Showing 60001 words to 63000 words out of 73884 words

Chapter 21 - Dangartakar Zuci Book Compelet

01 Sep 2026

508

aure, abba, abduljabbar, abdulkareem,
Dr muh'd ,Aminu,saleem da na'eem da ameer gaba d'aya ankon tsadaddiyar farar shadda suka
yi har da babbar riga sun yi matuk'ar yin kyau ga wani kwarjini da suka yi fuskar su d'auke da
tsantsar farin ciki sai faman gaisa wa suke da wad'anda suka hallaci wannan d'aurin auren,
bayan an gama d'aurin auren suka wuce yin reception na maxa an ci ansha a wurin sun sha
addu'a daga bakunan mutane na xaman lafia da xuri'a mae albarka haka aka watse kowa cike
da farin ciki.

Cikin gidan nan ya cika da mutane sosae en uwa da abokan arxiki sai taya su umma ake murna
tare da yiwa amare fatan alkhairi Allah ya bada xaman lafia.

Nauwara, fa'iza, jiddah, aunty asma'u, aunty kausar, aunty maryam da suna xaune a bedroom
d'in su nauwara kowanne yasha kwalliya ta Kece raini dukkan su fuskar su d'auke da Murmishi
sai hira ake suna cikin haka abduljabbar da abdulkareem suka shigo d'akin a nutse aunty
asma'u ce ta Kalli abduljabbar wanda yake sa6e babbar riga tana xamo wa yana sake gyara wa
alamar bai saba da sawa ba ae kuwa ta kyalkyale da dariya tare da cewa
"Allah abdul kaji kunya yanxu ace babbar rigar ma har yanxu baka iya sawa ba an fah girma "
Harara ya watsa mata tare da jan wani d'an siririn tsaki yace
"kin fiye sa ido da yawa asma'u ba wanda ya kula da hkan sai ke Allah ki fita a idona "
Ya K'arasa fad'i yana huro hanci abdulkareem wanda yake danne dariyar shi yace
"waii ke ina ruwan ki ne asma'u Indai ki ga wannan d'an nawa sai kin tsokane xan fa d'au mataki
akan ki"

"heeeeyyy lallai ma abdulkareem din nan Indai wannan abduljabbar d'in kake tare wa wataran
sai ya mun ganku a rana"

Gaba d'aya d'akin aka kwashe da dariya har da nauwara sai da ta murmusa shi kuwa uban
gayyar had'e fuska yayi tare da cewa
"ya xa'a yi ki dunga yi min magana kowacce iri ce a gaban kannen salon su rainani "
"Ahayyeee su raini manya dad'in abin kai di'n k'anina ne "

Ko kula ta bai yi ya nufi inda nauwara take a xaune a gefen bed jiddah wadda take kusa da ita a
xaune ya wani d'auke kai cikin isa yace
"hey d'an ban wurin naji dumin mata ta"
Dariya jiddah tayi tare da tashi da sauri tana cewa
"ni bari ma na bar maka d'akin kaji d'umin da kyau "
"Yawwa da kin kyauta er k'anwa ta su wad'annan en sa idon sai sun ga kwakwaf "
Tana dariya ta bar d'akin tare da fa'iza, kausar ta mik'e tsaye tana cewa
"ni fah yunwa nake ji ko breakfast ban yi ba ni ma nayi nan "
Tana gama fad'in hka ta fita daga d'akin tana kunshe dariya, xube wa yayi kan bed d'in tare da
fad'in "Washhh na gaji wlh da ni d'an gata ne da sai ayi min tausa"
Ya fad'i yana kallon fuskar nauwara wadda ta had'e fuska, aunty asma'u ma tashi tayi tana
cewa

"toh mara kunya so kake dai na bar d'akin, ba don nauwara ba da Allah ba Inda xan je sai dai
duk abin da xaka yi kayi a gaba na"
"Ahhh ae da Kinyi xaman ki waya kore ki sarkin sa ido "
Abduljabbar ya fad'i yana dariyar mugunta wani k'aramin pillown ta cillo mishi ya cafe yana
dariya sannan ta fice daga d'akin abdulkareem ya Kalli maryam yace
"my wife taso mu tafi ya yiwa kowa kora da hali tun Kafin ya kore mu ma "

Yana shafa kanshi yace "ni kada ka had'a ni da maryam ni bance kowa ya tafi ba "
"ae gwara mu baka wuri "
Maryam ta fad'i tana kamo hannun abdulkareem suka fice daga d'akin aka bar nauwara da
abduljabbar.

Tashi daga kan bed d'in nauwara tayi tana shirin ban mishi d'akin da sauri ya rik'o hannun ta, ta
juya da kanshi tana kallon shi shima ita yake kallo cikin marairaice fuska yace
"Haba habibty wai har yanxu baki hak'ura ne? "
Turo baki tayi kafin tace "ni ka cika min hannu ina da abin yi please "
Bai ce komai ba ya janyo ta tare da xaunar da ita kan bed d'in shi kuma ya tsugunna a k'asa
tare da dire gwiyoyin shi k'asa yana rik'e da hannun ta idanun shi akan fuskar ta cikin nutsuwa
yace
"gani a durkushe a gaban ki a karo na biyu baxan tashi anan ba har sai kin hak'ura na gaji da
wannan yanayin da kike nuna min baxan iya jure wa na gaji da axabtar dani da kenan ina sake
baki hak'uri "
Wani irin mugun tausayin shi taji ya kamata tare da wani mugun son shi da ya k'ara shiga cikin
xuciyar ta duk jikin ta yayi sanyi sosai bata ankara ba ta ga wasu hawaye suna fita a idanun shi
suna sauka akan hannayen ta da yake rik'e dasu, toh me yasa baxa ta hak'ura ba wacce irin
xuciya ce da ita mutumin da shi ya taimake ta a rayuwa ya cece ta daga fyad'en da akayi
yunkurin yi mata ya kai ta asibiti ya nema mata magani ta warke ta dawo tana tafiya tana kallon
mutane da idanun ta kamar kowa ya sata a makaranta har takai matsayin da ya nuna mata so
da k'auna ya aure ta har Allah ya basu albarkar yara 2 kaddara da sharri yasa ya rabu da ita
gashi gaskiya ta bayyana yayi nadama tare da Bata hak'uri ae ya kamata ta hak'ura kuwa ko
Allah Muna yi mishi laifi mu rok'e shi ya yafe mana balle kuma mu en Adam don hka cikin jin
tausayin shi murya a sanyaye tasa hannu ta goge hawayen fuskar shi tare da cewa

"Don Allah ka daina xubar da hawayen ka please "
"baxan dai na Idan har baki hak'ura ba"
Ya fad'i hkan yana sake rik'o hannun ta gam a cikin hannun shi a hankali ta fara cewa
"na hak'ura Yah abduljabbar daman ae d'an ajixine, ni tun tuni na yafe maka amman ina son
gaba kada dunga bincike Kafin ka yanke hukunci "

Cikin tsananin farinciki yace "nauwara da gaske kin hak'ura? "
Cikin jin tausayin yanda duk yabi ya rud'e cikin tabbatar wa tace "da gaske nake Allah ya yafe
mana gaba d'aya "
Da sauri ya rungume ta tsam a jikin shi tare da cewa "Ameeen thank u habibty nah, kuma

Insha Allah xan kiyaye gaba "
Ya cigaba da cewa "i luv u baby nah i really miss u "
Duk gaba d'aya ya rikice mata da godiya a hankali ta lumshe idon ta hawaye suna xuba a idon
ta wanda bata san name ne ba na farinciki ne ko akasin hka, had'a fuskar shi da ta ta xai yi
yaga hawaye a fuskar ta a rikice yace "baby nah bakya so na rabu da ke? " shiru tayi bata ce
komae ba ganin hka yasa shi cikata tare mik'e tsaye cikin sanyin jiki ya juya xai fita daga d'akin
ganin hka yasa ta tashi da gudu ta karasa inda yake ta rungume shi ta baya tare da fashe wa
da kuka runtse idon shi baya son kukan ta ko Kad'an a hankali ya juya tare da rik'e mata
kafad'un ta yace
"calm down nauwara what wrong with u? "
Kasa magana tayi don kuka yaci k'arfin ta hankalin shi gaba d'aya ya tashi xauna wa yayi kan
sofa tare da xaunar da ita kan kafafun shi nan ya fara rarrashin ta har ya samu tayi shiru sai
ajiyar xuciya da take saki akai akai duk fuskar ta tayi ja idanun ta sun kumbura ita kanta
batasan dalilin kukan nata ba ganin tayi shiru yasa shi cewa
"what happened to u nauwara, me yasa ki kuka haka? "
"ni kawai haka naji kukan yaxo min "
"ohhh my god nasan Akwai wani abun fad'a min kinji my dear "

Cikin sanyin murya tace "da gaske nake yi fah"
D'an xaro ido yayi Kad'an ya kama kumatun ta duk biyun yace "shine kika d'aga min hankali,
are you sure babu wani abin ?"

Jijjiga kai tayi ba tai magana ba d'an siririn murmishi ya saki tare da cewa "thank u once again i
luv u baby nah Allah yayi miki albarka "

A hankali ta bud'e d'an k'aramin bakin ta tace "Ameeen "
Bata peck yayi a kumatu da goshi sannan kan lips d'in ta sannan ya bar d'akin, xuciyar shi
wasai cike da farin ciki sai faman murmishi yake bai damu da tattare war da shaddar jikin shi
yayi ba sai dariya ake mishi wasu na tsokanar shi sai dai ya shafa gashin kanshi tare da
Murmishi ko uhm bai ce ba har ya fice daga part d'in umma ya nufi nashi.
Ita kuwa nauwara kwanciya tayi akan sofa tare da rungume pillow a kirjin ta wani sabon son
abduljabbar ne yake dad'a shiga xuciyar ta yanxu wasai take jin xuciyar ta.

Da yammaci aka gabatar da Mother's Day bayan sallahr mangariba kuma aka mik'a kowacce
gidan mijin ta banda nauwara daga FA'iza sai jiddah sun sha kuka sosai tsakanin FA'iza da
nauwara xasu yi kewar junan su don ba k'aramin shakuwa suka yi ba hka twins sun sha kuka su
ma,
Dakyar fa'iza ta cika nauwara suka tafi gida jikin nauwara a sanyaye, suna k'arasa wa gida
wanka ta iya yi tabi lafiyar gado don ba k'aramin gajiya tayi ba nan da nan bacci yayi awon gaba
da.......

Aishat A muh'd
[25/07, 09:59] Aishat A. Muhd: 🍀🍀☘☘🍀🍀
*K'ARSHEN WAHALA*
🍀🍀☘☘🍀🍀




*written by*
Aishat A muh'd


_dedicated to khalfana (sister d'in neena cool), muna godiya sosae Allah ya bar xumunci, ina
miki fatan alkhairi_��



*~Pg 95~*




Tana xaune a dinning area tana breakfast duk yau tashi tayi jikin ta a sanyaye saboda yau
ammin ta da inna, aunty safiyya xasu koma kaduna jin tayi an rufe mata idanun ta k'amshin
turaren shi kad'ai taji ta gane ko wane cikin mak'e murya yace
"canki wane?"
tana murmishi tace
"Haba kasan na gane ka kawai ka bud'e min ido "
Ta K'arasa fad'i tana Murgud'a baki kallon ta yayi cike da k'aunar ta ya bud'e mata idon tare da
janyo kujera ya xauna a kusa da ita yana kallon ta ita ma shi take kallo sun sauke en mintuna
suna kallon junan Kafin nauwara ta fara janye idonta tana cewa
"dafatan ka tashi lafia? "
D'an ta6e baki yayi tare da cewa "ehhh to lafia ba lafia ba? "

D'an xaro ido tayi cike da mamaki tace "Idan ba lafia ka tashi ba to yana ganka qlau da kai??"

"Idan kin ga gangar jikina lafia to nan "
Ya dafe xuciyar shi ya cigaba da cewa "ba lafia yake ba yana cike da son ki da kaunar ki ta
Kasa samun nutsuwa Har sai ta ji d'umin mahad'ar ta "
Ya gama fad'a yana kashe mata ido hararar shi tayi shi kuwa ya wani marairaice fuska sosai ya

bata dariya ganin yanda ya wani langa6e kai kamar k'aramin yaro ganin har yanxu ta kasa sakin
jiki dashi ba kamar da ba kuma yasan sai a hankali gashi kuma cike da wata iriyar sha'awar ta
yake d'aure wa kawai yake yi, don baya son ya matsa mata yafi son ya gama goge laifin shi
gaba d'aya a gurin ta .
"na had'a maka tea ne? ", girgixa kai yayi cikin kalar tausayi yace " Idan da ni kike to a koshe
nake, umma ta aiko min da shi yanxu ma da kika ganni abuja xan tafi ana nema na"

Cikin d'an mamaki tace "daga xuwan xaka koma?"

"toh ya xanyi tunda yanayin aikin namu kenan, da dai ni d'an gata ne da sai ki shirya mu tafi
tare"
Da sauri ta girgixa kai tana cewa "a'a ni ina kusa da umma "
D'an murmishi yayi yana shafa sajen shi yace "ba wani nan kema nasan kina son ki ganki kusa
da mijin ki kawai irin kawaicin nan ne irin na mata ko ba hka ba? "
Ya tambaye ta yana d'aga gira haushi ya rufe nauwara don ta gane abin da yake nufi hararar
shi tayi tare da mik'e wa da sauri ta bar wurin bin ta yayi da kallo Kafin ya dunkule hannun shi
ya daki table d'in yana cewa

"ohhh my god na kwafsa ashe Hka na saki baki ina magana gashi nan garin gyaran gira........ "
Da sauri ya mik'e tsaye ganin sauran 30 mint jirgin da xai bi xuwa abuja ya tashi don hka
Agurguje yayi sallama da en gidan ya tafi ko gimbiyar tashi bai samu ganin ta ba.


Sai wurin 12 su ammi suka tafi umma sai godiya take musu ita kawai hka taji tana bala'in son
ammi nan aka rabu cike da kewar juna.



Tun da ya tafi abuja kullum abduljabbar cikin waya yake yiwa nauwara ban da text mssg di'n shi
na ta taimaka ta yi picking d'in wayar shi dakyar da yarda take d'aukan wayar tashi tun tana k'in
yin magana har yakai da ta saki jiki suna d'an ta6a hira hkan ba k'aramin jin dad'i yayi ba,
na'eem da ameer ma sai dad'a girma ake suna ta xuwa skul d'in islamia da boko ga nauwara da
saleem suna yi musu lesson a gida baki ya dad'a bud'e yanxu ai ta xuba surutu ga wayo.


Saleem ma yanxu kok'arin had'a degree di'n shi yake an fara xama babban mutum ba ruwan shi
akwai nutsuwa da hankali, bai fiye fita irin yawo nan ba daga makarantar boko sai islamia don
ya dage da neman ilimi addini sosai, idan ya dawo xaka same shi yana yiwa twins lesson ko ki
ganshi a kitchen ya xage yana taya umma ko nauwara girki suyi tayi mishi dariya amman shi ko
ajikin shi kawai girki yana burge shi, kullum nauwara gode wa Allah take da yayi musu wannan
gatan na dace da en rik'o na gari, gashi saleem kamar su d'aya da abban su har dariyar shi da
murmishi shi yasa take yawan kallon shi kallon shi da take yana tuna mata da abban su wani

lokacin har tambayar ta yake lafia irin wannan kallon sai dai kawai ta girgixa kai tare da yin
murmishin yak'e tace ba komai.


Sai da abduljabbar yayi wajen 4 weeks bai xo kano ba sai da waya saboda tarin ayyukan da ke
gaban shi gashi gaba d'aya a tak'ure yake d'aure wa kawai yake ana hka ya d'an samu sararin
aikin yana shirye shiryen tahowa, wani aiki ya ttaso mishi dole ya hak'ura da xuwan ya tafi duk
haushin aikin ya ishe shi kamar xai yi kuka a lokacin hka yaji aikin da ya d'auke shi wajen 1
month again.


Da sauri ta fito daga toilet jin k'arar wayar ta tana d'aure da towel ajikin ta ganin abduljabbar ne
me kira yasa ta d'auka tare da yin sallama amsa wa yayi duk suka yi shiru lokaci d'aya Kafin
daga can abduljabbar yace

"habibty nah nayi missing di'n ki sosai don hka ki shirya tar6ar mijin ki ranar Friday nan da
k'wana 2 kenan "

Ji tayi gaban ya fad'i jin irin muryar da yayi amfani da ita wajen maganar tayi shiru don ta rasa
mai xata ce

"ya kika yi shiru ko baki farinciki da xuwan nawa ba "
"hmm ni na isa nace haka, Allah ya dawo da kai lafia "
"Ameeen habibty, ina twins d'ina? "
"suna parlour wajen umma "
"Yayi kyau, ina son don Allah ki je part d'ina da kanki nake son ki gyara min please "
Shiru ta d'an yi Kafin tace "okay ba matsala xan yi yanda kace "
"that's my girl, ngde sosae Allah yayi miki albarka "
"Ameeen "

Daga hka suka yi sallama ta ajiye wayar tana tunanin abin da ya kamata tayi mishi wanda xai ji
dad'i nan ta xurfafa a tunani...........



Aishat A muh'd
[25/07, 09:59] Aishat A. Muhd: 🍀🍀☘☘🍀🍀
*K'ARSHEN WAHALA*
🍀🍀☘☘🍀🍀

*written by*
Aishat A muh'd





*~Pg 96~*





Ranar Friday tun da ta tashi daga bacci bayan ta gama breakfast, ta nufi part d'in Yah
abduljabbar ta fara gyara mishi tun daga toilet, bedroom nd parlour ta tsabta ce su kayan
wankin shi ta tattara ta bawa mai yin wanki har wardrobe d'in ta gyara, Ohh ji don Allah yanda
ya tattaro kaya kamar wanda xai xauna a gidan kamar bashi da gida nauwara ta fad'i tana ta6e
bakin ta, ta canja mishi bed sheet, bayan ta gama gyaran ta turare ko'ina da turaren wuta ta
k'ara da air freshener masu k'amshi ta fesa a d'akin ta saki labulen ta kunna AC sansanyan
k'amshi da sanyi mai ratsa jiki ne yake tashi kawai tana gama wa ta fito ta nufi 6angaren umma
a gajiye take sosai ta xube akan carpet kusa da kafar umma tana cewa
"washhh Allah na gaji da yawa umma"
Kallon ta umma tayi tana cewa
"sannu, ban da rigimar abdul ba sai asa er aiki ta gyara ba gashi nan ya gajiyar da ke "
Tana lumshe idon ta tace
"Laaa umma ba komai Bari naje na shirya mishi abinci "

Kama baki umma tayi tana cewa "rabu dashi ya ci abin da muka girka, ki je ki kwanta ki huta "

D'an marairaice wa tayi cikin er shagwa6a tace "umma xan iya fah"
"toh

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
google.com, pub-9213700357025247, DIRECT, f08c47fec0942fa0