayi kowa xai sa
ni " Cewar hajia maamaa

Abba 2 wato abban su ilham yace "Haba maamaa taya xa'a yi mata hka da farko suna soyayya
da Abdullah kika k'i aura musu juna kuma tayi hak'uri da hkan Har ta dad'a xa6ar Wanda xata
aura a karo na biyu don Allah ki barta ta auri wanda take so"

"kaiiiii mustapha " hajia maamaa ta daka mishi tsawa sannan ta cigaba da cewa "sam kada na
k'ara jin wad'annan maganganun a bakin ka ina da ikon da xan xartar da komai a kan ku don
hka na riga da na yanke hukunci "

Cikin ladabi Abba 2 yace "Allah ya huci xuciyar ki yi hak'uri Allah ya sa hkan shi yafi alkhairi
Allah ya bata hak'urin jure wa"

"Ameeen " suka amsa a tare sannan daddy yace " ibraheem ya fad'a muku last month d'in nan
xai dawo "
Tuni fuskar hajia maamaa ta fad'ad'a da fara'a sosai tace "Masha Allah yau ba mu yi waya ba
shi yasa Allah ya dawo mana dashi lafia"

"Ameeen maamaa "
Daga hka suka cigaba da hira wani xuwa wani lokacin sannan kuma suka tashi suka nufi
6angaren nasu da yake weekend ne, lokacin da daddy ya fad'a wa mamee abin da suka
tattauna da hajia maamaa da en uwan shi sam mamee bata ji dad'in hkan ba ta so ace wannan
Karon an bawa 'yar ta damar xa6an mijin aure,amman bata da abin cewa sai dai addu'a kawai.

Bayan k'wana 2 da hkan iyayen safwan suka xo sun samu tar6a sosai a wajen su Abba bayan
an gaisa sun ci sun sha sannan suka bijiro da buk'atar su ta neman aure, nan su Abba suka
fara da basu hak'uri sannan suka fad'a musu anyi mata miji amman ita yarinyar bata ma sa ni

ba, hka suka baro gidan cikin sanyin jiki suna tunanin sanar da safwan wannan mummunan
labarin.

Da murnar shi ya tari iyayen nashi da suka dawo amman ganin damuwa akan fuskar tasu ya sa
jikin shi yin sanyi nan dai suka daure tare da fada mishi kafin su ankara sai ganin safwan suka
yi ya dafe xuciyar shi tare da lumshe ido xai fad'i baban shi ya taro tare da fad'in
"SAFWAN!"

Da k'arfi ya furta hkan cikin wani irin yanayi safwan yace "na'am Abba na ina rok'an ka ka
taimaka min kada na rasa husna ina son ta xuciya ta xafi take min sosai "

Sai ga hawaye yana xuba a idanun safwan wani mugun tausayin shi ne ya kama abban shi da
mahaifiyar shi nan fah suka dunga rarrashin shi tare da bashi hak'uri dak'yar hawayen suka dai
na xubo wa sai kukan xuci yake don shi kad'ai yasan abin da yake ji a cikin xuciyar shi yana son
husna ba Kad'an ba ashe ba rabon shi ba ce an bawa wani ita, hka yayi ta sumbatu sai dak'yar
bacci ya d'auke shi, iyayen nashi sunyi jugum jugum basa son damuwar d'an nasu ko Kad'an.


Cikin k'wanakin nan safwan ya rame sosai abin gwanin ban tausayi ko abincin kirki baya iya ci
kullum cikin tunanin yanda xai rabu da husna yake, gashi ko kiranta yak'i yayi a waya.

Ganin k'wana 2 safwan shiru bai Kira ta ba yasa hankalin husna ya tashi sosai nan ta kirawo shi
awaya yak'i ya d'auka tuni hankalin nata ya k'ara tashi sosai ta rasa yanda xatayi K'arshe tana
kuka ta fad'a wa mamee safwan ko lafia baya d'aukan wayar ta, kallon tausayin 'yar ta tabi
husna dashi baxa ta iya fad'a mata K'arshe rarrashin ta tayi.

Ko dayaushe cikin kiran safwan take shima nashi 6angaren kasa daure wa yayi ya d'auki wayar
bai 6oye mata komai ba ya sanar da ita duk abin da yake faruwa husna batasan lokacin da ta
yar da wayar ba da gudu ta fice daga d'akin nata.............





Aishat A muh'd

*&*

Sumayya salees sadeeq
[25/07, 09:37] Aishat A. Muhd: 🍃 *DANGARTAKAR ZUCI*🍃

*written by*

Aishat A muh'd

*&*

Sumayya salees sadeeq




*Page 51-52*




Cikin wani irin xafin nama Yah Abdullah da Yah ibraheem suka yi kan husna kowanne yana
kok'arin d'aukan ta don bata agajin gaggawa, Yah Abdullah ya riga ibraheem xuwa inda husna
take har ya kai hannun shi da niyyar d'aukan ta sai ji yayi Yah ibraheem yace

"stop it now Yah Abdullah "
Da sauri kuma cikin mamaki Yah Abdullah ya d'ago kanshi yana kallon k'anin shi kallo d'aya
yayi wa ibraheem ya karanto tsantsar kishi a cikin idanun shi don hka sai ya matsa gefe ya fad'a
tunanin daman ibraheem yana son husna kenan tun da gashi har ya nuna mishi kishi don xai
d'auke ta kuma wannan kishin da ya karanto a fuskar ibraheem ya tabbatar sai ana yiwa mutum
mugun so ake nuna kishin nan, daman ibraheem yana son husna to ina tsanar da yake mata,
shi kad'ai dai Yah Abdullah yake wannan tunanin.

Yayin da ibraheem kuma ya tsugunna saitin kan husna ya sa hannun shi yana gyara mata
gashin kanta da ya barbaxu har xuwa fuskar ta ya kura mata ido yana kallon ta kawai.

Ganin shi yak'i d'aukan ta ya d'ora ta kan bed don mamee ta duba ta kuma yak'i bari wani ya
d'auke ta ya sata a gaba yana kallon ta kamar wanda bai ta6a ganin ta ba.

"Haba ibraheem d'ina me ka tsaya yi maxa ka d'ora ta kan gado Xahra ta dubata tun da ka k'i
Abdullah ya d'auke ta "

Cikin nutsuwa yasa hannayen shi duk biyun ya d'auke ta sai da ya had'a ta da faffad'en kirjin shi
sannan cikin takun tafiyar shi ta kasaita ya k'arasa kan bed d'in hajia maamaa ya kwantar da ita
a hankali ya sa pillow ya d'ora kanta sannan ya dad'a tattara gashin nata ya samu waje ya
xauna kusa da ita a gefen gadon ya kamo hannun ta yana yana murxa tsakiyar tafin hannun
nata.

Kowa ya xuba ido cikin matuk'ar mamaki ake kallon ibraheem yanda yake yiwa husna tsana da
amman gashi har yana wani lalla6a ta (ni da sister sumy muka ce ae yanxu ma aka fara
wannan so min ta6i ne).

Da hka kuma hajia maamaa tace kowa ya fita daga bedroom d'in nan en uwa suka fita gaba
d'ayan su daga mamee sai ibraheem da hajia maamaa wadda take cikin tashin hankali lokaci
xuwa lokaci tana share kwallar idon ta, cikin k'ware wa mamee ta duba husna sai Dr ibraheem
ya xama d'an kallo kamar ba likita ba, nan mamee ta gama duba ta har tayi nasarar samun
numfashin ta ya dawo dai dai sannan tayi mata allurar bacci daga K'arshe tayi mata dressing
din ciwon da taji a goshin ta tana gama wa ta nufi hanyar fita daga d'akin da sauri hajia maamaa
tace

"zahra baki mana bayanin halin da take ciki ba xaki fita "
Dawowa cikin d'akin tayi cikin dauriya mamee tace "maamaa ba wani babban matsala ba ne
suma tayi sai kuma ciwon da taji a goshin ta amman Insha Allah xuwa nan da yamma xata farka
qlau "

"Alhamdullilah ngde wa Allah sai yanxu naji hankali na ya kwanta "

Cewar hajia maamaa ita kuwa mamee dafa kafad'ar ibraheem tayi tare da cewa " ibraheem ka
ban kunya sai kace ba jarumin namiji ba kana ganin matar ka a wannan yanayin ka kasa duba
ta duk ka wani firgice "

Murmishi yayi tare da sosa kai yace "ae ni mamee namance dani likita ne ma sai yanxu na tuna
tsabar rud'ewa ni wlh har tsoron tashi nake tayi kada ta sake ji wa kanta ciwo mamee"

Ya K'arasa fad'i cikin yanayin sanyin murya cikin tausayin shi tace "kada ka damu ibraheem
Idan ta farka xamu yi magana da ita kuma Insha Allah komai xai wuce amman sai kayi hak'uri"

"okay mamee Allah ya huce xuciyar ta Kafin ta tashi ma"

Er dariya mamee tayi kawai ta fice daga d'akin daman hajia maamaa ta shige toilet don rage
cikin ta don ba k'aramin firgita da rud'ewar ciki ta samu ba sai yanxu tukunna ta samu nutsuwar
rage cikin nata.


Ya kasa sakin hannun ta idanun shi ya xuba mata yana kallon ta cike da mamakin yanda husna
ta koma wannan ba don yayi saurin fallasa abin da yake xuciyar shi ba da tuni dakon son da
yake mata ya tashi a banxa ba lallai ya aure ta ba, don tun Kafin ya tafi England karatu ya sanar
da hajia maamaa ta rik'e mishi husna ta kular mishi da ita don ita tashi ce shi yafi dace wa da ita
fiye da kowanne namiji.

Yayi xurfi a tunani yaji muryar mumy akan shi da sauri ya dawo cikin hayyacin shi ya d'ago kai
ya kalle ta harara ta watsa mishi tare da cewa "sai ka tashi ka bata waje tasha iska ka wani xo
ka tsare ta da ido sai ka farkar da ita lokacin tashin ta bai yi ba "

"sorry mumy nah bari na tafi "
Ya fad'i hkan yana tashi tsaye bai gama mik'e wa ba sai ya rankwafo da kanshi saitin fuskar
husna ya sumbace ta a saman goshin ta kumatun ta da kuma saman tsakiyar le6en ta sannan a
Hankali ya furta

"i luv u so much my dear husna Allah ya baki lafia "

Sannan ya K'arasa mik'e wa kallon mumy yayi yaga ta xuba mishi tana kallon shi d'an d'aga gira
yayi yana cewa "mumy what wrong wannan kallon fah? "

"amman ibraheem baka da kunya a gaba na kake hka? "

Rungume ta yayi yana cewa "mumy idan banyi a gaban ki ba a ina xanyi "

"ina ruwan ki ba Matar shi ce ba ya biya sadaki an d'aura " Cewar hajja maamaa kenan bayan
ta fito daga toilet d'in, girgixa kai kawai Mumy tayi Sam hajia maamaa bata ganin laifin ibraheem
akan komai bayan shi ta ke bi wannan kaunace da kulawar da take bashi tun ran da aka haife
shi.
"Ya kamata kaje ka yi wanka ka kwanta ka huta don nasan ka gaji"
Cewar hajia maamaa kenan tana xama kan bed d'in.

"Okay maamaa ki kular min da mata ta sosai "
Fad'in ibraheem yana kama hannun mumy "kada ka damu khaleelu na "fad'in hajia maamaa
tana murmishi, daga hka suka fice daga d'akin.

Part d'in su suka tafi bayan ya shiga bedroom d'in shi wanka yayi tare da shirya wa cikin wani
3quater yellow da white d'in t-shirt mara hannu bayan ya fesa perfumes ne ya sha coffee d'in da
mumy ta kawo mishi Sannan ya kure speed di'n AC ya kwanta kan katafaren gadon shi tuni ya
lula tunanin husna yasan ba k'aramin fad'a xa'a sha da ita ba don shi kanshi yasan ta tsane shi
kuma shine da kanshi yasa ta tsane shi din yasan yayi kuskure kuma xai gyara kuskuren da
yayi Insha Allah, da hka bacci 6arawo ya d'auke shi daman kuma a gajiye yake sosai tun da ya
diro nigeria bai huta ba sai yanxu.


Yamma nayi aka fara shirye shiryen kai amare gidajen su amman ban da husna wadda take
kwance har yanxu tana bacci sakamakon allurar da akayi mata don hka Fadila da raudah basu
samu damar yin sallama da husna ba aka mik'a su gidajen su sun sha kuka sosai abin gwanin
ban tausayi, ana dawo wa daga kai su nan en uwa suka fara tafiya gidajen su na kusa kusa

kenan xuwa mangarib gidan yayi shiru babu hayaniya sosai don an ragu da yawa sosai kuma
part d'in saukar bak'in shi ne na K'arshe daga baya duk suna ciki suna huta gajiyar biki don an
gaji kuwa.


Mumy ce a tsakiyar palo tana tsaye da wani madaidaicin cup a hannun ta tasa spoon tana juya
wa sai ga ibraheem nan ya fito daga d'akin shi har ya sake wanka ya canja kaya xuwa black
jeans nd T-shirt pink mai gajeran hannu kayan sun matuk'ar amsar jikin shi yana ta xuba
k'amshi kan nan nashi yasha gyara da sajen nan sai kyalli yake yi murmishi ya saki wanda yake
k'ara fito mishi da ainahin Kyan shi ya k'arasa wajen yana cewa

"mumy nah me xan samu I'm hungry wlh sai dai bana son abinci mae nauyi "

Ita ma mumy cikin murmishi ta ce "fad'i abin da kake so son, amman Kafin nan shanye wannan
abin "

Ta k'arasa fad'i tana mik'a mishi cup d'in hannun ta kar6a yayi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
google.com, pub-9213700357025247, DIRECT, f08c47fec0942fa0