Showing 69001 words to 72000 words out of 73884 words
kuwa tana murmishi yana murxa
mata hannu yace "da gaske nake wlh baby na gaji da xirga xirgan nan "
"baxa mu barwa umma twins ba? "
"tabbb Allah baxan iya ba da yara na xan tafi "
"kai dear "
"yes! Baby nah baki san yanda nake son yara ba, har na matsu kin dad'a samun ciki kin haifa
min wasu twins d'in dukka mata, na'eem da ameer sun girma fah ya kamata su samu kanne ina
nan ina addu'a jiki na yana bani kin kusa samu ko ma har kin harbu Insha Allah "
Kwa6e fuska tayi tare da yin kalar tausayi da fuskar tace "kai dear twins fah kace tabbb ba
kasan xafin haihuwa bane da wahala fa wayyo Allah nah"
Dariya ta bashi ganin yanda tayi yana dariyar yace "ba wani wahala fah abin da tare ma xamu
haihun ina miki nakudar Kina haihuwar ae kada ki damu "
"Hmmm " abin da nauwara tayi kenan ,kallon ta yayi yana cewa
"komai na gidan ki an xuba bari ma Ki gani ko yayi miki"
Wayar shi ya d'auko ya fara nuna mata irin yanda aka canja gidan kamar bashi ba yayi matuk'ar
yin kyau gashi kaloli masu kyau aka shirya gidan dasu "Wow masha Allah gaskiya dear yayi
kyau sosai Allah ya k'ara bud'i ya kare min kai daga sharrin masu sharri nagode "
"Ameeen habibty na ki bar godiyar nan kin fi k'arfin komai a waje na"
Peck ta bashi a kumatu sannan ya ce "baby nah i luv u "
"i luv u too my dear "
cikin marairaice murya ta kwantar da kanta a saman kafad'ar shi tace "my dear anjima xamu fita
shan ice cream please "
Bakin ta ya rik'o da hannun shi yace "wannan bakin ya fiye kwadayi da yawa "
"xamu je don Allah "
Yana murmishi yace "don't worry baby nah xamu je, amman yanxu a dan rage min xafi Kafin
anjima Kinsan nayi missing di'n ki sosai "
Ya K'arasa fad'i yana kashe mata ido d'aya rungume shi tayi a jikin ta tana Godiya ga Allah da
ya mallaka mata wannan gwarxon mijin nata tana fatan mutuwa ce xata raba su.
Ae kuwa da yammacin ranar suka shirya don tafiya nauwara tana sanye da blue gown mai
touch d'in white ajikin rigar tayi rolling d'in kanta da white veil shi kuwa abduljabbar black trouser
nd T-shirt blue sunyi matuk'ar yin kyau ko twins basu tafi dasu ba don suna islamia, ko umma ta
yaba da wannan k'walliyar tasu, sun birge mutane da dama sai kallon su ake kishi ya ishi
nauwara ganin yanda emmata suke kallon abduljabbar ba don ta gaji ba tasa shi da mitar su
dawo gida kallon ta yayi yana murmishi yace "Haba baby nah baxa ki bar ni na lalubo d'aya ba
sai ki samu k'anwa koh yah "
Ya fad'i yana d'aga mata gira harara ta 6alla mishi tare da had'e rai kiris take jira ta fashe mishi
da kuka nan kuma ya dawo rarrashin ta don baxai jure fushin habibty di'n shi ba, Sun sha selfie
sannan suka yiwa su twins da su umma siyayyan kayan ciye ciye tukunna suka dawo gida
xuciyar su cike da farin ciki.
Duk wasu abubuwan da xasu buk'ata umma ta tanadar wa nauwara sun had'a kayan su sai
jiran ranar tafiya dakyar ya barta taje gidan jiddah, fa'iza da aunty kausar tayi musu sallama
ranar sunday misalin karfe 2:30 jirgin su nauwara ya d'aga xuwa abuja sun bar umma da abba,
aunty sadiya saleem da kewar su.
Alhmdllh sun sauka a abuja lafia Joseph driven Yah abduljabbar ne yaxo ya dauke su a airport
xuwa gida, Wow duk irin Kyan da nauwara ta gani a wayar abduljabbar na gidan sai yanxu taga
ni axahiri yafi mata kyau,sai da ya xagaya dasu ko'ina na gidan, d'akin su twins ma ya had'u iya
had'u wa sannan kuma abduljabbar da nauwara suka tafi bedrooms di'n su don yin wanka yayin
da er aikin da umma ta had'a mata da ita ta kwashe su twins don tayi musu wanka su ma.
Bayan sun kammala suka dawo falo duk sun sha english wears marasa nauyi na shan iska
akan dinning table suka xauna suka ci take away di'n da joseph yaje yayi musu bayan sun ci
sun sha suka dawo parlour suka xube suna hutawa da er hira.
Acikin satin abduljabbar ya sama wa su na'eem da ameer wata tsadaddiyar makaranta mai
kyau sosai ba 6ata lokaci suka fara xuwa skul d'in har da islamia Mai kyau ya samar musu da
sabuwar motar da xa'a dunga kai su makarantar da driven su a gida kuwa nauwara ta cigaba da
d'ora musu lesson rayuwa suke mai dad'i.
A Kano kuwa bayan Sati d'aya da d'aura auren abba da ammi, ammi ta tare a gidan abba xama
suke mai dad'i da fahimtar juna sun had'e kawunan su suna kyautata wa abba Idan ka shigo
gidan baxa ka ta6a gane kishiyoyi ba ne sai an fad'a maka ko ka fahimta ba k'aramin birge
mutane suke ba don Kafin a samu mata masu irin had'in kan nan xa'a dad'e a wannan xamanin
da muke ciki dai don son kai yayi yawa a xuciyar al'umma.
Aishat A muh'd
[25/07, 10:00] Aishat A. Muhd: í ¼í½€í ¼í½€â˜˜â˜˜í ¼í½€í ¼í½€
*K'ARSHEN WAHALA*
í ¼í½€í ¼í½€â˜˜â˜˜í ¼í½€í ¼í½€
*written by*
Aishat A muh'd
*~Pg 100~*
Satin su d'aya da dawo wa abuja abduljabbar ya shirya musu tafiya honey moon shi da
nauwara twins wajen aunty asma'u suka ajiye su saboda makaranta, hutun 2 month's ya samu
don hka suka d'aga xuwa k'asar Greece daman k'asa uku xasu Greece, switzerland, sai su biyo
ta Saudi Arabia suyi umarah.
Sun sauka a k'asar Greece k'asa ce mai kyau sosai da mutanen mu na Africa basu saba da
xuwan ta sosai ba a wani babban hotel yayi musu masauki suna hawa na uku, room d'in da
suke ciki katon parlour ne da one bedroom shima babba sai toilet, nan suka xube kan bed suna
huta gajiyar mikakkiyar tafiyar da suka yi.
Bayan sunyi wanka sun ci abinci sannan suka kirawo su umma suna sanar dasu sun sauka
lafia, sun kirawo aunty asma'u ta had'a su da twins suna ta xuba musu surutu kowanne yana
fad'in tsarabar da xa'a yi mishi, sai da suka yi k'wanaki uku suna hutawa basa xuwa ko'ina suna
manne da junan su ana xuba soyayya don abduljabbar yace ta shirya Insha Allah xai sun dawo
da tsarabar honey moon ya kuma dage da addu'a sosai.
A k'wanakin su na hud'u da xuwa k'asar Greece ne da wani yammaci bayan anyi ruwa an
d'auke suka fito abduljabbar yana sanye da white d'in trouser nd T-shirt red colour ya d'ora
jibgegiyar rigar sanyi black saboda yanda garin ya d'auki sanyi sosai, yayin da nauwara ta
sanya dogon wando maroon colour nd T-shirt black sai ta d'ora coat irin wanda mata suke
sanya wa har xuwa gwiwar ta tayi rolling d'in kanta da maroon veil tayi kyau sosai suna rik'e da
hannun junan su suna tafiya.
Sunyi yawo sosai a k'asar Greece di'n nauwara k'asar ta birge ta a sati ukun da xasu yi sun sha
yawo duk wani gurin shak'atawa da manya manyan malls na k'asar sun xiyar ci wajen da hka
suka yi bankwana da k'asar Greece suka yo switzerland nauwara tana santin k'asar don ta
matuk'ar yi mata kyau.
Bayan sun sauka a k'asar switzerland ne da sati biyun nauwara ta fara jin canjin yanayi a tattare
da ita yawan bacci da rashin appitate a baki sai kuma tashin xuciya kamar yau ta gama shirin ta
xasu fita da abduljabbar tana jiran shi ya fito daga wanka irin ta xauna jiran nan shi sai bacci
yayi awon gaba da ita a hka ya fito daga toilet d'in ya tsaya kallon ta cike da mamaki wannan
baccin na nauwara yana d'aure mishi kai sosai mybe fitar da kuke shi yake gajiyar da ita Cewar
wata xuciyar tashi gaban dressing mirror ya K'arasa ya gyara jikin shi ya K'arasa inda take tana
bacci a hankali yake tashin ta bud'e idon tayi yana kallon ta yace
"baby nah ko mun fasa fitar ne, ni wannan baccin naki na lafia ne anya babu ajiya ta Anan????
"
Yatsine fuska tayi ta bud'e baki xatayi magana wani amai ya taso mata da gudu ta nufi toilet ta
dunga k'wara shi sai da ta amayar da duk abin da taci, yana rik'e da ita kamar xai fashe da kuka
haka yake ji don ba k'aramin tausayi ta bashi ba ganin yanda take wahala kamar ba soja ba
bayan ta gama ya sake mata wanka sannan suka fito xuwa daga toilet d'in ya sa mata kaya
tukunna yace
"taso mu tafi hospital ni nagaji da wannan yanayin da kike ciki baxan iya jure ganin Kina ciwo
ba"
Cikin shagwa6a tace "ni gaskia a'a xan samu sauk'i bana son ayi min allura "
Kamo ta yayi tare da mik'ar da ita tsaye yace "baxai yiwu ba dole ne muje a duba min ke don
nasan me yake damun ki "
Ba don taso ba ta bishi suka je wani hospital sun samu nasarar ganin wani Doctor mai jan
kunne yayi mata en tambayoyi sannan aka yi mata urine test Inda suka hango d'an k'aramin ciki
a manne a jikin ta lokacin da suka sanar da abduljabbar nan take ya tsugunna tare da yin
sujjadar godiya ga Allah yana tashi daga sujjadar don tsanani murna ya rungume doctor d'in
Kafin ya jiyo kan na ya d'auke ta cak sai juyi yake da ita a office d'in Dr di'n ya bisu da kallo
alamar sun burge shi sosai daman en 9ja sun iya soyayya da kula da matan su kamar yanda ya
gani a Wajen abduljabbar, Cewar Dr a xuciyar shi bai san maganar ta fito fili ba har naji ina da
gefe na ce lallai doctor nan an gaya maka en 9ja basu da wannan wayewar nan me ka dau ke
su ne í ½í¸�, muma ae mun iya kawai dai don malam bahaushe akwai shi da son girma baya son
rai ni shi yasa ba kowanne yake yi ba..... lol
Jin abin da na fad'a yasa doctor ya sunkuyar da kae yana sosa k'eya alamar yaji kunya bai san
xan ji ba lol.
Bayan ya gama juyin da ita a office d'in doctor ya dire ta sannan a lokacin Dr yayi wa
abduljabbar bayanin yanda xasu kula da cikin Sannan ya rubuta mata magungunan da xata sha
wanda xai taimaka mata sosai wajen Inganta lafiar ta da ta jaririn cikin.
Da hka suka yi sallama da doctor suka fito xuciyoyin su cike da tarin farinciki more especially
abduljabbar da hka suka tari taxi har xuwa masaukin su.
Nauwara ta ga gata sosai a wajen abduljabbar wanda Idan yana wani abin har mamaki yake
bata kamar bashi da wasu yaran, shi haka Allah yayi shi akwai son yara sosai, nan da nan
nauwara ta dad'a wani irin haske kyanta ya k'ara fito wa sai dai ta d'an rame saboda laulayi yau
lafia gobe sai a hankali, satin ukun da suka yi niyyar yi sai da suka k'ara Sati d'aya sannan suka
wuce Saudi Arabia nan ma Sati ukun suka yi sannan suka yo gida nigeria, sun sauka lafia
aunty asma'u ce da su twins sai yaranta sune suka xo taryar su cikin tsananin farinciki na'eem
da ameer suka rungume iyayen nasu suna murnar ganin su don sunyi matuk'ar kewar su, kallo
d'aya aunty asma'u tayi wa nauwara ta fahimci ciki ne da ita don hka cikin murmishin tsokana ta
cewa abduljabbar
"kai daga xuwa honey moon sai ku dawo da tsaraba"
Cikin murmishi yace "alamar tafiya tayi kyau sosai "
Yana fad'in hka ya shige mota kunya ta rufe nauwara kamar ta nutse a k'asa aunty asma'u
kuwa dariya tayi tana cewa "Allah ya shirya ka abdul "
Da haka suna er hirar su suka K'arasa gidan nasu sai yamma likis aunty asma'u ta koma gidan
ta ta bar mata babbar 'yarta hanan Ko xata taimaka mata hakan kuwa ba k'aramin dad'i yayi wa
nauwara ba don jinin su ya had'u da hanan yarinyar akwai hankali da kamun kai.
Sai da suka yi wajen wata biyu da dawo wa sannan abduljabbar ya samu d'an short break na
tsayin 1week kacal suka tattara suka yo kano don tuntuni nauwara taso xuwa but ya hana ta
sam yace tare xasu xo don baxai iya missing di'n ta ba na tsawon wasu k'wanaki, lokacin cikin
jikin ta har ya dan fito ana ganin shi.
Sun sauka a Kano lafia umma,abba, aunty sadiya da ammi ba k'aramin jin dad'in ganin su suka
yi ba gashi sun hango Sun kusa samu wasu jikokin nan fa suka frasa inda xasu sa su don dad'i,
abin da yayi matuk'ar d'aure kan nauwara shine ganin wai ammin ta da ciki gashi nan ya fito
ana ganin shi lallai wani baya haifar d'an wani rayuwa kenan Allah yasa mu dace da
kyakkyawan rabo.
Washe gari fa'iza ,jiddah aunty kausar taxo gidan gaba d'aya kamar had'in baki sun sha murnar
ganin junan su fa'iza ma tana d'auke da cikin ita ma jiddah Allah maji rokan bawan shi gashi nan
ita ma da nata cikin kuma yanxu hindatu tayi nadama tun lokacin da aminu Yayi mata saki d'aya
da tayi niyyar k'ona jiddah da tafassheshen ruwan xafi Allah bai bata nasara ba aminu ya ganta
ya kar6e to shine yayi mata saki d'aya, dakyar ya dawo da ita don darajar yaran dake tsakanin
su, yanxu tayi nadama sosae xaman lafia suke da jiddah ae duk tsanani yana tare da sauk'i
komai wuya sai dad'i kuma *Innallaha ma'assabirin* littafin miss zahra mansur.
Yini guda suna shan hira nauwara kowanne ta bashi tsarabar shi sun yi mata godia sai yamma
tukunna kowacce mijin ta yaxo ya dauke ta.
Satin su d'aya a Kano sun xagaya gidajen en uwa har kaduna nauwara taje k'wanan ta d'aya ta
dawo kano, ranar sunday suka shige abuja saboda makarantar su na'eem da ameer, yanxu
saleem ya had'a degree di'n shi akan harkar kasuwanci bai nemi aiki ba Abba ya wulla shi
company nin su nauwara dake abuja don ya dunga kula shi ya had'a shi da kwararrun ma'aikata
masu tsoron Allah da amana a xuciyoyin su nan da nan company nin ya fara samun cigaba
yanxu saleem ganin shi sai week end a Kano sauran k'wanaki biyar di'n a kaduna tun an fara
xama babban mutum yanxu aure ya rage mishi don duk wani jin dad'i ya same shi, ammi kullum
cikin addu'a take ma yaranta dasu umma da abba da suka rik'e su tsakani da Allah....
Aishat A muh'd
[25/07, 10:00] Aishat A. Muhd: í ¼í½€í ¼í½€â˜˜â˜˜í ¼í½€í ¼í½€
*K'ARSHEN WAHALA*
í ¼í½€í ¼í½€â˜˜â˜˜í ¼í½€í ¼í½€
*written by*
Aishat A muh'd
*K'ARSHE* (last page)
Cikin nauwara ya shiga wata na shida yayi girma sosae kamar nasu twins abduljabbar ba
k'aramin tausaya mata yake ba kullum ya dawo daga aiki baya fita xai xauna kusa da ita yana
lalla6a ta tare da bata labarai masu dad'i da ban dariya ita kuma tana nannad'e a jikin shi tana
dariya haka na'eem da ameer xasu xo su kewaye su ana yi dasu kulawa sosai yake bata .
Kamar yau tana xaune a falon down stairs tana sanye da simple gown don tafi mata dad'in
sawa gaban ta fruit salad ne abduljabbar yana gefen ta yana bata a baki aka kirawo shi a waya
da sauri nauwara ta mik'a mishi wayar da yake tana hannun ta ganin sunan abba ne d'aga wa
yayi da sallama bayan ya gaida abba ne yake sanar dashi ammi ta haihu an sami baby boy tuni
fuskar abduljabbar ta fad'ad'a da fara'a sosai Alhmdullilah ya furta bayan ya ajiye wayar
nauwara wadda ta xuba mishi ido tace
"waya haihu ne?"
"ammi ce ta haihu yanxu an samu baby boy "
Cikin wani irin sauri ta mik'e tsaye tana cewa wanda har sai da marar ta ta d'an murd'a kan a
hankali ta dafe wajen tare da furta washh amman bata bi ta kanta ba tare da cewa
"da gaske kake don Allah "
Kamo ta yayi ya xaunar da ita kan kafafun shi ya d'an d'aure fuska yace "ban hana Ki tashi da
sauri haka ba sai kin jiwa kanki ciwo? "
Langa6e kai tayi tare da fad'in "sorry " d'an murmishi yayi Kafin yace "da gaske nake miki ammi
ta haihu na samu small bro ni ma "
Cikin tsananin murna ta rungume shi tare da cewa "Masha Allah Alhmdllh Yeeeeeee xan je
kano "
D'an hararar ta yayi yana cewa "da haka xaki Kano da wannan katon cikin ke da xuwa kano sai
kin haihu yarinya "
Kwa6e fuska tayi ta fara kukan shagwa6a ita fah sai taje har da shure shuren kafa irin na yara
Idan xasu yi kuka tuni hankalin shi ya tashi don baya k'aunar ganin nauwaran shi a haka nan ya
dawo lalla6a ta tare da yarda xasu je sai lokacin ta dai na kukan daman ae na k'ak'ale ne ko
hawayen kirki babu sai murxar ido girgixa kai yayi yana murmishi kawai ya d'an ja kumatun ta
yana cewa
"habibty rigima don kin ga bana jurar ganin ki Kina cikin damuwa shi yasa kike yanda kike so"
D'an hararar shi tayi da sauri ya dafe baki yana cewa "su6utar baki ne sorry "
Gaba d'aya suka kwashe da dariya sai jin maganar twins suka yi suna cewa "papa mamee
dariyar