Showing 72001 words to 73884 words out of 73884 words
me kuke? "
Abduljabbar da nauwara suka Kalli juna tare da yin murmishi nauwara tace " ammi ce ta haihu
an samu boy" nan suka fara tsallen murna suna dariya.
Bayan k'wana 2 da haihuwar suka tarkato xuwa kano har da aunty asma'u da yaranta nan fah
gida ya cika da 'ya'ya da jikoki don su fa'iza, aunty kausar, jiddah, aunty safiyya dasu inna da
baffah da saleem kamar had'in baki duk rana d'aya suka xo gida ya cika umma da aunty sadiya
sun kasa xama waje d'aya sai anan ake dasu, barin ma nauwara motsi Kad'an sai ta tambayi
nauwara me take so kula wa sosai take bata, babyn ammi yaci sunan abban su nauwara wato
sa'eed don yace ameer mai sunan abban su nauwara daban shi ma nashi sa'eed d'in daban.
Ranar suna jaririn yaci sunan sa'eed suna ce mishi arfat, bayan suna da k'wana 2 su nauwara
suka koma abuja, haka lokaci ya cigaba da tafiya cikin nauwara yana wata 8 fa'iza ta haihu d'a
namiji tana haihuwa da k'wana 3 jiddah ma Allah ya sauke ta lafia ta samu diya mace murna
Wajen jiddah ba'a magana har da kukan ta na farinciki ta gode wa Allah da ya bata haihuwa
daman ashe haka yara suke da dad'i wayyo Allah daman ana dawo da rayuwa baya da ta goge
abubuwan da ta aikata a cikin rayuwar ta amman ina ya riga da ya wuce sai addu'ar Allah ya
gafarta mana kura kuran mu Ameeen
Anyi suna d'an fa'iza yaci sunan daddyn Dr muh'd Wato Abdullah suna kiran shi da daddy
sannan er jiddah kuwa Mufeedah suka sanya mata.
K'ememe abduljabbar barin nauwara xuwa suna ita ma bata sa ran xuwan ba saboda yanda
cikin ta ya girma sosai ko taje baxa ta sake ba, yanxu nauwara kad'ai ake xuba idon haihuwar ta
iyaye da en uwa sai addu'ar sauka lafia suke mata, abduljabbar kuwa tun da cikin haihuwar
nauwara ya tsaya tsayuwar dare yake sosai da addu'ar Allah ya sauke ta lafia duk gaba d'aya
baya cikin nutsuwar shi saboda tsananin tausayin ta ganin yanda take fama da ciki duk ta
kumbura musamman kafafuwan ta.
Tuni saleem sun dinke da Hanan babbar er aunty asma'u suna xuba soyayya kuma kowa yasan
da haka a cikin en uwa kuma Anyi farin ciki sosae baran ma nauwara da yake yanxu ta dawo
wajen ta da xama tana d'an taya ta ayyukan da er aiki baxa ta yi mata.
Ranar Thursday da safe nauwara ta tashi da nakuda ganin yanda ta ke wahala gaba d'aya
Abduljabbar ya gigice ya kid'ime ya ma kasa yin komai sai sannu kawai yake xuba mata, sai da
Hanan ta kirawo aunty asma'u nan da nan taxo gidan tana fad'an me yasa bai kaita asibiti, shi
sai lokacin ma ya tuna da wani asibiti don duk ya gigice kamar ba soja ba baya jurar ganin
habibty di'n shi cikin wahala ne, cikin kankanin lokaci suka isa asibitin aka kaita room d'in
haihuwa K'ememe abduljabbar yak'i fita daga d'akin yana rik'e da nauwara yana xuba mata
sannu awan su 3 acikin asibitin Kafin nauwara ta haihu tarihi ya mai mai ta kanshi don 'ya'ya
biyu reras ta sake haihuwa sai dai duk mata ne kyawawa masu kama da nauwara.
Nan fah murna ta ishe abduljabbar ya rasa inda xai sa kanshi don tsananin farinciki haihuwa 2
amman 'ya'ya hud'u lallai Allah ba k'aramin kyauta yayi mishi ba da ya axurta da nauwara, sai
da ya tabbatar nauwara ta dawo dai dai har tayi wanka ta samu baccin hutu tukunna ya kar6o
yaran shi daga hannun aunty asma'u har tana mishi tsiya shi dai kawai murmishi yake, nan aka
fara kiran en uwa da abokanan arxiki ana sanar dasu nauwara ta haihu ta samu twins duk mata.
Sai dare aka sallame su daga asibitin bayan an tabbatar ba wata matsalar suka dawo gida nan
fa na'eem da ameer suka dunga tsallen murna sun samu kanne, washe gari umma da aunty
sadiya suka xo ganin yara k'wanan su 2 suka juya xuwa kano, shirye shiryen suna sosai Aunty
asma'u take shirya ita dasu fa'iza ana sauran k'wana 2 suna su fa'iza, aunty kausar, jiddah da
aunty maryam da aunty safiyya suka taho abuja saboda shirin suna.
Kaya sosai abduljabbar ya had'a wa nauwara da twins na'eem da ameer sannan twins d'in shi
mata, nauwara har da kyautar dankareriyar mota da yayi mata tare da wata sark'ar goal mai
tsananin tsada ba k'aramin kashe kud'i yayi ba har nauwara tana mishi maganar kashe kud'in
Yayi yawa yace mata ta barshi yayi komai yana da lokaci kuma sun fi k'arfin komai a wajen shi
rungume shi nauwara tayi tana jin dad'in yanda Allah ya bata miji nagari.
Kaiii twins fa sunyi goshi kaya ta ko'ina nauwara take samu umma, Abba, ammi, aunty sadiya,
aunty asma'u, aunty kausar, aunty maryam, aunty safiyya, inna, baffah, saleem, fa'iza, jiddah
dukkan su kowanne da nashi abin arxikin nauwara har ta rasa bakin godiya har da aiken Dr
muh'd da aminu kaya masu tsada sosai wai a sawa twins. Abdulkareem ma kyautar ta daban ya aikowa da twins har da sark'ar goal guda biyu masu
tsada, ya taya abokin shi murnar samun twins.
Ranar suna twins sun ci sunan umma fatyma d'ayar kuwa taci sunan safah sai suke kiran
wanda taci sunan umma marwa kenan safah da marwah sai fatan Allah ya raya su cikin addinin
islama,walimah su aunty asma'u suka shirya anci ansha an watse.
Bayan suna da k'wana 2 kowa ya watse aka bar nauwara da abduljabbar sai en yaran su a gida
suna cigaba da kula wa dasu cikin tsananin farinciki da k'aunar yaran nasu.
Bayan sunyi arba'in suka yo kano suka yi sati d'aya sannan taje kaduna tayi wa su inna
k'wanaki uku acan sannan suka koma abuja, a dai dai lokacin aka yanke bikin saleem da Hanan
wata biyu masu xuwa don Abba yace baxai shige wannan axumin ba bai yi mishi aure ba.
Komai nisan lokaci aka sa xai xo har ya shige dashi nan har bikin saleem yaxo duk wasu shirye
shirye an gama sun tarkato kano gaba d'aya don a gabatar da bikin da yake kuma mijin aunty
asma'u shi iyayen shi en kano ne don hka komai yaxo da sauk'i an kammala biki lafia amarya
Hanan ta tare a gidan ta da yake kaduna, daga hka kowa ya tarwatse ya nufi nashi gidan.
*BAYAN SHEKARU 6*
Ganin wasu kyawawan yara nayi su hud'u maxa biyu mata biyu suna xaune a parlour kallon
mbc 3 suke ana cartoon di'n toy Story duk sun nutsu suna kallon saboda yanxu suka gama
fad'an su na yara nauwara tayi niyyar dukan su abduljabbar ya hana ta don hka ta xuciya a
fusace ta bar falon to shine abduljabbar ya kunna musu cartoon suna kallo ya tafi rarrashin
habibty di'n tashi.
Dakyar ya shawo kanta suka fito parlour suna ganin ta suka mik'e tsaye tare da durkusa wa
agaban ta cikin had'in baki tare da rik'e kunnayen su suka ce
" I'm so sorry mamee baxa mu k'ara ba mun dai na rashin ji "
D'an hararar su tayi nan suka k'ara shagwa6e fuska tare da cewa "please mameen mu "
Tsugunna wa tayi tare da bud'e hannuwan ta da gudu suka k'araso cikin jikin ta tayi hugging di'n
su tare da basu peck a kumatun su tana shafa gashin kan su d'ago kanta tayi ta kalli
abduljabbar da ya langa6e kai yana wani marairaice fuska yace " sauran ni habibty "
Hararar wasa tayi mishi ae kuwa ba kunyar ganin yaran shi yaje ya rungume ta ta baya shi ma
nan fah su safah da marwah suka fara yi mishi dariya yayin da na'eem da ameer suka tsokanar
papa di'n su ganin yanda ya nannad'e a jikin nauwara kamar shi ne yaron.
Xaman lafia suke mai dad'in gaske a tsakanin su da yaran su suna basu lokacin sosai rayuwa
kullum cigaba suke samu daman duk *K'ARSHEN WAHALA* dad'i yana nan xuwa.
Bayan sun kammala yin dinner d'in dare wajen 9, safah da marwah suka yi tafi d'akin su don
lokacin baccin su yayi, haka na'eem da ameer ma suka nufi nasu d'akin aka bar nauwara da
abduljabbar a parlour shi ma bai 6ata lokaci ba ya d'auki habibty di'n cak a hannu suka shige
bedroom d'in su suna shiga toilet ya tsomata a bath di'n wanka wanda yake cike da ruwan d'umi
bayan sun yi wanka cikin farinciki da so da k'aunar junan su, bayan sun fito sun shirya cikin
sleeping dress kan bed suka fad'a suna rungume da junan su a kunne nauwara ta rada mishi "i
really luv u yayanah!"
Yana kok'arin kissing d'in ta yace "i luv yhu too my habibty Allah ya bar mu tare "
"Ameeen " tana gama amsa wa ya rufe bakin shi da nata tare da jan blanket suka fara kok'arin
faranta ran junan su, ganin haka yasa na tarkato na bar musu d'akin don na kyale su haka ni
ma na huta da typing......
_Asubah ta gari_
*ALLAHAMDULLAH*
_dukkan Godiya sun tabbata ga Allah da ya bani rai da lafiyar rubuta musu wannan labarin na
*K'arshen wahala* na fara shi lafia gashi a yau na kammala shi lafia_
*ke ta daban ce wlh a wurina my cwt sadeey saNaz i really luv u bani da bakin godia a gare ki
sai dai ina miki fatan alkhairi a rayuwar ki ya albarkaci rayuwar ki ya cika miki burikan ki na
alkhairi ya xa6a miki miji nagari wanda xai kular mana ke mu xo jigawa musha biki*_í ½í²ƒí ¼í¿»â�¤í ½í¸�
*KUNA RAI NA SISTERS NAH*
Hafsat A aliyu
Mmn abiddeen
My Sumayya salees sadeeq (sumynbash)
My khadijah neena cool
Nafeesat Anka
Asy khaleel
Ummiey xeey
Ummi hambali
Mrs muktar
Mrs Umar
Miss maryam
Aishat aliyu garkuwa
Haleemah Ameen
Biebie deee
Ummu safwan
Sa'adah
Khalfana
S A muh'd
_da sauran wad'anda ban ambata ba ku sani kuna rai na i really luv u guys_â�¤í ½í¸�
*masoyan asali*
Miss zahra mansur
Ummu abdul
deejah
Neena cool
Hadixa gidan d'orawa
Amina (mameen ammar da bilal)
_da sauran da ban ambata ba Aishat tana gaida ku_í ½í¸�
Jinjinar ban girma gare ku
K'arshen wahala fans
Aunty & sadeey novels grp
dandalin hausa novels
Online hausa writers
Hikima writers HWA
Ummu safwan novels
Mrs Umar novels
Hausa novels group
My style grp
Ladies zone
Musan kanmu marubuta
Ruky & ashba
saNaz novella
Novellas lodge
Biebie & samrah
Nagode da k'aunar littafin nan da kuka yi ina yi muku fatan alkhairi en uwa â�¤í ½í¸�
_ku tare ni a littafi na na gaba *YAYI SAKE* amman sai bayan sallah saboda gabatowar wata
mai albarka wato ramadan mu dage da ibada Allah ya nuna mana lokacin lafia Ameeen_
Aishat A muh'd ce